Sashe 170
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannunsa dikka biyu yasa ya rabata da jikin nasa dan ya samu damar ganinta da kyau. Kin yarda ta yi ta fara tirje mashi ita ala dole ba zai kalleta ba. Ba dan ya so ba ya barta ta ɓoye face ɗin nata a kirjinsa.
Dikkansu biyu wani irin daɗi na musamman suka ji yana ratsasu, sun samu farinciki matuƙa.
"Kawo kayan na sanya maki na sake yi maki kwalliya irin na jiya". Ya faÉ—a a hankali.
"A'a Hamma zan sanya da kaina". Cikin girmamawa ta yi maganar.
"Bakiso na sanyawa matata kaya kenan?".
Kai ta gyaɗa mashi alamar e. Allah sarki a yanzu dai Jaish yana da ƙoƙarin rama alkhari da alkhari, domin kuwa dik ƴan uwan Mahnoor harda kakarta Inna sai da suka rinƙa haɗa shi da Allah a kan ya kula da ita, shi kuma ya ɗauka masu alkawarin yin hakan, shiyasa yake iya ka bakin ƙoƙarinsa wajen ganin bai karyar masu da zuciya ba, ya cika alkawari.
"To tashi kisa bari na je na yi wanka ko?". Da to ta amsa mashi, sannan ta raba jikinta da nasa.
"Bari na zo na surka maka ruwan Hamma". Ta faÉ—a tana É—ago kallonta a kansa.
Jinjina mata kai kawai ya yi idanunsa a kan gurun wuyarta, ya yi matuƙar burgesa sosai gaskiya.
Tana miƙewa tsaye da nufin ta ɗauki kayanta ta sanya hijabi ta shige ɗakin Mahreen ta sanya kayan a wajen ba zato ba tsammani zanin jikinta ya zame ƙasa, kwanciyar da ta yi a jikinsa yasa zanin ya kwance ba tare da ta ankara ba.
Kawar da kansa ya yi kamar bai ganta ba, dan yasan kuka zata sake yi mashi idan ya kalleta, shi kuma baya son kukan, dan ya yi wa bappa alkawarin ba zai barta ta yi kuka ba.
A miliyan ta kama zanin nata idanunta a kansa, tana son gane ya ganta ne ko bai ganta ba. Ganin yana kallon ƙasa yasa ta yi saurin ɗaura zanin nata, sannan ta ɗauki hijabinta ta zura, a hanzarce ta wuce izuwa ɗakin Mahreen dan ta sanya kayan.
Bayanta ya bi da kallon yana jin wani irin daɗi, weist beat dake ɗaure a weist ɗin nan nata ba ƙaramin burgesa ya yi ba, ta tafi da imaninsa sosai, sai ya ji tamkar ya kai hannunsa ya taɓa a lokacin da ya gani, dannewa kawai ya yi ya kawar da kallonsa dan gudun kukanta, amma bai so dai'na kallon weist beat ɗin nan ba gaskiya.
Weist beat ne da mamanta ta bar mata su wajen guda 20, sai ta ɗaura guda 5 ta ajiye saura, da Mahreen ta ɗan girma sai ta ɗaura mata 3 ta ajiye sauran 12 ɗin, sun yi matuƙar haskaka weist ɗinta sosai, sun ƙara fito mata da shape ɗinta sosai, ga duwatsu beat ɗin sai wani irin sheki suke yi tamkar sabbi, kuma ya kai shekaru 3 a ɗaure a weist ɗinta fa, kawai suna da kyau ne da quality.
Haƙiƙa surar jikinta ya tsaya mashi a ransa, dik da yau ne karo na farko da ya fara gani, amma ba shakka ya kwaɗaitu ya kuma so shagaltuwa da kallonta kada ya daina, ashe tasan meyasa take ɓoye jikinta, ta tara abubuwan da zasu ɗauke hankalin dik wanda ya kalleta ne yasa take ɓoyewa.
