Sashe 165
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin maganar nan tasa yasa ta ji tamkar ta fashe da ihu mai sautin gaske, ta yi ta yi kada ta dakata watakila zata É—an samu sassauci a cikin zuciyarta, dama kamar jira take yi a ce mata Khadija fashe da kuka kawai ta fashe.
Ƙarisowar Zee wajen ne yasa ta danne kukan da ya zo mata ɗin.
"Aunty Khadijah ni ban samu waya ba, kowa sai ya ce mun bashi da shi, jama'a basu son bani dan basu yarda da ni ba, yanzu babu yarda sam a duniya!". Ta faÉ—a kamar zata yi kuka.
"Me zaku yi da waya?". Cewar wannan mai napep É—in.
Wani kallon uku saura kwata Zee ta watsa mashi, kun san ita fa ba sauki, ƙaddarar da ya faru da sune yasa ta yi laushi. Haka kawai sai ta ji bata yarda da guy ɗin ba, ta ji kamar bashi da gaskiya, dan haka sai ta ɗaure fuska irin ba wasan nan tana binsa da kallon rainin wayo.
"Kawunmu da muka zo wajensan ne zamu kirasa, dan mu bamu san gidan nasu ba". Khadijah ta bashi amsa. Kamar zata fashe da kuka ta yi maganar.
"Ayya Allah sarki, to shikenan ku zo muje na kaiku unguwar, sai na baku wayata ku kirasa ko?".
Khadijah na ƙoƙarin yin maganar Zee ta rigata da cewa. "Baza'aje ɗin ba, ka je zamu sami wani abin hawan". Cikin tsiwa ta yi maganar, Zee fa kamar mai aljanu a kai wlh, idan bata son abu fa sai a hankali.
"Ke Zee baki da hankali ne wai? Ke baki ga taimaka mana zai yi ba? Ki gaya mun idan ya tafi yaushe zamu samu wani da zai san unguwar har ma ya É—aukemu zuwa can ya kuma ara mana wayarsa mu kira kawu Sadiq?".
Tun da ta fara magana yake ta aikin girgiza kai irin shine fa É—in nan, wato Khadijah tana yabashi shi ne yake wani kaÉ—a kai.
"Aunty Khadijah na Allah basa karewa a duniya, ɗik min lalacewan duniya ba zaki taɓa rasa na Allah ba, dan haka tabbas zamu samu waɗan da suka fishi kyan zuciya, ni wannan bai kwanta mun a rai ba sam".
Oh Zee sarkin faɗa, to dai kinyi kuskure a nan, ko ya kake jin ɗan adam a zuciyarka ba'a fitowa karara a bayyana mashi, in ma sonsa kake tsananin yi ko kinsa, idan ka bayyanawa mutun tsananin sonsa da kake yi is very very hardly ya ɗaukeka da wata daraja, idan kuma kinsa kake yi nan ma ka bayyana mashi, to wlh da matuƙar wahala ya iya mantawa, zai riƙeka a zuciya ne sosai, zuciya kuma bata da ƙashi, ya kan iya yi maka wata muguntarma a sanadin haka. Sai mu kiyaye
Sosai guy ɗin ya ji ɗacin maganganun Zee, har ya miƙe zai bar wajen Khadijah ta fara bashi hakuri, saboda ita ya dawo ya hakura, ya kuma ja akwatin nasu ya ce su ƙarisa wajen keken napep ɗin nasa.
Haka kuwa aka yi, suka je suka shiga ciki ya É—aukesu suka bar tashan. Abinku da basu san unguwar ba, dik ta hanyar da aka bi da su sai su kalli kamar unguwar ya nufa.
Shi kuwa ya yi tafiya mai mugun nisan da a kallah ya kusa awa guda da su, yana tafiya har da ce masu ya yi unguwar a kusan karshen gari yake, Khadijah dai ta yi shiru ta kifa kai da jikin karfen napep É—in tana tunanin duniya, ita kuwa Zee da already dama bata yarda da shi ba sai take ganin kamar ba unguwar ya nufa da su ba.
