Sashe 88
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A takaice dai yau a tare suka wuni wajen kiwo, sai yamma suka dawo gida, yau dai basu ci abincin rana ba, saboda babu wanda zai yi girkin.
Mahreen fa sai da ta taɓa gashin Jaish ɗin kamar yadda ta faɗa, yana zaune a ƙarƙashin bishiya shi da bappa ta zo ta shafa gashin nasa. Ai a ɗari ya ɗago yana kallonta, ko a jikinta ta cigaba har da murɗa mashi gashin nasa, da yake a yanzu gashin nasa yana da tsawo zuwa bayan wuyansa, kun san larabawa da gashi, sannan kuma ga shi ya kai almost 3 to 4 months a kauyen bai yi aski ba, sai gashin ta kara tsawo sosai, hakan yana ɗaya daga cikin abin da yasa suke ce mashi aljani, dan yadda gashin nasa ya yi tsawo, sannan kun san yadda gashin larabawa yake, akwance ga tsantsi da sheki, ku kanku ku kwanta yadda fatar jikinsa yake fari tas kyakkyawan gaske, ga uban bakin gashi mai tsawo da sheki ai dole ku ɗan tsorata da kyansa, sai ma ya zaro idanun.
Yau wuni Mahreen ta yi tana mummurɗe mashi gashin kai kamar an aiketa, tana fa shakkarsa, amma tsabar ita ɗin in ta faɗa sai ta cika, sai da ko ta cika, tun yana mamaki har ya dai'na, kuma sam bai nuna alamar kamar ya ji haushin abin da take yi mashi ba, bappa ma bai hana ta ba, dan shi kansa yana son su rinƙa jan Jaish ɗin da maga ko Allah zai sanya watanara bakinsa ya buɗe ya yi masu magana, ya gaya masu daga ina yake dan su samu su mayar da shi in da ya fito.
Duk ta watsa mashi gashi, ta bi ta mummurɗesa ya zama kamar indomie, yau ya sha aikin Mahreen manyan ƙasa
Time da zasu koma gida da ya yi sam bata ji daÉ—i ba, ranta bai so ba, ta so ne Jaish ya cigaba da zama a wajen tana murÉ—e mashi kai har gobe, ita fa bata gajiya in dai tana tare da shi.
Haka dai suka koma gida, wanka Mahnoor ta yi suka shirya zuwa wajen Arɗo. Jaish dai ya nuna ba zai je ba, da kyar bappa ya lallaɓashi suka tafi.
Jama'a duk sun hallara, kowa sai baya baya yake yi da bappa, sauran manyan dattawan kauyen ne kawai suka É—an yarda suka gaisa da shi, su É—in ma sai É—ari É—ari suke yi, shi kam Jaish dama bai nemi su yi mashi magana ba, dama ko sun yi mashi ma ba kula su zai yi ba, dan haka tsayuwarsa a gefe ya yi yana kallon gefen da babu mutane.
Sai gulmarsa jama'a suke yi ƙasa ƙasa, masu satar kallonsa suna yi, masu rufe idanu wai suna tsoron ganin maye suma suna yi, haka dai suka tsaya har lokacin da Arɗo yasa su gwaggo suka banka maganin mayu a wuta hayaki ya fara balbalowa, jama'a basu da masaniyar hakan kawai unexpect suka ga hayaki yana bulbulowa. Nan take dayawa daga cikinsu suka fara tari mai sautin gaske, gwaggo bakar muguwa har da dumbulo maganin cikin hannayenta dukka biyu ta sake bankawa a cikin wutar, dan a cewarta idan Jaish maye ne ma ya ji azaba sosai......... Wato mutun dai ko ya mutu sai an ɗaure shi!!.
