← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 211

Sashe 95

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunani take yi tayadda zata haɗasu aure kafin ya koma Brazil, dan tasa baya taɓa wuce kwana biyu zuwa uku idan ta yi yawa in yazo.

Jugum jugum suka cigaba da zama a cikin parlourn, Auta ta yi barci saboda alluran da uncle Taheer ya yi mata, kowannensu da abin da yake tunani, uncle Abbas ma yana hanyar zuwa, saboda ya ji labarin abin da ya faru.

Muryar Yah Jawad ne ya karaÉ—e kunnuwansu a in da ya yi masu cikakkiyar sallama ta addinin musulunci. A É—ari kowa ya kai kallonsa kansu, tare yake da Chuchu, tamkar basu san anyi yaki bama, dukkansu biyu sun yi wanka, Chuchu kayan Gimbiya Fanan ce a jikinta, shi kuma Jawad kayansa, da alama akwai in da suka tsaya suka kwana har zuwa wayewan gari.

Miƙewa tsaye Momma ta yi tana faɗin. "Jawad ina kuka je? Ina kuka tafi kuka sanya mu cikin tashin hankali da jimami, tun daren jiya bamu da nutsuwa, mun rasa kwanciyar hankali da walwalarmu, babu ku babu daddynku".

Ƙarisowa cikin parlourn ya yi tare da sake hannun Chuchu da yake riƙe da shi, da alama ta sha kuka dan ga idanunta nan suna kumbure jajir da su. A gefen Auta ya zauna, a maimakon ya basu amsar da suke dakon ji daga bakinsa, sai ya ce. "Momma menene ya samu Auta?".

Gabaɗaya parlon binsa da kallo suke yi, Mammien dai da yake bata so dawowarsu a raye ba sai ta haɗe rai, ta ƙasa hakuri da son jin daga ina suke ta ce. "Ana tambayarka daga ina kuke kana sake jefa mana wani tambaya?".

Dawo da kallonsa a kanta ya yi tare da cewa. "Daga part É—inki muke, a nan muka kwana".

Wani irin ƙululun bakin ciki ne ya tokare mata maƙoshi, danasani ta fara yi na barin gate ɗin part ɗin a buɗe da ta yi, duk sai ta ji dama bata tambayesa ba, yanzu amsarsa ya ƙona mata rai matuƙa.

Haƙiƙa Momma ta lura da cewa Mammie bata ji daɗin bayyanarsu a parlon ba, sai dai bata munana mata zato wajen tunanin ko bata sonsu ne yasa ba ko tana yi masu fatan mutu, sai ta kyautata mata zato ta hanyar cewa kila dan basu dawo da wuri bane sun wahalar da zuƙatansu wajen tunani ina suke ne yasa Mammien ta ji babu daɗi har alamar jin haushin ganinsu ya bayyana a saman face ɗinta.

Mummyn Chuchun ce ta ce. "Kai amma masha Allah, Allah mun gode maka da ka kare mana Æ´aÆ´an nan namu, Allah ka kara kare mana su da kariyarka a koma ina suke".

Da amin dukka parlon suka amsa.

Kuka Chuchun dake tsaye bata iya ƙarisowa cikin ba ta fara yi. Hankali a tashe Jawad ya tambayeta lafiya take kukan? Da kyar ta iya bashi amsa a kan saboda Auta take kuka. Hakuri ya shiga bata tare da gaya mata ai zata samu sauki.

Ƙarisowa wajen Autar ta yi tare da kai hannu tana taɓa kumatunta tana mai cigaba da kwallah haɗe da sambatu ƙasa ƙasa.

Akka ce ta ce. "Zo nan Jannat!". Da kyar ta iya miƙewa, kusa da ita ta je ta zauna, goge mata hawaye Akkar ta fara yi haɗe da lallashinta har sai da ta yi shiru.

Mummyn Gimbiya Chuchu ta sake cewa Yah Jawad. "Jawad zama bai kama ku ba ai, domin kuwa daddynku bai dawo ba".

