Sashe 147
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani irin sako aka turo mata ta nutsa ciki take ta aikin karantawa, abin ya bata mamaki kuma ya taɓata sosai, sai take ganin kamar wannan yarinman ne da ya nemi izinin neman aurenta dad yaki yarda, kamar shi ya turo mata da saƙon, dan taga saƙo ne na zallar madarar kalaman soyayya masu ratsa zuciya.
Gabaɗaya sai ta ji wani irin yanayi haɗe da nutsuwa ya ratsata, dik da bata son shi sai da ta ji sakon nasa ya yi matuƙar birgeta, ya zuba kalaman da zasu kwantar da hankalin mai karantawa, da alama ya iya tsara zance sosai, ga wani irin yaba kyanta na daban da ya rinƙa yi, addu'oi sosai ya rinƙa kwaranya mata.
My people's kun ga ta in da yarima zai ɓullo wa Autarmu kuma ko? Ko waye ya bashi numberta? Wai ana so dole ne ma?. Muje dai zuwa, kowa ya iya allonsa ya wanke, iya ruwa fidda kai! Ni dai ina gefe ina shan maltina mai sanyi!.
Yar tahaliƙar nan bata san lokacin da ta fara sakin murmushi tana karantawa ba, lokacin da ta zo karshen rubutun sam bata so ya kare ba, bata gaji da karanta yabonsa a gareta ba, ya tsara zance iya zance.
Haka kawai saboda daÉ—in kalamai sai ta tsinci kanta da yi mashi reply, mutumin da tana ji dad É—inta ya ce ya dakatar da shi daga zuwa in da take, amma sai ga shi tana yi mashi reply a what'sapp, har da murmushinta.
Aikuwa tana tura mashi reply tamkar jira yake yi ya sake maido mata da sakonni masu zafin gaske, kalamai masu zafi da suka fi na baya.
Tuni ta nutsa cikin karantasu, ya ja hankalinta matuƙa, sai surutunsa uncle Taheer yake yi bata ma san da yana yi ɗinba.
Idan muka waiwaya muma waiwayo gidansu Khadija kuwa.
__________________________🦋💘
GIDANSU KHADIJAH 😥 💔
Kwance take saman gadonsu ita kaɗai a cikin ɗakin, Zee bata nan, da alama akwai in da ta je ne. Ta yi nisa cikin barcin da take yi, ta kudundune a cikin bargo saboda sanyin safiyar, jiya da ruwan sama suka kwana, ruwa tamkar da bakin kwarya haka ya rinƙa zuba, kun san irin wannan barci na sanyin ruwan saman daɗi ne da shi ga nauyi.
Dan haka barcinta ya yi nauyi matuƙa, ga cikinta a yanzu ya kara girma sosai, ya bayyana, a cikin fari dai tamkar zata haihu yau ko gobe, sai dai cikin nata watansa bakwai ne, da sauran two months.
A hankali Hauwa ta turo kofar ɗakin nasu ta shigo, tafiya take yi tamkar sabuwar ɓarauniya, kamar bata son taƙa ƙasa, tana sanye da wani shegen hijabi har yana jan ƙasa na munafurci, ita fa Hauwa wlh ko takaba matar nan bata yi ba, baban Zainab yana rasuwa da sati biyu ta shiga yawon zawarcinta abinta.
Wai shin ina Sadiq? Ina hajiyarsa? Ina maman Haidar? Mu je dai zuwa.
Ɗakin nasu da ɗan duhu kasancewar dukkannin labulaye ɗakin a sake, haka ta rinƙa lallaɓawa a cikin wannan duhu ta nufi wajen drawers na gadon, Khadija tana ta barci bata sani ba.
Cikin sanÉ—o ta fara bubbuÉ—e drawers É—in, ko tsoro bata ji ba, bata fargabar Zee ta shigo ta kamata, haka ta bubbuÉ—esu dikka ta caje ko'ina a cikinsu tsab, sai dai bata ga jakar kuÉ—in ba.
