← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 172 OF 211

Sashe 172

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥

44

EVIL KINGDOM😈🔥

GabaÉ—aya bayin nan sun jigata, sun ga ji sosai, wasu suna sare itatuwa, wasu suna fasa duwatsu, daji ne mai girman gaske fa. Amma a haka King Abdul Aziz yake azabtar dasu wajen saran dajin.

Cikin familynsa kuwa ba karamar dirama ake bugawa ba, domin kuwa kamar yadda kuka ji na ce maku matansa biyu ƴaƴansa huɗu to hakansu ke, sai dai fa matarsa ɗaya wato amaryarsa matar marigayi yayansa ne King Abdul Raof, bari dai na fayyace maku, amaryarsa matar yayansa ne, suna kuma da yaya maza biyu da suka haifa da yayan nasa kafin King Zuhair ya kashe shi, dukkansu kuma manya ne ƴaƴan, dan dik sun haura 25 years, nasan zaku sha mamaki a lokacin da zan ce maku Adam wato yarinman Gimbiya Sarina da ya je naman aurenta ɗa ne ga King Abdul Raof, makirci suka shiryawa King Zuhair domin su ɗauki fansa, batu na gaskiya shi Adam ba auren Sarina ya zo yi ba, leƙen asiri ya zo yi, sun yi amfani da sunan kingdom daban daban ne suka shigo cikin kingdom of power, a karo na biyu nasan zaku yi mamaki idan nace maku Yusuf saurayin Sarina na farko wanda ya yi yunkurin yi mata fyaɗe yaya ne ga Adam! Ainahin Yusuf ɗa ga abokin uncle Abbas ba shi ne ya zo wajenta ba, amfani suka yi da tsafi suka yi irin siffan wancan Yusuf ɗin, suka juyawa uncle Abbas ƙwaƙwalwa ba tare da ya sani ba, kunga dikkansu Sarina ta shuka masu rashin mutunci ba tare da ta san makiyansu bane. A nan dai ta kyauta sosai.

Yanzu dai kila ba zaku fahimci komai ba sai gaba, to in short dai da Yusuf da Adam uwarsu ɗa ubansu ɗaya, kuma wutar fansar kashe masu mahaifi da King Zuhair ya yi ne take ruruwa a cikin zuƙatansu, ta kowacce hanya so suke suga sun kai King Zuhair kasa.

Shiyasa suke bin dik wata motsin kingdom of power, sun samu labarin akwai yariman da zai je ganin Sarina, shiyasa suka garzayo izuwa kusa da Kingdom É—in, da yariman ya doso wajen sai suka yi amfani da tsafi suka gusar mashi da tunanin Sarinan, suka kuma sanya ya juya ya koma, sai Adam ya rikiÉ—a ya koma siffar wannan yariman ya je wajenta, shi ma Yusuf haka suka yi mashi a lokacin.

Abin da baku sani ba shi ne, aka ce idan zaka gina ramin mugunta ka ginasa dai'dai kai, da gangan Yusuf ya bari su commander Zafar suka wahalar da shi har aka ɗaure shi a cikin gidan yarin cikin masarautar, dik cikin taku ne, dama so yake a kawo wani abin da zai sa ya ɗauki lokaci a cikin kingdom ɗin dan ya samu damar bincike yadda yake so, amfani yake yi da tsafinsa idan dare ya yi ya fice daga cikin gidan yarin, ya shiga cikin kingdom ɗin ya tafi leƙe leƙen asirinsu, sai dai bai kai ga gama bincikensa bane King Zuhair ya ce a sakesu su tafi, shi ne yasa yanzu Adam ya sake dawowa dan ya karasa binciken da kyau kafin su fara shirin ruguje King Zuhair. Akwai gagarumim yaki fa, King Zuhair ya tara uban makiya kam ba'a magana. Ta ko'ina so ake yi a kaisa ƙasa.