Hankalinsa na'a kan Auta ya amsa da cewa. "Daddy ya tafi fillin kaka ai, mun haɗu da shi a lokacin da muke ƙoƙarin shiga part na dad".

Momma dake ƙoƙarin komawa ta zauna ne ta dakata tare da cewa. "Alhamdulillah, Alhdulillah ya Allah, to Allah ya dawo mana da shi lafiya".
GabaÉ—aya suka amsa da amin, mummyn Gimbiya Chuchu har da sakin murmushi, nan take farinciki ya bayyana a saman fuskokinsu.

Akka kuwa cewa ta yi. "Meyakai Zuhair wannan wajen? Shin harin da aka kawowa masarautar nan tana da alaƙa da wajen ne?".

A hanzarce Jawad ɗin ya amsa da. "Gaskiya akwai alaƙa, domin kuwa daddyn ya ce mun saboda Spender suka kawo wannan harin, kinga kenan Queen Zarina ita ma a yanzu ji take yi ta kawo karfin da zata iya kwatar Spender a hannun daddy".

Shiru gabaÉ—aya parlon suka yi, can Mammie ta ce. "Amma dama Spender baya gidan nan ne?".
Da wani irin kallo Momma da Jawad suka bita, tambayar tata ya yi kama da na wadda take son a kwace Spender daga hannun King, yadda kuka san ita ce ma ta turo a kwace, dan yadda ta ce dama baya gidan ne ya yi kama da kamar ta gayawa wasu cewa yana gidan ne dama. Sai dai kuma duk parlon Momma da Jawad É—in ne kawai suka lura da ita, ba wanda ya gane hakan. Akka kam ma sai cewa ta yi. "E Spender baya gidan nan, Zuhair ya kawar da shi daga nan saboda irin su King Abdulkarim".

Shiru ta yi kamar mai tunanin wani abin, sarai Yah Jawad ya lura da yanayinta ya canza kamar bata ji daÉ—in cewa Spender baya nan gidan ba, sai dai bai kawo wani mummunar zargi a kanta ba.....

Spender a hannun King Zuhair? Black Tiger ya kama Sweetie saboda bukatar Spender? Queen Zarina ta turo a kwatar mata shi ta karfin tsiya! Me alaƙar waɗan nan mutane da suka haɗe wajen buƙatar abu guda? Ainahi shi Spender na wanenen? Kuma a halin yanzu ina ma Spender yake? Yana hannun wanene? Mu je dai zuwa akwai rikici a gaba!.

Shiru gabaɗaya parlon ya yi, can Chuchu ta miƙe tare da faɗin. "Mummy bari na je nayi wanka, kayan Aunty Fanan ɗin nan sun yi mun yawa, so nake in ciresu".

ÆŠan satar kallonta Jawad ya yi ta wutsiyar idanu, dama ya yi mamakin tun da suka shigo bata wuce nata room É—in ba, dan ita ta takura mashi su dawo cikin Æ´an uwanta dan ta yi kwalliya ta sanya kayanta, ba dan haka ba bai yi niyar dawowa yanzu ba, ya yi niya sai da rana zasu dawo, ya fi son ya ajiyeta ya yi ta kallonta yana samun nishaÉ—i kawai.

Daren jiya kwana ya yi bai yi barci ba, zama ya yi tana barci yana gadinta, saboda gani yake kamar mayaƙan Queen Zarina zasu shigo su cutar da ita, shi bama ta kansa yake yi ba, ita yake tunawa, tana barci yana ta kallon face ɗinta, Allah ya gani yana kaunarta fiye da kansa, ko ganinta da ido kawai ya yi yana tsintar kansa cikin matsanancin farinciki sosai.

Amsa mata da okey mum ta yi, da sauri ta wuce sai satar kallonta yake yi, shi fa baya gajiya da ganinta sam sam. Aneesa da Fanan ma a tare suka miƙe suka fita waje, suna fitowa Fanan ta ce. "Wai Aneesa ina Yah Jaish ne? Kwana biyu ban sanyasa a idanuna ba, ko ya yi tafiya ne?".

