← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 211

Sashe 86

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥

25

A guje matasan wajen suka watse yau aljani ya mari wani ya suma.

Kan kace me zance ya baza kauye ai aljanin gidansu Mahreen ya mari yaron Inna Rabi ya suma, abin ku da kauye nan take suka canza mashi suna daga aljani zuwa maye, dama can kun san ba yarda da shi suka yi ba, to ga abu kuma ya zo ya faru, kun san kauye da iya champa abu, take suka champa shi (champi), sai dai kuma duk kauyen babu mai iya tinkarar Jaish É—in ya ce mashi ya bar garin ko wani abin makamancin hakan, dan tsoronsa suke ji, sai gangami ake yi ana kaiwa ArÉ—o complain a kan shi a matsayinsa na ArÉ—on kauyen ya É—aukar masu mataki a kan Jaish, su sun kasa.

Shi kuwa Jaish ɗin bai sauke Mahreen a ko'ina ba sai a tsakar gidan nasu, sai dai kafin ya sauketa sai da ta taɓa mashi gashin kansa, dan ta jima ita da Mahnoor suna gulmar arab hairn nan nasa, suka ce ba gashi bane, to yau da ya ɗauketa sai da ta taɓa ta tabbatar gashi ne, kyallin da gashin yake yi ga shi bakin kirin da shi ne yasa suke ganin kamar ba gashi irin na mutane bane da shi, Mahreen kam da hankali ya yi mata yawa ma har da cewa ai roba ce ba gashi ba, Mahnoor kuwa ta ce a'a gashi ne amma ba irin na mutane ba, na aljanu ne, to yau dai ta taɓa ta ji bana aljanu bane na mutane ne.

Ɗakin bappa ya shige bayan ya sauƙeta, binsa da kallo ta yi har ya ƙarisa shigewa ciki, ajiyar zuciya ta sauƙe, wasa wasa fa ita Mahreen ta fara son shi, tun asali kun san dama tana sonsa, lokacin da kowa yake gudunsa ya ce aljani ne a lokacin ita da bappa kawai suke kusantarsa, kunga kuwa idan tace tana sonsa ma bata yi laifi ba!.

Bappa kuwa da yake dattijon arziki ne sai da ya kira matasan da suka watse É—in ya sanyasu suka kama yaron Inna Rabin suka nufi gida da shi.
Da kafafunsa kuma ya taka izuwa gidan Inna Rabin dan ya bata hakuri, idan kuka lura da yanayin bappa zaku ga shi mutun ne mai son zaman lafiya, baya son yin hayaniya da kowa, haka zalika baya son ɓatawa kowa rai, shiyasa baya ganin cewa shi babba ne yake bawa kowa hakuri, har yara matasa ya kan basu hakuri idan suna faɗa, shi bai ɗauki bada hakuri a bakin komai ba face tubali ko ace makulli na zaman lafiya.

Da kyar ya iya shawo kan Inna Rabi ta yi shiru, da kuka take ta yi, dan tana tsoron Jaish É—in ita ma.

Allah da ikonsa kuwa tun marin da Jaish É—in ya yi wa yaron sai Allah ya rabbeshi da wani irin ciwon ciki mai tsanani wanda yasa jama'ar kauyen suka kara tabbatarwa da cewa Jaish fa mayen gaske ne, hakan yasa suka fara shirya ta yadda zasu koresa daga garin, sai dai suna tsoro, Allah ya bawa yaran Momma kwarjini sosai, komai zafin da ka É—ebo da nufin ka yi masu faÉ—a ko ka ga ya masu sun yi maka ba dai'dai ba, to kuna haÉ—a ido ko kana ganinsa zaka ji ina ka kasa, duk sai ka nemi kalaman bakinka ka rasa, wasu irin su Mama gani suke yi tamkar asiri Momma ta yi wa Æ´aÆ´an nata suka kasance a haka, bata san daga Allah bane kwarjinin nasu.

Ai Nennen da ta ji wannan labari haukacewa ne kawai bata yi ba, ta ce wlh ba zata koma gidan bappa ba, dan ita bata shirya mutuwa ba, haka kawai ta je Jaish maye ya cinyeta, wlh ba zata saƙu ba, shi kansa Arɗo mahaifin nata cewa ya yi ya fara tsoron Jaish gaskiya, dole su bulbula hayakin mayu a kauyen, gobe za'ayi gayya na jama'ar kauyen dukka izuwa kofar gidan Arɗon, dan shi ne Arɗon kauyen gabaɗaya, kamar ace sarkin kauyen kenan gabaɗaya, to Arɗon ya sanya sanarwa gobe da yamma kowa ya hallara a kofar gidansa, dole za'ayi turaren mayu, duk kuma mayen da aka kama wlh kashe shi za'ayi.