Hakan yasa ta shiga damuwa take ta aikin tambayarsa wai har yanzu basu iso bane? Sai ya ce mata ai sun kusa isowa. Har Khadijah tana yi mata faÉ—a a kan ta barsa ya yi aikinsa mana, zata wani tasa shi a gaba tana tambayarsa, ya ji da tuki ne ko da amsa tambayoyinta? Sai ta je tasa sun faÉ—i ko?.
Turo baki take yi ta yi shiru, hakan kuma ba shi ne zai sa anjuma kaÉ—an ta fada tambayarsa wai har yanzu basu iso bane?.
Bawan Allahn nan da yake babu Allah a ransa sai da ya fitar da su gefen gari, sun bar cikin mutane sannan ya dakatar da tafiya, Khadijah ta afka duniyar tunani bata ji ya tsaya ba.
A hanzarce ya juyo in da suke, Zee tana ƙoƙarin tambayarsa akan meyasa ya tsayar da su a wannan waje mai kama da dajin, sai dai bata kai ga buɗe baki ta yi magana ba ya yi hanzarin fito da sleeping power ya fesa masu a face ɗinsu.
Da yake Khadijah kanta na kife a jikin karfen mashin ɗin sai power ya sauƙa a jikinta ta bayan wuyarta, ita kuwa Zee tuni ta yanke jiki ta sume, ta kwanta a jikin head na kujerar mashin ɗin.
Jin abu ya zuba mata a bayan wuyarta ne yasa ta É—ago kai, tana É—agowa ita ma ya watsa mata rabonta, kan ta yi wani motsi ta sume.
Wani irin farinciki ne ya bayyana a saman face É—insa, kunna mashin É—in ya yi ya kara kutsawa cikin dajin da kyau da su, sannan ya ciro wayarsa tare da fita daga cikin napep É—in ya É—an yi gaba kaÉ—an. Dama kuskure ne ka sauka a kawo Kaduna ka hau kowani irin mashin da ka gani, hakan babban kuskure ne sosai, domin ba kalar fuskar da babu a wajen, akwai na Allah haka zalika masu taya kidnappers aikin suna nan.
PRINCESS TEEMA 🔥
A can Kano kuwa, su Khadijah suna barin gidan bai fi da awa ɗaya ba wasu irin jiga jigan motoci masu kama da jirgin sama suka keto cikin unguwar tasu, jama'ar unguwa tun suna ƙirga yawan adadin motocin har suka hakura kawai, saboda yawansu ya wuci tunani, yadda motocin nan suke tafiya kai kanka kasan ko shugaban kasan Nigeria ba za'ayi mashi irin wannan ba, a jere suke cikin nutsuwa, gabaɗaya motocin daga villa suka fito.
Kai tsaye kofar gidan nasu suka nufa, a lokacin Hauwa tana shirin fita domin ta je ta canza wannan kuÉ—i nasu Khadija, har ta gama lissafin kasashen da zata je hutawa.
Ta kammala shiri ta fito tsakar gida kenan wasu irin mahaukatan bodyguards suka danno kai cikin gidan babu ko excuse, kana ganin face É—insu sai ka tsorata, dan kuwa babu alamar mutunci ko imani a tattare da su, shiyasa suka shigo babu ko excuse, dan ma a san ba mutunci ne da su ba kuma ba shi suka zo yi ba.
Ga su wasu katti da su, ga sawo da ƙiba, dik suna cikin black shiga, bakin kayan yasa hasken fatarsu ta ƙara bayyana sosai, gabaɗayansu turawa ne, babu bakin fata ko larabawa a cikinsu, dikkansu suna riƙe da manya manyan bindigu kamar zasu tashi gari, sai wani zaro jajeyen idanun nan nasu suke yi kamar mutun ya ruga a guje.
