← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 164 OF 211

Sashe 164

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dan haka tun a daren jiya na bawa Rizwan aurenta, zai koma Dubai next week, so ya buƙaci da a ɗaura auren kafin ya koma, na kuma yi mashi alkawarin this coming friday za'a ɗaura ya wuce da matarsa". Cewar King, cikin nutsuwa yake yin maganar, ga izza ta jinin sarauta.

"Amma yaya Jawad ya tabbatar mun da cewa soyayya yake yi da Jannat ya abin zai kasance haka kuma?". Cewar uncle Abbas. Jiki a mace ya yi maganar, muryarsa ta canza sosai, da alama ya shiga damuwa matuƙa, kuma dama dole ya damu, dan kuwa ace mace ɗaya yaya da kani suke matuƙar so abin akwai taɓa zuciya, kuma dik suna yi mata wani irin soyayya ne wanda rabuwa da ita ba kamar cutuwa zasu yi ba, barema shi Jawad ai da wuya ma ya rayu yadda ya ɗauki son duniyar nan ya ɗaura mata, wlh abin akwai taɓa zuciya sosai, ga shi ita kuma an rasa me ya shiga kanta, idan tana tare da Jawad aka ce waye take so zata ce Jawad, haka zalika in suna tare da Rizwan, abin dai akwai mugun ɗaure kai.

Sosai jikin uncle Abbas ta yi la'asar, ya shiga tashin hankali da damuwa, yanzu ya zai yi da Jawad kenan? Ga shi ya hango tsantsar madarar soyayyar Chuchun a cikin kwayar idanunsa, waye za'a bawa waye za'a hana?.

Muryar king ne ta katsesu da cewa. "Ni ma lokacin da Akka ta gaya mun Rizwan yana son Jannat sai da na sake tambayarta Rizwan ko Jawad? Ta ce mun Rizwan, sam a lokacin zuciyata bata yarda ta karɓi hakan ba har sai da na kira Jannat da Rizwan ɗin, sai da suka gaya mun da bakinsu sannan na gamsu, kuma a baya na sha tambayar Jawad ɗin yana son Jannat ne sai ya ce a'a kawai yana kaunarta ne a matsayin kanwa, kullum haka yake ce mun, to kaga kenan shaƙuwace ta yaya da kanwa kawai a tsakaninsu ba soyayya ba, mune muke zargin kamar soyayya ce". Ya kai karshen maganar yana dawo da kallonsa a kan uncle Jahiz da ya tsaresu da ido yana sauraron wannan ruɗanin.

Uncle Abbas ya rasa bakin magana, ya rasa tacewa, tabbas in kuwa haka ne da gaske Jannat Rizwan ta ce take so, to kenan Jawad shi ne yake dakon makauniyar soyayyarta ba tare da saninta ba,? Yanzu ya zai ji idan aka ce mashi É—an uwansa aka bawa ita? Innalilahi wa Inna ilahir rajiun!.

Sallamar mommar ce ta katse masu dik tunanin da suka afka, ƙarisowa ta yi cikin parlourn kuyanga mama Haulat na biye da ita a bayanta hannunta ɗauke da katon tray mai ɗauke da luxury cups na cappuccino.

Kusa da King ta zauna tana hararar uncle Jahiz da yake binta da kallon zolaya. A gabansu kuyanga mama Haulat ta zube ƙasa domin kwasar gaisuwa, da alama momma ta yarda da mama Haulat sosai gaskiya, dan bayan kuyanga Zubaida mai yin serving ɗinsu abinci babu wata kuyanga da ta taɓa shiga parlon King sai ita.

Dikkansu uncle Abbas ne ya ari bakinsu ya amsa masu gaisuwar da ta É—aga masu É—in.

Sannu da hutawa momma ta yi wa King, cike da so da kauna ya amsa mata, sannan uncle Abbas and uncle Jahiz ma suka yi mata sannu da zuwa.

Miƙewa kuyanga mama Haulat ta yi ta fara kawo masu trayn cappuccinon gabansu suna ɗauka, King ta fara bawa sai uncle Abbas sannan uncle Jahiz, suna gama ɗauka momma ta miƙe tare da yi masu sallama sannan ta wuce gaba mama Haulat ta take mata baya, alkyabbar yana jan kasa fuuuuuuuuuuuuuu suka nufi waje.

Uncle Abbas dai ya kasa shan cappuccinonsa, saboda damuwa da tashin hankalin da ya shiga na halin da Jawad zai shiga idan ya samu wannan bakin labari, King and Uncle Jahiz kuwa shan abinsu suka fara yi cikin nutsuwa.

_____________________________🔥🤍🕊️

"Yah Jawad tunanin me kake yi ne?". Muryarta ta daki dodan kunnensa.

Yar firgita ya yi tare da dawowa daga duniyar tunanin da ya afka, dama tunani ya afaka yi yana imagine ga shi ya capki lips É—inta yana kissing, a zahiri ba da gaske bane, tana dai kwance a jikinsa tana jiran jin wasu zafafan kalaman daga bakinsa, ashe shi kuma ya afka duniyar tunanin yana shanye mata baki.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Tunanin me zan yi kuma da ya wuce tunaninki my Jannat? Kenake tunawa".

ÆŠan waro ido ta yi like wow É—in nan, sannan ta ce. "To tunani na na me kake yi?".

Shiru ya É—an yi, sai yaki gaya mata cewa ya yi tunanin ga shi yana yi mata kiss ne, ya canza izuwa wani topic daban, ya ce. "Tunanin yadda zamu rayu bayan aurenmu nake yi".

