← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 189 OF 211

Sashe 189

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abin yayi matukar bawa Jaish mamaki yadda kowa yake kallonsa yana dariya, shi ya kasa gane komai, ganin bappa ma ya yi mashi dariya ne yasa ya juyo da kallonsa a kanta, tun a hanya yana tahowa jama'a suke yi mashi dariya, dik wanda suka haÉ—u da shi sai sun yi mashi dariya.

A fujaje ta kawar da kallonta daga kansa ta juya tamkar tun ainahi ruwan take kallo ba shi ba.

Tunani ya shiga yi a kan to me kenan ta yi mashi da yasa jama'a suke kallonsa suna dariya? Dan shi yasan daga ita sai shi a cikin ɗaki ta fito ta barsa da nufin bari ta kawowa bappa abinci, kuma tana fita bai ɓata lokaci ba wajen tashi ya bi bayanta, dan ma lokacin da ta fito barci bai gama sakinsa bane yasa ya bari ta yi gaba, shi yasan babu in da ya je daga gida sai nan bare ya ce ya je wani wajen wani abin ya ɓata mashi jiki da yasa ake yi mashi dariya.

Shi ba zai iya tambayar bappa ba saboda yana jin kunyarsa, ga shi Mahreen bata nan bare ta fasa kwai wajen gaya mashi menene, ita kuma Mahnoor Æ´ar rainin wayo yasan ma ba samun amsa zai yi ba ko ya tambaye ta, dan ta saba yi mashi tsiya idan bappa na waje ya yi magana taki amsawa.

Duk sun ruɗar da bawan Allah sun sa yana ta aikin kallon jikinsa daga sama har ƙasa ko zai ga dalilin yin dariyar tasu, kasancewar bappa yana tare da su ne yasa bai yi yunƙurin titsiyeta sai ta gaya mashi dariyar me ake yi mashi ba.

Idan ya ce zai kawar da zancen ya cigaba da aikinsa to dik wanda ya zo wucewa sai ya kallesa ta tuntsire da dariya, wasu ma har da riƙe ciki a hanya da yana zuwa, ba zai iya jurar hakan ba, to meyakamata ya yi kenan?.

Ya jefawa kansa tambaya yana kara dawo da kallonsa a kanta. A fujaje ta sake kawar da kallonta yadda zaku san alamar tsagwaran maras gaskiya ne a tattare da ita ƴar ƙaniya, tasan me ta yi mashi, ta jefa bawan Allah cikin damuwa.

Shi dai bappa da ya yi dariyarsa har da hawaye yana rike ciki mai isarsa, sai ya koma ya duƙa ya cigaba da nomarsa, dik in ya ɗago ya kallesa kuma sai wata sabuwar dariya kamar zararre ta kubce mashi. Wow bappa angon Mairo yau ya sha dariya sosai.

Wlh Mahnoor wasa wasa ta kuyi iyashege fiye da tunanin mutum, ji yanzu cikin minti É—aya ta rikita bawan Allah.

Shiru ya taya yana son su haÉ—a ido ya harareta amma taki yarda su kalli junan, sai ma ta juya ga kogin mai gabaÉ—aya.

My people's a tunaninku me ta yi mashi yasa ake yi mashi dariya haka?.

Ganin kamar suna buƙatar samun waje su biyu ne yasa bappa ya bar wajen da ya basu dama su yi magana, har lokacin dariya kamar wani zautatce, da kyar ya iya danne dariyar tasa dan kada ɗan nasa ya ɓata rai, ya kutsa cikin gona ya basu waje.

Ai bappa na barin waje ta kwasa a guje ta sauƙa ƙasan dutsen. Ai a miliyan yabi bayanta dan ya gaya mashi me ta yi mashi.

Gudu ta fara yi a bakin kogin tana kewaye dan neman hanyar da zata samu ta gudu ta ɓuyan mashi. Shi kuwa yaki bata dama, dik ta in da ta bi sai ya tarota, ga uban dariyar da take yi mashi kamar cikinta zai fashe...........

Wai me kuke tunanin ta yi mashi ne? WaÉ—an nan luv bird É—in suna sha'aninsu wlh.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️ 🕊️

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

48

Gudu ta fara yi a bakin kogin tana kewaye dan neman hanyar da zata samu ta gudu ta ɓuyan mashi. Shi kuwa yaki bata dama, dik ta in da ta bi sai ya tarota, ga uban dariyar da take yi mashi kamar cikinta zai fashe.

Wai me kuke tunanin ta yi mashi ne? WaÉ—an nan luv bird É—in suna sha'aninsu wlh.

Mu koma baya kaÉ—an. Yau ta kama Sunday, tun da sassafe bappa ya fita da dabobinsa ba tare da ya karya kumallo ba, dan ya lura yanzu dabbobin nasa basa samun ishasshen abinci, wasu daga ciki sai rama suke yi, sun kuma yi yawan da za'a ce lallai a kula da su a gida.

Dan haka sai ya zaɓi ya rinƙa fita da su tun wuri domin su samu wadatatcen abubuwan da suke buƙata. Tin kafin kowa ya tashi daga barci ya fice, harta Mahreen tana barci.

Nenne kuwa tana cikin kitchen tana aikin tsinewa Jaish tana kuma yin aikin girki, ga takaicin bappa zai kara aure, ta kai kukanta ga ArÉ—o ya ce ta wuce ta bashi waje namiji ai dan mata huÉ—u aka yi sa ba É—aya ba, ita É—in mata nawa ta buÉ—e ido ta gani a gidansu da zata wani É—ebo jiki ta zo ta ce mashi ya hana bappa kara aure? To ta sani shi ne ma zai shigewa bappa gaba wajen neman auren Mairo, kuma nan ba da jimawa ba za'ayi shi tun da dai abin dik na gida ne.

