← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 203 OF 211

Sashe 203

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga bakin kofar shigowa parlourn Bilal da ya shigo a yanzu ne ya amsa da. "Hayaniyar mutane ne bama so yasa bamu je ba, ai ba laifinmu bane". Ya kai karshen maganar tare da shigowa ciki.

Hararar wasa ta watsa mashi kafin ta koma saman sofa ta zaune. "Kai Yah Bilal wato badan big bro yana part É—in nan ba da ba zan ganka ba ko?".

Saman sofar kusa da Ramish ya zauna, dik suna cikin shiga iri guda, sai suka haÉ—e kamar wasu twin's.

"Kai Big Aunty, ni ban san da Yah Ramish yana nan ba, kawai zuwa na na yi dan na dubaki fa".

Ta wutsiyar idanu Ramish ya kallesa, dan yasan karya yake yi, ya duba shi ne ta location É—in wayoyinsu yasan yana part É—inta shi ne ya biyosa, amma yanzu zai wani waske wai ita ya zo gani.

"Amma Aunty MieMie me yake damunki na ga fuskarki a haka kamar kina da damuwa?". Cewar Bilal again.

Ajiyar zuciya Ramish ya sauke, domin kamar Bilal ya shiga cikin zuciyarsa yaga tambayar da yake shirin yi mata kenan.

Fuskarta ne ya sauya izuwa ta damuwa sosai, cike da rashin jin daÉ—in abin da ya faru ta ce. "Nayi kuskure ne Bilal".

"Kuskure kuma?". Ya tambaya yana kai hannu ya ɗauki cup dake cikin tray ɗin da ta kawowa Ramish. Bottle watar ya ɗauko tare da ɓalle bakinta, ruwa ya zuba a cup ɗin, cikin nutsuwa ya kai bakinsa.

Jinjina mashi kai ta yi alamar kwarai kuwa kuskure.

Shanye ruwan tas ya yi tare da mayar da cup É—in ya ajiye, sannan ya ce. "Kuskuren me kenan?".

Ramish da yake kwance ne ya miƙe zaune yana binta da kallo, dan kuwa abin da zai saka Aunty MieMie a damuwa ba karamin abu bane, in baku manta ba jajirtatciyar jaruma ce, so sai suka zuba mata idanu suna sauraron su ji me ya ɗaga hankalin jarumar tasu.

"Na yi kuskure na ja dad ya haÉ—a Aneesa da Jawad aure yanzu haka rikicin dake faruwa a cikin gida ya hanani zuwa cikin, dik Æ´an uwana da su momma suna nan, mutanen Dubai dik suna nan, amma ni na kasa zuwa".

"Meyasa to?". Bilal ya sake tambaya.

"Aneesa ta sanar da mama cewa ni nasa dad ya yi mata aure da Jawad, ita bata son shi, yanzu haka mama ta É—aga hankalin kowa a cikin gida a kan ita ba zata yarda ba dole a warware wannan aure, bata ga wanda ya isa ya yi wa yarta auren dole ba, sai zagin mummy take yi wai ni muguwa ce meyasa ba zan sa a bawa Jawad Chuchu ba sai Aneesa? Wai dan ba uwa É—aya muke da Aneesa ba shiyasa zan cutar da ita, meyasa ban yi wa Chuchun da muke uwa É—aya uba É—aya irin haka ba? Dik hankalin kowa a tashe a cikin gida, shiyasa na yi zamana a nan kawai".

Ta kai karshen maganar kamar zata yi kuka, dan ita sam bata son wannan faÉ—a da iyayen nasu suke yi, kuma dik matsalar mamansu Ramish ce, ita ce bata da hakuri kuma bata da kawaici, ga shi yaran suna son junansu, kunga Bilal da Ramish kamar twin's suke, yanzu bayan waye zasu bi kenan? Ai kunga wannan faÉ—a sai dai su koma gefe su yi shiru kawai, dan basu da ta cewa, dik wanda ya ji zafin an zagi mahaifiyarsa sai dai ya sha Maltina mai sanyi dan zuciya ta sanyaya ya kawar da kai kamar bai gani ba kawai.

