← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 211

Sashe 96

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Okey ayi mun kwalliya sosai yanzu bai wuce saura 5 mins mu sauka a gida ba, kece burina da nake son fara yin tozali da kyakyawar face É—inta kafin kowa, dan haka ki shirya mun sosai".
Wani irin tsallen murna ta buga tare da É—an yin kara ta ce. "Wayyo Allah daÉ—i, Yah Rizwan ni kai'na burina na yi ido huÉ—u da kai, kada ka cinye mun lokacina, bari na yi maka kwalliya na musamman ka ji?". Kana ganin face É—inta zaka fahimci cewa tana cikin tsantsar farinciki mara misiltuwa, sai murmushi take yi baki ya ki rufuwa.

Shi kansa sai murmushi yake yi uncle Jahiz na ta tsokanarsa, dan a tare suka taho, jirgi daban daban suka hau, amma kusan tare suka sauƙa, sai dariya uncle ɗin yake yi yana cewa Allah ya yi Rizwan ya fara soyayya, saura su Ramish, sai dai shi kansa uncle Jahiz ɗin bai san da waye Rizwan ɗin yake waya ba, shi dai ya gane da mace ce, kuma soyayya suke yi.

Okey ya amsa mata da shi tare da katse kiran. Ɗaura wayar a saman bed ɗin ta yi, da gudu ta nufi toilet tana murna. A hanzarce ta shirya wankanta mai kyau, ta fito, cikin wani dandatsetsen doguwar riga mai matuƙar kyau launin purplish red, kayan ya yi matuƙar zama a jikinta, da yake calar tana da ɗan duhu sai hasken fatar ya ƙara fitowa sosai, umbrella gown irin na ƴaƴan sarakuna ne, haka ta ɗauko wani tsadadden alkyabbarta da ya sha kwliyar duwatsun gold, abaya ne na musamman wanda uncle Rahab ya saya masu ita da Auta iri ɗaya, yana da bala'in tsada saboda gold ɗin da yake ji, sai kyalli yake yi yana ɗaukar idanu, shi ta sanya a jikinta saman doguwar rigar tata.

Wai my people's nace ba? Shin kunga chuchu a cikin wannan haɗaɗɗen alkyabbar kuwa? Ya ilahi, kyau kam ya fita tsantsar fita, ta zuba perfume ɗin nan tamkar anyi ɓarinsa a jikinta, simple make up ta yi wanda zai ƙara fito mata da natural beautynta, lips balm ta sanya ba jan baki ba, hakan sai ya ƙara fito mata da pink lips ɗinta tamkar ta sanya jan baki.

Cover high heel ta É—auko kalar alkyabbar tata wato golden color ta sanya a kyawawan kafafun nata, ya ilahi ta yi kyau my people's, Chuchu ta cika Æ´ar wankar kuwa da gaske, ba dan ba dan ba da sai in ce tafi Guyson É—inmu iya É—aukar wanka, sai dai Guyson É—in ma fa ba baya ba, gwanine number É—aya.

40 mins ta ɓata wajen yin wanka da shiryawa haka, da yake ta saba yi sai bata wani ɓata lokaci ba, idan baka saba bane zaka ɗauki lokaci mai tsawo, amma ita ƴan mintuna sun isheta.

Jama'a ita da kanta ta san ta haɗu, kai duk wanda ya ganta sai ya kai zuciya nesa zai iya tsalle faɗawa tarkon sonta. A gaban dressing mirrornta ta tsaya, ta juya ta nan ta sake juyawa ta nan, sai dubawa take yi ina ne yake neman gyara ta ƙara gyarawa. Ganin ko'ina ya zauna dai'dai ne yasa ta ɗauko wayarta zata fara aikin ɗaukar hoton da ta saba, zuciyarta na can wajen masoyin nata wato Yah Rizwan, tunaninsa kawai take yi, tana son zuwa suga juna, amma ta tsaya ɗaukar hoto da yake abin ya zame mata jiki.

