← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 211

Sashe 49

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A'a bappa Mahnoor tana gidan ArÉ—o, wai a can zata kwana ba zata dawo gida ba dan tana tsoron wannan aljanin". Tana magana tana kai loma abinci bakinta.

"Kai kai kai aikuwa ba zai yiwu ba, bari na gama cin abincin nan ki zauna tare da bakon nan nawa in je in É—aukota". Da to ta amsa mashi ba ko tsoro.

Haka suka cigaba da cin abincin suna zuba hira har suka kammala, Bappan ya miƙe ya fito. Wanke hannunsa ya yi ya fice daga gidan zuwa gidan Arɗo.

Ita kuwa yana fita ta yi tsalle sai kusa da Jaish, hannunta duk miyar kuka ta rinƙa shafe mashi a kumatunsa mai kama da madara saboda haske, duk da haka bai isheta ba sai da ta lakato ragowar miya daga cikin kwanon nasu, ta sanya ɗayan hannunta ta matse mashi ɗan red lips ɗinsa ta tura mashi miyar da ta ɗebo a cikin baki tana faɗin. "Aljani kai ma yau ka ci abincin da Adda Mahnoor ta girka, wlh Adda Mahnoor ta iya girki sosai, idan ka ci sai kace a ƙara maka, sai ma idan ta dama fura ka ji shegen daɗi". Tana magana tana tura mashi miyar a bakinsa............. Tab ina ga wlh idan Jaish ya kama Mahreen ba mai karɓarta, rayuwa kenan yau Prince Jaish da kansa ne yake shan miyar kuka a hannun Mahreen, wai lallai kuwa wani abin sai ciwo, shi da yake da shegen kyankyani, kuma tsabar iskanci irin na Mahreen miyar da suka ci suka rage take cusa mashi a baki, Innalillahi wannan yarinya ta gama da Jaish kaca kaca, subhanahu ni dai kam kome zata yi ina team ɗinta iya wuya......😂

Duk ta shafe mashi kumatunsa da miya, bayan ta gama ne ta zo ta zauna ta nutsu a gabasa tare da kura mashi idanu kamar mai tunanin wani abin a kansa. Can kuma ko me ta tuna ta hau zuba mashi surutu. "Aljani ka tashi mana, ko dai ku a garinku na aljanu baku tashi daga barci ne? Ka tashi muje kaga masarana a gonar bappa sun fara girma, kullum ina addu'a ruwan sama dayawa ya zo dan masarana ya nuna, zan tsamma idan ya nuna, ka tashi ka ci abinci dayawa, ko dai in É—ebo maka zaka ci ne?". Sam yarinyar nan bata da tsoro.

Shi dai yana kwance ko motsawa bai yi ba, yana dai numfashi da take nuna yana raye, bayan haka ba wani abin da zata tabbatar maka da a wani hali yake ciki.

Miƙewa ta yi kamar wadda aka mintsina ta fito waje, kitchen ta shige wai zata ɗebo mashi abinci ta zo ta ciyar da shi....... Allah sarki bawan Allah ya samu gata har ciyar da shi za'ayi........😂

Ta ɗebo abincin kenan sai ga bappa, Nenne da kuma Mahnoor ɗin, bappa ya je ya tasosu a gaba, amma da kyar suka yarda suka biyosa, sai da Arɗo ya ɓata rai, shi ma fa Arɗon ganin kyan Jaish yake yi kamar aljani ko rafani haka, dan kuwa shi ma bai taɓa ganin mutun irinsa ba, kawai dai ya daure ne ya ce Nenne ta bi mijinta ita kuma Mahnoor ta bi babanta tun da ya zo da kansa a karo na biyu.

Habawa suna shigowa Nenne ta yi maza ta shige ɗakinta da gudu, wai dan ma kada aljanin yasan ta dawo da daddare ya shigo ɗakinta ya shaƙeta. Ita kuwa Mahnoor ta kanƙame bappa tana zare idanu.

"Gajin bappa me zaki yi da abincin da kika ɗebon nan? Ko dai baki ƙoshi bane zaki kara?". Cewar Bappan. "A'a bappa na ƙoshi, wancan aljanin zai je na bawa rabonsa a baki, shi kaga bai ci abincin ba".

Zaro idanu Mahnoor ta yi tare da cewa. "Ke Mahreen baki da hankali ko? Ke baki tsoro ko? Wlh yanzu dare ne sai kin je ya shakeki kin mutu ai". Ko a jikinta ta ce. "Adda Mahnoor kin cika tsoro, bappa ya ce aljani baya komai, kawai kune kuke tsoronsa, amma baya komai, to ni ko yana komai ma sai na je wajensa tun da yana burgeni". Tana kai karshen maganar ta yi maza ta afka cikin É—akin.

Da sauri bappa ya saki hannun Mahnoor ya bi bayanta dan kada ta je ta yiwa bawan Allah Jaish É—uren abincin dole, yasan kaÉ—an daga aikinta kenan.

Ita kuwa Mahnoor juyawa da sauri ta yi zata gudu cikin É—akinsu saboda tsoro sai ji ta yi Hamma Faisal ya kirata daga ta kofar gida.

Dakatawa ta yi tare da juyowa. Da yake akwai hasken wata tankar sai ta iya gajinsa. "Hamma Faisal kai ne a daren nan?". A sanyayye ta yi maganar.

"Ni ne, na zo gidan nan kafa uku bana samunki sai bappa kawai, ni kuma na kasa iya komawa gida ba tare da na ganki ba". Ya kai karshen maganar tare da shigowa cikin gidan.

