Sashe 118
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru ya É—an yi yana tunanin irin rayuwar nan tasu, shi dai kunga ya taso ya samu King matansa har uku, kuma kowacce da Æ´aÆ´anta, amma basu yin irin wannan zaman kishi na cutar da Æ´aÆ´an nasu haka, su ba ruwansu suna kaunar Æ´an uwansu, ba ruwansu da uwa daban daban suke, su dai sun san ubansu É—aya, ba ruwansu da kishin da iyayensu mata zasu yi, amma a nan ya rasa me matsalar Nennen nan, dan ba ke kika haifi yarinya ba sai ki yi ta gallaza mata? Ke kika halicceta ne?.
Zame hannunsa daga haɓar tata ya yi tare da shigewa ciki. Bappa da yake tsaye a bayansu tun ɗazun yana ganinsu ne ya fara zubawa Allah godiya a cikin ransa da Allah yasa aka ɗaura auren nan, a cewarsa soyayya suke yi da ya gansu a tsaye haka, bai san cewa shi Jaish tun da yake ma bai taɓa shigar mata faɗa ba, kai bai ma taɓa matsowa kusa da ita kamar yau ɗin ba, yana dai shigarwa Mahreen faɗa, dan ita kunga ai mutuniyarsa ce, amma Mahnoor gaskiya babu wani abin da ya taɓa haɗasu ko da sunan wasa.
Yana sake haɓar tata ta nufo waje da sauri, karaf suka ci karo da bappa. Gaisuwa ta ɗaga mashi tana goge hawayen face ɗinta.
Hannunta ya riƙo suka koma cikin ɗakin. Yana zaune a bakin bed suka isko shi, ya kurawa yatsun hannunsa idanu yadda kuka san yana son tuna wani abin.
Kusa da shi bappa ya zauna tare da sanya hannu ya kamo nasa hannun da ya kurawa idanun. Ita dai tana tsaye tana ganin ikon Allah, tana jiran ta ji me bappan nata zai ce?.
Buɗe tafukan hannun Jaish ɗin ya yi tare da matso da ita ya ɗaura nata hannun da ya riƙe a kan nasa. Cikin harshen larabci ya yi mashi bayanin cewa ga amanarta nan ya bashi ya ga dai marainiyar ce, ya dubi girman Allah ya riƙe mashi ita amana, kada ya kuntata mata, kada ya zalunceta, yana da tabbacin Mahnoor yarinya ce mai biyayya, kuma In Sha Allah zata yi mashi biyayya fiye da yadda yake tunani.
Shiru bai ce komai ba, sai ma sunkuyar da kansa ƙasa da ya yi, bashi da wata damuwa da wannan aure, dan bai san wanene shi ba ma.
Slowly ya ɗago da kallonsa, saman face ɗinta ya sauke kallon nasa. Kana ganin face ɗinta zaka san a firgice take baiwar Allah, tana son ta tambayi bappa meyasa za'a aura mata shi? Amma kuma kunya ya hanata, ita ba shi take so ba! Hamma Faisal shi ne zaɓinta, shi ne ta buɗe idanu ta kallah a matsayin masoyi, tsawon shekaru 5 kenan suna tare a matsayin masoya, tun bata fi ƴar 9 years ba kenan, kawai rana tsaka a zo a canza mata da wannan mutumi da take tsoro? Kai gaskiya abin da sake.
Amma dai haka ta daure tana tunanin wa kanta mafita. Haƙiƙa Jaish ya ga wasu abubuwa kwance a cikin idanunta, sosai ta bashi tausayi, shi ba yana tausayinta dan auren da aka yi masu aka rabata da Faisal bane, a'a, yana tausaya mata halin da take ciki a cikin gidan, dama Allah ya gani ba shi yake yi waɗan nan ayyuka da take yi ba, amma wlh ganinta kawai yake tana aikin ya gaji, wlh ya gaji da ganinta tana bautatuwa da tsabar bakar wahalar da take sha.
"Hamman Mahreen". Bappan ya ambaci sunansa. Dawo da hankalinsa haÉ—e da kallonsa a kan bappan ya yi, sai dai side É—insa ya kalah, ya ki yarda su haÉ—a idanu.
"Baka amsa mun ba, ka karɓi amanar da na baka? Zaka riƙe mun ita da amana?".
Shi kam me bappa zai nema a wajensa da zai ki yi mashi? Irin yadda bawan Allahn nan ya nuna mashi kaunar da iyayensa ne kawai zasu iya nuna mashi irinta a duniya, ai koma me ya yi bai biyasa ba, kuma koda bai ce mashi ya riƙe mashi ƴa da amana ba wlh dole zai riƙeta, saboda shi tun ainahi ma ai ba maci amana bane, babu cin amana a jinin Modarawa.
Dan haka sai ya gyaÉ—a kansa sama kawai alamar zai cikawa bappan maganarsa. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya bawan Allah ya sauke, koba komai ya ji sanyi a ransa, kuma a yanzu duk duniya ba wanda ya kaishi sanin wanene Jaish É—in, yasan yana da zuciya mai kyau.
Sake hannayen nasu ya yi, da sauri ta juya zabar ɗakin dan wani irin kuka da ya zo mata, tun bayan kukan rashin mahaifiyarta da take dirza sai yau ne ta ji kuka mai zafi irinsa ya zo mata, duk azabar da Nenne take yi mata ko kaɗan baya taɓata kamar idan ta tuna rashin uwa a duniya, yau kuma ga rashin masoyin da ya sota tun tana ƴar shekara biyu a duniya, an haɗata da wani mutum mutumi kawai.
"Waru haÉ—o (zo nan)". Bappa ya faÉ—a cikin sanyin murya.
