← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 211

Sashe 52

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bappa dattijon kirki miƙewa ya yi tsaye, sam shi bai kawowa ransa kyamansa yasa Jaish ɗin ya turesa ba, ya yi tunanin ma ko dai Jaish ɗin ya ɗan samu wata matsala a ƙwaƙwalwarsa ne, dan haka sai bai damu ba ya kaɗe jikinsa tare da sake matsowa ya riƙe kafaɗun Jaish ɗin ya yi mashi sannu cikin sanyin murya, ga Mahreen kuwa a sume kwance a ƙasa, duk yadda bappa yake kaunar yarinyar nan amma ya nufi Jaish dan ya karrama kalmar nan ta bakonka annabinka, sarai kuma ya ga Mahreen ɗin, amma saboda kyan zuciya irin nasa sai ya zaɓi ya fara taimakawa bakon nan nasa, bai san cewa bakon nasa iyashegensa in ji Yah Jawad tana da yawa ba, i really like Yah Jawad, musamman yadda yake faɗarwa Jaish ɗin gaskiya, ga shi ya gaya mana gaskiya rashin kunya yake damun Yah Jaish ba kunya ba...........😂

Ko ya zai yi a karo na biyu idan ya ɗago ya ga still bappa da yake kyama ne ya riƙesa?...... To ni dai bari na leƙa Dubai mu gani.

DUBAI.......ABU ABDUSSALAM EMPIRE🌹

Kamar yadda Æ´an tahalikan nan suka faÉ—a haka kuwa a kayi a gidan suka sake kwana. Washegari da safe tun karfe biyar da suka tashi suka yi sallar asuba basu mayar da barci ba.

Misalin karfe 5:30 suka tsala wanka, Obaid ne ya fara yin wankar bayan ya fito Omaid ya shiga. Da yake su a dukkannin gidajen uncles É—in nasu suna da kaya a rooms É—insu sai suka shiga dressing room É—in suka fara shiri.

Wando three cuter na ɗaya daga cikin uniform nasu na swat suka sanya a jikinsu, sai farar t-shirt mai karamar hannu mai laushi sosai. Wow arab hairn nan nasu ya sha gyara na ƙin ƙarawa, sun yi kyau sosai, bafa zaku taɓa iya rabesu ba.

Komai nasu gwanin birgewa da ban sha'awa, suna kaunar junansu over, ga su da shegen son wasa da juna, yanzu haka da suka shiga yin brush bayan tashin su daga barci sai da suka yi ta tsokanar juna, Obaid na goge bakinsa yana wani lumshe ido irin barci bai isheshi ba, ya ratayo karamar towel a wuyarsa yana goge bakin kamar yana jin tsoron taɓa hakwaran nasa. Da gangan Omaid ya shigo cikin toilet ɗin ya salallaɓo a hankali ya zo ya kwace brush ɗin da yake goge bakin nasa da shi ya sanya a nasa bakin ya fara goge nasa fararen hakwaran.

A kule Obaid ya buÉ—e baki zai yi magana, ruwa Omaid É—in ya tarfo daga pampom dake wajen wash hand base É—in ya watsa mashi a fuska, shi ma a fusace ya tari ruwan ya fara watsa mashi ba dakatawa har sai da Omaid É—in ya gudu ya fita daga toilet É—in da brush É—in a bakinsa, É—auko wata brush É—in Obaid É—in ya yi tare da haÉ—a wani tsadaddun mayukan goge bakin nasu, sannan ya cigaba da goge bakinsa, haka zaku gansu suna wasa gwanin birgewa, amma kada kuso ku gansu suna shiryawa wani mugunta, a wannan part É—in sam sam basu da daÉ—in kallo.

Bayan sun kammala shirinsu Obaid ne ya fara ficewa waje daga É—akin. Omaid ya rufa mashi baya, sai dai shi Omaid yana fitowa part É—in brothers É—insu ya nufa, domin ya gaishesu ya duba jikin Ramish, shi kuwa Obaid da hannunsa take ta faman yi mashi kaikayi na ya je ya jibgi waÉ—an can criminals É—in ai waje gabaÉ—aya ya nufa.

