← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 211

Sashe 109

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da ya ɗaura idanu a kan kanin nasa ya fahimci akwai wani abin, dan har lokacin a ɗan ruɗe yake, Yah Rizwan ya ɓata mashi komai, ya so gaya mata abin da yake ransa, ya kuma yi kissing nata kamar yadda ya yi niya, amma idan ya kama shi yana aikata hakan ko ya kamashi da ita a tare a nan ai ya shiga talatin............

My people's shin me kuke tunanin zai faru a cikin wannan companyn yau?

________________________🔥😥💔

GIDANSU KHADIJAH.😥💔

Ya ilahi, my people's Khadijan ta koma tamkar ba ita ba, kullum ɓoye kanta a cikin ɗaki take yi ta murji kuka kamar me, tun Zainab na tambayarta me yake damunta har ta hakura ta daina tambaya, taki yarda ta sanar da kowa abin da yake faruwa, cikin nata kuwa ya kusa isa level ɗin da ba'a isa a ɓoye shi ba, dan ma cikin fari ne, bashi da girma sosai ita ma bata da babban ciki, kuma Allah ya rufa mata asiri bata laulayi sosai, sai uban faɗa da tsanar mutane ta iya, ko Zainab dan dole suke tare da ita, dan ba yadda zata yi ne, amma ta tsani ganinta a kusa da ita sosai, ga dukkan alamu duk yadda aka yi uban cikin nan mafaɗaci ne sosai, dan kuwa abin da baku sani ba shi ne a ciki akwai ilimi biyu zuwa uku da ba kowa ne yake iya gane hakan ba sai wanda ya kasance mai ilimin addini sosai, domin kuwa faɗar Allah ne wannan ba faɗar bature ba, amma a hankali zan warware maku komai In Sha Allah.

A ɓangaren malamamin makarantarsu kuwa, kullum sai ya zo, amma Khadijan ta ki yarda ko da sunan wasa su haɗu, kwata kwata ma ta dai'na fita, saboda matsa mata da samari suke yi, tamkar abin ba lafiya ba sai da abin nan ya faru da ita ne suka fara tururuwar zuwa neman aurenta.

Sannan makudan kuɗaɗen da ta dawo da su ko naira bata sake taɓawa ba, tun da ta cusasu a bayan gado ta fita harkarsu. Yau tun safe basu ci komai ba daga ita har Zee ɗin,
Amma bata fito da kuÉ—in dan ta saya masu abinci ba, da alama ta mance da kuÉ—in.

A yau ne kuma suka tashi da mummunar al'amari na rasuwar Hajiyar su baban Zee wato kakarsu kenan, Hajiya lokaci ya yi, sai dai mu ce Allah ya jikan musulmi.

Kakarsu ta wajen uwa wato Hajiyar su Sadiq kam ma basu san a wani hali take ciki ba, tun da Sadiq ya tsallake ya bar Kano ba su sake jin ɗuriyarsa ba, Zee ta nemo waya a maƙota wajen wani mai shago ta kirasa numbersa a kashe, kusan kullum sai ta kira shi domin ya zo ya kawo masu ɗauki a kan wannan wahala da suke ciki, amma ina basu samunsa, sun kira number kakar tasu ma a kashe.

Yanzu haka wani irin cin kashi Hauwa take yi masu, Khadeejerh mai iyawa da ita É—in kunga tana fama da kanta, ita kuwa Maman Haidar tana can tana hidima ta yadda zata yi ta fitar da É—anta daga halin da yake ciki, bata da nutsuwa, hankalinta a tashe yake sosai, bata ma garin, tana can Abuja wajensa, zuwanta na biyar kenan yanzu ana hanata ganinsa, har yau bata samu damar sanyashi a idanunta ba, bata san a wani hali yake ciki ba, duk ta firgice, ta rame kamar ba ita ba.

Ta zama kamar mai cutar ƙanjamau, rasuwar Hajiyar tasu ma ita bata da labari, tana can tana up and down, sai bin manya take yi duk dan ta samu mafita, ta samu ko da sau ɗaya ne taga ɗan nata, sai ta je wajen wannan ta sha bakar wahala wajen sati tana biɗar ganinsa, idan ta samu da kyar ta gansa sai ya ce mata case ɗin a sama da shi yake, ya fi karfinsa, dan haka ta kara gaba zuwa sama ko zata dace, haka dai take ta fama, ta sayar da gidan mijin nata, dan kuwa shi kaɗai ne kadarar da suka mallaka, shi kuma mijin kunga ga shi ne ga kalarsa, in dan ta shi ne Haidar ɗin ya mutu a can ba ruwansa, ita ce dai ta tsaya tsayin daka wajen ganin ya fito. Ta juri rana, ruwa, iska da zafi dukka!!.

In takaice maku kuɗin gidan da ta sayar wajen 10 million ɗin ma ta kusa cinyesu a neman ganin manya, duk in da ta je sai ta bada kuɗin goro kafin ma ta samu a haɗata da P.An wanda ta je nema, shi ma P.A ya kwashi rabonsa, gata wawuya ba ilimi ba, sai ayi ta cutarta, wani ma karya yake yi mata ya ce zai haɗata da wanda zai fitar mata da ɗan nata amma sai ta biya, haka zai karɓe mata makuɗan dubbanin ɗaruruwa ya gudu ya barta, sai dai ta yi ta jan Allah ya isa.

Wani abin da wani ya yi mata sai da ya sanyani kwallah, dan kuwa sati tana bibiyarsa, ta je office É—insa ya fi kafa talatin, yana ciki amma sai P.A ya ce mata baya nan, haka mai gadi zai ce kada ta zauna a ciki dan tana wari, sai dai ta fito waje ta zauna, komai zafin rana haka take zama a tsakar ranar, uwa kenan, komai lalacewarta dai daban take da kowa.

