← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 211

Sashe 152

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta É—an É—ago kanta, hannunsa É—aya yana ta bayanta yadda yake dan bubbugata a hankali, jama'a sai kallonsu suke suna mamaki, dan su dai sun san ba haka ake wannan al'adar ba, Jaish ya kawo masu sabon salo, komai sai ya canza da nasa salon, su fa amarya tana zaune saman kujera ango zai tsugunna a gabanta ya hau yi mata kwalliya babu mai taya shi suke yi, amma shi da yake nasa na daban ne amaryar har taya shi zata yi, abin nasu ya bada kala.

Powder ta ɗauko daga cikin kayan, kasa ƙasa yadda ko kawunta dake gefensu ma bai ji me take faɗa ba ta fara yi mashi bayani a kan me powder da yadda zai sanya mata.

Tana kai karshen maganar ta É—ago ido dan ta saci kallonsa, karaf suka haÉ—a idanu, dan ita yake kallo.

Da sauri ta yunƙura zata sunkuyar da kanta, ɗaura tray ɗin ya yi a saman cinyarta, sannan ya riƙo haɓarta da hannun nasa, ya ɗagota suna fuskantar juna, ya iyahi me jama'a zasu yi banda ihu, sun ga salon Jaish ɗin ma ya fi nasu bada kala............

Sosan powder ya É—auko da hannunsa dake saman bayanta, kurawa face É—inta idanu sosai ya yi, har wani irin yar ya ji a jikinsa, tsikar jikinsa gabaÉ—aya sai da ya tashi, ji ya yi kamar bashi da lafiya, amma haka ya daure ya fara shafa mata powder.

Tafi jama'a suka fara yi suna ihuuu alamar jin daÉ—i. KaÉ—an ya shafa mata, sannan ta nuna mashi yadda zai sanya mata kwalli.

ÆŠaukowa ya yi da nufin yasa mata, a wannan lokaci ya zamar mata dole ta buÉ—e idanu su kalli juna ido cikin ido dan ya iya saka mata.

Da kyar ta iya buɗe idanun nata, sai kuma me? Sai ga Mahnoor ta mace da kallon face ɗinsa, ta mance da kunya, shi ma macewa ya yi da kallonta, ya mance da cewa kwalli zai sanya mata, idanunsu suka sarƙafe juna...... Da alama waɗan nan ma'auratan sun afka duniyar sama jannati, waye ya ce soyayya karya ce? To koma me dai ina da Maltina ta mai sanyi ni dai🤔

(Sai dai matsalar angon baya cikin hayyacinsa, ko ya zai kasance idan ya dawo dai'dai?🤔 Shin zai karɓeta a matsayin mata ko a'a? Mu je dai zuwa, lokaci zai warware mana komai.)

Sun macewa kallon juna har sai da Mahreen ta ce masu. "Hamma ka saka mata kwallin mana, ni fa ina so ne ku gama ku haura saman dutsen nan mu kuma a saka mana waƙa mu cigaba da rawanmu har ku dawo, amma kun tsaya kuna ta wani kallon kanku, to ba kun san juna ba dama?".

Miƙewa shi kuma bappa ya yi ya bar wajen ma mai gabaɗaya, ya nufi gida abinsa, ya yafe murnar da za'ayi idan Jaish ya gama cike waɗan nan al'adun nasu, dama idan ango da amarya suka cike al'adun, akwai wata murna na musamman da iyayensu zasu yi dan ƴaƴansu sun cancaci zama a tare kenan, to shi dai ya yafe wannan murna, kunya tasa ya bar wajen da sauri.

Shi ma ArÉ—o dik da yake matsayin kakansu yau Jaish yasa kunya tasa ya bar wajen, da sauri, dikka manyan iyayen dake wajen sai da suka watse, dan kunya, su a yadda suke yin nasu al'adar ba wata soyayya da ango zai nuna bare har aje ga batun kallon juna da runguma, suna yin nasu ne tamkar dai yaya da kanwa haka amarya da angon zasu kasance, kawai shi ya zo ya goge masu hadda ya wani tsare yar mutane da ido, ai dole iyaye su matsa su basu waje.

