← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 211

Sashe 160

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar ba zai tanka mata ba saboda ɓacin ran da yake ciki, sai kuma yaga rashin dacewar amsa mata da yake ƙoƙarin kin yi ɗin, hakan yasa ya danne ba tare da ya juyo ya sake kallon in da take ba ya yunƙura zai buɗe baki ya amsa kenan muryar uncle Taheer ta katse shi da cewa.

"To ina ruwanki da shi da zaki nemi ganinsa? Har da cewa tun safe baki ganshi ba! To me zaki bashi idan kin ganshi ɗin?". Ya yi maganar da alama ransa a matuƙar ɓace shi ma, kamar dai kishi shi ma yake yi dan ta tambayi ina Hoorain ya shiga tun safe.

Jin wannan magana na uncle Taheer É—in ne yasa ya fasa amsa maganar tata, sai ma ya nufi hanyar barin wajen.

A takaice ta ce. "Hoorain ka dakata ka ji". Ta kai karshen maganar tare da juyowa ga uncle Taheer da yake ta kallon face ɗinta cike da jin haushin kula mayaki ƙasƙantace mai bata kariya da take yi, amma fa a cewarsa ne Hoorain ƙasƙantacen bawa ne mai bata kariya, sam bai ɗauke shi da wata daraja ba, bai san cewa idan ba dan su Hoorain ɗin ba shi kansa kingdom ɗin ba zata zaunun mashi ba, da ayake yaken da ake yi ai da an jima da kashe shi, su Hoorain ai sune jarumai, kowa a kingdom ɗin nan da bazarsu yake taka rawa, sune ainahin mazajen.

"Uncle Taheer dole zan tambayesa ina yaje mana yau tun safe, kada ka manta fa kula da ni yake yi, meyasa ni ma ba zan kula da shi in damu idan ban ji motsinsa ba?............"

Tun time ɗin da ta ce ya dakata ya dakata da tafiyar kamar yadda ta buƙata, sai dai yaki juyowa ya kalli in da suke, sai ya juya gefe guda.

"Katseta uncle Taheer ya yi da cewa. "Baby yana da kyau ki san cewa ke fa daban kike da su, akan me zaki nemi sanin ko yana lafiya? Kin manta karen farauta ne shi ɗin? Baki da wata hujja na neman sanin ya lafiyarsa take!!". Cikin ɓacin rai sosai ya yi maganar.

"No uncle Taheer, ba haka bane gaskiya, dikkan mutane abu guda ne, da ni da shi dik ɗaya ne a wajen Allah, babu wani bawa da Allah ya ƙaskantar ko ya wulakanta, dikkan bayin Allan masu daraja ne, wanda Allah zai fiso kuma shi ne wanda yafi jin tsoronsa, bani da wani banbanci da Hoorain, kuma yana kyautata mun dole ni ma na............".

"Ki mun shiru!!".
Tsawan da ya daka mata ne yasa ta haɗiye sauran maganganun nata ba tare da ta ƙarisa amayar da su ba, dan ta ɗan tsorata gaskiyar.

"Ranki ya daÉ—e zan iya tafiya?". Cewar Hoorain da takaici ya gama cika mashi cikinsa, so yake yi kawai ya bar wajen, dan yasan idan ya tsaya tsab zai iya sumar da uncle Taheer É—in nan, so gara mashi ya tafi, sai dai ba zai yiwu ya tafi ba tare da ta bashi izini ba, dole ya jira izininta koma me zai faru ya faru.

Allah sarki shi dai kam Ansar sai binsu da ido yake yi yana mamakin hali irin na Hoorain, tunani yake yi da shi ne ya samu wannan dama da har Gimbiya mafi soyuwa a cikin kingdom É—in take damuwa da shi har haka ai da ya more ya kuma saki jiki, amma shi Hoorain ya samu dama yana wasa da ita.

