← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 201 OF 211

Sashe 201

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matsawa kusa da ita sosai ya yi, ya É—aura hannunsa a saman waist É—inta ta baya, a hankali ya kwanto da kansa a saman shoulder É—inta, idanunsa a saman face É—inta babu ko kyaftawa.

Juyo da face É—inta ta yi saitin nasa, sai dai bata yarda sun haÉ—a idanu ba, sai ta É—an lumshe idanun nata tana satar kallonsa.

"My Noor ke karshe ce a kyau, kuma kin iya satar kallon mutun, sai aga kamar baki kallon abu". Ya faɗa can ƙasa ƙasa. Bata san yana kallonta tana satar kallonsa ba.

Zaro idanu waje ta yi, kafin ta yi magana sai ya rigata da cewa. "Ko dai so kike yi ki haifa mun yaro mai kama da nine da kullum kike aikin satar kallona?".

Kai ta gyaÉ—a mashi alamar e. Da sauri ya É—ago kan nasa daga saman shoulder É—in nata. "Noor da gaske kina son yaronmu ya yi kama da ni?". Ya faÉ—a cikin nutsuwa.

Kai ta sake gyaÉ—a mashi alamar e.

"No Noor, ki buÉ—i baki ki yi magana kin ji? Zan fi jin daÉ—in hakan".

"Ni Hamma kunyar yin magana nike ji". A ɗan shagwaɓe ta yi magana.

Hannayensa dikka biyu yasa ya tallafo kyawawan kumatunta. Ya zamana suna fuskantar juna, a hankali ya haÉ—e fuskokinsu, idanunsa a kanta ya ce. "Kina son mu haifi yara ko baki so?".

Idanunta a datse ta amsa da. "Ina so mu haifa".

Wani irin daddaÉ—ar ajiyar zuciya ya sauke, ga dikkan alamu ya ji daÉ—in amsar tata, ransa ta sanyaya sosai.

Cike da zumuÉ—i ya ce. "In Sha Allah nan ba da jimawa ba zamu haifa, zo mu koma gida ki yi mana abinci ko?"

Da to ta amsa mashi tare da saƙalo neck ɗinsa da hannayenta dikka biyu. Shi kuma ya kai hannayensa dikka biyu saman waist ɗinta ya dagota sama sai saman chest ɗinsa, da haka ya nufi hanyar fita daga cikin gonar.

"Hamma dan Allah ka saukeni zan tafi da kafafuna ka ji?".

Ba musu ya sauketa tare da riƙo hannunta suka fice. Suna fita ta shammacesa ta kwace hannunta daga riƙon da ya yi mata, da ɗan gudu ta yi gaba ta barosa a baya.

Binta da kallo kawai ya yi, ita a dole tana jin kunyar jerawa da shi su nufi gida, dan tasan zasu yi ta haÉ—uwa da iyaye da dattawan kauyen, shiyasa ta gudu abinta.

__________________________🤸

Tun daga nesa ta hango cincirindon yara a kusa da gidan nasu, kamar dai faÉ—a ake yi, sanin cewa Mahreen bata islamiya yasa ta yi saurin nufar wajen dan taga su wanene da kuma abin da yake faruwa suka taru haka a wajen.

Ai tun daga ɗan nesa ta tsinkayo muryar Mahreen tana zazzage kwandon masifa. Haba ai a miliyan ta ƙarisa wajen dan tun da ta ji muryar Mahreen tasan faɗa ake yi.

Aikuwa faɗa ake gwabza kamar ba gobe, Mahreen ta cire hijabin dake jikinta ta ɗaure shi a waist ɗinta, ta sha ɗamara kenan, kafafun nan nata sun yi futu futu da kuran ƙasa kamar wadda aka tono daga cikin rami, kayan jikinta a cukurkuɗe kamar wadda aka kwatota daga bakin kura, alamar andoku ne ba karya a wannan faɗa.