Sai tari jama'a suke yi shi kuwa Jaish yana tsaye yana binsu da kallon mamaki, bappa ma bai yi tari ba, haka su Mahreen ma. Kan kace me ainahin masu aljanu a kai sun fara faɗuwa ƙasa suna ihu, nan take wajen ya hargitse da masu aljanu da almatsotsai dukka, ihu sautin muryoyi kala kala ne suka fara karaɗe kauyen gabaɗaya.
Mahnoor kam gam ta ƙanƙame bappa jikinta na kerma, shi kuwa Jaish da ba mayen bane sai ma harɗe nannaye a saman faffaɗar kirjinsa ya yi yana ta kallon ikon god. Duk shakkarsa da Mahreen take ji bai hana ta riƙo hannunsa tana tambayarsa menene wannan ba?.
Kallonta ya yi tare da yi mata alama da hannu a kan shi ma bai sani ba, hakan yasa ta yi shiru tare da ɗan kwantar da kanta a hannunsa tana binsu da kallo, bata taɓa ganin irin hakan ba, dan da wayonta dai ba'a taɓa kama mayya ko makamancin haka a gabanta ba!.
Sai da gabaɗaya masu almatsotsai a kai ɗin suka sume a ƙasa sannan Arɗo ya fito. Ba ƙaramin tsorata ya yi ba a lokacin da ya fito ya ga Jaish a tsaye a kan kafafunsa, abin ya ruɗar da jama'a dayawa, wanda suke zaton shi ne mayen sai ga shi a tsaye cak a kan kafafunsa, wanɗan da basu taɓa zato ba kuma sune suka zube ƙasa matsayin masu lalurar. Abin ya ɗaure masu kai, ya kuma jefasu cikin ruɗani, a maimakon su yarda da cewa Jaish fa mutum ne kamar su, amma ina sai ma suka sake kai abin gaba, a in da suka fara cewa ai Jaish shi ne shugaban mayun duniya gabaɗaya, wai shi ne sarkinsu, dan haka wannan magani ya yi mashi kaɗan ne shiyasa bai faɗi ƙasa ba, sai sun nemo magani mai karfin gaske, dan haka dole su shiga kauyukan Cameroon wajen ƴan uwansu sulluɓawan fulani su nemo magani, sam sam su ba zasu taɓa yarda cewa shi ɗin mutun ne ba, dan kyau ɗinsa fa daban yake, ga shi ya mari yaro ya fara ciwo kamar zai mutu.
Bappa dai da yake ya yarda da Jaish ɗin ko a jikinsa, sai ma cewa da ya yi su wuce gida, ɓacin ran kalmar da suke jefar Jaish ɗin da shi ne yasa ya wuce gida ya manta bai ce da Arɗo a yi wa su Mahreen tsakani da su Salisun ba, ya mance suka wuce gida.
Da Arɗo ya dawo cikin gida ya gayawa su gwaggo Jaish fa shugaban mayu ne, wannan maganin ta yi mashi kaɗan, wani irin tsoro ne ya ƙara kamasu, haba kan kace me sun shige cikin ɗaki har suna rige rige, Innar Mahnoor ɗin ce kawai bata gudu ba, kowa ya ƙara tsorata da lamarin aljanin Mahreen sosai. Shi kuma bawan Allah da Allah yasa ba jin fulatancin sosai yake yi ba, sam bai san me suke ciki ba, a tunaninsa ma wani al'ada ne nasu na banka hakaƙi a gari su saka mutane tari har da suma, shi bai ma san wasu halitta wai su mayu ba a duniya, tunani ma yake yi a kan wace iriyar al'adance wannan ta cutar da mutane da hayaki har su suma?........ Babbar magana, to jama'ar ruga shi fa Jaish bai ma san kuna yi ba bayin Allah, sai ku kara himma wajen banke kowa da hayaki kuna tonawa kanku asiri, ku yi maza ku kashe kowa sai naga waye zai gaji kauyen, yau ance wasu dayawa ne mayu a maimaikon Prince Jaish namu, gobe kuma sai a haɗa da Arɗonma mai gabaɗaya..........🤣
Duk wani mayen da ya suma a wannan wajen Arɗo ya ce kashe shi za'ayi har lahira tun da su mugaye ne, nan fa kauye ya riƙice, kowa sai cewa yake yi a'a wlh nasa ba maye bane, kawai ya suma ne, sun ki yarda a kashe masu ƴan uwan nasu, nan fa Arɗo ya ce dole a kashesu, dan kuwa basu da amfani a cikin al'umma.
