Sashe 89
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru ta buga tagumi tana tunani rayuwarsu a baya ita da su Kamran, har yau har gobe son Kamran yana nan a cikin zuciyarta, shi take buri da muradin gani, ance so mugun wasa, so tabarmar kaya, idan ka iya zama kaji daÉ—i, akasin hakan kuma ka ji a jikinka.
Tana zaune a wajen bata motsa ba har Ronnie ya dawo hannunsa ɗauke da trayn abincin kamar yadda ya saba kullum. Yau tracksuit ce a jikinsa daga wandon har rigar, launin ash color mai ɗan duhu, ya yi wa kayan kyau, ya ɗaure korean up white hairn sannan sai ya baro wani mai ɗan tsawo kaɗan a gaban goshinsa, ya ilahi, ni kam naga madarar kyau da ban taɓa gani ba a nan, Koreans fa akwai madarar kyau matuƙa.
In da ya saba ajiye abincin ya je ya ajiye, tun da ya shigo take kure mashi kallo, har ya ƙariso gabanta, kamar dai kullum yatsunsa ya kyasta mata a saitin face ɗinta haɗe da sakar mata lallausan murmushi mai narkar da zuciya.
"What are you thinking?". Ya yi maganar yana wani karyar da murya tamkar budurwar da ta shirya yaudarar saurayi ta karɓe mashi kuɗi.
Macewa ta kara yi da kallonsa, ta rasa meyasa shi wannan Ronnien kome zai yi sai ya burgeta, abin ya fara bata mamaki, komansa gwanin birgewa da shiga rai, ga shi da shegen salo kala kala, yanzu idan ya yi maka wannan, to fa anjuma wani daban zai yi maka, sai ka rasa daga ina yake koyosu.
Ganin bata yi magana bane yasa ya matso kusa da ita tare da ciro tsadaddiyar haɗaɗɗiyar wayarsa, ya saita camera haɗe da saita fuskokinsu ya ɗaukesu a hoto yana faɗin. "Bari na ajiye tarihi, a duk cikin waɗan da yaya yake kawowa cikin empeir ɗin nan dan buƙatar Spender daga wajensu babu wadda na taɓa kulawa ma bare mu yi hoto, gaskiya ke you're the best my queen". Ya kai karshen maganar tare da zama a gefenta yana jin wani irin burgesa da take yi yana ratsa zuciyarsa.
"Ronnie kai É—in kyakkyawa ne ajin farko". Ta faÉ—a kamar mai raÉ—a. Da sauri ya juyo da kallonsa a kanta, gera guda ya É—aga yana murmushi tare da É—an É—aga kansa sama, shi kansa yasan shi É—in kyakkyawa ne, amma idan kyawawan fararen tattabaru irinsu Sweetie suka faÉ—a cewa yana da kyau sai ya ji daÉ—i sosai.
"Ronnie ina Floris?".
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da dakatar da murmushin da yake yi ya bata amsa da. "Floris ta tafi wajen wasa".
Shiru ta ɗan yi tana tunanin akwai wani abin a ƙasa da yasa baya zama tare da ita da Floris waje guda, idan suna tare da Floris da zarar ya shigo Floris ɗin zata yi dabara ta zulle ta bar wajen, idan shi ne yake tare da ita da zarar Floris ta zo zai miƙe ya fita ya ce yana zuwa, daga haka ba zai sake dawowa ba sai Floris ɗin ta fita, kuma ita dai tasan da cewa ba faɗa ya yi da Floris ɗin ba, to meyasa basu haɗuwa su uku su zauna su yi hira?. Ta jefawa kanta wannan tambaya da bata da amsarsa.
Ganin alamun ta shiga duniyar tunani ne yasa ya ce mata. "Come let's eat food first before you continue what ur doing, thinking thinking lady kawai".
Siririn murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Am okey, we eat together with Floris since 12:30".
Ɗan lumshe idanunsa ya yi kafin nan ya sake warosu a kanta. "Ban yarda ba, let's go kawai my Queen, if not ba zan ci abincin ba nima". A shagwaɓe sosai ya yi maganar har yana ɗan turo baki.
Habawa shagala ta yi da kallonsa, in ya yi wannan shagwaɓar a gaskiya yana kifar da Gwamnatin mata da maza dake kallonsa.
Ta shagala da kallonsa bata ankara ba sai jinta ta yi a sama ya ɗauketa cak, kai tsaye sai wajen da ya ajiye abincin ya direta. Ƙasa ƙasa ya furta. "Meyasa kike son saka gown ne ke kam? Ki rinƙa sanya kaya irin na beb Floris mana".
"Addinina bai aminta da irin waÉ—an nan kaya ba, addininmu ya ce mu suturta ko'ina na tsiraici a jikinmu, mu rufesa mu killacesa, dan duk abin da yake a buÉ—e ba abu bane mai daraja, mai daraja shi ne wanda ake rufe shi ruf babu wanda zai kallah sai mamallakinsa".
Shiru ya ɗan yi yana tattauna maganganun nata, can kuma sai ya ɗauko spoon tare da fara zuba abincin yana faɗin. "No ba haka bane, duk abin da yake buɗe ana ganinsa dole za'a fi sonsa, saboda kinga za'a ga kyansa har aji ana sha'awarsa, abin da yake ɓoye kuwa ai ba wanda zai gani bare ya ji sha'awarsa"............. A wannan magana ta Ronnie fa idan kuka mayar da hankali da kanku zaku fahimci darasin da yake ciki, dan kuwa ya buɗe maku gaskiya ce a fili. Cewa ya yi abin da yake buɗe shi jama'a suke kallah har su ji sha'awarsa, me yake kawo zinace zinace? Amsar ita ce sha'awa, kenan kunga wani lokaci mu da kanmu muke jawo irin su fyaɗe a'a saurayi ya yaudari yarinya ya lalata da dai sauransu, ya ce abin da yake rufe babu wanda zai kallah ma bare ya yi sha'awa, na san nan kun gane ma da kanku ba sai na tsaya dogon bayani ba, dan haka duk macen da ta suturta kanta a ko'ina daraja ne da ita, Allah dai yasa mu gyara laifukan da muke yi na fili da na ɓoye ya kuma yafe mana kura kuranmu. Amin.
