Sashe 139
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin muryarta yasa ya dawo daga duniyar tunanin da ya afka, dawo da kallonsa a kanta ya yi. "Jeki ki ce Hamman naku ya zo, sannan yau ba zamu je kiwo ba".
Da mamaki ta É—ago ta kallesa. "Bappa ba zaku je kiwo ba kuma? To meyasa?".
"Saboda bikin aurenki za'ayi, ba zan je kiwo ba zamu zauna ni da Hammanki mu gyara maku É—aki, anjuma da yamma a dandali za'ayi bikin bidirin aurenki kamar yadda ake yi wa kowacce yarinya a kauyen nan, ba zamu bar al'adarmu ko guda É—aya ba, kamar dai yadda ake yi tun iyaye da kakannin, ke ma dole za'ayi maki".
Zaro idanu waje ta yi, tamkar kwayar idanunta zasu faɗi ƙasa, da yake ita tasan yadda al'adun nasu suke, sai yasa ta ji kanta na juyawa, yanzu fisabilillahi yaushe zata iya aikata irin waɗan nan abubuwa da suke gudanarwa a biki da Hamman nasu, to shi ma zai iya kuwa? Shi da yake sarkin kunya, har yau ya ƙasa haɗa idanu da bappa, yaushe zai iya waɗan nan abubuwa, karami daga cikinsu ne ma bata abinci a baki, wai hakan ne zai sa a yarda zai iya kula da ita, sannan ya goyata a bayansa ya hau saman wani dutse dake kusa da dandanli mai tudun gaske, sai ya kwana yana tafiya bai isa sama gabaɗaya ba, kuma a haka zai ɗauketa a daren ya haura sai gobe da safe zai iya saukowa, a cewarsu wai hakan ne zai tabbar masu da zai iya ɗaukar nauyin ɗawainiyarta, kamar yadda ya ɗauketa ya juri wahalar haurawa da ita sama, ya je can ƙololuwa ya sake dawowa, to haka ɗaukar ɗawainiyarta ba zai yi mashi wahala ba acewarsu.
Sannan idan suka sauƙo ga girki da zai yi mata, sannan zai yi mata tsantsarerren kyalliya irin nasu na al'ada da ake yi wa amarya kamar yadda ake yi, ya ɗaura mata ɗan'kwali ɗaurin amarya, waɗan nan kaɗan ne daga cikin al'adun nasu, sai dai mun haɗu a dandali kwaga sauran.
Kuna tunanin Jaish zai yarda ya yi dukka waɗan nan shirme kuwa? Wajen sati fa ake ɗauka kowacce rana da abin da za'a gudanar, tabɗijam! Akwai kallo sosai wlh, wayaga Jaish da yi wa Mahnoor kwalliya, yaseen ba mai hanani sai na yi dariyata, ina ma emojin dariyar yake........😂😂
Yo hauka ake da ba zan yi dariya ba, Prince Jaish da kansa da hura wuta ya dafawa amaryar da bai ce yana sonta ba abinci a bainar nasi! Sannan ya yi mata kwalliya, ya bata abin da ya girka É—in a baki, ga goyata su hau dutse, tun farkon dare suna tafiya har daren sai ta tsala zasu isa, kuma suna isa su sake juyowa su dawo, tab e lallai bappa baka son zaman lafiya, to ni dai ina daga gefe ina kuma kora maltina mai sanyi ina binsu da eyes, babu wanda zai hana ni shan maltina ta kuma in yi dariya ato.
Zaro idanu ta yi, tunani ta fara yi a kan lallai za'a samu matsala in kuwa haka ne. Jiki ba kwari ta nufi waje, bappa da kallo ya bita, sarai ya fahimci ta shiga damuwa na jin abin da ya faÉ—a, amma kuma dole ayi waÉ—an nan al'adu kamar yadda ake yi wa kowace É—iya, shi kansa yana fargaba yana É—ari É—arin yadda zata kasance idan har aka ce Jaish ya yi wannan abin, yana ganin kamar da wuya, amma ba shi da niyar fasawa a ransa.
Can wajen dabbobin ta iskosa yana ta ƙoƙarin ɗauresu, yanzu gabaɗaya ya canza, kamar ba Prince Jaish namu ba, har duhu soft skin ɗinsa ta yi, dark black arab hairnsa har ta ɗan yi brown kaɗan, saboda yanzu baya sanya mata mayukansa da ya saba, bata samun gyara sosai, kuma ga shi yaki yarda bappa ya datse mashi gashin nasa, ba yadda bappan bai yi ba amma yaki yarda, ya ce a bar mashi kayansa a haka yake sonta.
Cikin sanyin murya ta ce. "Hamma bappa ya ce kazo".
Shiru bai motsa ba bai kuma dai'na abin da yake yi ba, tamkar bai ji metace ba.
Ganin haka yasa ta kuma cewa. "Hamma bappa ya ce yau ba zaku fita kiwo ba, ba sai ka sha wahalar ɗaure dabbobin ba, ka barsu kawai". A wannan karon cikin harshen fillanci ta yi mashi magana, izuwa yanzu yana jin yaren nasu sosai, baya magana ne da tsab zai iya mayar masu da amsar dik abin da suka buƙata, yawan zamansa da Mahreen inuwa guda ne yasa ya iya yaren sosai, dama ita ai ko baka kaunar Allah sai ta sanya ka fara kaunarsa, yo dan dole yake sauraran hirarta, tun baya gane komai har ya fara fahimtar wace duniya ta dosa dan dolensa.
Sai a wannan lokacin ya É—ago kansa jin cewa ba zasu je kiwo ba, idanu ya zuba mata ba tare da ya yi wata alama ba. A yanzu tana fahimtar dik wata motsinsa me yake nufi, dan haka ta fahimci tambaya yake son yi a kan me zai hanasu zuwa kiwo dik da bai nuna alamar hakan ba, baiwar Allah tana da basira.