Ga wasu ƴan'matan da basu kai Mahnoor ba su biyu a kewaye da ita, sai wata yar yarinya da ba zata wuce kamarta ba tsaye a kusa da ƴan'matan tana kuka hawaye sharɓa sharɓa ga baki a kumbure kamar an naushi rubaɓɓen alala.
Suma waÉ—an nan Æ´an'mata biyun sun ci uwar É—amara kamar zasu tafi yakin duniya na uku, dik kayan jikinsu a cukurkuÉ—e, da alama da su fa ake gwabza wannan dambe.

Oh Allah mai iko, Mahreen gidan dirama, Mahreen duniya mai zaman kanta, Mahreen gidan rina idan ka taɓo ta sai ka sha arbi, kabewan kan kabari take bakincikin mai taushe, dik kafiyarka nan zaka ganta ka barta, yanzu banda neman bala'i fisabilillahi ina Mahreen ina faɗa da ƴan'mata har biyu? Ku gane mun hanya, da alamu kuma wlh ta jibgesu dukkansu biyu, dan sun ci wahala sai nishi sama sama suke yi suna haki, ita kuwa da Allah yasa ba kiba gareta ba sakayau take jin jikinta tamkar ta kwasa a juye ta tashi sama, su kuwa ba laifi suna da garin jiki.

A ruÉ—e Mahnoor ta ambaci sunanta tana zaro idanun, jikinta har kerma yake yi na ganin Æ´an'mata biyu sun kewaye mata kanwa, fatan ta kawai kada a dakar mata Æ´ar uwa, shi ne hankalinta ya tashi.

Tamkar Mahreen bata san da ita a wajen ba, ta cigaba da girgiza kugu tana wani bin Æ´an'matan da kallon uku goma, da yake dikka yara ne a wajen sai suke ihun. "Dik wanda ta fasa Allah ya tsine mata".

Mahreen kuwa da dama shi ne best abin da ta fi iyawa a rayuwarta wato faÉ—a, sai ta ji tsumin jikinta ya kara tashi da aka ce dik wanda ta fasa Allah ya tsine mata, dan haka nan take ta yi salle ta dire tare da buka kafarta a kasa, sannan cikin tsiwa ta ce. "Idan ba tsoro ba yarinya ta matso taga yadda zan gurji bakin shegiya".

Ni kuwa princess Teema nace ko wace ƙaddara ya haɗa waɗan nan ƴanmata da Mahreen? Ai kowa wace ƙaddara ce yau zasu gane annabi Isa ba ɗan Allah bane manzon Allah ne tun da suka faɗo hannun Mahreen, sai ta Allah kuma.

Dik cikin ƴan'matan babu wadda ta yi gigin matso Mahreen, da alama sun jibgu iya jibguwa ne yasa suke shakkarta a yanzu, kada su gudu ne dai a ishesu a kauyen da sunan sun ji tsoro, da wlh babu abin da zai hanasu cikawa zannuwansu iska, dan Mahreen ta basu tsoro, kamar wata mai karfin aljanu ta hau jibgarsu, kun san meyasa Mahreen take cin galaba a faɗa ne? To bari na baku sirrinta, saboda bata da kiba ne, da zarar sun fara faɗa da mutun zata daka tsalle kamar biranya ta haye saman shoulders ɗin mutun ta hau jibgarsa kamar me, wannan rashin kibar tata da iya daka tsalle yasa take more abokan faɗar tata............😂

Ganin babu wadda ta yi gigin matsota yasa ta sake buga kasa da Æ´an kafafunta ta ce. "Sun ji tsoro a basu kunun maÉ—aci su sha su yi wanke wanke, kuma na faÉ—a Æ´aÆ´an BoÉ—ejo bugaza kawai, in kun isa ku zo kuga ikon mai sama, wlh in murje yarinya a cikin kasa".

Yadda take masifar wlh sai ta baku dariya, dan tana yi dikan ilahirin jikinta yana motsawa, hannu na yi kafa nayi, ido da hanci dik suna yi.