Amma kuna tunanin shu'umai Yusuf da Adam zasu rabu da Sarina kuwa? Dan dikkansu biyu ta ci masu mutunci ba kaɗan ba. Akwai matsala kuwa, shiyasa koya ɗan adam yake kada ka walaƙanta shi, dan baka san wanenen shi ba, baka san a ina zaku haɗu gaba ba, Allah baya shawara da wani kafin ya aiwatar da abin da zai aiwatar, hmmmm bugu da ƙari gasu riƙaƙƙun matsaya, sai dai mu ce Allah ya ceci uncle Abbas bawan Allah, dan kuwa dik abin da ya sami Sarina kamar shi ya sama.........😥

To kun ji diramar waje, daga cikin gida kuma da mahaifiyarsu Yusuf sharariyar mushirikar nan, da kuma uwargidan King Abdul Aziz sam basa shiri, tamkar wuta da audiga haka suke, saboda kunga yanzu Abdul Aziz ne a kan mulki, so uwargidansa tana sa ran ƴaƴanta su karɓi mulki bayansa, sai dai kuma kash ƴaƴanta basu kai su Yusuf girma ba, ɗa namiji ɗaya da mace ɗaya take da su, kuma yara ne, namijin bai wuce 19 to 20 years haka ba ,ita kuma mace 15 years, shi ne yasa suke faɗa da mahaifiyar su Yusuf a kan mulki.

Amma kuma fa dik tsafin mamarsu Yusuf bata iya cutar da ko ɗan yatsar uwar gidan King Abdul Aziz, saboda ita ɗin baiwar Allah ce, tana da riƙo da addini, matsalarta ɗaya son da take yi yaranta su gaji babansu, ba komai yasa take son hakan ba kuma face dan ayi adalci, tana danasanin auren babansu, dan bata san bakin mugu bane sai da suka yi aure, to shiyasa ta tsaya ta bawa ƴaƴanta tarbiya irin na addinin musulunci dan su yi mulki bisa adalci da tausayawa bayin Allah talakawa, wannan ne dalilinta na son su yi mulki.

Ta tsani su Yusuf su hau kan wannan karaga, dan tasan sun fi ubansu ma iya zalinci, to my people's wani fata zaku yi wa gimbiya Zahra uwar gidan King Abdul Aziz a halin yanzu? Mu je dai zuwa.

Sai dai fa dik kudurin É—aukar fansa da su Yasuf suke yi shi King Abdul Aziz ba shi ne a gabansa ba, shi Spender ce a gabansa, ya yarda da kudurinsu ne kawai dan dikkaninsu makiyinsu É—aya ne wato King Zuhair, shi ne mamallakin Spender shi ne kuma ya kashe King Abdul Raof, kunga makiyin nasu É—aya.

___________________________🔥😈

Rana ta yi sanyi, yanayin gari ta canza, yalwar iska ya yawaita a gari, motsin mutane ya ragu, hayani babu, iska na ƙaɗa dogayen bishiyoyin dake cikin lanbun, sanyi mai daɗi na ratsa fata har izuwa cikin ƙashi na gimbiya Zahra uwargidan King Abdul Aziz dake zaune a cikin lambu saman wani haɗaɗɗen shinfiɗa na alfarma, ta ɗan yi rigingine a saman ɗaya daga cikin manya manyan throw pillows da aka ƙawata saman shinfiɗar da su.

Ta haɗe cikin alkyabbar nan nata mai bala'in kyau da tsada, daga ita sai wasu kuyangu guda huɗu dake yi mata hidima ne a wajen, ƴan'mata ne masu tasowa masu jini a jiki, sune kewaye da ita sun zube gwiwowinsu a ƙasa.

Ga wasu irin nau'i na cima daban daban a gabanta masu bala'in daÉ—in É—anÉ—ano, fresh fruit ga su nan nau'ika daban daban birjik a wajen.

Wata yar kyakkyawar matashiyar yarinya da bata wuci 15 years bace ta ƙariso wajen cikin shiga ta alfarma ta ƴaƴan sarakuna, fara tas da ita. A jikin maman nata ta zauna tana ɗan turo baki.

