← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 211

Sashe 59

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta ko'ina jami'ai ne uniform kala daban daban ke gadin gidan, rike suke da manya manyan bindigu, sai muzurai suke yi, suna ta kewaye a tsakiyar harabar gidan, yadda suke ɗin nan bana jin ko tsuntsuwa zasu iya bari ta iya giftawa ta tsararin samaniyar tsakar gidan, duk da cewa akwai satellite dake ɗauko rahoton duk wani abin da zai gifta ta sararin samaniyar gabaɗaya arear gidan, komai kankantar abu bai isa ya gifta ta arear ba tare da wannan satellite ɗin ta zakulo shi ta turawa na'urorin dake cikin gida bayanai ba, amma duk da haka waɗan nan jiga jigan turawan jami'an riƙe suke da bindigu suna wani kewaye suna ganin sama da ƙasa, kunsan dai yadda ake jibge jami'ai a gidan shugaban ƙasa, to suma hakan ce.

Daga kilometer biyu da gidan jami'ai ne jibge ta ko'ina, kai daga gani ƙasan ka doso gidan shugaban ƙasa.

Elysee palace ya kasance hawa uku ne kuma duniya guda, mu haura hawa na biyu kai tsaye ba ɓata lokaci.

Wani irin................🥱🌝

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 10/10/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥

E19

Elysee palace ya kasance hawa uku ne kuma duniya guda, mu haura hawa na biyu kai tsaye ba ɓata lokaci.

Wani irin babban parlour ne sosai mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali.
Daga yanayin design ɗin jikin parlourn kaɗai ya isa ya kashe idan mutum, ga wasu manya manya chenese chairs da sukayi matuƙar ƙawata parlourn.

Daga gefen hagu wasu irin set ɗin kujerun Dubai set ne a wajan kalar milk da sukayi matuƙar dacewa da parlourn. Babban main parlourn na ƙasa dai parlours ne four in one, saura na sama kuma parlours ne three three in one. Sofa set kala huɗu aka yi amfani da su, akwai milk color, coffee color, ash color sai white colors. So na parlour hawa na biyu akwai milk color set uku, sai parlors dake gefe cikon three in one ɗin su kuma akwai mai sofa set coffee set biyu, ɗayan kuma white color shi ma set biyu. Hmmmmm gidan nan ba'a magana sam sam.

Komai na cikin ya yi matuƙar dacewa da yanayin tsaruwar parlourn.
Ga wani irin London carfet mai matuƙar laushin a tsakiyar ko wana sets ɗin kujerun parlourn.
Daga gefen hagu wani babban glass ne mai ɗauke da manyan abubuwan masu matuƙar tsada a cikinsa.
Babbar plasma ɗin parlourn sosai yake da girma, ta ko ina sanyin Ac ne yake tashi saboda manya manya Aç da suke cikin parlourn.
Wani irin haske ne yake tashi a cikin saboda yadda manya manyan chandeliers É—in cikin parlourn suka haska ko ina da hasken su.
Daga ɓangaran dama wani irin dining room ne a wajan, mai ɗauke da step huɗu da zai kai ka zuwa inda dinning ɗin yake.
Sosai dinning room ɗin yake da girma, ga kujeru na set ɗin dinning ɗin yayi matuƙar dacewa da yanayin tsaruwar wajan.
Daga saman dinning ɗin wani farar mini chandelier ce a wajan me ɗauke da zagayayyun fitulu ƴan ƙanana, sai mirror ɗin dinning da aka ƙawata shi da wasu manya manyan warmers, a jikinsa a wajan show class me ɗauke da cups da mini plate a ciki, sai wasu irin chocolate da cookies da aka saka ko wannan cikin mahallin da ya dace.
A cikin wajan dinning ɗin akwai mini plasma ita ma mai matuƙar kyau na kallan labarai, sa cuttons ɗin labule white colours ne, ga babbar Acn wajan da take faman hura sanyi ta ko ina a cikin dining room ɗin.

Iya haɗuwa da tsaruwa parlourn yayi sama da tunanin mai tunani. Ta ko wani ɓangare idan mutum ya kalli parlourn sai ya sake ɗagowa ya kallesa.

Akwai elevator a gidan, sannan akwai stair case mai design of fish da yake da matuƙar ɗaukar hankali. Kun dai san duk wani ginin zamani ya ƙare wajen masu jajayen kunnuwar nan, daga wajensu ake ɗaukar designs.

Wasu kyawawan stage ne guda uku a kusa da dining room É—in, wata Æ´ar siririyar corridor ce a wajen.

Tafiya kaÉ—an zaka yi ka shiga wata haÉ—aÉ—É—iyar parlourn na wani part wadda komai na cikinsa milk and white ne, daga gani wannan part É—in zaku san na ganiyar na musamman ne a cikin gidan, daga gani mai wannan part É—in one in million ne, ya ji komai da komai na more rayuwa bawa, komai burinka ba zaka kure part É—in nan ba, kana shigowa cikinta zaka ce baka da sauran buri kuma.