Wai nace ni kam ina iyayen bappa ne da komai ArÉ—o ne yake tsaya mashi? Mu je zuwa.

Takaici Nenne kamar ta mutu, ta wuce cikin gida ta gayawa gwaggonta. A nan gwaggonta ta rarrashe ta kuma ce wlh ba zata bar irin abin da ya faru da Æ´ar uwarta ya sake faruwa da ita ba, kada ta damu zasu É—auki mataki.

To shi ne fa ta dawo gidan bappa tana jiran gwaggonta a kan matakin da zasu É—auka.

______________🌹💘____________

A hankali ta waro idanunta da suka yi mata nauyi sosai saboda barci, sun sha barci da shi da ita yau, tun da suka yi sallar asuba suke barci har karfe 8, a lokacin Mahreen ta wuce gidan Inna Rabin haddar weekend da suke zuwa.

Kasancewar a saman kirjinsa take kwance sai hakan ya bata damar ganin face ɗinsa da kyau, barcinsa ta yi nauyi sosai saboda ya sha aiki jiya sosai, ya ƙara masu faɗin bukkar tasu da itatuwa, ya dai sha aiki har karfe taran dare sannan ya yi wanka ya kwanta, shiyasa barcinsa ta yi nauyi, da kyar ya iya tashi ya yi sallar asuba ma saboda barci.

Zuba mashi idanu ta yi tana jin wani irin kaunarsa yana shigarta, a fili ta furta. "Kai hammana kyakkyawa ne sosai wlh". Ta yi maganar tare da manna mashi sumbata a goshinsa kamar yadda yake yawan yi mata.

A hankali ta raba jikinta da nasa ta sauƙo daga gadon. Hijabinta ta ɗauko ta sanya a jikinta ta nufi waje, yanzu fa Jaish ya hanata kwana da hijabi, yarinyar da kullum da hijabinta take amma yanzu gabaɗaya ya mayar da ita sai sorry, ba hijabi take kwana ya yi ta aikin latse mata tula tulanta kamar wanda ya samu aiki ana biyansa.

Kitchen ta shiga ta ɗaura ruwan wanka tare da fitowa ta shiga ɗakin bappa dan ta duba ko yana nan. Ganin baya nan ne yasa ta fito, kiciɓis suka yi da Nenne a tsakar gida.

"Ina kwana Nenne?". Ta faÉ—a ba tare da ta dakata daga tafiyar da take yi ba, da alama yanzu Jaish ya canzata sosai, dan kuwa wlh kaso sittin cikin É—ari na tsoron Nenne da take ji yanzu ya kau, kuna dai gani ta É—aga mata gaisuwa ma ba tare da ta tsaya ba tana cigaba da nufar in da take son zuwa, ai daga nan ma zaku gane huÉ—ubar Jaish ta yi tasiri a ranta. Kullum cikin karfafa mata gwiwa yake yi yana kara mata karfi.

Taɓe baki Nenne ta yi mamaki kamar zai kasheta, in a lower voice ta ce. "Daga yau kada ki sake shiga mun cikin ɗakin miji kai tsaye haka! Dole ki nemi umarni daga wajena". Nenne dai da alama ta rasa abin faɗa ne yasa zata wani kawo banzan sharaɗinta. Yo banzan sharaɗi mana, yarinya da ɗakin babanta ki ce kada ta kuskura ta shiga maki ɗakin miji? Sai yau ta san da mijin ta ne kenan? Yau ga ikon Allah.

Ko sannu Mahnoor bata ce mata ba, ta cigaba da abin da take yi, dan kuwa Jaish ya ce mata ba komai ake bi ta kansa ba. Da alama Mahnoor tamu ta zama Æ´ar air yanzu, Jaish ya koya mata duniyanci fa.

Baki galala Nenne ta saki na ganin Mahnoor bata amsata ba, abin ya yi mugun bata mamaki, wlh bata taɓa expect ɗin haka daga gareta ba. Ga shi ba halin ta daketa, dan kuwa Jaish ya daka mata Capital warning a kan taɓa mashi jikin mata, dole dai ta sake yin hakuri ta bisu da kallon takaici wanda gara kuka da shi.

Nenne ta yi mutuwar tsaye a wajen tana al'ajabi har Mahnoor ta juye ruwan wankanta a bokiti ta É—ebo na sanyi ta dai'dai ta zafinsa da shi, sannan ta É—aura wani a saman wuta ta fito ta shiga cikin toilet.

Nenne dai baki a sake tana binta da kallo, ita kuwa ko in da Nennen take bata sake É—aga idanu ta kallah ba. Sai ta yi wucewarta kawai.

Har ta fito daga wanka Nenne na tsaye, al'ajabi ya hanata motsawa. Kitchen Mahnoor ta koma ta sauke ruwan dake saman wutar ta yi masu É—umamen abincinsu, ta kwasa a kwanikan silver ta sake mayar da ruwan dan na wankan Jaish ne.

Sannan ta É—auki abincin ta nufi É—akinsu, wlh har lokacin Nenne na tsaye, dan gani take yi abin kamar a mafarki, yau Mahnoor ce da yi mata haka? Duniya kenan.

A in da ta saba ajiye masu abinci a nan ta ajiye, sannan ta kwaso kayan da zata sanya a jikinta da kuma kayan kwalliyarta, ta zo saman mattress a gefensa ta zauna tare da fara aikin shiryawa.
Chapter 189 · 0% Book details