"A'a Hoorain kada ka tafi, ina son yin magana da kai". Ta faÉ—a a tsorace, tana kuma É—agowa ta saci kallon uncle Taheer wanda ya gama zuwa wuya da takaici, kishi kamar zata kashe shi.

Cikin tsawa haÉ—e da bada umarni uncle Taheer ya ce da Hoorain É—in. "Daga yau na haramta maka sake yi mata magana! Sannan na soke bata gariya da kake yi! Na haramta maka É—aga idanu ka sake kallonta! Kada ka yarda ku sake haÉ—a hanya da ita, ka wuce ka bani waje yanzun nan bana son sake ganin ko mai kama da kai!".

Kamar zata yi kuka ta ce. "Uncle Taheer a kan............" Bata iya ƙarisa maganar ba sabo wani irin fusata da ya yi har bai san lokacin da ya cire hannu zai dallah mata mari ba.

Aikuwa kamar wani walkiya haka Hoorain ya iso wajen ya riƙe hannun nasa ya hanasa sauke mata marin, shi a dole ransa ya ɓaci yana kuma kishi har da ƙoƙarin kai mata mari.

Ta datse idanu tana jiran saukar marin, sai ta ji shiru, tuni jaruminmu Hoorain ya riƙe hannun nasa. Ƙoƙarin kwace hannun nasa ya fara yi, amma ina ya kasa, da hannu ɗaya kuma Hoorain ɗin ya riƙesa amma ya gaza kwatar kansa.

A hankali ta waro idanun nata dan taga ya aka yi marin bai sauka a kumatunta ba. Ai bata san lokacin da ta saki cool ajiyar zuciya ba, wani irin sanyi ta ji a ranta na ganin jaruminta ya tare mata faÉ—a, dama tasan da wuya idan yana wajen ya bari ayi mata wani abin, sai dai idan Jaish ne zai daketa, wanna babu yadda ya iya dole ya kawar da kansa, amma irin su uncle Taheer gaskiya ba zai bari ba, idan sun daketa a cikin gida wannan fine bai gani ba, amma a wajen kam a'a gaskiya.

"Ka sakar mun hanu!". Ya faÉ—a cikin tsawa, dan ya kasa iya kwatar kansa, shi ne zai nuna mashi jan ido ya sakesa.

Calmly haÉ—e da kwamciyar hankali ya furta.
"Zaka iya kwatar hannun naka ai!".

Zaro idanu sosai Ansar ya yi, ya tsorata na ganin Hoorain ya mayarwa da É—an cikin family amsa, tashin hankali. Ita kam Auta ranta fes abinta, dan Hoorain take so ba Uncle Taheer ba!.

"Ba zan daina kula da ita ba har sai ranar da mai girma King ya faɗi hakan da bakinsa, ba kai ka bani aikin kula da ita ba! Kasani wannan riƙe hannun naka ma da nayi dik a cikin aikina yake, kuma ba yau ba dik ranar da ka yi kuskuren hannunka ya taɓa jikinta, na yi maka alkawarin sai na datse maka shi!!".
Yadda yake maganar one after the other sai ya yi matuƙar burgeku, ga maganar tasa cikin sanyin murya da nutsuwa, babu hayani, ga zallar madarar jarumta a kowace word da zata fita daga bakinsa, yau karo na farko a rayuwarsa da ya taɓa yin makamancin hakan, baya shiga shirgin kowa, amma uncle Taheer ya kuresa ne, dan ma ya yi sa'a yana matsayin ɗan cikin family ne yasa ya raga mashi, bada ban haka ba da babu abin da zai hana bai karya mashi hannun ba!!.

Matsawa kusa da shi a tsorace Ansar ya yi tare da riƙo damtsen ɗayan hannun nasa yana faɗin. "Hoorain let's go, ka bari haka".