Yadda Arɗon ya rinƙa nanatawa bappan kwairaga a kan lallai ya tattare gabaɗaya jama'ar gidansa ya zo da su ne yasa Bappan ya fara tunanin ko dai Arɗo ma ya yarda da maganganun ƴan kauye ne da suke zancen cewa Jaish maye ne?.
Da yake bappan mutun ne mai ɗan wayewa saboda tafiye tafiyen da yake yi kasashen daban daban, shiyasa bai yarda da duk abin da suke faɗa ba, dan kuwa yasan da Jaish maye ne ko wani mugun to da shi zai fara cutarwa, dan a ɗaki ɗaya suke kwana, su wuni a daji wajen kiwo tare ba abin da yake yi mashi, sai ma tallafa mashi sosai da yake yi, dan ko jiya da suna wajen kiwo bappan yana zaune a ƙarƙashin bishiya wata kunama ta zo kusa da shi ba tare da ya sani ba, saura kaɗan ta harbesa Jaish ya ganta, da hannunsa yasa ya kamata ta harbesa a hannu, bappan ya sanya mashi maganinta, to da shi mugu ne ko mayen da suke faɗa da ba zai taimakesa daga harbin kunama ba, sai dai ma ya kara mashi wasu kunamun, amma da yake su kauye sai a hankali akwai karanci wayewa ga karanci addini shiyasa.

Ai Nenne dai ta koma gidan ArÉ—o da zama, ta ce wlh sai randa Jaish ya bar gidan zata dawo. ArÉ—o fa mutun ne mai zafi sosai, amma a wannan karon dole ya hakura ya bar Nennen a gidansa ta cigaba da zama, dan kuwa gwaggo ta hayayyako mashi da ruwan bala'i a kan Æ´arta ba zata koma gidan bappa maye ya lashe mata kurwa ba, idan ana son ta koma É—akinta dole mayen nan ya bar gidan.

Yaron Inna Rabi dai tun daga aka kaisa gida cikinsa ke matsanancin ciwo tamkar ba zai rayu ba, idan cikin ta wani irin murɗa mashi har wani irin sandarewa yake yi yana miƙewa kamar ransa ta zo fita, abin gwanin ban tausayi, sai kuka Innar take yi baiwar Allah.

Da daddare misalin karfe 9 suna zaune a tsakar gida da bappa da Jaish a saman tabarmar da Mahnoor ta shinfiɗa masu, abinci ta kawo masu, yau dai Jaish ya nunawa bappa alamar baya son cin nama, bappan ya ce mashi to me zai ci, ko dai zai iya cin irin abincinsu ne?. Hakika bappa ya ga ƙoƙarinsa ma na juriyar cin nama na tsawon lokaci haka da ya yi, dan ma dai bai da yawan ci ne, bai wani cin abincin rana, wata rana ma sau ɗaya yake cin abinci a rana, shiyasa namar ma bata yi saurin ginsarsa ba.

Cikin harshen larabci bappa ya tambayesa me zai ci?. Shiru ya yi kansa a ƙasa, baya yarda ya kalli face ɗin bappan a lokacin da yake kallonsa, sai ya kauce, idan ya kauce kuma sai ya yi ta kallonsa yana jinjinawa kyawawan halayensa da tarin alkairansa, da zarar ya juyo da kallonsa a kansa kuma zai yi maza ya kawar da nasa kallon, abin ma wani lokaci gwanin ban dariya.

Shiru ya yi bai amsa ba. A karo na biyu bappan ya sake tambayarsa me zai ci? Kai ya É—an girgiza alamar shi ba zai ci komai ba.

"A'a ban yarda ba dole ka ci wani abin, da safema fa kaki cin komai, kai haka zaka yi ta horar da kanka da yunwa?". Cewar bappa.

Ƙara yin ƙasa da kansa ya yi ba tare da ya yi magana ba. Miƙewa bappan ya yi yana faɗin. "Akwai wata kauye a gabanmu can su suna da shago, bari na je na duba maka ko suna da fanta da bread ne na saya maka sai ka sha". Kunsan fulani da kallon darajar bread and fanta...........🤣 (To fulani masu karanta book nan ayi hakuri amma gaskiya na faɗa, kuna daraja bread and fanta 🤣💃🤸)

Miƙewa shi ma Jaish ɗin ya yi tare da nunawa bappan alamar a'a kada ya fita, shi ba zai ci komai ba, a daren nan ya tafi har wata kauye kai gaskiya a'a ya barshi kawai.

"A'a ka bari na sayo maka, dan ba zan iya barinka da yunwa ba, kai bakona ne, dole na kula da kai, kamar yadda ba zan iya barin su Mahreen su kwana da yunwa ba haka kai ma ba zan iya barinka da yunwa ba, dan haka ka zauna dai bari na zo".

Rike hannunsa Jaish ɗin ya yi ya shiga nuna mashi alamar a'a shi dai bai yarda ba, ya yi hakuri ya bari shi baya jin yunwa. Kuma haƙiƙa yana jin yunwar, kawai baya son wahalar da dattijon nan ne, saboda yana hidima da su sosai, ya gaji da cin nama, ga shi babu wani abincin, tunani yake yi a cikin ransa ko dan ya faranta ran bawan Allah nan bappa, ya rage masa wahala dole ya koyi cin irin abincinsu ko da fura da nono ne kawai, idan ba haka ba wahalar da bappan da yake yi ta yi yawa, kullum sati sai an yanka mashi kaji guda goma, ai abin ta yi yawa, shi bai taɓa tunanin akwai irin dattijawan arziki irin bappa na, gaskiya mutum ne mai farar zuciya sosai.

Da kyar bappan ya yarda ya koma ya zauna. Mahreen and Mahnoor ne suka fito daga nasu ɗakin suka ɗauki abincinsu, a kusa da bappan suka zauna dan su ci. Sai leƙen Jaish Mahreen take yi, ga hasken wata tankar tana haska shi, ya sunkuyar da kai tamkar mai tunanin wani abin ko kuma mai ɗaukar darasin karatu.
Chapter 86 · 0% Book details