← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 211

Sashe 87

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallamar da Hamma Faisal ya yi ne yasa suka kai kallonsu a kan kofar shigowa. Kusa da Jaish ya zauna tare da miƙa mashi hannu kamar kullum. Kin bashi hannu su gaisa Jaish ɗin ya yi, har yau har gobe bayan su bappa mugun kyamar jama'ar kauyen yake yi, baya taɓa yarda ya gaisa da kowa, dan zai yi amai, su bappan ma ba karamin fama ya sha ba wajen ƙoƙarin cire kyamarsu a ransa.

Already Faisal ya saba da cewa Jaish baya yarda su yi musabaha, amma kullum yana gwada bashi hannu idan suka haÉ—u, dan a kullum gani yake yi tamkar zai yarda ya bashi hannun nasa su gaisa, sai dai ba wani canji, bai da ko alamar niyar gaisawa da kowa, ko bappa baya musabaha da shi sai dai ya nuna mashi alamar gaisuwa kawai idan suka tashi da safe.
Faisal baya jin tsoron Jaish, dan kuwa tun da yaga bappa bai guje shi ba, kuma Jaish É—in ma bai cutar da bappan ba sai ya share zancen mutanen kauye shi ma.

Hira sosai suka fara yi tsakanin bappa da Faisal Jaish ya yi shiru kai a ƙasa yana sauraronsu, ita kuwa Mahnoor ta je ta ɗaukowa Faisal ɗin abinci, ta zo suka gaisa sannan ta ɗauki abincinsu tare da cewa Mahreen su wuce cikin ɗakinsu.
Ba musu ta miƙe dan su tafi ɗin, saboda idan baku manta ba dama Mahreen ba shiri suke yi da Faisal ba, dan haka basu haɗa inuwa sam sam, shiyasa ma ta yarda ta bi Mahnoor cikin ɗaki ba dan ta so ba, saboda bata gajiya da kallon Jaish.

Suna shiga cikin É—aki Mahreen É—in ta ce. "Adda Mahnoor kin san me?".
Kai ta girgiza mata tana ƙoƙarin kawar da fitillar kwai dake wajen da suke zama su ci abincin nasu.

"Allah Adda Mahnoor da Hamma aljanina ɗin nan ya ɗaukeni ɗazun sai da na taɓa gashin kansa naji, ashe ba roba bace, gashi ne mai laushi kamar namu, kawai dai dan nashi ya fi namu baki kuma kinga yana sheƙi shi ne kawai banbancin".

Ɗan zaro idanu Mahnoor ɗin ta yi tare da cewa. "Haba da gaske?". Kai ta gyaɗa mata. "E da gaske, kuma gashin nasa wlh kamshi yake yi, akwai daɗin taɓawa".

Harara ta wurga mata tare da cewa. "Ke Mahreen dama ai komai na Hamman daɗin taɓawa yake yi maki, haka fa kika rinƙa taɓa mashi kumatu a gidan nan har sai da kumatun nasa ta kunbura ta yi ja, to dan Allah kada idan yana barci ki je ki yi ta taɓa mashi kyakkyawan gashin kan nasa har kisa ta fara muni tana zamowa ja ko kuma ma dai yawan taɓawan naki yasa gashin duk su cire, dan Allah ki bar masa kayansa kin ji yar kanwata?".

Turo bakin nan ta yi, a shagwaɓe ta ce. "Gaskiya a'a, Allah Adda Mahnoor idan dai na samu dama sai na taɓa, in yana barci zan rinƙa taɓawa, idan yana zaune da bappa ma sai na taɓa, dan in bappa yana nan ba zai yi mun komai ba, ke dan baki ji laushin gashin nasa bane shiyasa kike cewa kada na taɓa". Ta kai karshen maganar tana turɓune fuska irin na shagwaɓa.

Shiru Mahnoor ta yi, dan kuwa tun da ta ce sai ta taɓa gashin nan to fa ba makawa sai ta taɓa ɗin, kome za'a ce sai ta taɓa, kai ko Jaish zai daketa sai ta taɓa, bare ma sun san ba zai dakesu ɗin ba, ai shikenan.

Suna cin abincinsu suna hira gwanin birgewa, har suka kammala, sannan suka miƙe Mahreen ta tattare komai ta gyara wajen, sannan ta haye saman gado ta kwanta. Ita kuma Mahnoor sai da ta yi wanka kafin ta kwanta, saboda zafi da ake yi, kuma ita ta saba yin wankar dare kafin ta kwanta, Mahreen ce randa ya gameta ta yi wankar daren, ran da bai gameta ba kuma wankar da ta yi da rana ma ya wadatar. Amma fa duk ranar da ta yi wanka da daddare to tabbas sai ta yi kwalliyar nan nata na aljanu, ta mammaka kwalliyar sannan ta kwanta......... Ni kam na ce ai wannan kwalliyar kawai ya isa idan aljanu masu yawo tsakar dare suka zo giftawa ta ɗakin nasu suce ga ƴar uwarsu a nan a kwnace bari su ɗauketa su tafi da ita........🤣

Washegari da safe kamar yadda ta saba ta tashi da aikin gyaran gida haɗe da girki. Bayan ta gama komai tsab kamar kullum, sai ta ɗauki hijabinta ta nufi gidan Arɗo. Gaishe da su ta je ta yi a lokacin ita kuma Mahreen ta shiga wanka, dan ta ce wlh ba zata je gidan ba, dan Arɗo ya ce Jaish maye ne, dan haka tun da suka zagar mata Hamma aljaninta wlh ta raba gari da su, kowa ya yi ta kansa, Mahreen manyan ƙasa.