Ba musu ta dawo ta tsugunna a gabansa.
Miƙewa Jaish ya yi ya fice waje. Hannunta bappa ya riƙo, cikin sanyin murya ya fara bata hakuri tare da yi mata nasiha a kan ta karɓi kaddararta, ta dage ta ci jarabawarta, sannan ta sani Jaish ya fi Faisal nagarta da komai da komai, in ta yi hakuri a hankali komai zai dai'dai ta, sai magana ta karshe kuma shi ne. "Duk da nasan kina da kula da takatsantsan, amma ina son ki kara kulawa sosai, ki mayar da hankalinki wajen ganin kin gujewa abin da baya so, kin san cewa yana da zafin zuciya, kuma nasan ita ce kaɗai zata rinƙa kawo saɓani a tsakaninku, yana da zuciya da zafin nama, jininsa a tafashe yake, baya son abu sanyi sanyi da ɓata lokaci, ke kuma kina da sanyi over, dan haka sai ki kula, ki guji abin da zai sanya ransa ya ɓaci, dan idan zuciyarsa ta matso kusa komai yana iya faru, nasan kin san hakan, ina kara tunatar dake ne kawai, ki kula sosai, na mai tabbatar maki zaki ji daɗin zama da shi".
Kanta a ƙasa, ban da aikin kuka babu wani abin da take yi, ita dai Allah ya gani Faisal take so, bayan shi bata jin zata so kowa.
Rarrashinta bappan ya rinƙa yi, a haka Mahreen ta shigo ta samesu, ta dawo daga aikan da Nenne ta yi mata gidan Arɗo.
Ganin Æ´ar uwarta tana kuka ne yasa ta faÉ—o cikin É—akin da sauri tana tambayar ba'asi.
Rungumo juna suka yi tana gogewa Mahnoor É—in hawaye tana mai cigaba da tambayar bappa waye ya dakar mata Æ´ar uwa yaga tijara yau!!.
"Babu wanda ya daketa Mahreen, nasiha nake yi mata shi ne take kuka, ku tashi ku tafi É—akinku Allah ya yi maku albarka".
Da amin Mahreen ta amsa, sai ta É—aura da cewa. "Bappa ina Hammana?".
"Ya fita waje".
Miƙewa ita kuma Mahnoor ta yi ta nufi waje da sauri tana mai cigaba da dirzan kukanta. Da sauri Mahreen ta bi bayanta, suna shiga ɗaki ta kwanta a saman gado tare da ƙara rushewa da wani sabon kukan.
Sai aikin rarrashinta Mahreen ta fara yi, bata kulata ba kukan nata kawai take yi. Can kuma ko me ta tuna sai ta miƙe zaune a zabure. Da sauri ta diro ƙasa ta nufi waje tana goge hawaye.
Bokiti ta ɗauko ta juyo ruwan zafin dake saman wuta a kitchen, ta ɗebo na sanyi daga randa ta surka, sa hannu ta yi ta taɓa ya yi dai'dai. Ta ɗauka sai cikin toilet, tana ajiyewa ta fito da sauri. Already kunsan akwai hijabi a jikinta kullum dama, dan haka sai ta nufi waje kai tsaye.
Yana zaune a ƙarƙashin bishiyar kofar gida kamar yadda ya saba zama, gabansa ta ƙarisa, cikin girmamawa ta ce. "Hamma ga ruwan wankan can na kai ma, ka yi hakuri na manta ne yasa tun ɗazun ban kai maka ba".
Tun da ta fara magana ya kafeta da idanu yana kallonta, bai san meyasa yau ya ji kamar ta yi mashi kama da wata wadda ya sani ba, sai yake jin kamar ya taɓa rayuwa a wata duniya ta daban, kansa ya ji tana ɗan sara mashi a hankali hankali,
Magana ta gaskiya a lokuta da dama yana jinsu kamar Gimbiya Zunaira ce, baya cikin hayyacinsa, amma tabbas soyayya da yake yi wa kanwar tasa a jinin jikinsa yake, sau da dama yana jin kamar yana da wata wadda yake matukar kauna, yafi yawan ganin Mahreen a wannan matsayi shiyasa yake yawan sake mata, yau kuma sai ya ga hakan a tattare da Mahnoor, musamman ma yadda ta yi magana a kusa da shi, sai ya ji tamkar sun taɓa yin wata rayuwa a wata duniyar da ita, a zahiri ba da ita bane, da Zunaira ce.
Jin ya yi shiru bai ko motsa ba ne yasa ta É—ago da kallonta dan taga me yake yi. Tana É—agowa suka kalli juna ido cikin ido.
Gabanta ne ya bada ras a hanzarce ta yi ƙasa da kanta. "Hamma in tafi?". Muryarta ya daki dodan kunnuwarsa.
Miƙewa tsaye ya yi ya wuce gaba ba tare da ya yi mata magana ba. Da sauri ta miƙe ta bi bayansa. Kai tsaye cikin toilet ya nufa ita kuma ta wuce ɗakinsu.
Yau dai abincin dare turasa kawai baiwar Allah ta yi, amma ba dan daÉ—i ta ci shi ba, tunanin Hamma Faisal É—inta ne kawai a ranta, abin ya yi mugun sosa mata rai.
Haka baiwar Allahn nan yau sam bata rintsa ba, kamar yadda taga rana haka taga dare. Sai dai ba ita kaɗai bace bata rintsa ba, bappa kwana sallah ya yi yana rokon Allah da yasa Jaish ba mugu bane zai riƙe masa ƴa da amana, Allah Ubangiji ya bashi lafiya, sosai ya yi masu addu'a, shi kuwa Jaish yana ta barci abinsa.