Wani irin kallo ta wutsiyar ido da ya wurgawa Ansar É—in ne yasa ya sake mashi dantsen hannun nasa tare da ja da baya, dan shi yasan wanenen Hoorain, idan ya zuciya karo da shi babu daÉ—i, so karya jawa kansa cin jibga.

Uncle Taheer ɗin kuwa irin shi kada ya bada kansa a gaban Auta ta ce da Hoorain ya rikesa ya kasa kwacewa, sai ya yi ƙoƙarin saka dikkanin karfinsa zai kwaci hannun nasa, har da ƙoƙarin yadda zai yi ya kaiwa Hoorain ɗin duka.

Shi kuwa tun yadda ya rikesa da farko ko motsawa bai kara yi ba, da hannu ɗayan dai uncle Taheer ya kasa kwatar kan nasa, ta wutsiyar ido ya kalleta, ta zuba masu ido irin like wow ɗin nan tana kallonsu, wani irin daɗi take ji, tana son ganin Hoorain a cikin irin wannan fusata, shiyasa ranar da aka kawo masu hari a masarautar ta rinƙa kallonsa da yana yakin cike da jarumta.

Ajiyar zuciya ya sauke ganin alamar murmushi a saman face É—inta.

Dawo da kallonsa a kan uncle Taheer ɗin ya yi, sannan ya ce. "Bana magana biyu, amma yau zan sake maimaita maka abin da nace, in har ka kuskura shaiɗan ya ruɗeka ka kai hannunka a jikinta da sunan duka na yi maka alkawarin datse maka hannu! Na rantse da girman Allah!!". Yana kai karshen maganar da ɗan karfi ya watsar da hannun uncle Taheer ɗin, wani irin baya baya ya yi kamar zai faɗi kasa saboda wurgi da hannun nasa da ya yi, a haka ma fa bai saka karfinsa wajen wurgar da hannun ba, da ya saka karfi kam ina ga uncle Taheer sai ya faɗi ƙasa.

Yana wurgi da hannun uncle Taheer bai tsaya wani ɓata lokaci ba ya juya cikin taku mai cike da tsantsar jarumta ya bar wajen.

Bayansa ta bi da kallo just like wow ɗin nan, sam bai sake juyowa garesu ba har ya fice daga wajen. Da sauri Ansar ya rufa mashi baya. Ji ta yi ita ma kamar ta bi bayansa ta je ta bashi hakuri, dan tana ganin ransa ya ɓaci sai dik bata ji daɗin hakan ba.

Uncle Taheer dai ya kwashi kunya da kayan takaici a idanun Auta, an yarfa shi, kuma shi kansa ya san Hoorain dai ba tsaransa bane, idan ya ce zai yi mashi wani wargi tsab zai ɓaɓɓallasa, dan fa zama assistant commander ba karamin jarumi bane yake iya kai wannan mataki, so shiyasa kuka ga ya shafawa kansa ruwan sanyi bai bi bayan Hoorain ɗin ya ce zai yi faɗa da shi ko wani abin makamancin hakan ba, shi dama karfinsa kawai dan ɗan cikin family ne, da wannan power yake amfani yasa dik mayakan su yi mashi biyayyar dole, kurinsa dikka shi family ne, dole su bi umarninsa, amma batun faɗa ku kanku kun san idan kuka cire commander Zafar caf cikin kingdom ɗin nan babu mai iya taɓa kwalar rigar sadauki Hoorain kuma ya sha, karya ne wlh, babu wannan a cikin gabaɗaya mayakan, kawai dai shi shiru shiru ne yasa ake ganin like ko an sanya mashi yatsa a baki ba zai ciza ba.

Dik jikin uncle Taheer ya yi la'asar ya ji kunya sosai, haka ya wuce cikin gida fuuuuu ya barta tsaye a wajen, a cewarsa zai je ya gayawa mama ta gayawa King dole Hoorain ya daina tsaron Auta daga yau.
Chapter 160 · 0% Book details