Sashe 91
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abin da baku sani ba shi ne, duk wanda ya yi kuskuren shiga wannan É—akin da Ronnie yake shiga da sunan É—akin Black Tiger, duk wanda ya yi kuskuren shiga wannan É—akin shikenan an shafe babinsa, magana ta gaskiya in dai ka shiga wannan É—akin to fa ka tafi kenan har abada, wlh mutum baya rayuwa, Ronnie kawai yake iya shiga kuma ya fito lafiya lou, wani lokaci ya fito da farinciki idan ya shiga, wani lokaci kuma ya fito fuska a É—aure, idan abin ta yi tsamari ma har da hawaye yana iya fitowa idan abin tafi karfinsa, duk da haka baya É—aukar good 5 hours ba tare da ya ziyarci cikin É—akin ba, to me a cikinta kenan?.
A yanzu ma bai kula Floris ba kai tsaye ya nufi wannan É—akin, da yake ita Floris É—in tasan me tsarin wannan É—akin sai ta ja da baya tare da nufar parlon dan ta jira shi a can.
A wannan karon ya jima a cikin É—akin, ya É—auki a kallah awa É—aya da rabi kafin ya fito, fuskar nan tasa a É—aure tamau kamar hadari, kai tsaye wajen part É—in ya nufa.
A parlon ya isko Floris sai safa da marwa take yi tana jiran fitowarsa....... Yana fitowa ko kallon in da take bai yi ba ransa a matuƙar ɓace ya nufi nasa room ɗin.
Da sauri ta rufa mashi baya, sai dai kafin ta iso ya banko kofar ya murza key ta ciki. Ƙasake ta tsaya a wajen tana mamakin abin da bai taɓa yi ba yau ya aikata, to me yake damunsa har haka? Ta jefawa kanta tambaya. Ganin babu mai bata amsa ne yasa ta ja ƙafafuwanta, jiki duk a mace ba kwari ta nufi hanyar nata room ɗin............
To fah me ya ɓatawa Ronnie rai har haka? Me aka yi mashi? Ina aka kai Sweetien? Me zasu yi mata? Da alama nasu game ɗin yanzu zai fara, sai ku gyara zama my people's, amma ni dai bari na leƙa wani part ɗin kafin mu dawo kan wannan cakwakiyar, dan su sai anyi masu shiri na musamman.
____________________🔥🌼🌹
DUBAI
Sanyin Acn da yake a ɗakin ne ya fara ratsa ƙashin jikinta har izuwa cikin ɓargo, hakan yasa ta fara motsawa, kyawawan yatsun kafafunta dake motsawa ne ya ja hankalinsa.
A hankali ya furta. "I will call you back uncle". Yana kai karshen maganar ba tare da ya jira amsar da za'a bashi ba ya katse kiran.
Kusa da gadon da take kwance ya matso, three cuter and t-shirt mai laushi na shan iskace a jikinsa, ya yi kyau sosai, arab hairnsa ya sha gyara matuƙa, sai tashin kamshi yake yi.
Number Dr Raj ya danna, short sms ya rubuta mashi tare da tura mashi, sannan ya zauna a gefen bed É—in yana kallon face É—inta.
A hankali yatsun hannunta ma suka fara motsawa, tamkar wadda aka dannawa allura da karfi ya karye a cikin jikinta haka ta waro idanunta da suke jajir kamar wuta waje, idanun nan nata a kumbure sosai saboda kuka, gabaÉ—aya from head to toe idan ka ganta sai ka tausaya mata, duk da tana sume kallo É—aya zaka yi mata ka fahimci lallai ba shakka a birkice take, sam bata da nutsuwa ko na second É—aya.
Mai da idanun nata ta yi ta datse su gam tare da fara faÉ—in. "Wlh zan yi, zan yi kome kuke so, kada ku cutar da rayuwata, wlh ni marainiya ce, ku ji tausayin maraicina............"
Shiru ya zuba mata idanu yana sauraron sambatun nata, ga dukkan alamu baya son taɓata ta daina sambatun, kamar akwai abin da yake son ji.
Sallamar Ummie a cikin room É—in yasa ta dakata da surutan da take yi, kai kallonsa kan room door É—in ya yi. Ummie ce da Sharifat suka shigo a tare. Da farko Ummie ta ce ba zata zo ta dubata ba, amma da Sharifat ta matsa mata sai ta hakura ta zo. Ummie fa har da launin fatar Leesharh da take chocolate yasa ta tsaneta ba iya dan tana zargin mijinta yana sonta ba, kun san wasu larabawan dama da tsanar bakake fata ba gaira babu dalili.
Zame haɗaɗɗen white glass dake face ɗinsa ya yi, a hankali ya mai da kallonsa a kan Ummie dake ƙoƙarin zama a saman haɗaɗɗun kujerun dake room ɗin........... Da sauri Sharifat ta dawo kusa da ita, a hankali ta fara ruwan hawaye tana faɗin. "Leesharh ki tashi dan Allah, tun jiya fa nake ta kiran sunanki amma kin ki tashi............" Dakatawa da yin maganar ta yi sakamakon hannu da ya ɗaura mata a saman lips ɗinsa alamar ta yi shiru.
A daƙile Ummie ta ce. "Ya jikin nata Bilal?". Shiru ya kafeta da idanu ba tare da ya amsa ba, dan kuwa mugun zarginta yake yi sosai, dama da shi da Ramish sam basu shiri da ita, shi Ramish dama baya shiri da kowa kamar wani aljani, gara Bilal ɗin sau dubu.