Miƙewa ta yi ta koma wajen wardrobe ɗinsu, a hankali ta buɗe kofarta, sai dai ga mamakinta sai ta ga cikin wayam babu komai, ko ɗan'kwalinsu babu a ciki, ina suka kai kayan sakawar tasu kenan? Ta jefawa kanta tambaya.
Waigowa ta yi ta nufi wajen bayan gado, matar nan tsabar kwarin gwiwa har da hayewa saman bed ɗin ta leƙa ta baya ko Allah zai sa ta gani.
Wayam babu komai, saboda tsabar karfin hali har da saukowa ta nufi toilet dan ta duba ta gani.
Babu in da bata bincika a cikin toilet É—in nan ba, har da buÉ—e cikin wc tsabar kanta famko ne babu komai a ciki, tsab ta bincike ko'ina, ita fa bata tunanin ga wajen da ya dace ace abu makamancin haka ya kasance, idan ba rashin basira ba fisabilillahi me zai kai jaka cikin wc idan ba tunanin dabobi irin na Hauwa ba!.
Fitowa ta yi sumomoi sumomoi tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki, ta nufi hanyar fita daga cikin ɗakin, tamkar zata rusa ihu na rashin samun biyan buƙatarta.
Khadijah kuwa har lokacin bata farka ba, Allah sarki abin ku da barcin mai ciki.
Har ta kai bakin kofa zata fita kenan sai tunanin ta ji sun ce yau zasu tafi Kaduna ya faÉ—o mata a cikin ranta, cikin sauri ta juyo ta dawo cikin É—akin, tabbas ta ji suna hira daren jiya a kan yau zasu ta fi wajen kakarsu a Kd, to da yiwuwar shiyasa suka kwashe kayansu dake cikin wardrobe É—in dikka suka sanya a akwaiti kenan, to dik yadda aka yi wannan jakar kuÉ—in ma tana cikin akwatin.
Ai kuwa jin wannan tunani nata ya yi mata daÉ—i ne yasa taji tamkar ta kurma ihun daÉ—i, har da yar tsallenta, kamar har ta ga kuÉ—in ta gama take ji a ranta.
A hanzarce ta fara neman ta ina akwatin kayan nasu yake? Ta sake duba cikin wardrobe babu, ta duba wajen gado nan ma babu, nan take ta fara É—aure fuska dan ta ga alamar murna zai koma ciki, tsabar shegen son abin duniya har toilet sai da ta sake komawa ta duba, nan ma babu komai.
Kamar zata yi kuka ta nufi hanyar fita daga É—akin, har ta kai kusa da bakin kofa sai kuma ta juyo da sauri ta nufin gefen wardrobe É—in ta wajen jikin bango kusa da mirror.
Aikuwa tana zuwa ta isko jakar kuɗin a saman akwatinsu da suka gama shiryata tsab saura tafiya, bayin Allah sun shirya komai nasu tsab, jiran Zee kawai Khadija take yi ta dawo su tafi, ta je kwaso masu sauran wasu abubuwan da zasu buƙata ne a tsohon gidansu, shi ne Khadija ɗin ta ce bari ta ɗan kishingiɗa ta huta kafin ta zawo su wuce tasha in da zasu hau mota, shiyasa Hauwa ta tashi hankalinta sosai ta ƙasa hakuri har sai da ta shigo masu ɗaki neman kuɗin, dan tasan yau zasu tafi, idan suka tafi kuma shikenan ta rasa wannan kuɗi.