"Ni ma ban san dalilin da zai hanaku zuwa ba, kawai dai ya ce na kiraka ba zaku je ba yau". Ta bashi amsa tana yin ƙasa da kai. Ba zata iya gaya mashi za'ayi bikin aurensu bane, kunya abin ya bata yasa ta yi karyan bata san dalili ba.
Aikuwa bai gamsu da maganarta ba, dan kuwa ya gano karya take yi, hakan yasa sai bai motsa daga in da yake ba.
Ta fahimci dalilin rashin motsawar tasa, wato gaskiya yake son ji kenan, lallai ma ya iya tsiya shi ma. Kara yin ƙasa da kai sosai ta yi, kunya kamar zata nutse cikin ƙasa ta ce. "Da gaske Hamma ni ban san dalili ba".
Still bai motsa daga in da yake ba, dan bai gamsu da zancen ba.
Ganin haka yasa ta ji a ranta ko dai ta watsa a guje ta yi cikin gida ta barshi a wajen ne? Tun da ta isar da sako ya ji da kunnensa bappa na kiransa ai dole ya je. Sai kuma ta yi tunanin idan ta yi hakan ai raini ne, bappa ya gargaÉ—esu sosai a kan rai'na na gaba da su, dan haka bai dace ta yi hakan ba, to ya zata yi? Ita dai a gaskiya ba zata iya gaya mashi shirye shiryen bikinsu ake yi ba.
Tana tsaka da tunanin mafita ne sai gani ta yi ya ɗaga hannunsa yana yarfarwa kamar wanda wani abin ya kama mashi hannun ya maƙale. A ɗari ta ɗago da kanta haɗe da kallonta a kansa.
Cigaba da yarfar da hannun nasa ya yi yana son cire kaskar jikin shanu da ta maƙale mashi jikin fata tana son shan jininsa, cizonsa ta yi a hannun yasa ya farga da ita.
Ai data ga haka bata san lokacin da ta manta da cewa tana jin kunyarsa ba, a fujaje ta matso kusa da shi tare da riƙo hannun nasa.
Bai yi kokarin kwacewa ba, saboda dayawan lokuta yana gani idan suka kama jikin bappa ita take cire mashi ta sanyasu cikin wuta, babu kaskar dayawa a jikin dabbobin nasu, saboda bappa yana yawan duba gabaɗaya jikin dabbobin, rana yake warewa a kowace karshen sati ba ya zuwa kiwo, zama yake ya hura wuta kusa da su ya yi ta cire masu kaskar yana sanyawa cikin wuta, hakan yasa basu da yawa, kun san suna yawan maƙale jikin shanu su yi ta shan mashi jini, wanda bai sansu ba wasu irin kwari ne kanana kamar ƙuda da suke maƙale jikin dabbobi suna shan masu jini, sun iya cizo sosai fa.
Har kashe shanu suna iya yi idan suka yawaita a jikinta, suna da haɗari gaskiya, sun iya ɓarna, dole ka rinƙ kula da jikin dabbobinka idan ba haka ba su kamu da cuta ka rasa daga ina matsalar take, kan ka ankara idan ka yi wasa sai ka ji dabbarka ta mutu.
Zuba mata idanu ya yi yana kare mata kallo a lokacin da take cire mashi wannan kaskar, haka kawai yake jin tausayinta, tana da innocent face, fuskar ban tausayi, ga shi kullum na duniya sai ya ci karo da ita tana kuka Nenne ta yi mata wani bakin izayar, hakan tasa ko bata kuka sai ya rinƙa kallon face ɗinta kamar tana kuka, sai ya rinƙa jin tausayinta yana ratsa shi.
A lokacin da ta kama yatsun hannun nasa tana son cire mashi kaskar sai da ta ji kirjinta ya bada dum dum, saboda yadda yatsun nasa suke dogaye kuma gasu ba sirara can ba, ƴan ɓul ɓul dai haka, ga su da haske kamar madara, yau dai ta taɓa jikinsa, duk sai ta ji kamar ba jikin mutun ta taɓa ba, ga wani haske da faratunan hannun nasa suke yi, har wa yau skin ɗinsa is very soft.
Kerma hannunta ya fara yi wajen kama kaskar, sarai ya lura da a tsorace take, sai ya basar kamar bai ganta ba.
Da kyar ta iya kamar kaskar ta cire mashi, a can gefe ta jefar da ita, sannan ta É—an ja baya kaÉ—an daga kusa da shi tana yi mashi sannu, dan kuwa ta cijesa a hannu, ga wajen har ya yi alamar jini.
Shi kam face ɗinta yake ta kallo, cikin ransa yake jin kamar ya taɓa rayuwa da ita a wata duniyar, wato tunanin gimbiya Zunaira ce take yi mashi gizo a ƙwaƙwalwarsa ta dalilin ganin face ɗinta a kusa da shi................ Ni kuwa nace anya face ɗin Mahnoor idan ta cigaba da matsowa kusa da shi ba zai sa ya dawo cikin hankalinsa ba kuwa? Kuna dai ganin a duk lokacin da ya ganta kusa da kusa sai tunanin gimbiya Zunaira ta yi mashi gizo, ya rinƙa jin kamar ya taɓa yin rayuwa a wata duniya ta daban, to mu je dai zuwa, lokacin zai warware mana komai.
"Hamma in tafi ne?". Ta faɗa kallonta a ƙasa, tana son ɗago idanu ta saci kallonsa dan taga me yake yi, amma ta kasa gudun kada ta tsinci yana kallonta su haɗa idanu.