← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 211

Sashe 135

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To kaunaty sai ki buɗe idanun naki ai, bama ki iya barcin karyar ba, ji yadda eyelashes ɗinki suke kerma". Can ƙasan maƙoshinsa ya yi maganar.

Turo baki ta yi, ba tare da ta buÉ—a idanu ba ta furta. "Kai Yah Jawad me haka ne wai? Na yi barci na kazo ka tasheni".

"Tom shikenan ayi hakuri, cigaba da barci ni ma bari na je nayi nawa barcin".

Jin ya furta kalmar tafiya ne yasa ta yi saurin waro idanu tare da miƙewa zaune. "Kai Yah Jawad dare fa bai yi sosai ba, yanzu karfe 12 ma bata cika ba ne zaka tafi?". A shagwaɓe ta yi maganar.

Cikin zolaya ya ce. "Awww dama a duniyar mafarki ma akwai time ne? Ko dai yanzu kam kin gane ba mafarki bane?".

Hannu tasa ta rufe fuska na rashin kunya tana É—an sakin murmushi, kumatu a kumbure cike da iska data hura ta ce. "Kai Yah Jawad nasan ba mafarki bane yanzu, kuma ni ka dai'na tsokanata".

"Eyyeeee Jannat matar Jawad, dan ni aka haifeki, kin ma ji sunanmu kusan iri É—aya, Jannat and Jawad". Yana magana yana murmushi cikin sigar zolaya.

"Kai Yah Jawad ni ban san yaushe ka zama haka na".

ÆŠan matsowa kusa da ita ya yi. "Tun lokacin da Jannat É—ita ta fara girma na zama hakan". Kamar mai raÉ—a ya yi maganar.

Pillow ta É—auka ta jefa mashi a fuska tana É—an dariya maras sauti sosai.

Bai bari pillown ta sauƙa a face ɗin nasa ba ya riƙeta tare da ɗan kara matsowa kusa da ita.

"Idan kina turo mun wannan ɗan bakin kina sakawa na ji ina buƙatarsa, kwanta ki yi barci sai da safe". Yana kai karshen maganar ya miƙe tsaye.

"Yah Jawad meyasa zaka tafi yanzu?". Kamar zata yi kuka ta yi maganar.

"Saboda dare ya yi". Ya bata amsa a takaice.

"Tom shikenan ka kula mun da kanka, sannan ka yi mafarkina".

Jinjina mata kai kawai ya yi alamar to ya ji, baya son sake yin magana dan kada ta tsayar da shi. Kwanciya ta koma ta yi ya ja bargo ya rufa mata izuwa wuyarta, sannan ya tofa mata addu'oi kafin ya manna mata sumbata a goshi.

Kofar fita ya nufa ba tare da ya sake furta kalma ba, da kallo ta bishi har ya fice ya rufo mata kofa.

Yana fita ta miƙe ta ɗauko remote daga cikin drawer bedside, kashe wutar ɗakin ta yi, ta koma ta kwanta bayan ta ajiye remote ɗin.

Yana shiga room ɗinsa shi ma ya haye saman bed, sai dai kuma ya ƙasa iya yin barci, tunaninta ya tsaya mashi a rai. Kamar yadda ya ga rana haka ya ga dare......... To asuba ta gari malam Jawad namu na zamani jikan Akka tamu ta amana.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

Shirye suke cikin uniform É—insu gabaÉ—aya Æ´an'matan, suna zaune a saman dining table chairs dake part É—in King, su momma kowa yana zaune, Akka ma tana wajen, yau sun haÉ—u fa, ga uncle Jahiz and uncle Abbas.

Sai kallon uncle Jahiz mammie take yi tana ayyana yadda zamansa zai kasance shi da Aliya bayan an haÉ—asu aure. Ita kuwa Aliyah ayyanawa a ranta take yi yadda zamanta zai kasance da King Zuhair.........E lallai waÉ—an nan sun yi nisa, akwai cakwakiya gaskiya.