A ɓangaren Leesharh kuwa, tasata a gaba Sharifat ta yi a kan lallai ta zo su je ta gaishe da Yah Ramish ɗinta. Sosai Leesharh ta tsorata, tana tsoron shiga ta gansu, dan da yake bata da gaskiya sai taga kamar idan suka ganta zasu gane abin da ta zo yi, wannan dalilin yasa bata son zuwa in da suke ko da Sharifat ta buƙaci hakan. Amma da yake yau rashin lafiya ne sai ta ce to su je ta gaishe da su ɗin.

Wanka ta yi ta shirya cikin arab abaya mai shegen kyau launin maroon color, ta yi matuƙar kyau sosai da sosai, ta yafa gyalen kayan a kanta, ba make up sai natural beautynta.

Fitowa suka yi suka nufi part na su Ramish É—in, zuciyarta sai dukan uku uku yake yi, fargabarta É—aya me zata je ta tarar? Wannan shi ne fargabar da take yi.

Baki a É—auke da sallama suka shiga room da Ramish É—in yake kwance, gabaÉ—aya family suna a tare da shi except Obaid da yake É—akin horo yana aikin da ba'a sanya shi ba. Omaid kuwa yana tsaye a kusa da Guyson yana latsa wayarsa, hankalinsa ma baya a tare da su, sai magana Abu Abdussalam yake yi mashi hankalinsa ya yi nisa, chatting yake yi da wata class mate É—insu da ta kasance kawar Obaid, Obaid suna shiri da yarinyar, sabuwar zuwa school É—in ce, ni da ku dai mun san sai hali yazo É—aya ake abota, to dai da walakin goro a miya a kan wannan yarinyar. Chatting yake yi da ita in da take gaya masu yanzu daddynta zai mayar da ita school su kuma sai yaushe zasu dawo?....... Nikam nace baban wannan yarinya da kasada yake, yarinya mace da aikin swat fisabilillahi, gaskiya bai kyauta mata ba, daga gani ita ma bata jin magana a gida kamar dai su É—in.

Wani irin muguwar faɗuwar gaba Leesharh ta ji lokacin da ta sauke idanunta a kan ƴaƴan King Zuhair, musamman ma Bilal da yake tsaye a kan Ramish dake kwance kamar gawa, haƙiƙa Bilal ya shiga tashin hankali sosai, idan ka gansa gabaɗaya a hargitse yake saboda tashin hankali, sai ka tausaya mashi.

Tun da suka shigo ta tsaresa da idanu tana ƙoƙarin tuna a ina ta taɓa ganin face ɗin nan, tabbas ta taɓa ganin face ɗin Bilal a wani waje, to a ina ne? Ta mance, amma tabbas daga fitanta a gidan AAJ zuwa yau akwai in da ta taɓa ganinsa. Sai dai kuma da ta sauke kallonta a kan Dr Raj sai ta kasa iya banbancesa da Bilal ɗin kuma, sai ta shiga ruɗanin waye ta taɓa gani a cikinsu? Kuma basu wani kama sosai, kawai dai jini ba wasa ba, sannan kuma kowani ɗan adam da yadda yake kallon mutun, kai zaka iya ganin kamannin wane da wane amma ba lallai wani kuma ya ga kamannin ba.

Bata ƙara shiga fargaba da faduwar gaba ba sai da ta sauke idanunta a kan Ramish dake kwance, Allah ya gani tana tsoron wannan bawan Allah, ba komai ya ja mata wannan tsoro ba kuma face rashin gaskiyarta, yanzu a jikinta tana jin cewa tabbas cutar da shi masu nikaf suke son yi, amma duk da haka bata tunanin kin taimaka masu saboda tana son babanta sama da kowa a rayuwarta.