Ya nisanta cikin tunanin dik wani motsinta tun ranar da ya fara É—aura idanunsa a kanta har izuwa yau, zazzakar voice É—inta ne ta katse shi a in da ta ce. "Hamma na juye maka ruwan saura ka je ka yi wankan kawai".
Nisawa ya yi tare da É—aura idanunsa a kanta. "Bappa yana waje?". Ya tambaya tamkar ba shi ya yi maganar ba, saboda yadda ya motsa lips É—in nasa a hankali.
"A'a bai dawo ba tukun nan". Tana magana tana satar kallonsa ta kasan ido.
"To zo ki zauna a nan kada ki fita waje bari na yi wanka na zo".
Ƙarisowa ciki ta yi tana amsawa da to. Miƙewa shi kuma ya yi ya nufi waje.
Saman mattress É—in ta haye ta kwanta tana tunanin yadda ta ji jikinsa a karo na biyu, abin ya tsaya mata a rai, ita kaÉ—ai kamar ba lafiya ba sai ku ga ta saki murmushi, idan kuma ta tunano yadda zaninta ya kwance a gabansa sai ta É—an É—aure fuska a fili ta ce Allah yasa bai ganta ba, in ta tuna yadda ya rarrasheta kuma sai ta ji wani irin farinciki na musamman yana ratsata.
Da yake akwai ɗan zazzaɓi a jikinta sai yasa barci ya ɗauketa a ɗan wannan kwanciya shiru da ta yi tana tunanin, kun san zazzaɓi da iya saka mutun barci, musamman ma idan ya haɗu da mura.
Sosai barci ya É—auketa kafin ya fito wankan, ko da ya gama wankan ya dawo cikin É—akin barcin nata ma har ya É—an yi nauyi.
Ɗan zuba mata idanu ya yi yana jin tamkar ya kai hannu ya ɗage rigar nata ya kara kallon weist beat ɗin nata, sun yi mugu mugun tafiya da imaninsa, da gurun wuyarta da kyansa ya ratsa zuciyarsa matuƙa, abu biyun nan sun tsaya mashi a rai.
A gefen bed É—in ya zauna ya kasa cire idanunsa a kanta, zuga shi kawai zuciyarsa take yi tana ingiza shi da ya É—age hijab and rigar nata ya ga beat É—in.
Daga karshe dai kasa hakura ya yi ya kai hannunsa, haka kawai yau karo na farko a rayuwarsa hannunsa ta fara kerma dan zai taɓa wani abin, kamar wani maras gaskiya.
Kamar zai fasa, sai dai kuma zuciyarsa taki aminta da ya fasa É—in, da kyar ya iya kai hannu nasa ya É—age mata hijabin a hankali, yau fa zuciyar maza sai harbawa da karfi take yi kamar dai wanda yake cikin tsananin tsoro, ashe akwai abin da zai bawa Jaish tsoro? To tsoron me ma yake ji?
Ya yi babban sa'a riga da sket ce a jikinta ba doguwar riga ba, kunga ya samu damar É—aga rigar ba tare da wata wahala sosai ba.
Wani irin faɗuwar gaba ya ji a lokacin da ya kama gefen rigar nata zai ɗaga..... Ni kam na ce su Jaish ana satar kallewa yarinya weist, kai anya yaran King Zuhair akwai mai ta ido kuwa? Dan naga kunyar Jaish ɗin ma yana neman komawa sai kan wanda ya zaɓa zai ji ta, ko da yake Mahnoor kanwarsa ce.........😂
(Maman Sultan kina zagin Yah Jawad kullum to ga Jaish ɗinki zai yi satar kallon jigidan yar mutane 🤔 ku kuma haka kuke kenan da satar kallo ko? Gara shi Yah Jawad kai tsaye ya tafi ɗoɗar, to wlh ku canza hali, ku canza hali maman Sultan, ki zo ki koyawa Jaish lamura ato, idan ba haka ba mu miki.............. Na dai yi shiru.)
