Sashe 104
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A saman gadonsa ya kwantar da Akkar tare da zama a gafenta yana mai bata hakuri tare da yi mata alkawarin tabbas koma a ina Spender yake dole zai kwato kayansa ya dawo da shi.
Me alaƙar King da Spender ne wai?. To ku buɗe kunnenku ku ji, Spender dai mallakin King Abdul Malik ne wato mahaifin su King Zuhair mijin Akka kenan, a yanzu da baya raye kunga kuwa mallakin ƴaƴansa ne wato King Zuhair, uncle Abbas and uncle Jahiz, nasan kowa zai so jin menene wannan Spender, amma mu je zuwa zaku ji komai a hankali, sai dai kuma abin tambayar a nan shi ne, King Zuhair da yake babban sarki da kowace kujerar mulki a faɗin ƙasar Tunisia take ƙarƙashin tasa kujerar, suna da karfin iko da isa, kada ku manta ko gate ɗin masarautarsu babu wani mahalukin da ya isa ya nuna da ɗan yatsa, jarumai ne waɗan da akewa mayaƙansu ma laƙabi da dangerous warriors, amma duk da haka ya aka yi Spender ta bar hannunsu take hannun Pretty? Akwai bala'i gaskiya, wai ni ina mummyn twin's ɗin ne ma kam? Tana raye ne ko ta mutu? A ina ta samu Spender har ta nasu? Kai mu je dai zuwa, dan waɗan nan tambayoyi ma kara jefa mun ƙwaƙwalwata cikin zafi zasu yi.
Tana daga kwance tana ganin jiri ta fara faɗin. "Zuhair kada ka yarda ka fitar da zancen Spender ya ɓata saboda abokan gaba, kawai ku nemosa ta ƙarƙashin ƙasa".
Hannayenta ya riƙo cikin nasa tare da yi mata alkawarin aiwatar da hakan cikin ƙanƙanin lokaci.
A takaice a cikin wannan dare ya bugawa duk wasu amintattun cikin fada busar gayyata, sai hidimar gyaran masarautar ake yi saboda yakin da aka buga.
Yana buga masu busar gayyatar ba'afi minti biyu ba suka hallara a cikin meeting room É—insa, zama ta sirri ya gudanar a tare da su, ko ni kai'na basu bani damar jin abin da suka tattauna ba bare na kawo maku labari, sai dai ga dukkan alamu sun gamsu da tattaunar tasu, dan sun tashi taron fuskokinsu ba yabo ba fallasa, dama dai kunsan su ba dariya suke yi ba, musamman ma commander Zafar, ai shi wannan fuska kamar hadari take kullum.
King bai iya kwanciya barci ba har sai da ya samu matsaya a kan ta yadda zasu nemo Spender!. Sannan ne ya yi wanka ya samu ya sanya haƙarkarinsa a gado.
Haka ita ma Momma sai da ta samu tabbacin mijin nata ya samu nutsuwa ya dawo cikin hankalinsa sannan ta iya kwanciya.
Kafin King ya dawo uncle Abbas da ya yi isowar yamma ya zo dan su gaisa sai bai samesa ba, shi ma Rizwan ya zo da nufin ya sanar da shi batunsa shi da Chuchu a lokacin bai dawo ba, hakan yasa ya wuce part É—in Momma suka sha hira da chuchu, Jawad kuma yana tare da uncle Abbas a lokacin, sai tsokanarsa daddyn nasa yake yi yana tambayarsa ina Jannat? Sai ya wani kafe wai shi bai san in da ma take ba dan bashi da wata relationship da ita.
____________________________🔥🕊ï¸
Washegari da safe, uncle Abbas and uncle Jahiz sai Akka suka zauna zama ta sirri, sai dai King bai iya sanar da su cewa Spender ta ɓata ba, dan in ya gaya masu za'a samu matsala, Akka ta hana ma ya sanar da su, sun dai yi zama na tattaunawa a kan ɓatar Jaish da sauran matsalolinsu.