Cikin nutsuwa suke cin abincin nasu, gabaɗaya room ɗin tsit kake ji, babu abin da yake tashi a cikin face ƙarar spoons. Kuyanga Zubaida sai aikin serving ɗinsu take yi, duk wanda yake da bukatar zai ƙara wani abin haka zata ƙara mashi.

Guyson dai yana zaune kusa da Mommarsa, har da wani ɗan kwantar da kansa a saman shoulder ɗinta, kamar kullum ya dauki wannan kwalliya tasa mai ruɗar da masu kallo su yi ta santin kyansa, kansa sanye da hular sanyi mai gashi sosai a jiki, ya yi shiru baya ma cin abinci, shagwaɓa kawai yake ta aikin zubawa Mommar tasu tana biye mashi, dan son da take yi mashi na daban ne, musamman ma yadda ta sha wahala a kan na wannan ciwon cikin nasa, shiyasa yake manne mata, saboda ya saba idan ta je Dubai ciwonsa ya tashi to wlh duk girman nan nasa yana saman jikinta, ko lafiyarsa lau ma yana jikinta kullum abinsa.

Yaki cin abinci wai sai anjuma around 9 zai yi breakfast sai ya sha magungunarsa, dan dole suka haƙura suka kyalesa, amma sun so ya yi breakfast a lokacin.

Rizwan yana cikin room É—insa yana zuba barci, bai fito ba, dama shi baya cin abinci a tare da su, shi kansa Jawad idan baku manta ba tafiyar Jaish yasa ya fara shiga cikin iyayen nasa suna ci a tare domin ya rage kewar É—an uwan nasa.

Shirye cikin wani irin luxury pea long coat, daga ciki kuma tuxedo shirt ce mai bala'in kyau fara tas, ƙasa kuma blue jeans ne kalar pea coat ta sama. Ya shigo wajen, sai tashin kamshi yake yi kamar anyi ɓarin perfume a jikinsa, bakinsa a ɗauke da cikakken sallama, cikin nutsuwa ya shigo.

King and Uncle Jahiz har suna haɗe baki wajen amsa mashi sallamar. Sai a lokacin da ta gansa ne ma Akka ta tuna da dalilin da yasa ta kira su uncle Jahiz su zo, wannan yakin da aka yi yasa ta manta da dalilin, amma yanzu ma da ta tuna bata yi maganar ba, dan yanzu suna cikin tashin hankali na ɓatar Spender daga hannunsu, yanzu ta Spender take yi ba tsayawa wani shirirta ita da jikokinta ba.

Tun da ya shigo take ta aikin satar kallonsa, ya yi kyau sosai, da alama office zai tafi, shi kuwa da yake ba kunya ne garesa ba, tun da ya shigo idanunsa a kanta, sai kallonsa King and Uncle Abbas suke yi ko a jikinsa.

Kusa da uncle Jahiz ya zauna yana É—agawa King gaisuwa, bayan sun gaisa sai ya dagawa uncle Abbas sai uncle Jahiz, sannan ya gaida Akka, da yake tana cikin tashin hankali sai bata tsaya wasa da shi ba, kawai ta amsa gaisuwar a takaice. Ya yi tunanin ko dai gigin tsufarta ce yau ma ya tashi take share mutane, hakan yasa bai wani damu da ganinta so silent ba, ya cigaba da gaisawa da iyayensa.

Gabaɗaya jikokin nata sun sha madarar mamakin ganin yadda yau ta amsawa Yah Jawad gaisuwa kai tsaye kuma cikin sanyin murya ba tare da sun kai ruwa rana ba, abin da mamaki sosai gaskiya, a cikin jikokin nata kuma babu wanda yasan da batun ɓatar Spender, bama su san menene shi Spender ɗin ba.

Dannewa ya yi ya É—agawa su momma nasu gaisuwar, sannan suka yi musabaha da uncle Taheer.

Umarni ya yi wa kuyanga Zubaida a kan ta zuba mashi abinci da sauri dan zai fita ne.

