← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 211

Sashe 83

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai fasa maganar ya yi, duk yadda ya kai ga kaunar Auta haka ya ja baki dan dole ya yi shiru a in da ya sanya kansa a ɗari ya nufi waje, yana tafiya cike da jarumta sosai. Ya kai dab da kofar fita room ɗin ya juyo ya kalli Momma, da yake shi da itan sai Allah kawai, da idanu ya yi mata magana alamar ta aiwatar da abin da ya sanya Yah Jawad, wato ta haɗa kan su Mummy su sauƙa kasan kenan, yasan ita kaɗai ce zata iya yin hakan, dan jaruma ce!!.

Waje ya nufa yana tunanin kala kala, kansa har sara mashi take yi a kan batun Auta, duk sai ya ji jikinsa ya mutu, ba dan ƙarar egwa da suke ji bama da a kan Zunaira zai fasa fita ya tafi nemanta, amma ba yadda zai yi, dole ya kaiwa jama'arsa ɗauki dan cikar tabbacin adalin sarki!!.

Haɗe kansu Momma ta yi suka nufi in da ya buƙata ɗin.

A ɓangaren Chuchu da Yah Jawad kuwa, dan dole Jawad ya goyata a bayansa ya shiga faɗa dan ya ceci rayuwarsu su rayu, dan kuwa mayaƙan Zarina sun bazu a cikin kingdom ɗin ta ko'ina, so yana tafiya dan neman hanya suna shan gabansa tare da kawo mashi hari, hakan yasa dole ya fafata ya kwace takwabin hannunsu dan cetan kansa. Kuka sosai chuchu take yi mashi, bata taɓa zaton yana da taurin zuciyar iya kashe mutun ba, dan kuwa ita a mai raunin zuciya take ganinsa, bata san ba haka abin yake ba, hmmmm ba'a shiga fili bane kawai, amma ai a yaran King ba rago, dukkansu masu iya ƙare kansu ne har ma su tsayawa wasu.

Tsabar fafatawa yaki har Jawad ya fita daga cikin masarautar ba tare da ya ankara ba, faÉ—a kawai yake........... Fatana dai Allah ya maku ikon kare kanku ku rayu!.

A ɓangaren Hoorain kuwa, tamkar zai yi hauka, ga Auta a gefe tana ƙara mashi ciwon kai ta hanyar kukan da take yi mashi na cewa ya mayar da ita wajen ƴan uwanta, tana son ganin Aunty Chuchunta, tun safe basu haɗu ba, wlh ba zata kara hakura ba kawai ya mayar da ita. Da kyar ya shawo kanta ta yi shiru.

Daga karshe bashi da zaɓin da ya wuce dole ya goyata su haura katanga, hakan ce kawai zata taimaka mashi, a lokacin kuma har an ci rabin yakin, ba karya a wannan karon waɗan can mayaka sun yi masu muguwar ɓarna, dama ance ba kullum ake kwana a gado ba, kullum su suke yin nasara, to yau dai sai shiru, dan kuwa ta kansu abin ya juye. Kum san ba ta yadda za'ayi ace kullum su suke nasara, ina hakan ba zai taɓa yiwuwa ba, akwai jarabawa da sauransu ai!!.

"Ranki ya daɗe ki hau bayana ki riƙe ni da kyau kin ji?". Ya faɗa yana sakin hannun nata da yake riƙe da shi. "Me zaka yi idan na hau bayan naka?". Cikin muryar kuka ta yi maganar.

"Hawa saman katanga zan yi mu dira ta baya tun da babu hanya". Zaro idanu waje sosai ta yi. "Hoorain ni tsoro nake ji, idan muka dira muka ji ciwo fa?........" Bata iya ƙarisa maganar ba saboda yadda ya ɗago idanu ya tsareta da kallo, ya kalleta ido cikin ido, hakan yasa dan dole ta yi shiru tana kallonsa.

