← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 211

Sashe 115

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba karya sun yi kyau kam matuƙa, kayan ya bi shape ɗin Leesharh sosai, dama na gaya maku tana da shape mai tafiya da imanin duk wani lafiyayyen namiji, mata ma idan suka ganta sai sun sake juyowa sun kalla bare maza.

Haƙiƙa Sharifat ɗin ta ɗan ji wani abin a ranta na ganin duk kayan da zasu sanya sai ya fi zama a jikin Leesharh tamkar dan ita aka yi, kuma komai na kayan iri ɗaya, amma sai ya fi bin shape ɗin Leesharh ya fita zat, ta kasa yarda cewa Leesharh ta fita good bye and welcome, da alama Sharifat tana da kishi sosai gaskiya.

Amma bata bari hakan ya yi tasiri, tana kore tunani, yanzu ma kore tunanin ta yi tare da riƙo hannunta suka nufi waje, kamar wasu taurari haka suke haskawa........... Eyeee my people's yara sun shirya sace zuƙatan zaratan samarin Abbie, gaskiya ne!! To dai mu je zuwa muga su zasu yi nasara ko dai samarin Abbien ne zasu yi nasara.( Ni dai na ce Leesharh Sharifat zata kai ki ta baroki ar
To🥱🤣)

Kayan abincin nasu Sharifat ta É—auko, a parlon suka isko Ummie and Abbie suna yin breakfast, cikin girmamawa ta É—agawa Abbie gaisuwa, da yake shi ba mutun ne mai fara'a ba, kamar dai Mommar Zunaira yake shi ma, bashi da fara'a sai waÉ—an da yake kauna sosai yake sakarwa fuska, hakan yasa face ba yabo ba fallasa ya amsa mata gaisuwar tata tare da zuba masu ruwan albarka.

Amin suka amsa da shi, sannan suka juya, Leesharh ta É—agawa Ummie gaisuwa, ita kuma Sharifat ta É—an yi gaba da kayan abinci.

Rai a jagule ta amsa a takaice da lafiya, da alama amsar ma bata kai zuciya ba, saboda Abbie yana wajen ne ma yasa ta amsa.

Bayan Sharifat ta bi suka nufi part na samarin Abbien.
Yau a parlon ta samesu dukkansu, sun sauya shigar da yake jikinsu daga jallabiya izuwa ƙananan kaya. Bilal and Ramish suna sanye da hoodies dan ana ɗan sanyi sanyi, shi kuwa Dr Raj t-shirt and Jeans ne a jikinsa.

Ramish yana riƙe da cup mai ɗauke da cappuccino, yana tsaye a tsakiyar parlourn, ga zura hannu ɗaya a aljihun wandon jikinsa.

Bilal yana tsaye wajen center table, ya É—aura kafarsa É—aya a saman center table É—in tare da haÉ—e hannayensa dukka biyu waje guda ya zubawa Ramish É—in idanu, shi kuwa Dr yana zaune saman two seater yana binsu da kallo, da alama magana mai mahimmanci suke tattaunawa.

Sallamarta yasa suka dakata da maganar da suke yi, dama Dr Raj ne yake magana a lokacin. Da kallo Dr ya bi Sharifat É—in, shi kuwa Ramish da kallonsa yake a kan Bilal bai yi mashi kamar ma mutane ne suka shigo cikin parlourn ba, ko gezau bai motsa ba.

Bilal ma dai satar kallonsu ya yi dan gulma.

"Hakan ba mai yiwuwa bane, is better for you to look for another way". Ramish ne ya yi maganar a sanyayye, har lokacin kallonsa naa kan Bilal.

Mamaki ne ya kama Leesharh na jin maganarsa, tamkar ba muryan maza ba, ba kuma muryan mata ke garesa ba, da yawan maza suna da ƙaton murya, muryarsu a fashe yake, amma shi muryarsa tana da sanyi sosai ga daɗi sauraro sai kaifi irin na King Zuhair.