Ba zai iya gaya mata har yana imagine na kissing É—inta ba, dan hakan zai janyo raini a tsakaninsu, gara ma sai sun yi auren, shiyasa dik yadda zuciyarsa take ingiza shi ya yi kissing É—inta baya yarda ya yi, dan yana da ilimin addini na farko, yasan hakan kuskure ne, na biyu ita É—in kanwarsa ce har yanzu, sai ranar da aka É—aura masu aure ne zancen zai canza, shiyasa yake kame kansa, rungumar juna kuma sun saba ne tun kafin natun soyayya.

"Yah Jawad ina mamaki sosai, wai yau ni ce nake soyayya da yayana da nafi kauna a duniya! Kasan daÉ—in da nake ji kuwa?".

Kai ya girgiza mata yana ƙoƙarin yin magana kenan wayarsa ta fara ƙara. Wani irin faɗuwar gaba ya ji ta dira mashi kamar ba lafiya ba.

Hasbunallahu wani'imal wakil ya furta lokacin da ya ji hakan, sannan ya zura hannu a aljihunsa ya ciro wayar. Ganin sunan my daddy wato uncle Abbas ne yake yawo a saman screen É—in yasa ya yi saurin raba jikinsa da nata, ya É—an yi one step sannan ya É—auki call É—in.

Ya sha mamakin ganin kiran, saboda yanzu suka rabu babu jimawa, meyasa yake sake kiransa?.

"Hello daddy". Ya faÉ—a a sanyaye, kirjinsa sai dukan uku uku yake yi kaman wanda ya yi wani laifin aka kama shi.

"Jawad ka sameni a part É—ina nan da 20 mins". Shi ne abin da uncle Abbas ya faÉ—a, daga haka ya katse kiran.

Dum dum ya ji kirjinsa ta yi da karfi, a hanzarce ya nufi hanyar fita, dan yadda ya ji muryan daddyn nasa sai yake ganin kamar yana cikin damuwa da tashin hankali, hakan yasa ya ce gara ya je tun yanzu ya ji menene, sai ya alaƙanta sauyin sautin muryan daddyn nasa da faɗuwar gaban da yake ji.

"Yah Jawad ina zaka je?". Ta faÉ—a a É—an ruÉ—e kuma da mamaki, dan taga irin saurin da ya kwaso.

"Ina zuwa Jannat". Abin da ya faÉ—a kenan, daga haka ya fice da sauri.

Shiru ta ɗan tsaya na ƴan mintoci kafin ta wuce ta haye saman bed ɗinta ta kwanta tana tunanin soyayyarsu da shi yadda zata kasance bayan aure....... Hmmm akwai gagarumin matsala kam, to ni dai bari na leƙa su Khadija mutanen Kaduna mu ji ya suka isa, zamu dawo daga baya mu ji kiran me uncle Abbas yake yi wa Jawad?.

Sorry my people's, da babu gwara babu daÉ—i sai mun haÉ—u gb.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 2024-11-21....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥

_____42

SU KHADIJAH.

Karfe ɗaya dai'dai na rana suka sauƙa a kawo Kaduna, Khadija ta ce Zee ta nemo masu aran waya su yi kira, su sake gwada number kawu Sadiq ko tana shiga, abinku da yarinta da shiririta, tun suna gida fa suke gwada number a kashe, amma sai suke ganin kamar idan suka zo Kd suka kira zata shiga.

Da okey Zee ta amsa, Khadija ta samu waje saman irin bencin da ake ajiyewa na zaman jama'a haka, nan ta zauna tare da matso da akwatin nasu kusa da ita, Zee ta wuce zuwa neman masu aran waya.

Sai kalle kalle Khadija take yi, da kallo É—aya zaka yi mata kasan tana cikin damuwa, da alama ma kuka take son yi, sai a yanzu tunanin basu sanar da maman Hanif ba ya faÉ—o mata, sai ta ji babu daÉ—i, dan kuwa ko ba komai maman Hanif ta yi É—awayniya da su, ta fita zakka a cikin familyn baban nasu.

Wani matashi ne ya zo ya zauna a kusa da ita yana faÉ—in. "Sannunki Æ´an'matan".

Bata kula shi ba, bama ta ɗago ta kalle shi ba, ta cigaba da tunanin da take yi abinta, dan ita yanzu duniyar nan binta da kallo kawai take yi, bata da wani sauran kataɓus.

"Wani kike jira ne ko wani wajen zaki je ne?". Ya sake tambayarta kamar dole sai ta tanka shi.

Shiru kamar babu ita a wajen, ko motsawa bata yi ba.
"Idan akwai in da zaki je ki yi magana sai a kaiki! Ni fa mai keken napep ne".

Jin haka yasa ta É—an É—ago ta kallesa, a É—an takaice ta ce. "Kasan unguwar Rimi?".

A hanzarce ya ce mata e yasani kawai ta tashi su tafi, to dama ita already tasan sunan unguwar su Sadiq, mamanta tana yawan kama sunan unguwar, gidan ne dai tun da suka yi wayo basu taɓa zuwa ba, amma idan ba'a canza yanayin tsarin unguwar ba tabbas idan taga kofar gidan zata iya ganesa, dan tana da shekaru 6 sun je da mamanta, tasan ya kalar gate ɗin gidan yake da yanayin tsarin ginin.

"To can zaka kaini bari kanwata ta zo mu tafi". Ta faÉ—a a takaice.

Da shegen shisshiginsa yana ganin yadda take magana sai ya ce. "Amma wani abin ne yake damunki ƴan'mata? Dik da ban sanki ba ban taɓa ganinki ba sai yau, tabbas naga damuwa a saman face ɗinki, in ba damuwa ko zaki iya gaya mun kila in iya taimaka maki".
Chapter 164 · 0% Book details