ÆŠan kawar da kallonsa ya yi, a hankali ya ce. "Duk wanda zai yarda da ni a cikin kingdom É—in nan ina tunanin bayan Abbona babu wanda zai kai rabinki a yarda dani, amma meyasa a nan kike ganin kamar zan gaza?".
Shiru ta yi tana Æ´an kame kame, hakika ta yarda da shi fiye da tunaninku, tasan shi É—in jajirtatcene mai aiki da cikawa, amma haka kawai sai ta tsinci kanta da jin karayar zuciga a kan bin nasa su dira ta saman katanga, gani take yi kamar zata karye.

"Kina tunani akwai abin da zan iya bari ya cutar dake ne?".
Kai ta girgiza mashi alamar a'a.
"Ko kina tunanin zan iya wahalar da ke ce?". Nan ma kai ta girgiza mashi alamar a'a.

Tafin hannunsa ya buɗe tare da miƙo mata. "Trust me babu abin da zai faru In Sha Allah........". Ƴan hannunta ta ɗaura a saman nasan alamar ta yarda da shi, ta yi hakan tana ɗan murmushi fuska duk hawaye.

A dubu É—ari cikin tafasar jini ya É—agata sama tare da kaucewa gefe da ita, yana É—agata kifiyar da aka harbo da nufin a harbeta É—in ne ya wuce fiw da karfi ya caki itacen da yake bayansu. A dubu ya juyo yana kallon kifiyar kafin ya dawo da kallonsa a kan bujumin mayakin da yake tsaye a can É—an nesa da su. Tamkar a mafarki Hoorain É—in ya hangosa lokacin da ya ja kifiyarsa ya saita Zunairan zai harbeta, hakan yasa bai san lokacin da ya É—agata sama suka kauce ba!!.

Kafin su yi wani yunkuri mayaka ne suke tururuwar haurowa saman katangar wajen suka fara dirowa cikin gonar. Wani irin ɗaure fuska sosai ya yi, sauketa ƙasa ya yi, jikinsa har wani tsuma yake yi, ransa idan ya yi dubu ya ɓaci, dan kuwa tun da yaga mayaƙan har cikin gonar nan hakan na bashi tabbacin an cisu da yaki kenan? Abin ya yi bala'in ɗaga mashi hankali, tunaninsa ɗaya ina Abbonsa da ya yi saken hakan ta faru?.

Kewaye shi mayankan suka yi, a kallah sun kai su 20, gasu bujumaye da su, sun horo iya horuwa, tamkar wasu dodanni masu cin É—anyar namar É—an adam, sam basu da kyan gani, suna da muni sosai.

Tamkar ba zaƙaƙuran dodannin mayaka ne suka kewayesu ba, sam babu alamar tsoro a idanunsa, sai ma tafasa da jikin jikinsa yake yi mashi, jikinsa na tsuma, burinsa kawai su zo ya sauke zafin da zuciyarsa take yi mashi a kansu, dan shi gani ma yake waɗan nan ai ƙananan kwari ne, matsalarsa ɗaya Autace, ita ce zata iya sanyawa a ci nasara a kansa, da dai zata tsaya shiru a gefensa shi kuma zai tsaya mata da izinin Allah zai ceceta.

Gadan gadan mayakan suka tunkaresa, bayansa ya mayar da Auta tare da ce mata kada ta matsa daga in da take kome zai faru, sannan ta dubi girman Allah kada ta yi mashi kuka.
Ina tuni jikinta ya fara kerman tsoro, hawaye ta fara yi tun ma bai gama cewa kada ta yi kuka ba, tuni face ɗinta ya wanke da hawaye, haƙiƙa ta yi matukar tsorata da ganin waɗan nan dodannin, zufar tsoro ta fara haɗawa.

Bashi da mafitar da ya wuce ya kawar da kai kawai, hakan kuwa ya yi ya kawar da kansa yana ƙoƙarin ciro takwabinsa, dan waɗan nan dodannin ba zasu saurara mashi ba, hakan shi ma ba zai saurara masu ba.