Shiru dikkansu suka yi, shi Ramish ma sunkuyar da kansa ƙasa ya yi, dan yasan mamarsa ce mai wannan matsala dikka, shi kuwa Bilal da ya ji mama tana can tana kwashewa mummynsa albarka dan Aunty MieMie ta yi laifi sai aka sauke a kan uwarsu sai ya ji ransa ta sosu, amma sai ya danne ya ce.

"To amma kema Aunty MieMie meyasa zaki ce dad ya bawa Jawad auren Aneesa? Baki yi shawara da ita ko tana da wanda take so ba kawai ki yanke mata hukunci". Yana magana yana satar kallon Ramish da ya yi ƙasa da kai ya rasa ta cewa.

"Bilal ba laifina bane wlh, bani na ce dad ya bawa Jawad Aneesa ba, ni Jannat ma naje rokan a basa ba Aneesa ba, abin ne ya juye mun ta yadda ban zata ba". Cike da damuwa sosai ta yi maganar, ga damuwar an bawa kanwarta wadda bata so, ga damuwar Aneesa na kuka da ita, sannan ga bala'in da ake yi a cikin gida, mama bata duba bakin da suka zo ba ta nemi ta zubarwa da King mutunci a gabansu, ta kafe dole a raba wannan auren ita bata bayar ba, Æ´arta wanda take so zata aura, kuma ita Æ´arta ba zata yi auren gida ba, bare zata aura.

A nan ne mummynsu Aunty MieMie É—in ta ce. "Kenan baki son haÉ—a jini da Abbas É—in ne?".

Nan fa ta fara sabon sababi a kan mummy na binta da sharri, Momma dai da bata son abin kunya sai ta wuce part ɗin King, dik da baki suna cike a part ɗin nasa dai tasan babu wanda zai shiga mashi uwarɗaki, dan haka sai ta wuce master room ɗinsa ta yi kwanciyar a saman bed ɗinsa ranta cike da damuwa, dan har ga Allah ranta ya sosu a kan yadda mama ta ke ƙoƙarin zubar masu da mutunci, sannan ta ji takaici yadda mamar ta nuna tana kyamar Jawad ya auri Aneesa, bata son haɗa jini da shi, ko me dalilinta?.

Dik fa wannan bidiri da ake yi a cikin gidan King or uncle Abbas basu da labari, bama su dawo daga wajen ɗaurin auren ba, suna can mama na bidirinta a nan............GIDAN SARAUTA KAGA ABUBUWA DAYAWA WLH, KOWANI RIKICI BA ZAKA RASA A CIKI BA, MUNAFURCI, MUGUNTA, CIN AMANA, ADALCI, RASHIN MUTUNCI, MUTUNCI, TIJARA, ƳAN ISKA, ƳAN ALBARKA, KAI KOMAI SAI KA GANI.

__________________________

"Aunty MieMie ni fa ban gane ba, ki mun dallah dallah, da farko kin ce kin yi kuskure, yanzu kuma kin ce bake kika ce dad ya aurawa Jawad Aneesa ba, ban gane ba". Cewar Bilal da ta ruÉ—ar da shi.

Nan fa ta fara gaya mashi dallah dallah a kan ita ta je rokarwa Jawad Jannat ne sai dad ya ce ya bashi Aneesa.

"Tab lallai kuwa, e a nan gaskiya ba'ayiwa mama adalci ba, kuma ita ma Aneesa ba'ayi mata adalci ba, ta ya za'ayi ba'a tambayi yarinya da mamarta ba kawai a yanke masu hukunci? Gaskiya ba'a kyauta masu ba, dole mama ta ji babu daÉ—i". Cewar Bilal.