Uncle Abbas ne ya ce. "Jawad ina Rizwan?."

"I think bai tashi ba daddy". Ya bada amsar yana É—auko spoon É—aya daga cikin waÉ—an da kuyanga Zubaida ta jeresu a wajen.

Cikin nutsuwa ya fara cin abinci, sai satar kallonsa take yi, shi kuwa tsaboda tsokana sai ya fara yi mata abin da ya saba yi mata idan suka zauna saman table, wato ya yi ta taɓa mata kafafunta da nasa kafar ta ƙasan table ɗin.

Duk abin da suke yi wlh King yana ganinsu tsab, kuma ya ci alwashin yin wani abin a kan hakan, jira yake yi su gama cin abinci zasu je su tattauna da uncle Abbas and uncle Jahiz a kan hakan, daga nan sai su yanke hukuncin da ta dace.

Sai da suka kammala cin abincin ne ya miƙe da nufin ya tafi office, dan sauri yake yi.

"Zauna ina da magana". Cewar King Zuhair.

Komawa ya yi ya zauna.

"GabaÉ—aya ku bani hankalinku a nan". Cewar King again.

GabaÉ—ayansu nutsuwa sosai suka yi, suka tattara mashi hankulansu haÉ—e da kallonsu a kansa.

Ɗan gyaran murya ya yi tare da gyara zamansa, cikin ƙasaita ta jinin sarautar haɗe da a dake ya fara magana kamar mai bada umarni.

"Sarina, Fanan and Aneesa ku shirya zuwa yamma zaku yi baki". Ya yi maganar idanunsa a kansu dan yaga reaction É—insu.

A fujaje Sarina ta zaro idanu, kamar zata yi kuka ta ce. "Dad baki kuma? To su waye?".

Fanan da Aneesa kuma kallon kallo suke fara yi wa juna haÉ—e da bin fuskokin iyayen nasu ma da kallo.

Cigaba da yin magana ya yi ba tare da kawar da kallonsa daga kansu ba.

"Na samu takarda daga masarautu daban daban a kanku, É—a ga sarkin Sudan ya turo mun sako yana neman wa É—ansa alfarmar a bashi dama yana son Sarina, a taron da aka yi jiya suka samu damar ganinku, so sun nemi alfarmar zuwa su haÉ—u da ku".

Ya É—an dakata da yin maganar yana kallon fuskokinsu gabaÉ—ayansu har da iyayensu mata.

Duk cikin room É—in face É—in mama, Mammie and uncle Jahiz ne kawai suka nuna alamar basu ji daÉ—in maganar ba. Shi uncle Jahiz abin da yasa bai ji daÉ—in hakan ba shi ne, a ganinsa an yi masu sauri, wai basu girma ba, Sarina almost 20 to 21 years take da shi a yanzu a duniya, amma haka yake cewa basu girma ba, dan kawai shi boko tafi arabiya yawa sosai a kansa, kuma shi girman cikin turawa ne ba larabawa ba sai yake ganin aibun hakan.

Ni kuwa nace to yau dai su Omaid basa nan waye zai taya Sarina koran wannan É—an sarkin da zai zo? Akwai matsala to! Za dai muga ya zasu kaya, dan dai da alama ba zata so shi ba tun da ta fara da complain tana É—aure fuska.

Cigaba ya yi da cewa. "Ƴaƴan sarakuna ne mabanbanta suka nuna sha'awarsu na son haɗa danganta da mu, sai dai sai da na zaɓi waɗan da suka dace ne na basu izinin su zo ku gansu su ganku ku tattauna a tsakaninku, dan haka sai ku shirya".

Dawo da kallonsa a kan Momma ya yi, ba tare da ya basu izinin yin magana ba ya É—aura da cewa. "Rahilarh kema fa aiki ya ganki sai ki shirya".

ÆŠan zaro mashi idanu ta yi tare da cewa. "Aikin kuma? To aikin me?".
Chapter 135 · 0% Book details