Shiru ta tsaya tsoro da fargaba ya hanata yin magana kuma ta kasa ƙarisawa cikin ɗakin. Omaid ne ya nufo hanyar fita daga ɗakin yana latsa waya, hankalinsa ya yi nisa wajen chat da wancan yarinyar. Yana can yana taɓa waya har ya ƙariso tsakiyar ɗakin, bai ankara ba ya bangaji Leesharh dake ƙoƙarin kauce mashi hanya da ta gansa ya nufo in da take tsaye.

Ai kuwa yana bangazarta wayar hannunsa ta faɗi ƙasa. A ɗari ya ɗago kansa tare da zare idanu, ganin itace bai yi wata wata ba ya cire hannu ya dalla mata mari mai sautin gaske wanda yaja gabaɗaya ɗakin suka ɗago idanu suna kallonsa.

Ita kuwa a ɗari ta sanya hannun ta dafe ƙuncinta, wani irin azaban zafin marin da ta ji ne yasa ta fara ruwan zafafan hawaye ba tare da ta sani ba. Shi kuwa dama haushinta yake ji saboda suna zargin bata da gaskiya Guyson ya ce su rabu da ita kada su sake dangantata da mutanen banza, haushin hanasu bincike da ɗaukar mataki a kanta da Guyson ya yi ne gaja suka tsaneta sosai. Haushinta da yake ji yasa ya sake ɗaga hannu zai kara dalla mata mari a karo na biyu.
Da gudu Sharifat ta ƙariso wajen ta riƙe hannun nasa tare da saka mashi kuka, kafin ta iso wajen ta riƙe hannunsa ma Dr Raj da Rizwan har suna haɗa baki wajen cewa kada ya yarda ya kara mata mari, yanzu ma wannan da ya yi mata bata gama dawowa cikin hanyacinta ba, idan ya kara mata ai sai ta sume.

Abbie ne ya kalli Omaid É—in. "Jeka abinka my son". Ya faÉ—a.
Wucewa ya yi ba tare da ya ɗauki wayar tasa da ta faɗi ƙasan ba, a cewarsa wlh shi ba zai duƙa ya ɗauki wayar ba, idan kuma ya ce lallai sai Leesharh ta duƙa ta ɗauko mashi wayar ba zasu wanye lafiya da brothers ɗin nan nasa ba, bare ma yadda ya ji har suna haɗa baki wajen hana shi kara mata mari lallai ya tabbata ba zasu wanye lafiya ba, hakan yasa ransa a ɓace ya fice daga ɗakin ya kyale wayar a ƙasa tare da fisge hannunsa daga riƙon da Sharifat ta yi mashi......... Ran maza ya ɓac!!.

Sharifat ɗin ce ta tsugunna ta ɗauka mashi wayarsa tare da riƙo hannun Leesharh ɗin tana hawaye ta nufi waje. Bata kai ga fita ba Abbie ya dakatar da ita a in da ya ce ta zo. Ba musu ta juya ta dawo garesa, gefensa ya nuna mata ta zauna, hannu yasa ya kwantar da kanta a saman laps ɗinsa har lokacin tana riƙe da hannun Leesharh ɗin bata saki ba.

Goge mata hawaye Abbie ɗin ya fara yi tare da tambayarta me abin kukan to, shi ma Yah Rizwan tamyar da ya gefa mata kenan. Cikin kuka ta ce. "Abbie Yah Rizwan wlh I really like Leesharh, because she's so silent innocent and good girl, and marainiya ce, no dad no mum, bata da kowa sai Allah sai kuma ni, meyasa Omaid zai mareta dan sun bugi juna? Jiya Obaid ya mareta bata yi mashi komai ba, su idan basu son mutun sai su yi ta yi mashi mugunta, to ni ina son Leesharh sosai........". Da kyar ta ƙarisa maganar saboda ta tuna cewa Leesharh bata da iyaye.
Chapter 52 · 0% Book details