Sashe 199
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai ta girgiza mashi alamar a'a, ta zo da nufin gyara abu komai ya sake lalacewa, ta ya za'ayi ya É—auki Aneesa a bawa Jawad fisabilillahi? Ba a tambayi yarinya ko tana da wanda take so ba, sam ran Aunty MieMie bai yi daÉ—i ba kuma bai so hukuncin da King ya yanke ba, domin kuwa tasan dole Aneesa zata yi kuka da ita ta ja an aura mata wanda bata so, ya ilahi wannan abu sam bai yi mata daÉ—i ba!.
"Zan iya tafiya fada ko dai akwai wani sauran magana da kike da shi?". King ya jefa mata tambaya.
Sai a lokacin Ramish ya yi ɗan gyaran murya tare da ajiye cup ɗin dake hannunsa a saman bedside drawer, ya ɗan jingina bayansa da jikin headboard na bed ɗin, shi yana da ɗabi'ar karanta ya mutun yake ji a cikin zuciyarsa idan ya kalli face ɗinsa, so ya fahimci damuwar da Aunty MieMie take ciki matuƙa wanda King ya gaza fahimta, cike da so da kauna ya kalleta cikin sanyin murya ya fara magana ƙasa ƙasa a nutse.
"Big Aunty, jeki abinki, jeki yi abin da dad ya umarceki zan yi magana da shi".
Ɗan zaro mashi idanu ta yi, ita dai tasan King yana kaunarsu, yana kuma nuna masu soyayya a fili, sannan yana basu dama sosai a rayuwarsu, sai dai shi kaifi ɗaya ne da in ya yi magana tankwarasa ya juya maganar abu ne mai matuƙar wahalar gaske, kai abu ne ma da ba zai yiwu ba, ita ma ta gwada sa'arta ce kawai, abin kuma ya ki aiki.
"Trust me big Aunty, jeki kawai". Cewar Ramish again.
Jinjina mashi kai ta yi tare da miƙewa tana yi wa dad ɗinta addu'a da fatan alkhairi haɗe da fatan isa fada lafiya ya kuma dawo lafiya.
Da amin ya amsa yana mai sanya mata albarka har ta fice daga cikin É—akin.
Miƙewa Ramish ya yi yana faɗin. "Dad let me escort u".
Jinjina kai King ya yi kafin ya miƙe yana faɗin. "Dama ina buƙatar shawararka a fada".
"Shawara kuma dad?".
Jinjina kai ya yi alamar yeah shawara.
"So for what kenan?". Yana magana ya riƙo hannun dad ɗin nasa.
"A kan kuɗin shiga ne, tunani nake yi kamar mu kara yawan ma'aikatu domin a kara rage matasa masu zaman banza marasa aikin yi, sannan kuma kaga za'a kara samu kuɗin shiga again tun da ma'aikatar zata rinƙa fitar da kaya zuwa makotan ƙasashe, ko ya kace?".
Shiru ya É—an yi yana tunani. Can sai ya ce. "Yeah dad shawara ce mai kyau, za'a rage masu zaman banza and akwai amfani daban daban apart from that".
Jinjina kai King ya yi. "To amma wani irin ma'aikata kake ganin yakamata mu buÉ—e?".
Kai tsaye ya ce. "Ma'aikatar karafuna, i means karafunar mota hakan, ba karamin cigaba zai kawo maku ba, sannan zai kara É—aga kasar sosai musamman idan kayanku yana da saukin kaso ashirin cikin É—aki fiye da kowacce kasa".
Jinjina Kai King ya yi alamar ya gamsu da maganar É—an nasa. A haka suna tafiya suna hira har suka isa fada.
____________________________😥
A ɓangaren Chuchu kuwa, lokacin da ta farka ta ganta a room ɗin Jawad sai ta ji sanyi a ranta, da face ɗinsa ta fara cin karo da sassafiyar nan. Wayarsa ta ɗauka ta duba time karfe bakwai saura minti goma, a hanzarce ta diro kasa daga saman bed ɗin.