Kawo mata abincin da ya É—eba a spoon É—in ya yi saitin bakinta. BuÉ—e bakin ta yi ya zuba mata, sannan ya tsareta da idanu yana kallon yadda take taunar abincin a hankali cikin nutsuwa. Sai bayan ta haÉ—iye ne ta bashi amsar sa da cewa. "Duk abin da jama'a zasu gani su yi sha'awarsa su kuma yi rububinsa kai kuma a matsayinka na mai zuciya me zaka yi da shi? Ai babu wata daraja a wajen abin da kowani shashashan kare da doki zai gani ya ji ya burgesa, wanda ya kai da wanda bai kai ba duk ya ji ta burgesa kenan? Hakan na nufin baka cika na daban ba kuma baka cika zakara a cikin empeir É—in nan ba kenan?!".
Ƙura mata idanu sosai ya yi har ta kai karshen maganar, nazari ya fara yi a kan maganganun nata.
Cigaba ta yi da cewa. "Idan har kai É—in zakara ne ko kuma kai na musamman ne to kamata ya yi komai naka ya fita na musamman, kamata ya yi ka nunawa jama'a da banbanci a tsakaninku, kamata ya yi ka zama cewa abin da kake so babu wanda ya isa ya gansa bare ma har ya so ko ya ji sha'awarsa".
Ban da kallo babu abin da yake binta da shi, kalamanta kamar sun yi tasiri a cikin zuciyarsa.
Ganin ya nutsa cikin kogin nazari da tunanin yasa ta kai hannu ta karɓi spoon ɗin hannun nasa. Nisawa ya yi tare da ɗan kawar da kallonsa daga kanta alamar ya dawo cikin hayyacinsa kenan. Abincin ta cigaba da ɗebawa tana kai mashi saitin bakinsa, a hankali yake karɓa yana tauna.
Tabbas ta lura da yanayinsa gabaÉ—aya ya canza, abincin ma taunarta kawai yake yi, amma ga dukkan alamu bata yi mashi ba.
Ta yi nisa cikin ciyar da shi É—in da take yi ta ji sautin daddaÉ—ar sexy voice É—in nan nasa ya daki dodan kunnenta a in da ya ce. "Waye ya koyar dake abin da kika gaya mun É—in nan?".
A takaice ta ce da shi. "Addinina". Adadi ya maimaita kalmar, jinjina mashi kai ta yi alamar tabbatarwa ba tare da ta yi magana ba. Shiru ya yi suka cigaba da cin abincin har suka ƙoshi sosai, bai sake yin magana ba.
Miƙewa tsaye ya yi jiki ba kwari ya ce. "Ba zan gaji da rokan yaya da ya barki muje wajen wasa ba, yanzu ma bari na je na roƙesa ya barki mu je fili ki ga wasana da zan buga, zan ji daɗin hakan". Yana kai karshen maganar ya nufi waje ba tare da ya jira amsarta ba.
Da kallo ta bi bayansa tana mai cigaba da yabawa tsantsar madarar kyau da Allah ya yi mashi, ga tsawo da faÉ—in kirji irin nasu na Æ´an Wrestling. Tana zaune a wajen har ya je ya dawo. Fuskarsa a É—auke da annashuwa, da alama yau dai ya yi nasara sosai.
Yana zuwa ya ja hannunta da nufin su tafi. "Ka tsaya na gyara É—akin mana". Ta faÉ—a a hanzarce.
"No ki barshi za'a gyara". "To ka bari in É—auko wani abin na rufe gashin kaina". Nan ma a'a ya ce mata, daga karshe ma sai ya É—agata cak, shi fa da alama yana jin daÉ—in É—aga Æ´an'mata kyawawa sama.
Kai tsaye wajen wasa ya nufa, yau wasan takalmin taya zai buga, su shiddane dai'dai zasu yi gasar, dukkansu sanye suke da tracksuit masu bala'in kyau da tsada, sai dai na Ronnie ya fi nasu kyau, dan shi na musamman ɗin na musamman ake buga mashi, tun daga company design ɗinsa daban dana kowa, babu kuma wanda ya isa ya sa ayi masa irin nasa ya sanya, idan ya yi hakan zai fuskanci mummunar hukunci daga hannun Black Tiger, hakan yasa ba wanda ya taɓa kwatantawa ma.
GabaÉ—aya Æ´an wasan jikin kayansu wajen cikinsu an rubuta number, kowa da numbersa, na Ronnie shi ne number one, shiyasa yau kuka ga ya É—aure gashin kansa, dan ya ji daÉ—in gudu.
Yana sako kafarsa a filin aka fara ihu ana tafi haÉ—e da fito, a kujeransa da yake zama kallon wasa ranar da ba zai buga ba ya zaunar da ita, Floris tana gefen master Devil tana aikin yin tapi jaruminta Ronnie ya shigo fili.
Takure jikinta waje guda Sweetien ta yi, ba komai yasa hakan ba kuma face master Devil da ta gani, tana bala'in tsoronsa, bare ma kirar jikin nan nasa dole aji tsoronsa, shekaru da dama yana Wrestling, yanzu kuma ya dawo horar da ƴan Wrestling ɗin, ai kunga dole ya razana duƙata, dole hantar ciki ta kaɗa da ganinsa!!.