Wajen hotuna kala goma ta kashewa kanta. Bayan ta gama hoton ma sai da ta sake ƙurawa kanta idanu a cikin mirror, sai ɗan jujjuya face take yi dan ta ƙara tabbatarwa da kanta yes ta yi kyau.

Daga bayanta wajen room door cikin sanyin murya ta ji ya ce. "Jannat kin yi kyau har kin gaji da kyau, please kallon mirrorn nan ya isa haka kada ki kwashe mana kyan naki gabaÉ—aya".

Lallausan murmushi ta saki. "Kai Yah Jawad ka barin na kalli kaina da kyau, dan kada na bar wani waje bai gyaru da kyau ba ya rage mun kyauna ko ma ya ɓata gabaɗaya". Ta yi maganar tare da juyo da kallonta a kansa cikin wani irin salo na rigima da yanga mai jan hankali.
Bawan Allah ba da gangan ta yi mashi irin wannan salon ba, kawai rigima da yanga ce saboda ta ɗauki wanka. Shi kuwa wannan kallo da yadda ta juyo da yangar nan ne ta kara ruɗar mashi da ƙwaƙwalwarsa, ga shi ta yi kyau iya kyau, haba me Yah Jawad zai yi? Ai sai suman tsaye ya yi tare da ƙura mata idanu sosai.

(Na ce ban gane ba! Yah Jawad ya da haka? Komai Chuchu zata yi wa Yah Rizwan sai ka riga shi sani da gani🙄 watarana ma ka wani shiga tsakaninsu suna waya ka dakatar ka sanya chuchu katse kiran, nace ya ne? Yanzu ta tsara mashi kwalliya a matsayinsa na mijinta ka zo ka wani rigashi gani a kan menene wai?😒 Rai na ya fara ɓaci da abin da kakewa Yah Rizwan namu na zamani fa🌝 kabarsu su shana tun da kai ka ɓoye naka soyayyar haba mana, ko ya kuka ce my people's, sai ya rinƙa wani shiga tsakaninsu haka ake yi ne? Yanzu dai ga shi ya riga Rizwan ganin wannan tsadaddiyar kwalliyar, wannan abin ya sakani kuka😥😌)

Ganin ya kafeta da idanu ya kasa yin magana ne yasa ta É—age dara daran idanun nan nata sama tare da yin wani irin fari da su mai É—aukar hankali tana faÉ—in. "Yah Jawad wai kyau na yi maka ne da ka tsare ni da idanu haka?".

Shiru bai amsa ba, dan baya tare da ita, ganin face É—inta kawai yake yi yana hasaso gasu sun yi aure shi da ita........ Tab gaskiya da matsala idan har bai aureta ba, wlh idan aka hanashi ita da matsala, har wani hasasowa yake yi an É—aura masu aure, toh gaskiya akwai matsala.

Jin still bai amsa mata bane yasa ta sauko da idanun nata a kansa. "Yah Jawad!". Ta ambaci sunansa tamkar zata yi mashi kuka.

Wani irin ajiyar zuciya ya sauke tare da kawar da kallon nasa daga kanta izuwa ƙasa, ingazashi kawai zuciyarsa take yi a kan ya gaya mata abin da yake ransa kawai, dan a gaskiya yau ya ji ba zai iya hakuri sai ta ƙara girma ba, wani ɓangare na zuciyarsa ne ta ce mashi a'a ya bari ba'a irin wannan lokacin ya dace ya gaya mata ba, ya bari sai ya ɗauketa sun fita yawo sannan ya sanar da ita, hakan zai fi ɗaukar hankalinta. Aminta da hakan ya yi sannan ya dawo da kallonsa a kan nata, sai tura baki take yi wai yaki kulata dan haka ta yi fushi.

"Jannat ke ɗin duniyar kyau ce, sannan ta musammance kuma ta daban". Ya faɗa can ƙasan maƙoshinsa ta yadda ita kanta bata ji me ya faɗa ba.