Ganin bashi da niyar amsa mata ne yasa ta miƙe ta nufi waje, sai ɗari ɗari take yi, dan kuwa yadda taga ya tsareta da idanun nan tasan akwai wani abin a ƙasa da yake zargi, nan take ta ruɗe, tunanin kashe Leesharh ɗin da suka shirya ita da hajiya two seater kawai ta fara yi, tasan su waye su Bilal ɗin sarai, ita ta renesu, zaƙwaƙuran jami'ai ne masu aiki da ƙwaƙwalwa, tun da suka sanya hannunsu a kan Leesharh is better for her da ta janye ƙudurinta, idan ba haka ba zata jawa kanta balai'n da dukka danginta babu mai iya tare mata, dan idan abin nasu ya motsa wlh ko maganar Abu Abdussalam basa saurara bare ta sa ran zasu ɗaga mata kafa, ta san pata pata zasu yi da ita, bare ma Ramish da dama shi ba wani jin maganar mutane yake yi ba, idan ya tsara abu fa to sai ya yi shi, idan ya tsara abu yasan cewa King Zuhair ba zai aminta ba to wlh baya taɓa yarda ya yi magana da King ɗin a lokacin har sai ya kammala abin da zai yi ɗin sannan ya nemi daddyn nasa haka yake wannan tafiyar, a duniya mamarsa ce kawai take yi mashi magana ɗaya baya bata hakuri bare ya ce zai kwatanta yin wannan abin, da zarar ta ce Ramish ka bar wannan abin bana so, to fa a lokacin zai share wannan abin daga ƙwaƙwalwarsa ya ce ya barta har abada, ita kaɗai take yi mashi magana ɗaya ba ƙari kuma ya bi cikin hanzari, uwa uwace, yana girmamata sosai.
Amma King idan ya ce mashi baya son abu ya rinƙa takura mashi kenan har sai ya kyaleshi ya yi.
Ummie na fita Dr Raj na shigowa, saura kaɗan ma su ci karo. Sannu ya yi wa Ummien tare da ƙarisowa ciki ba tare da ya jira amsarta ba. Sanye yake da kaya irin na jikin Bilal ɗin sai!.
A gaban gadon Leesharh É—in Dr ya zauna.
Kallon Sharifat dake ruwan hawaye Bilal ya yi. "Little tashi ki je room É—inki". Ya faÉ—a a sanyaye.
Miƙewa tsaye ta yi tare da nufar wajen da Ramish yake kwnace, bawan Allah ya yi wani irin haske sosai a kan wanda yake da shi, ba shakka wannan magani da Leesharh ta bashi yana da tsananin karfi sosai, ya sha wahala sosai ɗan tahaliƙin nan, ga shi sun ɓoyewa King Zuhair abin da yake faruwa, saboda sun san King yana matuƙar kaunar ƴaƴan nasa, idan ya ji labari komai zai iya faruwa, shiyasa suka ɓoye mashi, dama idan baku manta ba a baya ya buƙaci su Ramish ɗin su je, kunga a kan washegari zasu tafi ne wannan abin ya faru, shi ne Bilal ya sanar da King ɗin anyiwa Ramish kiran gaggawa a wajen aiki ya tafi, dan haka sai ya dawo zasu zo, to a haka suka rabu da King ɗin lafiya, basu je sun duba jikin Mama ba har ta warke. Sai dai abin da basu sani ba shi ne tabbas King ya san komai da yake faruwa dangane da su, dan kuwa yadda yake bibiyar rayuwarsu yana kula da su tabbas ko kansa baya kula da shi haka, duk wani abin da suke ciki yana sani, ya sanya masu kula da matakan tsaronsa a matsayinsa na uba na gari, su sam basu san da hakan ba duk da suke jami'ai, shiyasa wanda ya haifeka fa komai iliminka komai baiwarka da wayonka sai dai ka gwadawa wasu ba dai shi ba, dan kuwa shi dai a tsirara yake kallonka ato, gara ma mutun ya san da hakan.
King yasan komai, yana da niyar yi masu dirar mikiya a Dubai ɗin ne ma wannan yaki ya riskesu, da zuwan bazata zai masu, a tunaninsu sun ɓoye mashi.
A kansa ta É—an tsaya tana kallon face É—insa, har cikin ranta take bala'in kaunar Ramish, mafarkinta a kullum su yi aure, Allah sarki shi kuma bai ma san tana yi ba, bashi da ma wata kusanci da ita, yasan dai yana da kanwa mai kawo mashi abincin, sannan autarsu a gidan, shikenan, ba kaunar uwarta ma yake yi ba bare ace ita ma zai kaunace ta, uncle nasu kawai suke so Æ´an albarka.
Dr Raj ne ya ce mata. "Little zaki iya tafiya ba wata damuwa kin ji?". Jinjina kai ta yi tare da nufar waje da gudu saboda wani irin kuka da ya kubce mata. Duk abin da ya faru a kan idanun Leesharh da tun É—azun ta dawo cikin hayyacinta ya faru.
Tabbas tasan da cewa Sharifat na son Ramish, ta gaya mata tun lokacin da suka koma kwana É—aki É—aya, a lokacin ne ta fara nadamar abin da ta yi wa Ramish É—in, saboda ba karya Sharifat ta nuna mata kauna na wuce misali, idan ta cutar da Ramish tamkar ita ta cutar, a yadda ta kaunacetan nan kuma wlh tasan idan ta cutar da ita Allah ma ba zai kyaleta ba.