Girgiza kai ta yi tare da cewa. "E to ya yi tafiya sai dai kuma na ji dad da momma suna magana a kan ansamu matsala a tafiyar tasa, in da ya ce zai je an duba baya can, babu kuma wanda ya san in da ya tafi, yana lafiya ko yana da matsala ba wanda ya sani, yanzu haka dad ya ce su Yah Ramish su fara binciken ina yake, momma kuma ta ce a'a ya bari zata sanya yayanta ya nemosa, hakan zai sa cikin ƙanƙanin lokaci a gansa".
Idan baku manta ba na taɓa gaya maku cewa duk wani labari idan kana son sani to ka tambayi Aneesa zaka sami bayani dallah dallah kamar wata aljana, sai ka rasa a ina take samo gaskiyar labarai waɗan da babu alamar karya a cikinsu, komai yadda ya faru take faɗa, yanzu batun ɓacewar Jaish daga Momma sai Yah Jawad and Dad ne kawai suka sani, amma kunji ita har ta samu labarin da mamanta ma bata sani ba.

Zaro idanu waje sosai Fanan ta yi, nan take ta yi narai narai kamar zata yi kuka, dan ita fa yanzu da gasken gaske take bala'in kaunar Jaish, bata san kudirin Mammienta na son haÉ—ata aure da shi ba, abin da ta sani kawai shi ne tana son shi da iya gaskiyarta.

Murya a karaye ta ce. "Innalilahi wa inna ilahir rajiun, hasbunallah wani'imal wakil, ya Allah a duk in da wannan bawan naka yake ka taimaka ka kare mana shi da kariyarka, ya ilahi ya lilliahi, wayyo Allah, dan Allah Aneesa duk halin da ake ciki dan gane da shi ki rinƙa sanar da ni kin ji?". Ta kai karshen maganar hawaye na zuba daga face ɗinta.

Sake baki Gimbiya Aneesa ta yi tana mamakin Fanan ɗin, dan ita bata san da cewa tana dakon son Jaish ɗin ba, abin da ta sani dai basu sonsa saboda mugu ne, iyakarta kenan, amma yau ga Fanan har da kwallah dan ance ya ɓata? A baya kuma ba wanda ya kaita zaginsa na cewa shi mugu ne bashi da imani, abin da mamaki.

Shiru ta yi tana kallonta bata bata amsa ba har suka shiga cikin room É—in Fanan É—in, suna zuwa ta faÉ—a saman gadonta ta hau murzan kuka, mamaki ya hana Aneesa tambayar me ya sameta............

A ɓangaren Chuchu kuwa, tana shiga cikin ɗakinta wayarta dake saman bed ya fara ruri, a hanzarce ta ƙarisa wajen. My Yah Rizwan shi ne sunan da ya bayyana a samam screen ɗin.
Jikinta har kerma yake yi wajen tsumayar É—aukar wayar, ta yi kewarsa sosai. Picking call É—in ta yi tare da kara wayar a kunnenta fuska É—auke da murmushi.

Cikin sanyin murya ya ce. "Assalamu alaiki my jannaty".

Wani irin cool murmushi ta saki kafin ta amsa da. "My Yah Rizwan wlh na yi kewarka sosai, tun jiya fa ban ji daddaÉ—ar voice É—inka ba". Kamar zata yi kuka ta kai kashen maganar.

Siririn murmushi ya saki tare da cewa. "Am so sorry my Jannaty, ni kai'na na shiga damuwa sosai na rashin jin voice ɗinki, amma ayi hakuri kada ayi mun kuka, fatana dai Allah yasa my baby tana cikin ƙoshin lafiya haɗe da farinciki?".
Cool murmushi ta kara saki kamar tana gabansa kafin ta bashi amsa da. "Ina nan lafiya my noor, bari na yi wanka nazo mu yi hira ka ji?".
Chapter 95 · 0% Book details