Sashe 210
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Motoci masu tashin jini shidda ne a gaba suka dira a kofar gidan bappan, still Jaish yana tsaye yana kallonsu, wasu jiga jigan jami'an sojoji ne suka fara firfitowa daga cikin motocin, waɗan da suke baya ma suka diro ƙasa. Da gudun gaske suka kewaye ko'ina a arear gidan bappa, hannunsu rike da manyan bindigu sai wani muzurai suke yi da idanunsu jajir kamar gauta.
Tsorata iya tsorata Mahnoor ta yi, da sauri ta kwace hannunta daga riƙon da ya yi mata zata gudu cikin gida kenan ya ce ta dawo.
Ba musu ta dawo ta tsaya ta bayansa, ita kuwa Mahreen sai kallonsu take yi tana karawa, a albarka irin nata ma wai kyau suka yi mata,
Wasu tsala tsalan motoci sabbi dal dal ne suka biyo bayan motocin sojojin nan, motoci huÉ—u ne cif dikkaninsu kirar PININFARINA BATTISTA, bakake kirin sai kyalli suke yi.
Sai wasu motocin sojoji da Æ´an'sanda uku suna take masu baya.
Har daf gaban Jaish waɗan nan motoci suka kariso, kun san da yake ƙauye akwai fili, sai yazama dik motocin nan kofar gidan bappa ya ɗaukesu.
Still Jaish yana tsaye idanunsa a kansu ko motsawa bai yi ba, kaman wanda ruwa ta cinyesa.
Motocin suna tsayawa wani katon soja ya zo ya fara ɓalle kofofinsu yana buɗewa. Kusan a tare Ramish da Bilal and uncle Jahiz suka fito daga cikin motocin, kowa da nasa.
Gabaɗayansu suna sanye cikin shigar three-piece suit irin wanda suka kalarci taron ɗaurin auren Rizwan da shi, sun yi matuƙar kyau sosai.
Ai razana Mahreen ta yi, kun san jini ba wasa ba, sai taga sun saje mata da Jaish, taga sun zama mamarsu É—aya, ta kalli Jaish ta juyo ta kallesu, dik ta rikice. Ita kanta Mahnoor ta rikice kuma ta tsorata, ta kalli Jaish ta sake kallon Ramish, ta kasa gane komai. Still jirage nata shawagi a sararin samaniya.
A miliyan Jaish ya zaro idanunsa waje yana kallon Ramish, nan take ya ji kansa ya yi wani irin mugun sara mashi, da karfi ya datse idanunsa tare da dafe forehead É—insa da hannu bibbiyu yana jin wani irin jiri mai karfi tana É—ibansa.
Kafin su Ramish su ƙariso gabansa ya yanke jiki zai faɗi ƙasa Ramish ya yi zafin naman isa garesa ya taresa, ai Mahnoor bata san lokacin da ta juya a guje zata gudu cikin gida ba. Mahreen ce ta riƙo hannunta har da ce mata ta tsaya su kalli kyawawa masu kama da Hamma, ita fa yarinyar nan sai addu'a. Mahnoor ta tsorata da su amma ita ko a jikinta, kyau ma Ramish ya yi mata dan yana cikin kaya matsu tsada, dik sai ta rikice a kansa.
A saman shoulder ɗinsa Ramish ya saɓi Jaish sai cikin motarsu, basu yi wa kowa magana a kauyen ba, basu nemi kowa ba kuma basu taɓa kowa ba, Jaish kawai suka ɗauka suka taga motocinsu suka bar ƙauyen.
Suna tafiya jiragen dake sama suka take masu baya har ma suka wucesu. Tashin hankali, kallon kallo Mahreen da Mahnoor suka fara yi wa junansu, kuka zasu yi ne ko ihu sun rasa, barema Mahnoor da ta kamu da son Jaish ga shi an É—aukesa, ita kuma Mahreen an É—auke bata abin kauna mai tare mata faÉ—a, ya kuke tunanin makoman Mahnoor?.
Da gudun gaske Mahreen ta watsa ta nufi wajen bappa a gona dan ta sanar da shi wasu sun zo sun É—auki hamma, ita kuma Mahnoor ta shige cikin gida da gudu tana sakin kuka mai sauti.
Su kuwa su Ramish kai tsaye airport suka nufa, dama ba zama suka zo yi ba, barema shi Ramish da yau yana da taro da misalin karfe 5 na yamma a Dubai, so ba zasu wani ɓata lokaci ba.
Suna airport suka hau jirgin Abuja, dama already sun yi bukking, jet da suka zo da ita kuma a Abj ɗin suka barota saboda wani dalili nasu na kansu da basu bayyana ba, motocin da suka ƙarisa da su cikin kauyen kuma dama daga gidan gwamnati ana turo masu da shi.
Amma my people's me kuke tunanin dangane da yadda aka yi su Ramish suka iya zaƙulo Jaish? Hmmmm akwai matsala fa.
Suna sauka a Abj suka nufi hotel É—in da suka sauka, a nan suka raba hanya, Bilal and Ramish zasu É—auki jet É—insu su wuce Dubai kai tsaye, su uncle Jahiz kuma zasu wuce da Jaish Tunisia, hakan ma yasa Ramish ya zo da uncle Jahiz domin ya koma da Jaish.
Baku tunanin ya aka yi suka tsallake rikicin dake Kingdom of power suka zo ɗaukar Jaish?🤔
Ramish and Bilal ne suka fara yin gaba suka bar uncle Jahiz a hotel É—in tare da Jaish da bai farfaÉ—o ba.
Kamar yadda Ramish ya faɗa karfe uku dai'dai suka yi wa Dubai dirar mikiya, sosai Abu Abdussalam ya ji matuƙar daɗin hakan.
