Sashe 117
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nunawa Jaish saman tabarma bappa ya yi a kan ya zo ya zauna.
Ba musu ya zo ya zauna, a tsanake cikin sanyi da nuna kulawa bappan ya gaya mashi dik abin da yake faruwa, daga karshe ya ce. "Banso hakan ba, kuma Allah ya ga zuciyata Faisal na so ya auri Mahnoor, amma kuma ba zan iya kiran ƴata da bazawara ko kuma in ji wani ya kira mun ita da hakan ba, abin kunya ce babba mu a wajenmu, bani da zaɓin da ya wuce in..........."
Dakatawa ya yi da maganar bai kai karshenta ba sakamakon sake bankowa cikin gidan da aka yi a karo na biyu. A lokacin Mahnoor tana tattare gidan tana gyara abubuwan da faɗar da su Jaish ɗin suka yi suka watsa komai, ita kuma Mahreen tana zaune kusa da Arɗo ta buga uban tagumi tana tuna yadda Jaish ya yi ta jibgar matasan can, a gaskiya abin ya yi mata mugu mugun daɗi kuma ya ƙayatar da ita.
Ba kowa bane ya banko cikin gidan ba face Faisal, kamar wani zararre, yana wani zaro idanun, ga dikkan alamu baya a cikin hayyacinsa, sai wani huci yake yi, ga shi babu ko riga a jikinsa, daga shi sai wando dogo ta wata shadda koɗaɗɗiya, gashin kan nan nasa kamar dambu mahaukaciya ko ace bukka, ya tara gashin sosai, gata da cika, da alama ya yi birgima da gashin nasa a cikin turɓayar ƙasa ne, dan gabaɗaya gashin nasa ta zama yadda kuka san power aka zuba mashi, saboda ƙasa da ta wankesa.
Jikinsa duk ƙasa, kai in takaice maku ya fita a hayyacinsa, ya fita sahun mutane.
Yana shigowa a gaban bappa ya zube gwiwowinsa, yana zaro idanu, ga idanun nasa alamar ya ci kuka ya ƙoshi, sun yi jajir gulu gulu da su, haka kamar mahaukaci ya fara sambatu.
"Wlh bappa ina son Mahnoor, kuma kowa ma ya san da haka! Kai kanka ka sani, ba ka bani aurenta ba ma? Dan Allah bappa kada ka ɗauketa daga gareni ka bawa wani ƙaɗo can bare da bai san darajarta ba, ka ji tausayi na bappa, zan iya mutuwa a kanta, aradun Allah ina kaunarta, wayyo na shiga ukuna......."
Yana tsaka da yin maganar ne idanunsa suka sauka a kanta, ta tsaya turus a tsakar gidan baiwar Allah, Allah ya gani tana son Faisal ɗin, ita yanzu ma ƙoƙari take ta fahimci wani abin, tana son ta san menene ya sanya Hamma Faisal ɗin nata ya birkice haka? Ta ji yana faɗin kada a rabasu, to waye zai rabasu? Ta gaza gane kada a rabasu kamar yaya? Bata fahimci komai ba.
A zabure ya miƙe tsaye, hannunta ya zo ya ruƙo, ya jata har gabansu bappan, kuka bawan Allahn nan ya shiga yi da hawaye bibbiyu kamar ƙaramin yaro, faɗin ya fara yi. "Mahnoor ki gayawa bappa kina sona, dan Allah ki gaya mashi ba bakon ƙaɗon nan nasa kike so ba, ki gaya mashi kada ya rabamu kin ji?". Yana magana hawaye da gudun gaske suka cigaba da wanke mashi fuska, ya haɗa uban gumi, fuska kamar wanda aka watsawa ruwa saboda gumi, jikinsa har kerma yake yi, tsikar jikinsa duk sai tashi suke yi, wlh sai ya baka tausayi idan kaga yadda ya mace a kanta.
Daga ArÉ—o har bappan an gaza samun mai kwarin gwiwar iya yi mashi magana, ko ya taushesa, sun zuba mashi idanu kawai.
Ƙoƙarin kwace hannunta daga nasa ta yi, dan ta gudu izuwa cikin ɗaki, baiwar Allah ba zata iya tsayuwa wannan rashin kunyar ba, yanzu ta fagimci batun aurenta kenan ake yi, sai dai ta gaza gane da waye a cikinsu ake batun auren nata? Me kuma yasa Hammanta kuka?.
Mahreen ce ta miƙe tsaye tare da ƙarisowa in da suke, hannu tasa ta fara ƙoƙarin taya Mahnoor ɗin kwace hannunta daga riƙo da ya yi mata, da yake kunsan ita fa bakinta baya shiru, kuma kun san ba shiri da Faisal ɗin suke yi ba dama sai ta ce. "Kai Hamma Faisal ai dama bama sonka, dama Adda Mahnoor ba zata aureka ba, dan ni bana sonka, ka sake mata hannu........."
Bata ƙarisa maganar ba ya ɗauketa da wani irin gigitattacen mari wanda yasa sai da ta yi baya baya ta faɗi ƙasa. Zuciyarsa tafarfasa yake yi tamkar an ɗaura dalma a wuta, dama shi ma yana da zuciya har haka?.
Yana ji da tsananin bakinciki tazo tana sake gaya mashi mai É—aci, ai dole ya dallah mata mari.
Yadda kuka san zuciyar Jaish zata fashe, yadda kuka san shi ya mara ba Mahreen ba, a wani irin zuciye ya miƙe tsaye, nan take ransa ya ɓaci, da hannu ɗaya yasa ya pincike rikon da ya yi wa Mahnoor ɗin, wani irin mari mai tsananin zafin da ya sauke mashi a saman ƙuncinsa ne sai da yasa shi ganin wasu irin taurari masu hasken gaske suna gilma mashi, sake ɗaga hannu ya yi a karo na biyu zai ƙara mashi wani marin.