Su Mahreen dai gida suka wuce abinsu, Mahnoor ta je ta hau yi masu girkin dare da zasu ci. Nenne dai ta zama yar gidan Arɗo yanzu,............. A gaskiya Jaish kana wuta a kauyen nan, duk ka sanya jama'a bala'in tsoronka, mata sun bar gidan mazajensu sun koma gidan uba kamar babu mutuwar a can gidan baban nasu, duk saboda kai?..... To ni dai bari na leƙa wani ɓangaren.
__________________________🔥🌼â¤ï¸
DARK WORLD🔥🌹
Washegari da safe Ronnie ya tafi school, a tare da Floris Sweetie ta wuni, sai hira su ke yi, a nan Floris ta bata labarin iyayenta da suke a cikin birnin, sosai Sweetie ta sha madarar mamakin irin halin Ronnie, kawai ka ɗauko ƴar mutane ka ajiyeta a nan haka ake rayuwa, su iyayen nata ai rashin addini ne duk ya ja haka, idan ba rashim addini ba yaushe zaku ɗauki ƴarku budurwa ku baiwa Ronnie ya dawo da ita cikin empeir ɗin ya ajiye fisabilillah?. Ko da yake suna a ƙarƙashin ikon Black Tiger ne dole su bi ra'ayin Ronnie su bashi ƴa.
Sai around 1:30 Ronnie ya dawo daga school, kai tsaye room ɗin Sweetie ya nufo, a lokacin ta shiga cikin toilet dan yin alwala, Floris kawai ya isko a kwance saman gadon. Tana ganinsa ta miƙe zaune.
Ƙariso ciki ya yi, ɗan rungumarta ya yi tare da bata sumbata a kumatu kafin ya zauna a gefen bedside drawer. "Hiran me kuka yi yau?". Ya faɗa murya a kasale.
Kashe mashi ido ɗaya ta yi kamar yadda ya saba yi mata, da alama akwai abin da suke ɓoyewa. Jinjina kai ya yi kamar mai sauraren wani abin mai daɗi. Dai'dai lokacin Sweetie ta fito ta ɗauro alwala. Kamar yadda ta saba yin sallah haka ta tsaya ta tada sallah ba tare da ta ce da Ronnie ɗin ko uppan ba.
Binta da kallo shi da Floris suka yi, sun kasa iya cigaba da hiran da suke yi, sai kallonta suke yi har ta idar da sallar, addu'oi sosai ta yi tare da shafawa, sannan ta miƙe ta dawo kusa da Floris ta zauna. "Welcome Ronnie" . Ta faɗa a sanyaye.
"Queen of beauty ya naga kin ƙara kyau ne yau?". Tamkar bai san motsa lips ɗinsa ya yi maganar, sai ka ji tamkar shagwaɓa yake yi, saboda a gajiye yake, ga kasala........... Ni kam nace ai dole ta ƙara kyau, dan kuwa ta samu hutu, ga Ac na bugata, sannan ga sabulai masu tsada, kwanciyar hankali ne dai kawai bata da shi, hankalinta gabaɗaya yana kan ƴar uwarta Pretty and Kamran, amma ta samu abin da take fata kam dukka saura wannan.
Miƙewa ya yi ya nufi waje tare da ce masu yana zuwa, dama Sweetie yake ta marmarin gani yasa yana dawowa daga school ya zarcu nan.
Da sauri Floris ta miƙe ta bi bayansa suka bar Sweetie ita kaɗai.