Sun kai su 20 suka shigo cikin gidan, ta kowani lungu da tsako a cikin gidan sai da bodyguard guda É—aya ya je ya tsaya, a guje suka kewaye ta ko'ina suna wani leke leke domin su tabbatar da ba wata motsi na cutarwa.
Ji kake yi dip dip dip wasu security jami'an fararen kaya sun sake kutsowa cikin gidan su shidda.
Ai a miliyan Hauwa ta juya zata gudu ta koma cikin parlour, wani security farin kaya da suka shigo daga baya ne ya tare gabanta, ya tareta, ya hanata shigewa cikin parlourn, dan an basu umarnin in sun shigo cikin gidan kada su bar ko tsinke ya motsa, komai ya tsaya a yadda yake kenan.
Tuni ta hau kerman jiki, tsabar tasan bata da gaskiya har faÉ—i take. "Wlh ba gidana bane, mai gidan baya nan, kuma wlh matarsa ce ta kashesa, dan Allah kada ku yi mun komai, wlh bani ma aikata laifin ba, idan ma kuÉ—in su Khadija ne ga shi can a É—aki ban É—auki ko biyar daga ciki ba, dan Allah ku yi hakuri".
Ko sannu babu wanda ya ce mata, kamar wasu saƙaguna haka suka tsaya irin tsayuwar jarumai suna kallonta da jajayen idanun nan nasu.
Wasu dakakkun maza madaka katti ne suka sake shigowa cikin gidan suna shinfiɗa wani irin haɗaɗɗen white carpet, tun daga waje jikin motocinsu suka shinfiɗa shi har izuwa cikin gidan, har bakin kofar parlour tsawonsa ya kai. Bayan sun kammala shinfiɗawa ne suka tsaitsaya a gefe gefen carpet ɗin, suma hannunsu riƙe yake da wasu mahaukatan bindigu na ƙasashen ketare.
Shiru suka tsaitsaya tamkar ba mutane ba, sai ka rantse da Allah basa numfashi, saboda irin tsayuwar da suka yi, sun ƙame waje guda.
Wani irin ƙara ƙamewa gabaɗayansu suka yi a lokacin da wata kafa ta tako saman carpet ɗin ta nufo cikin gidan.
Tun daga kan luxury hiking boots shoe mai bala'in kyau da tsada launin milk color dake kafarsa, tun daga kan takalmar kafar tasa ta ji tsoron É—aga idanu ta kalli face É—insa, cikin nutsuwa, isa da izza yake takowa har izuwa in da take tsaye.
Matashin ne da ba zai wuci 35 years ba, cikakken namiji ne da dik in da ake neman namiji to ya kai, yana sanye da white face mask a face ɗinsa, tsadadden haɗaɗɗen Jessy wato kayan ƴan kwallo ne a jikinsa, daga yanayinsa zaka fahimci wannan kuɗi sun jiƙasa over, dik da yana sanye da face mask hakan ba zai hana ka gane bashi da mutunci ba, dama tun daga kan yadda yaransa suka watso cikin gidan zaka fahimci wannan ya bawa mutunci baya, sam basu haɗa hanya ba.
Ko waye shi? Ni kai'na ina son sani, dan irin wannan isa da taƙama dole mu so sanin wanene shi.
Tamkar baya son motsa laɓɓansa ya furta. "Where's Khadijah?". Cikin harshen turanci ya yi maganar.
Hauwa da bata jin turanci tuni ta kara tsurewa tana muzurai kamar an tare ɓera a tarko, jikinta na kerma kamar mazari.
Da ido guy É—in ya kalli wannan jami'in da ya tare gaban nata, bai furta komai ba jami'in ya wani daka mata tsawa mai sauti a in da ya maimaita tambayar da guy É—in ya yi da farko wato ina Khadija?.