Ajiyar zuciya Sharifat ta sauke domin wani sanyi ta ji a ranta na sauraron voice É—insa, baya da yawan magana, ko kana tare da shi zaka jima baka ji maganarsa ba, muryarsa mai tsada ce.

A saman table ta É—aura masu abincin nasu tare da nufo saman sofa kusa da Dr Raj ta zauna tama murmushi.
Turus Leesharh ta tsaya a wajen table ɗin, already Sharifat ta wuce gaba ta barta, ita kuma tana tsoron ƙarisawa wajen nasu ita kaɗai, sai kawai ta tsaya turus a wajen.

Bilal da tun da suka shigo yake satar kallonta ta wutsiyar idanunsa ne ya juyo da kallonsa mai gabaÉ—aya a kanta, ta tsaya kamar wata sakarya tana raba idanu.

Kamar zai yi mata magana sai kuma ya fasa, saboda Dr Raj ya saka mashi idanu a kanta, sai ya basar kamar bai ga tana tsaye ba.

Ganin tana tsaye yasa Sharifat ta ce. "Leesharh ki zo ki........". Ƙasa ƙarisa maganar ta yi saboda idanun masoyin nata da ya sauka a kanta, maganar da ta yi ne yasa ya kawar da kallonsa daga kan Bilal izuwa kanta, kaifafan idanun nasa suka sa ta kasa idasa maganar tata, Sharifat tana da abin dariya sosai, yayanta ne, gidansu ɗaya, tana bala'in sonsa amma tana bala'in tsoronsa, ko cikin idanunsa bata iya gani, ko maga take yi idan ya kalleta sai ta haɗiye maganar, ni kam zan ga ta yadda za'ayi wannan soyayya, na tausaya mata, dan kuwa shi dai Ramish bai san tana yi ba, infact yama tsani mahaifiyarta, ita ɗin ma albarkacin Abbiensu take ci ya barta tana zuwa part ɗinsu, ku kunsan yadda ya tsani Ummien nan da wuya idan zai yarda da wani zancen sonta, sai dai idan dole Abbien zai yi mashi, kuma wlh shi ba kunya ce da shi ba, dan ya zauna ya gayawa Abbie baya sonta ƙaramin aikinsa ne, mutum ne mai magana kai tsaye, ba ruwansa da abi da maganar zata haifar, shi dai zai faɗi san ransa ato, ga shi idanunsa babu kunya ko ɗigo, a bushe suke.

Jin takasa ƙarisa maganar yasa tun basu ganta ba suka gane Ramish ya kalleta kenan, dan kuwa ba ita kaɗai ba ko jami'ansa idan suna magana da zarar ya sauke idanunsa a cikin nasu sai sun sha jinin jikinsu su ɗan daga ta da yin maganar, sai daga baya su cigaba, yana da idanu masu kaifi ne sosai.

Ta wutsiyar idanunsa Ramish ya kalli Leesharh É—in jin Sharifat ta ce ta zo ta zauna, shi ne bari ya ga wacece ma?. Ga mamakinsa sai ya ga yarinyar da ya mara É—azun ne, tunani ya fara yi a kan wacecec ita É—in? Dan lokacin da Abbie ya Æ´antata ai kunga yana sume.

Wata zuciya ce ta ce mashi bai wuce kwashen Æ´an uwan Ummie bane, tuna hanan yasa ya nufi saman table É—in dan ya yi breakfast abinsa, a cewarsa dik abin da ya shafi Ummie bashi da lokacinsa.

A hanzarce Sharifat ta miƙe, fuska a ɗauke da ƙayatattcen murmushi, tana murna ta ce. "Yah Ramish bari na yi serving ɗinka". Allah sarki soyayya kenan, har wani nishaɗi take ji a duk lokacin da take yi mashi hidima, daɗi sosai take ji, shi kuwa tamkar gunki bai san tana yi ba.