Mummyn Gimbiya Chuchu ce ta buƙaci King da ya yarje mata zata shirya gagarumin walima na dawowar Guyson kamar yadda ta yi alkawarin kuma kamar yadda take shiryawa duk wanda ya dawo daga cikin ƴaƴan nasu, sai dai wannan karon zata haɗa da walimar nasarar yakin da suka ci, da yake ita bata san da batun ɓacewar Spender ba yasa ta bukaci hakan, su suna cikin jimami ita kuma murna ma take yi, ko da yake dole zata yi murna dan a ganinta sun ci nasara a yaki ai abin murna ne.
Da farko King ya so hanata shirya walimar, amma sai Akka ta yarje mata, ta yi mata hakan ne kuma dan kada a fahimci batun ɓatar Spender, dama a duk lokacin da suka ci nasara a yaki sukan shirya walima da manya manyan masarautu zasu halacta, duk wani mai riƙe da muƙami zai hallara, suci su sha, su yi kyaututtuka, ayi abubuwa dai na bajinta da taimakawa talakawa, to kunga idan ba'ayi ba wannan karon dole jama'a zasu ce akwai wata a ƙasa, hakan yasa Akka ta ce mummyn ta yi.
Kan kace me aka hau shirin walima. Shi kuwa Yah Jawad yau tun da sassaqfe ya shirya dan yana da gagarumin aiki a office, jiransa ma ake yi, sai kiransa a waya suke yi, sun takura mashi.
Jiya a tare da Rizwan ya kwana É—aki É—aya, kamar zasu cinye juna saboda so, ko shirin tafiya office da ya yi yanzu sai da Rizwan É—in ya taimaka mashi saboda kauna.
Yana fitowa daga part ɗin daddyn nasu ya nufi part ɗin King dan ya gaishe da su Momma kafin ya wuce office. Yau kingdom of power a cike take da baki, su uncle Jahiz sun zo, Guyson tun da suka zo yana tsakanin mummyn Gimbiya Chuchu da mommarsa, shi fa irin mutanennan ne mai ƙulafucin uwa, sai dai suna mugu mugun shiri da mummy, badan kaunar da yake yi wa mummyn ta musamman bace bama da ba zai iya motsawa daga kusa da mommarsa ko nan da can ba, amma yana kaunar mummyn, dan tana da farar zuciya tana kuma kaunarsa.
Duk girmansan nan, yana da kanne uku a duniya, amma tsabar shagwaɓa da kulafucin uwa a ɗakin momma saman gadonta ya kwana, bai san da batun dawowar King ba, tun karfe 8 ya yi barci abinsa, a saman cinyarta ma ya kwantar da kai ya yi barci, sai da ya yi barcin ne ta lallaɓa ta kwantar da shi ta tafi wajen King.
JAWAD
Dab zai shiga É—akin Momma ita kuma tana fitowa, karo suka yi a in da kanta ya bugi faffaÉ—ar kirjinsa.
Baya ta É—an yi tare da sanya hannu t........
ðŸ¤KADA KU MANTA WANNAN DADDAÆŠAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥ðŸ¤
🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI â¤ï¸ðŸ”¥
ð— ð—”ð—Ÿð—Ÿð—”ð—žð—œð—¡
FATEEMA ZAHRA MUSA â¤ï¸â€ðŸ”¥
â¤ï¸A-K-A ð‘·ð‘¹ð‘°ð‘µð‘ªð‘¬ð‘ºð‘º ð‘»ð‘¬ð‘¬ð‘´ð‘¨ðŸ”¥
â¤ï¸ð‘«ð‘¨ð‘»ð‘¬ 28/10/2024.....âœï¸ðŸ“šðŸŒ¹
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
اللَّهÙمَّ صَلّ٠عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌ، اللَّهÙمَّ بَارÙكْ عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌâ¤ï¸
💘ZANGO NA BIYU....âœï¸ðŸ“šðŸ”¥
E29
Baya ta É—an yi tare da sanya hannu tana murje gaban goshinta, da alama ta É—an ji zafin karon da suka yi.