Da sauri ta fice ta nufi part É—in Aunty MieMie tana kwallah tana waigosa, to kun ji yadda aka yi ta tafi wajen Aunty MieMie ta gaya mata abin da yake faruwa. Tana barin É—akin Rizwan yana shigowa kamar wani shiri.
Ya sha madarar mamakin ganin kansa a room É—insa part din uncle Abbas a lokacin da ya tashi daga barcin nasa, jikinsa dik ciwo yake yi mashi lokacin da ya farka, da kyar ya iya tashi ya yi wanka, Jawad ne kawai a ransa a lokacin, shiyasa yana yin wanka ya yi maza ya shirya ya nufo É—akin nasa.
Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke a lokacin da ya sauke idanunsa a kan ɗan uwan nasa, ya ji matuƙar daɗin ganinsa, a hanzarce ya nufesa dan ya duba lafiyarsa.
Still yana nan dai kamar yadda suka barshi, ko motsawa bai yi ba, a gefensa Rizwan ya zauna yana tunanin kalaman mamarsu na karshe a kunnuwansu.
"Rizwan na baka amanan Jawad, ka kula da shi tamkar yadda zaka kula da kanka, sannan ka tabbatar kana kulawa da dik wanda zaku yi tarayya da shi, domin ni ban yarda da gidan nan ba, ban sani ba ko ina da rabon sake sanya Rahilarh a idanuna, wata kila kuma kafin ta zo rai zai yi halinsa, dan Allah idan ma bata zo ta sameni da rai ba ka ce mata na bata Jawad duniya da lahira ta kula mun da shi, ban yarda ya girma a hannun babanku ko matarsa ba, ya girma a hannun Rahilarh shi ne wasiyata a gareka, ka zama mai biyayya ga manyanka, ka zama mai hakuri sai dai ba irin hakurina ba, ni kai'na nasan hakurina ya yi yawan da shi ya cutar da ni har haka, bana yi maku fatan hakuri mai yawa irin nawa, ina yi maku fatan wani lokaci idan anyi maku abu ku yi magana dan ku samu sassauci a cikin zuƙatanku, rashin amayar da magana ya jefani cikin wannan hali da nike ciki.............". Dakatawa da yin maganar ta yi tana wani irin tari mai sanya dik mai sauraro ya ji zuciyarsa ta karaya.
Kuka sosai Rizwan yake yi yana faÉ—in. "Mommy ba zaki mutu ba, In Sha Allah zaki rayu damu, ki dai'na faÉ—in batun mutuwan nan".
Sosai ta yi tari kafin ta samu ya É—an tsagaita mata, sai ta cigaba da cewa. "Rizwan mutuwa tana a kan kowa, ni dai nasan lokacin nawa ne ya yi, ka dai'na kuka komai zai wuce, lokacin kaÉ—an zaka dai'na jin ciwon rabuwa dani ka fara mantawa dani, wasiya ta karshe da zan yi maka shi ne ka zama mai manta baya ka kula da abin da zai zo gaba, ka tsaya tsayin daka wajen ganin baka maimaita abin da ya faru a bayanka ba koma me shi...........".
Rufe mata baki ya yi da tafin hannunsa yana cigaba da kuka yana girgiza kai, cikin kuka ya ce. "A'a mommy, har duniya ta tashi ba zan dai'na jin zafin rabuwa dake ba, In Sha kuma sai mun rigaki mutuwa, ki dai'na faÉ—in hakan, dan Allah ki yi shiru".
__________________________
Ƴar firgita ya yi tare da dawowa daga duniyar tunain da ya afka.