Yana isowa kusa da ita ta datse idanu gam, tun da ta ji marinsa ta ƙara jin tsoronsa sosai. Kamar bai ganta a wajen ba ya wuce ya zauna a saman chair, cike da murna Sharifat ta fara serving ɗinsa.

Zama Bilal ma ya zo ya yi a chair dake kusa da shi yana faÉ—in. "Lil zuba mun nawa abincin sai ki É—auki sister nan taki ku tafi".

ÆŠan turo baki ta yi tana satar kallon Ramish. "Ni Yah Bilal hira nazo taya ku".

Sarai ya kalleta tana satar kallon mashi É—an uwa, a ransa ya ce zaki yi ki gaji ki bari.

Ita dai Leesharh tana tsaye shiru, Dr Raj kuwa shiru ya yi yana nazarin maganganun da suka tattauna, da alama ba zai yi breakfast yanzu ba.

Zuba masu abincin ta yi, cike da class suka fara ci, ita kuma sai ta zauna a saman chair É—aya tana ta aikin satar kallon shi.

Shi kuwa Bilal duk ransa bai so tsayuwar Leesharh a tsaye ba, duk ya takura, yana cin abinci ne amma hankalinsa kacokam yana a kanta, ya rasa sukuninsa, amma kuma baya son kulata bare ya ce ta samu waje ta zauna, Dr Raj ya saka mashi idanu, haka dai ya daure ya danne yana ganinta a tsaye ba yadda za'ayi.

________________________🔥🤯

JIMETA YOLA NIGERIA.

GabaÉ—aya matasan nan kansa suka nufa, suna zuwa da nufin su hau jibga mashi sandunar nasu yasa hannu ya kwace sandar mutun É—aya tare da rage tsawonsa sandar da wani ya zo buga mashi ta wuce fiw bata same shi ba.

Cikin ɓacin rai ya fara jibgarsu da sandar hannun nasa da ya kwata yana kaucewa nasu dukan da suke kawo mashi, su da suke kiwo ma sun san ta yadda zasu daki mutum bare shi da yake renon Commander Zafar? Ai wlh lilis ya dakasu kamar ai aikosa, yana dukansu yana tunanin me ya yi masu suka zo jibgarsa haka?.

Tsurewa Nenne ta yi har ta ji cikinta ya murɗa, nan take ta ji tana son shiga banɗaki, wani tunani ne ya faɗo mata a ranta na cewa anya kuwa ba garkuwa ma ta haɗa Mahnoor da shi ba kuwa? A tunaninsu bashi da karfin iya nemo masu abinci da zasu ci ma bare har ya bata kulawa, sai ga shi ya jibgi matasa wajen guda 20 shi kaɗai, kuma ya iya kauce dukan da suka rinƙa kawo mashi bai taɓasa ba, gaskiya da sake, in dai haka ne wannan zai iya zamawa Mahnoor babban garkuwa ma kuwa, ba zai bari ta walaƙanta ba.

Nan take Nennen ta ji ina dole a raba wannan aure idan ma an ɗaura, dan su ba garkuwa suke neman mata ba, wanda zai walaƙantata suke neman mata...... Lallai akwai cakwakiya babba ma kuwa, tabɗijam!!.

Mahreen dake tsaye a bakin kofa ita da Mahnoor suna kallonsa ne ta daka wani irin uban tsalle tana faɗin. "Hammana jarumin namiji ne! Adda Mahnoor kina ganin yadda ya yi masu bahagon makahon duka! Wayyo daɗi kasheni, Hamma dan Allah ka koya mun irin wannan faɗar ka ji? Ina son in ga nafi kowa karfi a garin nan, dan na rinƙa dukan kowa a garin nan". Tana kai karshen maganar ta watsa a guje ta nufi she babu ko tsoro a tatare da ita.

Tana zuwa ta daka tsalle.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 30/10/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
Chapter 115 · 0% Book details