Sai dai kuma da bappa ya tafi manyan dattawa ma suka tafi sai yan kallon suka fara tsoron Jaish É—in, su dama dan bappa suka tsaya, suna ganin kamar idan bappan yana nan ba abin da zai same su. Amma dai saboda tsabar soyayyar Jaish da salonsa ya burgesu sai basu gudu ba, suka tsaya ganin gulma.

Maganar Mahreen yasa ya farga tare da sauke ajiyar zuciya, a hankali ya kai tsinken kwallin cikin idanun nata, É—an kyaftasu ta yi saboda idanu basa son bako. ÆŠan tsuke fuskarsa kaÉ—an ya yi dan a tunaninsa ya ji mata ciwo ne yasa ta kyafta idanun, shi ne ya É—an tsuke fuska alamar sorry kenan.

Sosai ta ji daÉ—i yadda har alamar tausayinta ya bayyana a saman face É—insa kowa yana iya gane hakan, godiya ta yi wa Allah. Jumma uwar soyayya and lecture ai antashi kanta, Jaish ya goge mata hadda, tuni ta karisa wajen saurayin nata da shi ma yana wajen, ba ko kunya ta gaya mashi haka zasu yi a ranar nasu bikin.

Ni ko nace ai dama babu wanda ya kaiku iya iyashege idan kuka ga abin da ya yi dai'dai da ra'ayinku.

Cikin nutsuwa, salo mai jan hankali haɗe da kula da tausayawa ya sanya mata kwallin. Shi kansa sai da ya kara shagala da kallon idanun nata, yaki sakar mata haɓa, saboda kwallin ya kara fito da hasken idanun nata suka yi tas, ta ƙara kyau sosai.

Inna Rabi ma fa ta gudu, Jaish ya ja ta ji kunya ta ware, yanzu matasa ne kawai suka rage a wajen, yara sun gogewa iyayensu hadda, sun ja iyayen sun ji kunya sun gudu.

"Hamma saura janbaki fa". Ta faÉ—a tana rufe idanunta, dan kallon da yake yi mata ya yi mata yawa.

Yadda ta motsa lips ɗinta a kusa da shi sosai ta furta saura janbakin nan ba ƙaramin tafiya da imaninsa ta yi ba, sai ya dawo da kallonsa a kan ɗan bakin nata.

Mahreen dai sun fara shiga hakkinta, ita dai ayi a haura dutse su tafi a sakar mata kiÉ—a, kun san dama idan suka haura dutsen ma ba wacewa jama'a zasu yi ba, cigaba da bidirin bikin za'ayi ana abubuwa har sai sun dawo.

"Hamma ka saka mata jan bakin mana da wuri, sai kallon bakinta kake yi kamar zaka cinye shi". Cewar Mahreen sarkin azarɓaɗi, yarinyar nan taki bari soyayya ta kullu, ta saka masu idanu.

Hannu ya miƙawa amaryar tasa a kan ta bashi janbakin dan shi bai san me shi ba. Idanunta a rufe har sai da ya taɓa kumatunta sannan ta buɗesu, a hanzarce ta miƙo mashi janbakin.

Ai irin wannan al'adun ma ko mutun baya son yarinya in dai kyakkyawa ce sai ya fara sonta, bare ma idan ya zo yi mata kwalliya yana kallon face ɗin nan nata, ai dole ya afka duniyar lovayya, uhmmm dama ga Mahnoor da shegen kyau, Jaish ka shiga tarko, ni kuma princess Teema ba zan yarda ba, sai na raba wannan al'amari, dik wadda ta ji haushi ina gidanmu ta zo ta sameni.......🥱😂

A hankali ya buÉ—e janbakin ya fara goga mata a É—an lips É—in nata, dik sai ya nemi sukuninsa ya rasa, wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa ce take ratsa shi, bare ma idan ta É—an motsa lips É—in nata, dik sai ya rasa gane kansa.