Yana yi yana fargabar kada ta farka ta kama shi ya ji kunya, kamar mai É—aga kwai a saman bajajjen faranti haka ya É—age rigar tata.
Aikuwa yana ɗagewa ta firgita ta miƙe zubur a tsakiyar mattress ɗin. Tana miƙewa ta waro idanunta da suka yi ja saboda barci.
Kai tsaye suka yi ido huÉ—u da shi. Allah sarki tsabar tana killace jikinta ma har ga kai ga tana cikin barci ma in aka buÉ—e mata sai ta farka.
Ganin shi ne yasa ta yi ƙasa da kai jiki dik a mace, shi ma wani irin kunyarta ne ya ji ta kama shi, sai ya ji dama bai yi ba.
"Ka yi hakuri Hamma, na tsorata ne shiyasa". Muryarta ta daki dodan kunnensa.
Shiru ya kasa furta uppan, saboda bai san me zai ce mata ba. Sallar la'asar ma fa zai yi ya biyewa ruÉ—un zuciyarsa na son ganin beat É—in, yanzu ga shi ta ja mashi jin kunya.
"Noor ina son wannan beat dake kwankwason naki, sun mun kyau sosai". Ya faÉ—i hakan yana É—ago da kallonsa a kanta.
"Ina da wasu a É—akin bappa, in É—auko maka ne?".
Kai ya girgiza mata tare da juyowa gareta da kyau. "Wannan da yake jikinki ne ya burgeni ba wanda yake É—akin bappa ba".
Ƙasa sosai ta yi da kai, cike da kunya ta ce. "To bari na je ɗakin Mahreen in ciro shi na kawo maka shi".
Ajiyar zuciya ya sauke. "Ba amfani zan yi da su ba, in gansu a jikinki shi ne kyan, sun yi matuƙar dacewar da ke, ki yi hakuri na tasheki daga barcinki".
Shiru ta yi ta rasa abin faɗa. Ganin bata yi magana ba yasa ya miƙe ya nufi saman dadduma. Hiƙama ya tayar tare da kabbara ya fara sallah.
Zuba mashi idanu sosai ta yi, dik yadda zai motsa a sallan idanunta na'a kansa babu ko kyaftawa. Cikin nutsuwa yake gabatar da sallarsa.
Sai dai yana idarwa ta yi saurin kawar da kallonta daga kansa. Addu'oinsa ya gabatar kafin ya miƙe ya nufeta. Tana zaune kamar yadda ya barta bata motsa ba.
Gefenta ya zauna ƙasa kasa ya ce. "Ki kwanta ki cigaba da barcinki mana".
"Barcin ya watse ai, kuma kaga babu kyau yin barcin bayan la'asar, yanzu ma ban sani bane barcin ta É—auke ni". A nutse ta yi maganar.
Jinjina kansa ya yi tare da cewa. "Nima da kwanciya zan yi amma na fasa bari na je waje".
Da to ta amsa mashi, miƙewa ya yi ya fita waje. Ita ma miƙewa ta yi ta bi bayansa.
A tsakar gida ta zauna tare da buga uban tagumi tana tunanin abin da ya faru a yanzu na É—age mata riga da ta kamasa ya yi. Wani irin bakon yanayi mai wuyar ganewa ta ji yana shigarta.
A haka har Mahreen ta dawo daga islamiyya ta sameta, goshin mangariba kenan. A lokacin kuma Nenne ta dawo cikin gidan.
Kamar wata munafuka ta yi ƙasa da murya ta ce. "Ke Mahnoor mijin kin nan yana nan?".
Kai ta girgiza mata alamar a'a baya nan ya fita.
Ajiyar zuciya ta sauke. "To tashi ki zo ki mun wanki, kayana dik sun yi datti, kin fi sati rabonki da yi mun wanki, dan haka tashi maza ki yi mun da sauri".
Ba musu ya amsa da to, fuska ba yabo ba fallasa ta miƙe ta bita izuwa cikin ɗakinta.