Riƙo hannunsa da yake ƙoƙarin zaro takwabinsa dake manne a ƙugunsa ta yi tare da sanya mashi kuka tana faɗin tsoro take ji, dan Allah ya mayar da ita cikin gida, waɗan nan mutanen abin tsoro ne sosai...........

Bata idasa maganganun nata ba ɗaya daga cikin mayakan da suka iso ne yasa kafa ya take Hoorain ɗin a dai'dai shouldersa sai da ya tafi luuuuu ya kifa a ƙasa.

A wani irin ɗari ya ɗago kansa tare da buga ƙasa da hannunsa ɗaya kafin ya miƙe tsaye a kan ƙafafunsa. Nan take ransa ya kai kololuwa wajen ɓaci, har wani huci yake yi, zuciya na tafasa, har wani tashi tsikar jikinsa yake. Duk da bata taɓa ganin face ɗinsa a zahiri ba, bata san yana murmushi ko baya yi ba, bata san ya yake ba, amma a wannan lokacin sai da ya yi mugun bata tsoro, dan kuwa har idanunsa sai da suka yi wani irin sauyawa lokaci guda, jikinsa nan gabaɗaya wani irin kerma yake yi saboda ɓacin rai, ya zama tamkar zakin gaske kamar yadda Abbonsa yake kiransa, ashe zakin ne da gaske.

Zaro takwabin nasa ya yi, sabuwa dal da ita, tsabar kyallin da take yi har mutun ya kan iya kallon kansa a jikinta, gata da kaifin bala'i. Cikin nuna tsantsar jarumta ya nufosu, a dai'dai lokacin mayakin da ya taka shi ɗin ya sanya hannu zai kama Autar. Ai kuwa a tsananin fusace yana zuwa ya datse mashi hannun nasa daga saman wajen shoulder ɗinsa, pit hannun ta fita daga jikinsa, wage baki ya yi da wani irin katuwar murya ya kurma kururuwa mai saurin gaske, ga muryar nasa ƙato babu daɗin ji ko kaɗan, sautinsa mai doɗe sautin ji.

Haba ai a dubu sauran suka afka mashi da faɗa, fafatawa suka fara yi babu kama hannun yaro, sai ƙoƙarin kashe shi suke yi ko su kama shi, sai dai ya fisu sanin dabarun yaki, da alama su horon kawai aka basu ba'a koya masu dabarun yakin ba, gina masu jiki da horo kawai aka yi dan su razana zuƙatan mutane a gani da ido, sai dai ko a gani da idon ma basu razana zaki Hoorain ba kam, sai ma haushi da suka bashi suka sa ya ji tamkar zai haɗiyi zuciya saboda bakin ciki......... Auta kam ta gama tsorata a in da ta kame kam waje guda ta kasa motsawa, sai ruwan hawaye dake tsere a saman face ɗinta, tamkar wadda ta yi tsumar tsaye.

After some hours

Idan muka koma wajen su commander Zafar kuwa, haƙiƙa sun jigata sosai, sun wahala, commander ma baka iya ganesa, saboda jinin da ya wanke mashi jiki daga sama har ƙasa, fuskar nan tasa jinin jama'a ne kala kala da ya yi ta datsewa wuya, an kashe masu mayaka a kallah zasu kai 100, sannan wasu sun jigata sosai an rautasu.

Raga irin na kama zakin nan suka jefawa commander suka kama shi, dan kuwa sun kasa kama shi da hannu, shi ne kuma har yanzu yake da kuzari sosai a cikin mayaƙan, sannan shi ya tsaya tsayin daka a bakin gate na farko na kingdom ɗin ya hana kowa wucewa, shiyasa suke son kama shi dan su sami hanyar wucewa ciki su haɗu da sauran ƴan uwansu da suke ciki su ƙarisa kashe kowa a tunaninsu.
Chapter 83 · 0% Book details