Da kyar bawan Allahn nan ya iya ƙarisa saka wannan janbakin, ta yi kyau sosai, dan bai cika mata abubuwan a face ɗin nata ba, kaɗan kaɗan ya saka, ba'a taɓa yin amaryar da aka yi wa kwalliya mai kyan nata ba, kyanta ya ƙara bayyana.

Haba me zai faru? Ai tsalle Mahreen ta yi ta dire, ta ce allan baram daga yau Jaish ne zai rinƙa yi mata kwalliya, wato dama ya iya kenan ko? Shi ne baya yi mata.

Ita kanta Mahnoor É—in ta yi mamakin yadda ake ta yaban kwalliyar tata, Jumma sai santin hakan take ta yi.

Shi dai kawu Ibrahim kunya ta kusa nutsar da shi cikin ƙasa, ni kuwa nace ai wlh da Jaish yana ainahin Jaish ɗinsa, kuma yana son mace za'ayi wannan biki ai da bama zaku iya zuwa ba saboda kunyar da zaku sha na abin da zai yi. Yau da alama yaron Mommarsa ya mance da yana jin kunyar bappa ya wani tsare mashi ƴa da kallon kauna!.

In takaice maku labari haka ya miƙe ya saɓeta cak a saman shoulder ɗinsa, ya karɓi wutar torch light da kawu Ibrahim ya miƙo mashi.

Shi ana goyon amarya dan kar a gaji da wuri, shi kuwa yana ɗaukarta a saman shoulder ɗinsa, komai na al'adun nan sai da ya canza masu da nasa salon mai ƙayatarwa.

Dutsen ya rinkara gadan gadan, tana fa da tsawo da faÉ—in sosai dutsen, ga bishiyoyi da ciyayi sosai a sama, kun san haka duwatsu manyan nan suke, akwai bishiyoyi a kansu.

Haurawa ya farayi jama'a suna yi masu addu'ar adawo lafiya, ga mangariba ta fara kawo kai, ni kam nace Allah yasa ya ci angwancinsa a saman dutsen kafin ya sauko ba shikenan biki ya kare ba? Daga nan sai su wuce gida ya yi jinyarta, idan suka ga ya sauko sa ita bata da lafiya ai dole a dakatar da dik wasu tsarfa na al'adun nan a barshi ya wuce da ita gida, haba al'adu ne haka kala kala kamar ba gobe!! Ko ya kuka ce my people's? To mu dai bisu saman dutsen muga ya suke tafiya ato, dan mu sai mun leƙa komai dallah dallah!!......😂

Suna haurawa aka saki kiɗar nan nasu dai na yaren fillanci, habawa Mahreen ta ce ku bani waje, tuni ta afka cikin ƴan'mata da samari aka fara raƙashewa.

Su kuwa Jaish sun yi tafiya mai nisa kafin nan ya fuskanci lokacin sallar mangariba ta yi, da yake saman dutsen akwai ƴan ramukan da zaku tarar da ruwan sama da ya taru a cikinsu, sai ya sauketa kasan wani bishiya da nufin ya ɗauro alwala ya yi sallah, ya kunna wutar tocin da suka bashi ya miƙa mata a kan ta zauna ta jirasa bari ya yi alwala ya zo.

Ga garin akwai hadari sosai alamar ruwan sama za'ayi, da rabon ruwa zai yi wa wasu duka.

"Hamma nima zan bika na yi alwalar!". Ta faÉ—a a sanyaye.

Da yake safiya a saman dutsen sai anbi a hankali, idan ba haka ba in mutun ya yi garaje ƙasa zai faɗa, sai ya miƙa mata hannunsa a kan ta zo ya riƙeta su tafi a hankali, dan kada ta je ta faɗi ƙasa.
Chapter 152 · 0% Book details