Kujera ta É—auko mashi daga cikin kitchen ya zauna a tsakar gidan, sannan ta É—auko mashi rabon abincinta daga cikin kitchen É—in ta kawo mashi, ta koma ta É—ebo mashi ruwa a cikin kwarya, ta rufe kwaryar da pai pai, baiwar Allah bata sanar da shi rabon abincinta bane, saboda kyan zuciya irin nata sai ta hakura ta bashi. Ta ci abinci a gidan ArÉ—o wajen kakanta Inna.

Da yake gidan kawunsa ne sai bai nuna wani pulako ba, da alama ya saba cin abinci a gidan, dan haka sai ya buɗe abincin ya fara ci, ɗakinsu ta shige dan ita bata yarda ta yi hira da shi a cikin gida, kai ko a idanun Mahreen bata yarda su yi hira, Mahreen ɗin ma kunyarta take ji, in kunga ta sake tana hira da shi to sun haɗu a wajen kiwo ne ya sameta ita kaɗai tana zaune, daga lokacin da Mahreen ta bayyana a wajen to hiranta da shi ya ƙare, dan ko zai yi magana sau dubu ba zata amsa shi ba, sai Mahreen ta tafi, bare kuma ace bappa ko Nenne suna kusa, ai nunawa take kamar bata taɓa saninsa ba, kullum dare idan ya zo hira to shi da bappa suke hiran, ita dai idan ta kawo mashi abinci sai ta shige ɗaki, idan ya gama hiransa da bappa sai ya tafi sai da safe in sun haɗu a daji, haka ake soyayyar gwanin ban dariya.

Tana shiga ta haye gado ta kwanta, already ta yi sallah a gidan Arɗo, kwanciya ta yi ta takure waje guda, dan tana tsoron gidan a yanzu, gani take yi kamar Jaish aljani zai zo ya shaƙeta, sai tunani take yi a kan ita ta ganshi ma ta sa bappa ya kawo shi gidan, idan ma kashewa ne ita zai fara kashewa kenan, tuna haka yasa ta kara takurewa waje guda ta dunkule kamar maggi star.

Mahreen kuwa da kyar Bappa ya hanata ɗurawa Jaish abinci, sun sha fama kafin ta hakura, zama ta yi kusa da bappan suka fara hira yana biyewa shirmenta da tambayoyinta marasa kan gado a kan Jaish ɗin ko in ce aljanin nasu, haka bappa ya rinƙa biye mata har san da barci ya ɗauketa, sannan ne ya ji iskar duniya tana kaɗawa, haka ya miƙe ya ɗauketa sai ɗakinsu, a kusa da Mahnoor ya kwantar da ita, hasken farin wata na haska masu har cikin ɗakin nasu.

Yana kai ta ciki ya fito tare da zama kusa da Faisal saman kujera da ya É—auko daga kitchen, hira suka fara yi da Faisal É—in, kun san fulanin daji da iya hiran dare kamar rana, tsakar dare, zaka samesu zaune suna hira kamar wasu aljanu, ko tsoro basa ji, dare tamkar rana yake a wajensu. Haka bappa da Faisal suka yi ta hira har almost 11:40pm. Sannan ne suka yi sallama, Faisal dai ya cinye rabon abin Mahnoor tas ba tare da yasan rabonta ya ci ba. Dayawan lokuta rabonta take bashi ita ta hakura, dan Nenne kam bata bashi abin.

Bayan tafiyarsa ne Bappa ya koma cikin ɗakinsa tare da ɗauko wani tsummar rigarsa ya fito ya jiƙata da ruwa, ɗakin ya koma ya gogewa Jaish ɗin miyar kukan da take saman kumatunsa wanda Mahreen ta shafe shi da shi, tas ya goge mashi kafin ya kwanta a gefensa tare da yin addu'ar barci..ASUBA TA GARI IYALAN BAPPA KWAIRAGA.

Washegari da safe kamar yadda suka saba ne, bayan sun yi sallar asuba Mahnoor ta fito ta share gidan tsab, sannan ta je bakin kogi ta É—ebo ruwa kafa uku ta cikasa randunar dake cikin kitchen, bayan ta gama ta hura wuta ta sanya ruwan wankanta ita da Mahreen, da ruwan ya yi zafi ta juye a bakiti ta É—aura ruwan turo, already suna da ragowar miyan jiya, dama idan zasu yi miyar dare haÉ—e da na safe suke yi, da safe sai su yi sabon two su dumama miyar su ci da shi.

Da yake wutar tana ci sai da ta yi talge kafin ta shiga wanka, ita kaÉ—ai a tsakar gida kamar aljana, tun karfe biyar take wannan aiki, ita kam Mahreen kafin bappa ya samu ta tashi ta yi sallar asuban ma ai sai an kai ruwa rana, wani lokaci da kuka take tashi har ta yi sallah tana kuka, tana idarwa a wajen zata baje ta cigaba da yin barcinta, bata tashi sai an tasheta su tafi karatu, nan ma wani lokaci da kuka take tashi.

Nenne kuwa sarauniya uwar mugaye, bata firowa sai karfe bakwai kafin nan Mahnoor ta gama girki ta gama komai, wani lokaci ma har sun tafi karatu.

Haka ta kammala duk wani aiki da kuka san mace tana yi a gidanta, kamar matar aure baiwar Allah, ta yi shirinta sannan ta tashi Mahreen a kan ta tashi ta je ta yi wanka su wuce karatu. Da kyar ta yarda ta tashi, tana turo baki ga shegen iya shagwaɓa ta nufi cikin toilet ɗin, ruwan wankan nata har ya huce, dan ma da zafi sosai Mahnoor ta surka mata, ya huce ya zama ba sosai zafin, haka ta yi wankan ta fito, kaya iri ɗaya suka sanya doguwar riga ta atamfa koɗadɗiya.
Chapter 49 · 0% Book details