← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 211

Sashe 6

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

❤️🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 16/9/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

💘STEP TWO....✍️📚🔥

E__________________3🔥

Wani irin gigitacen mari ta sake dallah mashi wanda ya sanya shi yin tangal tangal kamar zai faɗi ƙasa. Cikin ƙunar rai ta ce. "Babu in da zaka je! Daga yau idan ka sake yi mun magana a kan babanka ko wasu banzaye can tsinannun da suka kurɓata maka tunani sai ranƙa ya ɓaci fiye da tunaninka, ni kaɗai kake da shi a duniya, dan haka ka goge komai dake cikin ranka, daga yau ma ba zaka sake fita ko nan da can ba..." Ta kai karshen maganar cikin tsananin ɓacin rai tana furzar da huci mai zafi, tana kai karshen maganar kuma ta finciki hannunsa da karfin tsiya har sai da ya furta wash da karfi.

Cikin fusata ta jashi da karfin gaske suka kama hanya, azaban zafin jikinsa yake ji saboda fincikarsa da ta yi da karfi, ciwon da damisar ta ji mashi wajen duk yana yi mashi raÉ—aÉ—i, amma haka ta cigaba da fincikarsa har suka isa gida.

Zuciyarsa tafasa take yi mashi, gabaɗaya gaɓɓan jikinsa yana yi mashi ciwo. Wani ɓangare na zuciyarsa tana gaya mashi ya tirge yaki binta, ya bijirewa maganarta kawai ya gudu ya tafi neman Pretty da babansa amma kafin nan ya fara zuwa ya duba lafiyar Sweetien da yake tunani tana cikin ramin can.

Ɗayan ɓangare na zuciyar tasa kuma tana ƙara gaya mashi girman uwa, tuna mashi da irin fafutuka da famar da Mammar ta yi a kansa take yi, tunawa ya rinƙa yi da yadda ta sha wahala a kansa, ta sadaukar da komai nata dan shi, har rayuwarta ta sha sanyawa a haɗari dan ta ceci tasa rayuwar, a yanzu idan ya bijire mata sam bai yi mata adalci ba, a yadda kuma yake karatun Alkur'ani yake karanta fassararta da English yasan cewa in dai ya yi wa Mamarsa haka Allah ba zai barshi ba, uwa ta wuci wasa. Amma kuma yana son sanin babansa, yana son sanin ƴan uwansa, zuciya bata da kashi, ba zai iya hakura bai je ga su Pretty ba, ba zai iya hakura bai nemo in da take ba.

Wasu irin zafafan hawaye ne suke bin ƙuncinsa, a tunanin mammar saboda marin da ta yi mashi ne yasa yake wannan kukan, bata san cewa shi ko zata ɗaure shi ta kwana tana dukansa in dai zai rayu da safe ta rabu da shi ya je ga Pretty da babansa zai yarda da hakan ba, sam bai ma ji zafin marin da ta yi mashi ba, azaban zafin dake cikin zuciyarsa ta take zafin marinta. Raɗaɗi zuciyarsa take yi mashi, ya rasa mafita.

Haka ta cigaba da jansa har izuwa cikin ɗakinsa. Da karfi ta turashi ya faɗa saman gadonsa, da alama ta manta da cewa yana da ciwo a jikinsa, ɓacin rai ya rufe mata idanu bata ganin komai face ta san yadda zata yi ta hana shi ko leƙa waje......... Lalla Mamma ta ɗebo da zafi, da karfi da ya ji zata raba soyayyar da Allah ya haɗa, Allah ne ya sanyawa Kamran kaunar Pretty, ba dan komai yake sonta ba face dan Allah, shi kansa ko kashe shi zaka yi ka tambayi meyasa yake sonta sai dai ka kashe shi, dan ba zai baka dalili ko guda ɗaya ba, saboda tun ranar da ta faɗo duniya, ko cibiya ba'a yanke mata ba, a haka yana ɗaura idanunsa a kanta zuciyarsa ta kamu da kaunarta, a wannan lokaci me zai so? Shiyasa nace maku ba dan komai yake sonta ba face dan Allah, son da yake yi mata kaddararsa ce, a tare aka haifesu da Sweetie, meyasa bai taɓa jin son Sweetien ba sai Prettyn? Dame tafi Sweetie? Babu abin da ta fita da shi, amma a haka zuciyarsa ta kafe Pretty take so while ita kuma Sweetie tana sonsa, son yaya da kanwa kawai yake yi wa Sweetie, Pretty ce kaddararsa, ita farincikinsa, sau ɗaya ya ganta ranar da aka haifeta, a ranar ya ɗauketa da hannunsa, ya ceci rayuwarta, tun daga lokacin kuma sai da ya shafe shekaru goma bai sake ganinta ba, amma dai'dai da rana ɗaya bai taɓa mantawa da ita ba, kullum tana cikin tunaninsa, a tsawon waɗan nan shekaru da suka yi basu tare kullum yana cikin ƙunci da damuwar rashinta, ya zo ya ganta sun sake sabo, har soyayyarta mai zafi fin na baya ya kara shigansa, sun saba, ita ma tana son kasancewa a tare da shi kullum, rana tsaka kawai mamma ta rabasu? Ta ce kada ya sake fita ma bare ya nemosu? Yanzu bashi da tabbacin suna mazauninsu ko basa nan? Bai san ina takamaimai suke ba, wannan abin da taɓa zuciya, anya zai yarda da hakan kuwa? Ku dai kun san yadda yake jin sonta a ransa.