Abin da banku sani ba ban gaya maku ba shi ne, Ramish, Bilal, Dr Raj, uncle Jahiz tun ranar Jumma'a bayan É—aurin auren Rizwan da misalin karfe 3 na rana suka baro kingdom of power suka nufo kasar Nigeria, so su dik rikicin da yake faruwa a kingdom of power basu sani ba, ga shi uncle Jahiz zai koma can yanzu, me kuke tunanin zai faru? Kada ku manta ankawo masu hari watakila ma suna can suna gwabza yaki waya sani!.
Abu Abdussalam bai samu damar ziyartar É—aurin auren Rizwan da ya ce zai je ba, saboda wannan taro da suke da shi na karawa Ramish and Bilal girma da za'ayi ga kuma walimar da Abbie É—in nasu ya shirya masu.
Lokacin da su Ramish suka dira a Dubai har an fara gabatar da taron, gabaɗaya family sun hallara a cikin hall ɗin, ba'a gidansu za'a gabatar da taron ba, ba kuma a wajen aikinsu ko a gidan gwamnati ba, Abu Abdussalam ya buƙaci da su kama tampatsetsan hall saboda dubban baki da za su zamu halatta.
Mu koma baya kaɗan, a tsawon kwanaki da suka shuɗe bamu leƙo Dubai ba abubuwa da dama sun faru, ciki harda amsawa masu nikaf da Leesharh ta yi a kan zata yi masu last aikin da suka buƙata, sun canza mata wayar da yake hannunta, ana saura kwana biyu wannan taro Leesharh bata san daga ina ko ya aka yi aka kawo mata waya ba, sai dai taga waya kawai a cikin akwatinta, ta sha madarar mamaki sosai, amma sai ta danne ta cigaba da bin umarninsu dan sun ce mata shi ne last mission.
Alakarta da Ummie ya kara tsananta, Ummien ta tsaneta sosai, sam bata son ganinta, Abu Abdussalam kuma kullum cikin ƙara janta a jiki yake yi, yana kaunarta saboda Allah sosai.
Sun sha samun saɓani ita da Ramish and Dr Raj tana shan marika a hannunsu, Bilal ne kawai bai taɓa marinta ba, shi tausaya mata ma yake yi hakan yasa yake kyautata mata sosai, in kuma yana nan baya barin su Ramish su taɓata ko da ta samu saɓani da su.
Tamkar Ramish yasan akwai abin da ya kawota gidansu, haka kawai ya tsani ganinta, ya kuma dakawa Sharrifat warning a kan kada ta kuskura ta sake zuwa mashi da Leesharh part ɗinsu, dan baya son ganin mai kama da inuwarta a arear wajen, Bilal ya yi ƙoƙarin bashi hakuri amma ya nuna a kan hakan zasu iya samu matsala da Bilal ɗin ma, hakan yasa suka kyalesa Leesharh ta dai'na zuwa part ɗin.
Wannan dalilin yasa ta dai'na samun information da take bawa masu nikaf a kansa, amma dik da haka tana samun wasu bayanai nasa ta bakin Sharifat Æ´ar soyayya, zuwansu Kingdom of power dik ta samu labarin wajen Sharrifat kuma ta sanar da masu nikaf, sannan Leesharh ta fara zuwa school kamar yadda Abu Abdussalam ya faÉ—a, wani lokaci ma Bilal da kansa yake kaita, sai dai fa malaman sun gane takardun karya ne takardun nan na Leesharh, amma basu yi wani magana ba dan a tunaninsu Abu Abdussalam ne ya buga mata takardun karyan da ta tsallake, kunga kuwa idan shi ne ai basu da bakin magana, Allah sarki basu san ba shi bane bai ma san na karya bane. Wannan shi ne kaÉ—an daga cikin abubuwan da suka faru a baya. To mu koma kan labarinmu.
Ko da suka zo gida dan su yi wanka su shirya babu kowa daga cikin family, dik suna wajen taron da Abu Abdussalam ya shirya, taron kara masu girma kuma sai sha biyun dare za'a gabatar da shi a can headquartersu.
Hall É—in nan shake yake da jama'a ga uban securitys ta ko'ina, kada ku manta Abu Abdussalam fa hukuma ce mai zaman kansa, dik wata kaki a karkashinsa take, ba iya Æ´an'sanda ko sojoji ba, dik wasu kaki da kuka sani a kasansa suke, so hakan yasa tsaro ya yawaita sosai a wajen, gabaÉ—aya hall É—in a kewaye yake da jiga jigan tsaron da ko guda idan da dama ba zasu bari ya gifta ya shiga cikin hall É—in ba tare da saninsu ba.
Ga manya manyan Cameras ta ko'ina, amma fa dik da wannan gabaÉ—aya hall É—in kewaye yake da bomb ba tare da saninsu ba.
Suna ta shagalinsu dai su kam. Sai around 5 dai'dai Ramish and Bilal suka ƙariso cikin hall ɗik, sun sha gayu cikin two-piece suit mai bala'in tsada. Dama already gabaɗaya familyn Abu Abdussalam da manyan bakinsa kujerun zamansu yana a saman stage, an kawata hall iya ƙawatuwa.
Abu Abdussalam yana a tare da Ummie, Sharifat dai tana tare da Leesharh, suna zaune kusa da kusa. Ga wani haÉ—aÉ—en mic da aka kawata wajensa domin yin magana. Dikka manyan kai ne a cikin hall É—in babu yara.
Albarkarcin Abu Abdussalam da su Leesharh ai ko a mafarki ba zata taka matsayin kusantar wannan taro ba, amma yau sai gata a cikinsu kuma saman stage waje na musamman, abin gaskiya abin a jinjinawa Abu Abdussalam ne.