Sashe 27
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Hajiyarsu Sadiq da ta ji haka ta bincika kuma ta gane hakan sai ta ce da Mmn Zainab maza maza ta kama kanta, ta yi maza ta fita harkar Hauwa dan ba kawar zama bace, duk mace mai kwaÉ—ayi da rokon maza da mata abu to tabbas tana gab da jefa kanta ga halaka, dan kuwa kwaÉ—ayinta zai kaita ya barota.
Da Hauwa ta biyo mata zuwa Islamiya Sadiq da kansa ya kora mata jawabin kada ta sake zuwa gidan, kuma kada ta sake ko É—aga idanu taga maman Zainab, kowa ta yi rayuwarta, ta so ta masa rashin kunya ta zage shi, sai Hajiyarsu ta taka mata birki ta kara mata da bayanin ko sannu kada ya kara haÉ—ata da maman Zainab basu so, kowacce ta bi nata layin.
Abin ya baƙanta mata rai sosai, already dama ita Hajiyar tasu tasan yaran gidansu Hauwa ba yaran kirki bane, uban nasu ne wato kanin baban Hauwa shi ne mutumin banza maras zuciya da kwaɗayin abin duniya, shi ne ya koyawa yaran kwaɗayi da roƙo yana zaune su ciyar mashi da gida, har tutiya yake yi ya haifi jari, ɗiyar arziki su suka riƙe mashi gida. Coz Hajiyarsu tasan da wannan, amma da taga Hauwa na zuwa makaranta har da Islamiya sai ta yi tunanin to kila ita ta fita zakka a cikinsu, ashe kuwa duk kanwar ja ce bata sani ba, shiyasa bata ɓata lokacinta wajen cewa zata yi wa Hauwar nasiha ba kawai ta yanke hukuncin rabata da ƴarta, dan tasan duk gidansu haka suke ba kamun kai ga ɗan banzar rashin kunya da rena manya, komai girman babba ya yi masu zage shi fes zasu yi babu ruwansu.
To a takaice a haka aka raba maman Zainab da Hauwa, bayan kamar sati biyu suka sake jonewa, sai dai basu bari an gane suna tare ba, suna kawancen ne kawai daga islamiya sai school, a cikin unguwa basu taɓa nuna kamar sun san juna, ko sannu basu yi wa juna. A haka suka cigaba da yin rayuwa har lokacin da aka zo neman auren Hauwa, wani bakano da ya zo biki a garin Kaduna, a unguwar su Maman Zainab ɗin za'a ɗauki amaryar a kaita Kano, so Hauwa tana cikin kawayen amarya, a nan dai suka haɗu da mijin nata har ta kawo shi gida, aka yi abin da za'ayi, a lokacin mijin nata yana ji da ɗan dukiyarsa dai'dai gwargwado, shiyasa ta yarda ta amince ta aure shi ya tafi da ita Kano, amma a lokacin sun kammala secondary sai dai babu abin da Hauwa kam ta iya in ba satar amsar ƴa'ƴan jama'a ba, dama ita fa ba karatu take zuwa ba, yawon neman samari take fita ato, kuɗin makarantar ma daman yayan mamanta yake biya mata ba bappan nata da ya riƙeta ba, shi yaransa ai basa makaranta, Hauwar ce kawai ta shiga makaranta a cikinsu.
In short bayan aure Hauwa da kamar wata biyar baban Zainab ya zo wajen wani abokinsa a Kaduna, a hanya suka haÉ—u da maman Zainab ta je wajen kanwar mamarta tana dawowa, ta tsaya a bakin hanya zata nemi abin hawa dan ta dawo gida, a nan ya ganta, sai dai bai tare ta a hanya ba, ya bi bayanta shi da abokin nasa, abokin nasa yana da mota, so basu yi mata magana ba ta hau abin hawa suka bi bayanta har sai da ta shiga gida.
Da ta shiga gida sai suka yi sallama da babanta, Sadiq baya nan lokacin sai Hajiyarsu ta sanya katuwar hijabi ta fito, a takaice suka faɗi abin da ya kawo su, ganin irin abin da suka yi yasa Hajiyar tasu ta fahimci lallai lallai baban Zainab yana da hankali da kuma ilimi, kuma ya cancanci a bashi aure, saboda alama ya nuna shi ba wasa ya zo yi ba, da wasa ne ba zai nemi gidansu ko iyayenta ba, ita kai tsaye zai tara, amma ya biyota gida, bayan ya biyota gidan ma bai dakatar da ita ba ya nemi ganin babanta, lallai ba shakka yana da hankali sosai. Hakan yasa ta ce mashi ya yi hakuri ya dawo gobe, dama a ranar zai koma Kano, ai kuwa ya ce ina kwana Kaduna ta kara kama shi, kun san kanawa da son fararen mata (😅) ya kuwa ce dole ya jira amsar Hajiyarsu.