From toe ya fara kallonta yana É—agowa har izuwa face É—inta, da sanyi safiyar nan har ta tsantsara kwalliya, kai Chuchu duniyar kwalliya, idan ka ji mutum ya ce make up bata burgesa to fa bai haÉ—u da na Chuchu bane, ita É—in duniya ce.
Har ta tashi ta yi wanka, tsantsara kwalliya ta yi dan Yah Rizwan ɗinta, wandon jeans doguwa ce sai riga zuwa gwiwarta a jikinta, a takaice dai Pakistan dressing ta yi, mayafin kayan babba ne yana ja mata har a ƙasa, ga shi kuma net ne da ya ji flowers, haƙiƙa kayan sun yi mata kyau sosai, gata fara kayan launin maroon and milk, abin ba'a magana.
Shakar daddaÉ—ar kamshin perfume É—inta ya yi tare da lumshe idanunsa, a hankali ya sake warosu a kanta.
"Ina kwana Yah Jawad?". Ta faÉ—a a sanyayye.
Kawai kura mata idanu ya yi babu ko kyaftawa tamkar idan ya rufe idanun zata ɓacewa ganinsa.
Sake maimatawa ta yi. "Yah Jawad ina kwana?".
Hannu ya kai saman kansa ya É—an shafa arab hairnsa tare da sauke ajiyar zuriya.
"Jannat ki na yi mun son ranki a gidan nan". Ya yi maganar ce a zatonsa a cikin zuciya ya yi, sai da ya ji ta ce. "To ni Yah Jawad me kuma nayi maka?". Tana magana tana turo baki. A san nan ne ya fahimci ashe a fili ya yi maganar ba'a ɓoye ba.
Girgiza mata kai kawai ya yi tare da cewa. "Babu komai, yanzu dai da kika yi wannan tsantsararren kwalliya ina zaki je? Kuma yau ba school ne?".
Tana ƙoƙarin yin magana sai ga Momma ta fito daga cikin room ɗin. Shiru ta yi shi kuma ya ɗagawa Mommar gaisuwa.
"Office zaka je yau É—in nan hakan zata yiwu kuwa?". Momma ta tambaya.
"Yeah Momma, sai kirana ake ta yi ne, wani aiki ne da muka yi apply since last two months ago sai yanzu fa daddy ya sanya baki aka sakar mana aikin, shi ne zan je in saka hannu".
"Tom shikenan ka kula sosai, dad É—inku dai ya ce su Jannat su zauna yau kada su je school saboda wannan yaki da aka yi, su dakata tukun nan zuwa kwana biyu komai ya koma normal". Tana magana tana kallon shi.
Sa kai Chuchu ta yi zata wucesu, dan ta lura hiransa da Momma ba karewa zai yi ba. Cikin sauri ya riƙo hannunta yana kawar da kallonsa daga kan Mommar. Harara Mommar ta watsa mashi tare da sa kai ta wuce abinta.
Tana wucewa ya matso kusa da ita. "Ina zaki je bamu gama magana ba? Ko kallonki mafa ban gama yi ba". Cike da so da tsantsar kaunarta ya yi maganar.
Cigaba da turo mashi baki ta yi bata yi magana ba. "Lafiya naga kin ɓata rai kuma? Yanzu fa face ɗinki ɗauke da ƙayatattcen murmushi amma daga Momma ta fito ta wuce shikenan kika dai'na murmushi why?".
Girgiza kai ta yi tare da cewa babu komai. Ƙara matsowa kusa da ita sosai ya yi tare da rage tsawonsa ya ɗan rankwafo kanta kaɗan. Ƙasa ta yi da kai tare da ɗan ja baya kaɗan, dan har sautin numfashin juna suna ji, hakan yasa ta ɗan matsa.
"Menene ya faru? FaÉ—a mun kin ji ko?". Ya faÉ—a murya kamar mai raÉ—a. Still dai girgiza mashi kai ta yi tare da cewa babu komai.