Wannan kuɗi na Khadija fa idan za'a canza shi a kuɗin Nigeria to ba za'ayi maganar millions of naira ba, sai dai billions of naira, da alama wanda ya bata wannan kuɗi a gaskiya yana ɗaya daga cikin manyan masu kuɗin kasarsu, kuma a haka take tunanin buga shari'a da shi ta ɓata mashi suna idan ta haihu! My people's thinks about that fa da kyau, mutumin da zai kwashi kuɗi makudai irin waɗan nan ya baka ai kasan ya wuci tunaninka, kuma a hakan fa kaɗan ya ɗan tsakura daga cikin dukiyar tasa ya bata, a haka zata ja da shi? Ni dai a ganina gaskiya Khadija zata yi ganganci in ta ce zata yi hakan, kuma wlh zata iya janyo matsalar da zai sa ta rasa ranta, kai bama ita kaɗai ba harta Zainab idan abin ya kwaɓe ba tsira zata yi ba! Ku dai duba mun wannan lamari fa.
Akwai matsala gaskiya, da ta yi hakuri ta barwa Allah komai, ko ba ji ma ko ba daÉ—e gaskiya zata yi halinta, domin kuwa Allah bai yi alkawarin tallafawa azzalumai ba, mu je dai zuwa.
Wani irin uban tsalle da ta daka tare da kware baki zata yi ihu ne sai ta tuna ashe a cikin É—akinsu take, jikinta na kerma ta kai hannu a kan jakar kuÉ—in, idanunta garau ta waro a kansa.
Mu koma baya kaɗan, kwanaki huɗu da suka wuce maman Haidar ta dawo Kano, dik ta rame ta kwanjame, tamkar ƙashi da rai haka ya zama, abin tausayi kuma shi ne har wa yau bata sami damar ganin Haidar ɗin ba. Wasu ma idan ta je wajensu cemata suke yi an kashe su Haidar ɗin ai, dan haka ta dai'na wahalar da kanta, an rufe babinsu yanzu ta koma gida.
Sam taki yarda Haidar ya mutu, tana ta shan wahalar bibiyar manya dan ta samu sahihin ainahin labarin in da yake ko da ba zata samu damar ganinsa ba. Yanzu haka karewan da kuɗin hannunta ya yi ne yasa ta dawo gida ba dan ta so ba, babu mai bata abinci bare abin sha, a ƙasan gada ma take kwana, ba ta da wata mafaka, ganin yunwa yana ƙoƙarin yi mata illah ne yasa ta gudu ta dawo domin ta ɗan harhaɗa wasu kuɗaɗen ta sake komawa.
Sai dai kuma tana dawowa ta iske mummunar labari na rasuwar mahaifiyarsu, aikuwa wani ihun da ta kurma ta yanke jiki ta faɗi ne har yau ba'a sake gane kanta ba, tana gadon asibiti tare da maman Hanif dake jinyarta, ko leƙa asibitin Hauwa bakar munafuka taki yi, kuma ko naira biyar taki basu su yi jinya, sai dai maman Hanif ɗin ce yar albarka take ta ɗawainiya, baiwar Allah ita ma ba karfi ne da ita ba, abinci ma da kyar suke iya samun cin sau biyu a rana, amma dik da hakan bai sa ta juyawa ƴan uwan nata baya ba, dik wanda ya shiga matsala dai ita ɗin ce kawai take tsaya mashi.
Wannan a takaice kenan abin da yake faruwa, su Khadija sun je asibitin har sau biyu suna dubata, a lokacin bata farfaɗo ba, yanzu da ta farfaɗo kuma ko magana bata iya yi, sai shiru kawai tana bin mutane da ido, sannan ta samu cutar mutuwar ɓarin jiki wato paralyze, ɓarin hagunta ya mutu gabaɗaya daga hannun har kafa, bata iya motsa shi, innalillahi wa inna ilahir rajiun, ya Allah mun tuba, mun tuba ya Allah, Allah ka rabamu da mummunar ƙaddara, kasa mufi karfin zuƙatanmu, ya Allah ka karemu daga zalintar wani da har alhakinsa zai bibiyemu, hasbunallahu wani'imal wakil. Kun ji abin da yake faruwa a halin yanzu, to mu koma kan labarinmu!.
STORY