Ita kuwa ta ce mashi haka ne dan tana son su yi maganar da ƴaƴan nata barema Sadiq da yake da hankali sosai, ƙaramin yaro ne a lokacin amma akwai hankalin manya sosai kamar wan da ya girma a cikin dattijawa.
In takaice maku labari wannan shi ne sanadiyar aure baban Zainab da maman Zainab bayan anyi bincike da komai da komai. Baban Zainab ya sha jigila tsakanin Kano da Kaduna yana zuwa hira.
Lokacin da aka yi auren su maman Haidar kamar su cinyeta saboda so, ko kwatancen haske fata suke yi a magana to da nata fatar suke kwatantawa, suna bala'in sonta barema Hajiyarsu da ta É—auketa kamar Æ´arta, suna zaman lafiya da kaunar juna haÉ—e da girmama juna, ganin mutuncin juna.
Rana tsaka kawai Maman Zainab da jajuɓowa kanta wahala ta nemo number Hauwa ta hannun wata kawarsu ta Islamiya, ta kirata ta sanar da ita ai ita ma a Kano ta yi aure, yadda kuka san Hauwa ta shanye mata kurwa.
Haba Hauwa kam bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen karɓar address ta ce gobe gata nan zuwa. Wannan shi ne musabbabin sake haɗuwarsu a Kano, suka cigaba da kawance, Hajiyarsu maman Zainab bata sani ba, Sadiq bakinciki ta isheshi kamar ya kashe Hauwa, amma haka ya danne, kuma bai gayawa Hajiyar tasu ba, dan shi tun ainahi ba mutun ne mai faɗar duk abin da ya gani ba, baya son gutsiri tsomi, yana da kawar da kai a kan abubuwa ba komai yake nacewa ba.
Lokacin da baban Zainab ya sanya Sadiq ɗin a school daga nan ne Hauwa ta fara jin wani iri a ranta, dan kuwa mijinta ko naira baya bawa kannenta, zasu taso daga Kaduna su zo wajenta ko kuɗin motar komawa baya basu, ta yi mashi ƙorafi har ta gaji ta hakura.
Baban Zainab tun da suka yi aure da maman Zainab arzikinsa sai kara bunƙasa yake yi, da farko ƙaramin makaranta ya sanya Sadiq, daga baya ya ɗauko Haidar ya haɗasu.
Bayan an haifi Khadija da Zainab ya canza masu Sadiq É—in makaranta zuwa ta Æ´aÆ´an masu kuÉ—i, nan fa Hauwa hankalinta ya tashi, abinku da mai kwaÉ—ayi, mai hali baya fasawa, ga maman Zainab da iya bata labarin abin kyautatawa da baban Zainab yake yi masu sannan yake turawa Hajiyarsu ma Kaduna. Hauwa zuciya ta yi bakinkirin kamar gawayi saboda haushi ita ba'ayi mata mai kyau ma bare ayi wa danginta. Ita kuwa maman Zainab tana gaya mata wai dan ta tayata murna ta samu miji na gari, bata san hasada take yi mata ba.
A haka dai suka cigaba da tafiya, Hauwa fa taga ba zata iya jurewa ba hasada zai kasheta, nan ta bazama ta fara nemanwa kanta mafita, to a wannan gaɓar ne ta haɗu da wata kawar banza ta jefata bin bokaye, farkon abin da ta fara yi ta mallake mijinta ta rufewa danginsa baki a kanta. Tana mallakesa ta fara kwasan kuɗinsa ta shiga harkar dillanci, duk tana rame tana bushe, Maman Zainab kuwa ko'ina a cike ɓul ɓul gwanin sha'awa.
Bayan ta kwashi kuÉ—insa ta bi sahun dillalai sai ta sake kwasan dubu É—ari biyu nasa ta koma wajen boka dan a shiga tsakanin maman Zainab da dangin mijinta da mijin nata gabaÉ—aya, a lokacin asirin ya ki kama baban Zainab, sai dai su maman Haidar, ta raba maman Zainab É—in da dangin mijin nata, su maman Haidar suka dawo basu kaunarta, su da a baya kamar su cinyeta saboda so, amma suka zama basu kaunar ganinta sam sam, aka rasa daga ina matsalar take, ashe Hauwa ce ta hassasa komai. Wannan shi ne farkon shiga matsalar maman Zainab kenan a rayuwarta, amma ta cigaba da hakuri har duk abin da ya faru ya faru.
A takaice kenan abubuwan da suka faru a baya, nasan zaku fahimta duk da in short na baku labarin, idan zaku lura a rubutuna ban cika tsawaita bada labarin baya ba, zan dai yi maku yadda zaku fahimta, amma bana son dogon labari a kan abin da ya wuce, ayi wanda ake yi a yanzu, dan ban son ɓata lokaci. Coz yanzu nasan kun fahimci labarin maman Zainab ko?.