Hasbunallahu wani'imal wakil, ko wacece BoÉ—ejo bogaza kuma? Kai Mahreen duniya, Æ´aÆ´anta sun ja mata zagi koma wacece.

Ma'anar bogaza dai irin mata masu kama da Hajiya two seater nan ne, wato masu kiba sosai kenan, shiyasa Æ´aÆ´an nata suke da garin jiki suma, Mahreen akwai iya shege, wato bogaza take ce mamar yaran.

A ruÉ—e baiwar Allah Mahnoor ta sake cewa.

"Ki yi wa Allah Mahreen ki rabuwa da faÉ—ar nan ki zo mu tafi gida".

Ai ina ko kallon in da Mahnoor É—in take bata yi ba bare ta tankata, cigaba da zazzaga masifa ta yi ba kama hannun yaro, ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, har da datse idanu ta yi yanzu kam, so take ta zugo yaran su matso ta kara jibgarsu kafin ta tafi gida.

Ita da ta kama yar mutane ta daka yayyunta sun biyo jin ba'asin me kanwarsu ta yi mata ta daketa sai ta haÉ—e da yayyun dik tana surfa masu surfen da nikar balainta, kuma fa wlh suna da manyan yayyun da tsab É—aya daga cikinsu zata iya yi mata dukan mutuwa, amma da yake tana da baki kuma bata da tsoro sai bata wani damu ba.

Abin da ya faru shi ne ta baro wajen bappa zata je gida kenan a daidai wajen ta haÉ—u da wannan karamar yarinya dake tsaye kusa da Æ´anmatan nan mai suna Bintu tana wucewa. Ke Bintu da neman bala'i kin san halin Mahreen sarai ba wai baki sani ba sai tsautsayi ya É—ebeta ta ce. "Ke Mahreen Æ´ar gidan Nenne mai siririn kafa ina zaki je?".

Aikuwa Mahreen bata bari maganar ya faɗi ƙasa ba ta amsa mata da. "Allah sarki Bintu ƴar gidan Boɗejo bogaza wajen ubanki malam Sani mai katon kafa zan je".

Nan fa Bintu ta ji zafin Mahreen ta zagar mata iyaye, shi ne ranta ya ɓaci, cikin fushi ta ce. "Iyayena fa ba abin wasanki bane Mahreen, banaso kada ki sake cewa mamana bogaza ko ki cewa babana mai katon kafa!".

Tana cigaba da tafiyarta bata ma tsaya ba ta ce. "Kai ashe iyayenki ne? Ai ni dik É—aukata daga sama suka faÉ—o". Cike da shakiyanci da iyashege ta yi maganar.

Hegiya Mahreen akwai mannin hauka yarinyar wlh, dik wani salo na faɗa da bakar magana ta iyasa, in faɗar cacan baki ne tsab zata yi nasara, haka zalika idan na duka da hannu ne ma, bata taɓa bari a taɓa lafiyar jikinta, idan kuna neman abin da zai ɗaga hankalin Mahreen to ku kawo mata batun taɓa lafiyar jikinta, ta tsani wannan kamar yadda ta tsani mutuwarta, amma ita kuma zata jibji ƴaƴan mutane fa.

"Mahreen wasa wasa ban da dungurar uwar miji da taɓarya, na gaya maki kada ki sake saka iyayena a cikin maganarmu". Bintu da karfin hali take, ita fa ta fara cewa Mahreen ƴar Nenne mai siririn kafa, amma take cewa kada a sako iyayenta a magana yau ga ikon god.

Dakatawa da tafiya Mahreen ta yi, sai da ta watsa mata kallon uku goma da waÉ—an nan idanun nata irin na bappanta sannan ta ce. "Wa ma kike da suna? BoÉ—ejo bogaza kike ko Bintu? To na faÉ—a malam Sani mai katon kafa, in kin isa ki kira wanda zai likeni ya mayar da ni ta bakin allura".

Cikin fusata Bintu ta amsa da. "Ni ma na faÉ—a Nenne mai siririn kafa kamar burugalin burga fura da nono........."
Chapter 201 · 0% Book details