"Lafiya Suhaima?". Gimbiya ta faɗa tana kallon face ɗinta. Shiru ta yi bata yi magana be, yarinyar akwai riƙo da addini, ga tarbiya sosai da ta samu daga wajen mahaifiyarta, tana da son mutane da saukin kai, sai dai bata son hayaniya.

Yayanta wanda warriors guda biyu suke aikin take mashi baya ne ya shigo cikin wajen, shima yana cikin shiga ta kowani irin yarima mai ji da kansa.

A kusa da ita ya zauna shi ma tare da yin ƙasa da kansa.

"Lafiya Suhail naga kamar ranƙa a ɓace?". Cewar mahaifiyar tasu, ta yi maganar tare da miƙewa daga kishingiɗar da ta yi.

"Babu komai Ammie". Ya bata amsa voice É—insa akwai sanyi alamar yana da nutsuwa sosai, ya kuma samu tarbiya.

"Ammie in faÉ—a maki me yake damunsa?". Cewar Suhaima da yarinta yake É—awainiya da ita, tana magana tana murmushi.

"E faÉ—a mun me yake damunsa mamana".

ÆŠan É—ago kai ya yi ya kalleta. "Ni nace maki hakan? Na ce ki faÉ—a mata". Ya jefa mata tambayar yana kallonta.

Kai ta fara girgizawa alamar a'a ba shi ya ce ba.
"Tom kada na ƙara jin bakinki a nan wajen".

"Kai Yah Suhail zaka fara ko?". Cikin shagwaɓa ta yi maganar.

Da yake yau baya cikin mood na wasa sai bai amsa mata ba, ya kawar da kansa, damuwa yake ciki sosai a kan haÉ—uwarsa da mahaifiyar su Yusuf da ya yi a yanzu a kan hanyarsa ta zuwa wajen Ammien tasu, dama a tare suke tahowa da Suhaima, da suka haÉ—u da ita da Adam ne sai ta dakatar da su, Suhaima kam ta gudu taki tsayawa, shi kuma da yake Ammiensu ta hanasa raina babba sai ya tsaya ya saurareta.

Zaginsa fes ta yi kamar an aikota, ta tsanesu ne kamar ta kashesu, dan ma ta gaza iya hallakasun ne da ta jima da yin hakan, su sun fi mahaifiyarsu ma riƙo da addinin Islama, shiyasa ta gaza iya aikata masu komai, sai dai ta ƙare a zagi da hantararsu kawai.

Bayin Allah dik zagin da zata yi masu basa ce mata ko uppan. Sai dai su tsaya shiru, idan ta kammala zagin nata sai su bata hakuri su wuce abinsu, ta so yin tsafi da jinin Suhaima, amma ina ta kasa, sun riƙe Allah sun fi karfin mushirikai dama kowa na duniya.

Yanzu haka tana can ita da Adam suna shirya yadda zasu yi su hallaka King Zuhair, Adam ya sake gano masu wasu sirrika dangane da kingdom of power a wannan zuwan da ya yi wajen Sarina, shi kuma Yusuf baya nan, yana can yana ƙoƙarin yadda zai yi su haɗa kai da Queen Zarina dan su shafe babin kingdom of power a doron duniya, shi ne ya tafi zaman meeting da Zarina ɗin, idan kuma suka yi sa'ar haɗa kai fa to wlh Allah ne kawai zai iya kwatar King Zuhair, saboda dikkansu shu'umai ne na bugawa a jarida, ga Black Tiger baban sheɗani na karshe ma yana shirin murƙushe King Zuhair, kuma dik bawan Allah King Zuhair namu na amana bai san suna shirya mashi wannan gagarumin abin ba, Allah sarki shi ta Spender ma yake yi, bai tsare masu komai ba, bai hana su jin daɗi ba, bai takura masu ba amma suke neman ɓatar da shi a doron duniya. To sai dai mu ce Allah ya kwacesa daga hannunsu.
Chapter 172 · 0% Book details