Ganin sai turo mashi baki irin ta yi fushin nan take yi ne yasa ya tambayeta me ya faru?. Kin yi mashi magana ta yi, sai ma É—an murguÉ—a mashi baki cikin yanga tare da juya mashi baya da ta yi ita a dole ta yi fushi.

A hankali ta ji saukar hannunsa a saman shoulders É—inta, ya É—an rage tsawonsa tare da saita fuskokinsu suna fuskantar mirror, ta cikin mirrorn suka kurawa juna idanu babu ko kyaftawa.
Gera guda ya ɗaga mata tare da kashe mata ido ɗaya. Ai bata san lokacin da ta manta da fushi ta saki ƙayatatcen murmushi ba. Shima ɗan siririn murmushin ya sakar mata.

"Sarkin rigima kawai, yanzu me na yi maki da kika yi fushi?".

ÆŠan turo baki ta yi tare da juyowa ta shige jikinsa da kyau kafin ta ce. "Ina ta tambayarka na yi kyau ko ban yi ba kaki ka kulani, shiyasa na yi fushi".

Matso da ɗan bakinsa saitin kunnenta ya yi, can ƙasa ƙasa ya fara yi mata raɗan kalamai masu daɗin gaske kamar haka.
"Am sorry my sister, ke kanki fa kin san ke ɗin makura ce wajen kyau, meyasa zaki ɓata bakinki wajen tambayar kin yi kyau ko baki yi ba? Kin san cewa a kan kyanki faɗema ɓatawa ne amma sai ki rinƙa sanya mutun ɓata komai, babu wasu kalamai a duniyar nan da suka isa su zayyana yanda kyanki yake, duk abin da kika ji ana faɗensa to bai kai bane, abin da ya kai babu wasu kalaman da zasu iya zayyana shi, dan haka ke makura ce my lovely sister".

Mata mu da shegen son a yabemu tuni wani irin farinciki na musamman wanda bata taɓa jinsa ba ya cika mata zuciya tab, hannu tasa ta rungume shi sosai tana murmushi. Bawan Allah duk ta sanya ya susuce kamar ba shi ba, tsabar iyashege kuma wai bata fahimci cewa sonta yake yi ba, ta ɗauka kaunace ta tsaknin yaya da kanwarsa, akwai matsala kam babba.

Kasa yin wani kataɓus ya yi, kwantar da kanta a saman kirjinsa ta yi, ƙasa ƙasa ta ce. "Yah Jawad duk cikin yayyunmu Allah nafi sonka, kana da kirki sosai".

Nisawa ya yi, ya ƙasa iya magana, saboda shi kaɗai yasan halin da yake ciki.

Cigaba da yin maganarta ta yi. "Yah Jawad ina son kasancewa a tare da kai kullum, idan muna tare in jin daÉ—i sosai, kafi su Yah Rizwan sosai, kasan me?".

Shiru bai amsa mata ba, hakan kuma bai hana ta cigaba da cewa. "A duk lokacin da muke tare sai in rinƙa jin kamar ba'a duniya nake ba, ko guduwar lokacin bana iya gani, kana ɗauke mun komai a duk lokacin da muke tare, ina manta kai'na da kai'na saboda farincikin Allah".

Da kyar ya iya jan dogon numfashi tare da sauƙewa a hankali, yatsansa guda ɗaya ya ɗaura a saman lips ɗinta, alamar ta yi shiru, saboda ba zai iya cigaba da sauraren kalamanta ba, hakan yana kara jefa shi cikin yanayi, dama a kullum yana addu'ar Allah ya tsareshi kada ya wuce gona da iri idan suna tare, Allah yasa kada ya yi abin da zai sa ta dai'na ganin girmansa, shiyasa baya son jin kalaman nata, saboda daɗinsu suna ratsa ƙashi da ɓargonsa.
Chapter 96 · 0% Book details