Da saurin bappa ya miƙe ya riƙe hannun nasa ta baya, a fusace ya juyo tare da damko wuyar bappan ba tare da ya lura cewa shi ɗin bane, a tunaninsa wasu ne irin su Faisal ɗin.
Ya juyo da kyau da niyar ya karya hannun wanda ya rikesa ɗin, duk da ɓacin rai da zafin zuciya da ta rufe mashi idanu hakan bai sa ya gaza gane cewa bappa ya shaƙe ba. A hanzarce ya zame hannunsa daga wuyar nasa yana sunkuyar da kansa ƙasa, ransa ya ɓaci ne na Mahreen da Faisal ɗin ya yi wa mutuniyar tasa.
A hankali ya sakar mata hannunta da ya kwace daga cikin na Faisal. Yana saketa ta kwasa a guje sai cikin É—akinsu tana sauke numfashi.
Hannunsa ya miƙawa Mahreen dake baje a ƙasa tana kuka. Da sauri ta riƙo ta miƙe tsaye. Ɗakinsu ya nuna mata da ɗayar hannun nasa alamar ta je.
Ai da gudu ta wuce. Shi kuwa Faisal da ya yi suman tsaye ko motsi bai yi ba ne bappa da Arɗo suka ƙariso kusa da shi, bappa nasa hannun ya taɓashi kawai sai ga Faisal ya tafi luuu sai ƙasa, da karfi ya furta. "Shikenan ni Faisal na mutu".
Yadda ya yi maganar gwanin ban dariya gwanin ban tausayi, ya ji marin manya ne yasa ya zama kamar ya zare, kamar ƙwaƙwalwar ta samu matsala, shiyasa zaku iya jin abin da ya fi wanda ya faɗa yanzu ma, ba laifinsa bane, ya ji hannun jinin Modarawa ne.
Cikin harshen fillanci Arɗo ya ce da bappa wannan magana ta batun auren nan a barta sai komai a daidaita, sai a san abin yi, yanzu dai su ɗauki Faisal a sama mashi magani ya samu lafiya, dan da alama hankalinsa ta gushe ƙwaƙwalwa ta taɓu.
Na'am da zancen sirikin nasa bappa ya yi, matasa suka nemo aka É—auki Faisal É—in zuwa gidan ArÉ—o, a tare suka wuce da bappan, amma kafin su tafi sai da suka zubawa sauran matasan da Jaish ya jibga waÉ—an da basu farfaÉ—o ba ruwa.
Baya sun farfaÉ—o ne suka tasasu a gaba suka tafi.
Nenne tana can cikin ɗaki tana ciza yatsa tammar zaga yi hauka, ban da nadama da danasani babu wani abin da yake ranta, ta yi babban danasani na sanyawa a haɗa wannan aure......... Ni kuwa nace danasani tun daga yanzu Nenne? Kada ki bada mata mana! Ai bai kamata ki fara danasani tun yanzu ba! Yana da kyau ki kara ɗaura ɗamara ne hegiya!. Ai duk wanda ya gina ramin mugunta to ya jira ranar afkawarsa ciki! Ai baki ga komai bama tukun nan. Dama ke kin taɓa gani ko kin taɓa jin zalinci ta ɗaure ne? To jama'a sai a kula, komai yana da iyaka yana da karshe musamman ma zalunci!!. Aka ce idan jemun ɗan uwanka ya kama da wuta?? Ku ƙarasa mun!!.
Baiwar Allah Mahnoor tun da ta shiga É—aki kuka take yi sosai har Mahreen ta shigo ta sameta. A gefenta ta zauna suka cigaba da kuka a tare, ba mai rarrashin É—an uwan.
Shi kuwa Jaish da ko a jikinsa, shiryawa ya yi ya fito ya kaÉ—a dabbobin bappan ya tafi kiwo abinsa, yau bai ma jira bappan ba, dan ya ji lokacin da suka ce zasu je su nemawa Faisal magani, dan haka sai kawai ya tafi abinsa.
Bai dawo ba sai can yamma kamar yadda suka saba, bappan har lokacin bai dawo gida ba, dan kuwa Faisal dai a maimaikon sauki sai abin ya kara gaba sosai, kamar ya zare ne fa!.
Lokacin da ya dawo daga kiwon babu kowa a tsakar gidan, É—akin bappa ya nufa dan ya É—an huta sannan ya je ya yi wanka.
Yana shiga ita kuma tana fitowa, baya ta ɗan ja dan ta bashi hanya ya wuce. Ta sunkuyar da kanta ƙasa ta mannu da jikin bango.
Shiru bai wuce ba ya tsaya a bakin kofar. Ganin haka yasa ta É—an É—ago idanunta dan ta saci kallonsa ko me ya hana shi wucewa?.
Tana É—ago kai suka yi four eyes, dan kuwa idanunsa yana kanta, ba komai yake gani ba kuma face hawayen da yake saman face É—inta ga idanunta a cike tab da wasu zafafan hawayen.
Ƙasa ta sake yi da kai tana ƴan kame kama kamar maras gaskiya.
Hannu ya kai ya ɗago haɓarta, wani irin dukan uku uku kirjinta ya yi, wiki wiki ta fara yi da idanu kamar an tare ɓera a tarko.
Da hannunsa É—aya ya yi nuna mata alamar meyasameta take kuka?.
Kai ta fara girgiza mashi alamar babu kenan. Tabbas yaga tsoro a kwance a cikin idanunta hakan yasa ya yi tunanin duk yadda aka yi Nenne ce ta daketa, shiyasa ma taki faÉ—a, saboda tana tsoron bala'in Nennen.