Tana dawowa a hanya, sai bitar karatunta da Inna Rabi ta kara mata take yi, cikin nutsuwa take tafiyarta, kwatsam taga mutane a gabanta kamar wasu aljanu.
Zaro idanu ta yi tana kallon su É—aya bayan É—aya, yaran Inna Rabi guda biyu ne sai abokansu.
Murya na rawa ta ce "Hamma Salisu ina kwana". Yaron Inna Rabin kenna, kanin wanda Jaish ya dallawa mari.

Sandar kiwon dake saman shoulder ɗinsa ya sauke ƙasa tare da ce mata. "Yanzu ina mayen naku mai rama maku duka idan anyi maku?".

Narai narai ta yi da idanu, dan tasan yaran Inna Rabin da shegen zuciya ga faÉ—a, saboda zafin zuciyarsu yasa wancan yaron da Jaish É—in ya mara ya yi saurin kaiwa Mahreen duka a maganar da bata kai ta kawo ba, suna da saurin hanu wajen duka ga fushin bala'i.

"Kayi hakuri Hamma Salisu". Ta faÉ—a kamar zata yi kuka.
"Ba hakuri na ce ki bani na ai, kin ganmun nan ramawa Hammanmu abin da mayen gidanku ya yi mashi muka zo yi a kanki, sai ki kira mayen naku mu gani, ya zo ya hanamu in ya isa".

Wani irin faɗuwar gaba ta ji, dan ita wlh bata son abin da zai taɓa mata lafiyar jikinta, kwana biyu Nenne bata taɓa mata lafiya ba dama, sai bin sandar hannunsa da kallo take yi, addu'a take yi Allah ya hana hannunsa ɗaga sandar nan har ya ce zai buga mata shi, ƴan hannayenta sai kerma suke yi, alamar ta tsorata, ga manyan idanun nan nata sun fara cika da kwallah.

Daga ta bayansu kamar daga sama suka ji muryan wani dattijo ya ce. "Kai Salisu me kuke yi a wajen?". A hanzarce suka kai kallonsu wajen, mahaifinsu ne. A daƙile Salisun ya ce. "Bappa ba komai......". Bai ƙarisa maganar ba Mahnoor da ta ga sun juya suna kallon bappansu haba ai sai ta watsa a guje, ta samu hanya kafa me naci ban baka ba? Sai hanyar gida.

Da gudu suka rufa mata baya, sai kwala ihun sunansu bappan nasu yake yi, amma ina basu tsaya ba. Gudu take yi da iya karfinta.
Da karfi ta nufi kofar gidan tana ƙoƙarin banke buhun kofar gidan ta shiga Salisun ya capko hijabin jikinta da nufin ya janyota baya kada ta shiga gidan, dan su samu su daketa koda sanda uku ne su yi mata kafin su sake haɗuwa da ita a wani wajen sai su ɗauki fansa na gaske, dan sun ce wlh ba zasu barta ba ita da Mahreen, ko dare ne sai sun bi su rama abin da aka yi masu, dan a cewarsu su Mahreen ɗin ne silar da yasa mayen ya kama masu ɗan uwa......... Kenan yanzu idan Allah ya karɓi rayuwar yaron su ma fa haka zasu ce zasu kashe su Mahreen dan rashin ilimi da hankali, kai wato wani lokaci mutane masu zuciyar gado ma fa basu yi ba a rayuwa, dan irinsu basu yafiya kuma basa manta gaba wlh.

Yana damko hijabinta while tana ƙoƙarin shiga cikin gidan suka ci karo da Jaish da bappa da suke ƙoƙarin fitowa, sun gama cin abincin safe zasu fita zuwa gona. Da karfin Salisu ya ja hijabinta ta yi baya, bayan da ta yin nan kuma a tunanin Jaish ɗin faɗuwa ƙasa zata yi saboda karon da suka yi, sam bai lura da su Salisun a bayanta bane, hakan yasa ya kai hannu da sauri ya riƙo hannunta.

Sai da ya riƙe hannunta ne ya ji daga bayanta ana jan hijabin jikinta, sun shaƙe mata wuya kan nata ya yi sama. Hakan yasa ya riƙeta da kyau take da fitowa wajen.

Subhanallah, ai suna ganin Jaish É—in suka saketa tare da watsawa a guje suka bar wajen, ashe rashin kunya suke ji da shi, balai'n tsoron Jaish É—in suma suke ji.

Da kallo ya bisu kafin ya dawo da kallonsa a kan face ɗinta, ruwan hawaye take yi saboda shake mata wuya da hijabin nata da suka yi. Sake mata hannunta ya yi tare da sa kai ya wuce gaba abinsa. Ƙarisowa wajenta bappa ya yi da sauri, tambayarta ya fara yi a kan meya haɗata da su Salisu? Ya yi maganar yana goge mata hawaye!.

Bata ɓoye mashi ba ta sanar da shi duk abin da ya faru. Shiru ya ɗan yi yana tunanin wannan rikicin kuma tab, shi yasan halin mutanen nasu, tun da suka fara hakan ba barinta zasu yi ba, sai sun ɗauki wannan fansa da suke ikirari, tabbas dole ya san abin yi a kan hakan kada wannan matsala ta girma, kar ya yi sake a illata mashi ƴaƴa, hakan yasa ma ya ce yau ba zai barsu a gida su kaɗai ba, gara ya tafi da su gona, in yaso idan sun je wajen Arɗo da yamma ya gaya mashi a yiwa su Mahreen tsakani da su Salisu, dan baya son abin da zai taɓa mashi lafiyar ƴaƴansa.
Chapter 87 · 0% Book details