A fili ya furta. "Ba zan taɓa dai'na jin raɗaɗin rabuwa dake ba mommy, wannan ciwon ba zata taɓa warkewa ba! A kullum tana a cikin zuciyata, da ita nike kwana nike kuma tashi! Allah ya jikanƙi da rahma ya gafarta maki yasa mutuwa hutuce a gareki". Yana magana idanunsa suna a kan face ɗin Jawad, zafafan hawaye ne suka cika idanun nasa tab, ya fama ciwon dake zuciyarsa na rashin uwa na tsawon shekaru.
Dr Raj and Bilal ne suka shigo cikin É—akin domin duba jikin Jawad É—in. A kusa da Rizwan Bilal ya zauna tare da kai hannu yana share mashi kwallar da ta zubo mashi a yanzu.
"Be a strong man please my bro, by the grace of god babu abin da zai samu kaninmu, continue pray for him, very soon zai tashi". Cewar Bilal.
Jinjina kai Rizwan ya yi ba tare da furta uppan ba, shi kaɗai yasan raɗaɗin da yake ji a ransa, tabbas rashin uwa babbar musifa ce ga ƴaƴanta komai girma da mulkinsu kuwa, ba zaka taɓa gane hakan ba sai idan bata tare da kai, ita ɗin bango ce ga dukkanin ƴaƴanta, waɗan da iyayensu suka riga mu gidan gaskiya Allah ya yi masu rahma ya gafarta masu, waɗan da nasu kuma suke raye Allah Ubangiji ya kara masu lafiya ya kuma bamu ikon yi masu biyayya haɗe da kyautata masu mu sanyasu farinciki a rayuwarsu ko Allah zai jiƙanmu.
Dr Raj ma hakuri ya bashi kafin ya fara duba lafiyar Jawad É—in.
Sosai abin ya ɗaurewa Dr kai ganin yadda yanayin komai na jikin Jawad ɗin ya koma yake tafiya dai'dai, amma da zarar ya farka daga barcin alluran da suka yi mashi gabaɗaya sai jikin ta rikice ya fara yin wasu abubuwa kamar mai fama da tsananin zazzaɓin typhoid, kun san zazzaɓin typhoid idan ta tsananta tana da shegen saka mutun surutai har ma da ƴar fisge fisge kamar mai aljanu, idan ma ba'a sani ba sai a zaci aljanu sabon kamu ne da shi, domin zazzaɓin tana saukarwa da bawa gizon tsoro ne a cikin kwakwalwarsa, sai ya rinƙa ganin kamar abu zai bugesa ko wani abin makamancin haka, tana rikita jinin mutun ne sosai.
A nan wajen dai dik kwarewan Dr a iya aiki sai da abin ya yi mugun ɗaure mashi kai, Allah sarki basu san tsafi ce take aiki a wajen ba ba wani abin ba. Sai dai bai gayawa Rizwan abin da ya gani ba, sai ya fake da ce masu gara a karawa Jawad alluran dan har yanzu jikinsa bata karɓi hutun nan yadda yakamata ba, yana buƙatar karin hutu sosai, ya dai yi masu dabara basu gane komai ba.
________________🌹💘________________
A ɓangaren cikin gida kuwa, sai shirye shirye ake yi gobe za'a ɗaura aure, ƴan uwan maman Jawad sun zo daga kasar Saudiya, su suka ɗauki nauyin haɗawa Rizwan ɗin kayan lefe, sun nuna bajinta kam, tun da Rizwan ya sanar da su dama Auntynsa babba ƴar mamarsa wadda suke uwa ɗaya uba ɗaya ta ce ita zata yi kayan lefe, ba yadda bai yi da ita ba a kan ta bari taki, har ma sai da ta haɗa mashi da zagi wai ya ci gidansu, sannan ne ya yi shiru ya kyaleta ta yi, su biyu iyayensu suka haifa, daga wannan Auntyn tasu sai mamarsu, shiyasa suke bala'in son Auntyn tasu, sai dai ba'a Saudiya take da zama ba ita, a kasar America take, dan bature ta aura ba balarabe ba, yanzu daga America ta wuce Saudiya suka taho tare da sauran ƴan uwansu.