Sarai Ramish yasan saboda shi yasa Bilal yake ƙoƙarin kawar da cewa mamarsa ta yi laifi, amma shi kansa yasan ta yi abin da bai dace ba, domin kuwa ko da King bai kyauta mata ba ai tasan in da zata samesa ba sai ta tsaya tana zazzagawa mummy masifa a idanun baki ba, wannan ai rashin mutunci ne, amma saboda ganin idonsa ne suke ƙoƙari nuna mamarsa ta yi dai'dai. Shiru dai ya yi yana addu'ar Allah ya canza mashi halin mamar nan tasa, masifarta ya yi yawa.

Shiru suka yi a parlourn, Aunty MieMie tana son gayawa Bilal irin zagin cin mutuncin da mama take yi wa mummynsu, amma kuma ta kasa yin hakan saboda Ramish dake wajen. Sun yi mashi kara suka danne.

Kada ku manta da Aunty MieMie da Bilal and Chuchu sune yara Mummy. Ramish and Dr Raj sai Aneesa su ne Yaran mama.

_____________🌹💘_____________

Sarina a hankali take lallaɓawa kamar wata ɓarauniya, daga gani bata kullo alkhairi ba, daga part ɗin mummy in da ake ta zuba uban dirama ta fito, sanye take da silk gown wanda ya bi shape ɗin jikinta, kunsan halinta da shegen son kaya mai fitar mata da dik wani surar jikinta.

Ganin hankalin su mummy dik yana a kan diramar maman ne ya bata damar gudowa part É—in momma ba wanda ya ganta. Can uwarÉ—akan momma ta shiga. Babu kowa a part É—in dik suna part na mummyn Chuchu.

Mama da neman bala'i har part ɗin mummyn ta je ta sameta, dama kuma kunsan a ƙaida idan irin wannan biki ya zo to baki sun fi sauka a part ɗin uwar gida, hakan yasa bakin suka fi yawaita a part ɗin mummyn, sannan kuma yarta ake aurarwa.

Ba ƙaramin daɗi ta ji ba a lokacin da taga babu kowa a cikin ɗakin Mommar, a hanzarce ta ƙarisa ciki har da rufo kofa, wlh Sarina bata da tsoro, ko me ya kawota room ɗin momma kuma?

Anata hidimar biki ita tana can tana faman kulle kulle, ko me suke kullawa kuma?.

Dik wasu drawers dake cikin É—akin ta hau bubbuÉ—ewa tana bincike a ciki, tana yi tana zaro idanu, zuciyarta sai bugawa yake yi da karfi karfi, har hannayenta na kerma alamar zallar rashin gaskiya.

Sosai ta hau bincike cikin ɗakin, har da kasan gado ta leƙa, momma kuma tana part ɗin King, kuyanga mama Haulat tana cikin gida wajen masu girki ta can baya kenan, momma ta wakiltata ta jagorancesu.

Dik wardrobe dake cikin dressing room sai da ta bubbuÉ—e kofofinsu, ba abin da bata buÉ—eba a cikin dressing room É—in, ganin bata samu abin da take nema bane yasa ta dawo cikin room É—in, jiki dik a mace ta juya ta nufi kofar fita, ranta dik a jagule alamar bata ji daÉ—in rashin nasararta ba.

Har ta kai tsakiyar É—akin sai kuma ta juyo da gudu ta dawo wajen mattress na bed, a hanzarce ta É—aga mattress É—in ta wajen pillows. Nan take wasu envelope har guda uku masu É—an matsakaicin girma suka bayyana. Wani irin murmushi ta saki mai wuyar fassaruwa, jikinta har rawa yake yi wajen kai hannu ta kwashi envelope É—in dikka.

A hanzarce ta saki mattress É—in ta ruga da gudu ta nufi waje, tsabar ta kware a sanya high heel haka ta kwasa a guje da shi a kafafunta a saman wannan tiles mai uban smooth É—in, kun san zai yi tsantsi ai, amma haka ta kwasa da gudu saboda buri ya cika, da alama aikota aka yi fa.
Chapter 203 · 0% Book details