Luxury bed room ne fiye da tunaninku a cikin wannan parlourn, tun daga kan gado zuwa labulaye har zuwa kan chandelier izuwa kan tiles ɗin ɗakin, glass na dressing room and bath pan na toilet, komai da komai white and milk colour ne, komai na cikin room ɗin nan the most effective thing ne, tamkar ba za'a mutu ba, komai ya ji a room ɗin, su kansu furnitures da aka zuba a part ɗin zaka san e lallai wannan part na musamman ɗin na musamman ne, furnitures ne da a wannan part ɗin kawai zaka iya samun irinsu, dan gabaɗaya furnitures ɗin haɗe suke da computers haɗe da na'urori, ko drawers na room ɗin baka isa ka buɗesu ba sai da izinin mai shi, da alama koma waye mai wannan part ɗin mutun ne da ake kauna over, dan tun daga kan matakan tsaron da suke kewaye da wannan part ɗin zaka fahimci e lallai ba ƙaramin kai bane a wajen, ku dubi yadda gidan yake da uban tsaro amma a haka aka gargame wannan part ɗin da uban tsaro har haka. Alkalamina bai isa ya zayyana maku haɗuwar part ɗin nan ba, kawai dai abin da zan ce maku shi ne wannan part ɗin karshe ne wajen haɗuwa.

Wani irin fitinannen kamshi mai kwantar da hankalin mai shaƙa ne yake tashi a gabaɗaya arear part ɗin, kana dosowa wajen zaka ji hankalinka ya kwanta a lokacin da ka shaƙi kamshi, shi yake fara yiwa kowani kofar hanci bawa welcome a duk lokacin da ka doso, kana saka kafarka a ciki kuma wani irin sanyin Ac mai haɗe da kamshin ne zai yi maka welcome. Komai na cikin part ɗin tsabar tsabta tamkar yanzu aka buɗesu a leda, kar kar suke!!.

Kwance yake a saman wani irin haÉ—aÉ—É—en King bed mai bala'in kyau da tsada, shin fiÉ—e yake da zannuwar gado masu bala'in kyau, laushi da kuma tsada, ya lume cikin bargo ya kuma rufe gabaÉ—aya jikinsa gar zuwa wuyarsa da haÉ—aÉ—É—en bargonsa mai bala'in laushi, jikin bargon tamkar jikin mage, idanunsa a rufe da eyes care mai shegen kyau, gashin kansa ta sauko mashi har gaban goshinsa, baka iya ganin face É—insa, saboda gabaÉ—aya room É—in duhu ne, ko light É—in wajen drawers ba'a kunne suke ba bare a je kan sauran bulbs É—in.

Sai dai akwai light mai bada haske É—an kaÉ—an a jikin na'urar dake jikin bed side drawers É—in dake kamar waya.

Wani mutun ne ya shigo cikin room ɗin, kai tsaye wajen drawer ya nufa, kasancewar room ɗin babu haske sosai sai yasa ba'a iya ganin wanenen ya shigo. Remote ya ɗauko a cikin drawers ɗin bayan ya sanya fingerprint ɗinsa, a saman drawers ɗin ta side guda akwai wani wajen da yake tamkar waya da glass a jikinsa, akwai password sannan akwai fingerprint a jiki duka, haka dukka furnitures na part ɗin suke, shiyasa nace maku idan bada izinin mai part ɗin ba ko tsinke ba mai iya taɓawa a ciki!.

Kunna wutar É—akin ya yi da wannan remote da ya É—auko, iya wutar chandelier dake tsakiyar room É—in ya kunna, nan take wani irin haske ya gauraye cikin room É—in gabaÉ—aya, a haka ma bai kunna wutar É—akin gabaÉ—aya ba, iya chandelier kawai ya kunna.

Hasken da gauraye room ɗin ne yasa wanda yake kwance a saman wannan King bed ɗin ya ɗan matse idanunsa alamar baya son hasken......... Wow duk da bai buɗe idanunsa ba ni dai nasan ban taɓa ganin kyakkyawan guy irinsa ba, ban san ma ya zan gaya maku haɗuwar guy ɗin nan ba........

(Saura na ji kun ce na juyawa Romeo baya🥱 yo na ga kyau iya kyau, ni fa ina son kyau sosai. 🌝 Domin manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana matuƙar kaunar kyau, yana matuƙar son kyau da kuma kamshi, kunga a matsayinmu na masu koyi da shi ai dole mu so kyau mu kuma so kamshi🤸💃 sai dai fa babu mummuna a halittar Allah, komai na Ubangiji mai kyau ne sosai, duk wanda ya ga cewa yana kallo wani mummuma a cikin halittar Allah to maza ya yi saurin korar shaiɗanin dake kusa da shi, dan shaiɗan ne yake son zugasa ya kaisa ga halaka, dan babu mummuna a halittar Allah, komai na Ubangijinmu mai kyau and tsabta ne sosai.)
Chapter 59 · 0% Book details