Ko ruwan sama ake yi haka zata zauna, ta gama cin bakar wahala, ta basu kuɗi kamar ba gobe, P.A ɗin ma mugu ne sai ya yi ta karɓar mata kuɗi yana kuma ce mata ta dago gobe ogansa baya nan, abin dai ba daɗi, koda baka kaunarta sai ka tausaya mata a wannan gaɓar.

Daga karshe randa Allah ya nufa ta samu damar ganin mutumin ya fito daga cikin mota zai shiga office, tana ganinsa ta ruga da gudu ta nufesa, securitys ɗinsa suna tare ta kada ta isa garesa ta bangajesu ta isa gabansa, har ƙasa ta zube gwiwowinta tana kuka tana ce mashi dan girman Allah ya ceci yaronta.

Mutumin nan ba kunya bare tsoron Allah har a kai ga tausayi yasa ƙafa ya hamɓareta ya wuce gaba fuskar nan kamar na shanu, har da dakawa securitys ɗin nasa tsawa a kan su fitar mashi da wannan almajira da talauci yasa ta sami taɓin hankali a nan hai, sai warin datti take ta cika masu waje, ya ce kada a sake barinta ta doso mashi office baya da buƙata. Ya bi ta kan yatsun hannunta ya takesu ya wuce, yatsun nata sai da suka fashe suka fitar da jini, saboda takalmar kafafunsa masu ƙarfin gaske ne.

Haka securitys ɗin suka kamata suka jefa waje, sai kuka take yi......... Yanzu wa gari ya waya fisabilillah?. Da ace sun yi zaman mutunci da su Sadiq, da shi kaɗai bai isa ya tsaya mata ya yi iya bakin ƙoƙarinsa har a samu Haidar ɗin idan yana da rabon fita ya fito ba?! Wlh da Sadiq yana nan ba sai ta zo nan tana shan wannan bakar walaƙanci da kaskaci haka ba, da tana gida zai yi komai, amma ga shi nan tana ganin illar mugunta ai, su ba tsayayyen namiji suke da shi a cikin familyn ba, ga rashin ilimi da rashin wayo, kowa ya ce mata kuɗi ta ɗeba ta bayar, sai ma ta tambayesu nawa zata kawo, mugaye su suke yanke nawa zata kawo, ita kuwa ta cire ta miƙa, Allah sarki ita dai ɗanta kawai take son ya fita, duk da haka ko ta bada a walaƙantata, yanzu duk ta yi yaushi ta rasa ina zata sanya rayuwarta ta ji sanyi.

Duk wannan halin da take ciki kawarta hajiya Hauwa tana gida ta baje tare da É—aura É—amarar cin dukiya da gasken gaske, idan ta yi crossing leg É—in nan nata a saman sofa, ta tasa su kaji gassasu and yogurt a gaba tana cin duniyarta da tsinke babu wanda zai takura mata, ga shi Hajiyar tasu ma rai ya yi halinsa, gidan babu wani tsayayye, Hauwa kam duniya sabuwa abinta.

Zata yi saye sayen kayan daÉ—inta, su Khadeejerh suna ji suna gani zata ci ko a gabansu ko É—anÉ—ane bata yi masu.

Allah ya rufawa Khadeejerh ɗin asiri ma cikin nata bashi da kwaɗayi kuma baya zaɓe, ai da ta wahala ƴar tahaliƙar nan a hannun Hauwa.

Hajiyar tasu da ta rasu ma ba wanda ya sani a tsawon awanni, su Khadijah suna É—aki kamar kullum, ita kuma Hauwa sai abin da hali ya yi, ta fita ya kai sau uku tana zuwa unguwa ta je ta dawo, ta kuma yi girki amma duk da haka bata san cewa surukartata ta rasu ba tsabar bata da albarka.

Sai da Maman Hanif ta kawo masu ziyara gidan ne ta iya ganewa, ta zo ne dan ta ji ko ya labarin Æ´ar uwarta maman Haidar ake ciki, sai kawai ta tadda bakar labari na rasuwar Hajiyarsu. Ta yi matukar kiÉ—ima tare girgiza, hankalinta idan ya yi dubu ya tashi!.

Duk da ba shiri su Khadija suke yi da kowa a gidan ba haƙiƙa sun sha kuka na rasuwar Hajiyar.
Hauwa kuwa wani irin daɗi ta ji, faɗi take gara ya karun mata, jin daɗi babu tsayawa, ita fa ga dukkan alamu bata tuna akwai ranar tafiya gidan gaskiya, anya jahilcin Hauwar nan ma ya barta ta yarda da lahira kuwa? Akwai matsala, wannan wutarta daban yake idan bata tuba ba, Allah baya yafe laifin wani, ko ta tuba a ina zata ga baban Zainab har ya yafe mata abin da ta yi mashi, dan shi ta cutar da shi cuta mafi muni a rayuwa, duk wannan abin shi ta yi wa, ta ja Hajiyarsu ma ta rasu saboda bakin cikin abin da ya faru ne yasa hawan jininta ya tashi har zuciyarta ya kumbura, yanzu rai ya yi halinsa, rayuka biyu Hauwa ta salwantar waɗan da basu ji ba ba kuma su gani ba. Innalilahi wa inna ilahir rajiun, ga maman Zee a can prison tana karɓar azabar laifin da a kan Hauwa yakamata ya rataya.

Haka maman Hanif ta kira jama'a aka yi kira mai wankar gawa ta yi wa Hajiyar tasu, daga haka aka je aka rufeta a gidanta na gaskiya.
Chapter 109 · 0% Book details