Cusa kansa ya yi cikin katifar tasa, wani irin kukan zuciya yake yi mai tsuma rai, har wani irin shessheka yake yi kamar wanda ake zarewa rai, ji yake yi kamar zai iya haÉ—iyar zuciya ya mutu, gabaÉ—aya zufa ta wanke mashi jiki.

Ko kaÉ—an a wannan lokaci mamma bata ji tausayinsa ba, ta É—auka soyayyar wasa yake yi wa Pretty, dan tana ganin kamar bai san menene so ba, ta É—auka haÉ—uwar yau ce kawai ko na Æ´an kwanaki, bata san sun jima a tare ba tare da saninta ba, batasan soyayyar bata wasa bace, sannan bata yanzu bane, soyayya ce da ta faro tun ranar da aka haifeta, rashin sanin daraja da mutuncin soyayya yasa sam bai bata tausayi ba. Da alama zuciyar mamma ya rigada ya bushe, ta kekashe bata jin tausayin komai da kowa, har shi kansa É—an nata bata tausaya mashi, ashe ba'a banza take bashi irin horon da take bashi É—in nan ba, babu tausayi a ranta yasa komai magiyar da zai yi mata a kan ya gaji ta bari ya huta, amma bata É—aga mashi kafa har sai ya cike lokacin da ta É—eba mashi, bawan Allah.

Tana jin irin kukan da yake yi mai tsananin ratsa zuciya, amma ta yi burus da shi tasa kai ta fice daga ɗakin. Kai tsaye waje ta nufa domin ta samo igiya irin na jijiyar itace mai karfi ta ɗaure shi, dan ta ci alwashin ba zai sake fita waje ba bare ya je gurin waɗansu har su sake kurɓata mashi tunani.

Kukansa ya cigaba da yi yana addu'ar Allah yasa ya mutuma kawai ya huta, dan zuciyarsa ba zata iya jure rashin Pretty ba, ga tunanin Sweetie da yake a ɗayan ɓangaren zuciyar tasa, yana tunanin makantar nan nata, yanzu idan Pretty ta ɓata ita kuma ya zata yi? Yasan da wuya Pretty ta iya dawo da kanta cikin wannan ramin nasu, dan hanyar da ta bi ma sam sam bashi da haɗi da in da suke, dajin nan yana da girma kuma yana da haɗari, akwai namun dawa sosai a cikinsa, da wuya Pretty ta iya kai labari, da wuya ta rayu in dai ta cigaba da tafiya a kan wannan hanya da take, tunani yake ya Sweetie zata rayuwa ba mai yi mata jagoranci zuwa in da take da buƙata kamar yadda Pretty take yi mata?. Addu'a yake yi Allah yasa wannan sadaukin ya haɗu da Prettyn ko kuma ta haɗu da mai tamakonta.

Tun yana iya kuka mai sauti har sautin ta dai'na fita, ban da ruwan hawaye babu abin da yake fita daga idanunsa. Babban damuwansa ma amanarsu aka bashi, bai riƙe amana ba, ya karya yardan da aka yi mashi, idan ya tuna da hakan sai kara rushewa da kuka, yarda da shi yasa mum twins ta bar sakon ta bashi amanarsu, ta san zai iya riƙesu ne yasa ta bashi, amma ga shi yanzu mamma tasa ya kasa cika amanar da ya karɓa.

Saboda tsananin sabo da yake a tsakaninsa da Rocky ne yasa Rockyn ya zo bakin kofar ƙogon yana ta zuba masu kurnani, da alama yana jin kamar Kamran ɗin bashi da lafiya ko wani abin makamancin haka, kun san fa ita dabba idan ka yi sabo sosai da ita sai ku zama kamar twins, bare shi da a gabansa aka haifi Kamran ɗin, tun Kamran yana jariri suke tare, ai dole ma ya ji hakan a jikinsa.

Ko da Mamma ta dawo hannunta a É—auke da igiyoyi masu karfin gaske, a bakin kofa ta isko Rocky, kun san ba zai iya shiga ciki ba. Yana ganinta ya nufeta yana gurnani. Sarai ta san me yake yi wa, amma sai ta yi kamar bata sani ba, ta sharesa zata wuce.

Tsalle ya fara yi yana kama jikinta alamar baya son ta tafi. Sam taki yarda ta bi ta kansa, sai ma ture shi da ta yi ƙoƙarin yi ta wuce, hakan yasa ya yi tsalle sosai zai capketa, da sauri ta wuce ciki ta barsa.

Ai kuwa da karfinsa da Allah ya basa ya fara ƙoƙarin lallai sai ya bita cikin wannan kogon yau, sai dai ina, kogon dutsene mai karfin gaske, wane shi ya iya fasata ya shiga, haka ya rinƙa gurnani yana tsalle ya bugi jikin kogon har ya jiwa kansa ciwo.

Har cikin ransa Kamran É—in ya ji zafin wannan ciwo da Rocky ya ji, haka kawai ya ji zuciyarsa ta tsananta zafin da take yi mashi, hakan yasa ya fahimci lallai wani abin yana faruwa da wanda yake kauna, so sai ya É—aura zarginsa a kan Pretty, ya yi tunani ko itace wani abin yake faruwa da ita, sam bai kawowa ransa Rocky ne ya ji ciwo ba, dan baya tunanin akwai wanda zai zalinci Rocky ko ya yi mashi wani abin a wannan dajin, shiyasa sam bai kawowa ransa shi É—in bane.
Chapter 6 · 0% Book details