← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 200 OF 211

Sashe 200

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kingdom of power taga manyan baki, dan kuwa ba kananan mutune ne suka zo ba, familyn mamarsu Jawad mutane ne masu tarin arziki da ji da kansu, basu É—aukar wasa, jiga jigan hajiyoyi ne.

Kai jama'a! Wato sun yi wani abin da ake cewa lefe, ya ilahi ya lillahi, kun san su ba lefe suke yi kamar namu na gargajiya ba............🌝🙄

Abin da ake kira lefe shi suke yi ba muna lefe ba, sai da suka shirge akwaitina ɗaiɗaiɗai har gudu 36 wato dozen mai goma sha bibbiyu har dozen uku, dikka shake suke da kaya irin su jinsin Abayas kawai, dama Rizwan ya gaya Auntyn tasa matarsa ƴar wanka ce mai shegen san kwalliya, ai kuwa sun zuba mata kayan gayu iya gayu, dik son gayun Chuchu fa sai ta gaji da canzawa bata gama sakasu ba, ga ƙananan kaya suma nasu akwaitin dozen guda mai goma sha biyu, kayan wanka irin na cikin ɗaki ma da nashi dozen ɗin, abin dai sai wanda ya gani, dan baki ya yi kaɗan ya faɗesa, sannan Aunty ta kara wa Chuchun da makullin dankareriyar mota kirar *PININFARINA BATTISTA* wadda a kallah kuɗinta ya kai kimani 2.9 million dollars.

Dik isa da izzar kingdom of power sai da suka jinjinawa kayan da familyn mamarsu Jawad suka kawo, sun tashi kai matuƙa gaya.

Chuchu kuwa Aunty MieMie ta je ta rarrasheta da kyar ta ce su je ta mayar da ita wanann É—akin da ake yi mata gyara dan masu lalle sun zo zasu yi mata.

Da kyar ta yarda suke tafi, sai dai fa Auntynsu Jawad ta tashi kansu Aunty MieMie, dan kuwa da tawagar masu lalle nata na musamman ta zo da su, ta ce su zasu ɗauki nauyin yi wa amaryarsu komai, dan haka masu lallen da Aunty MieMie ta kira su yi hakuri kawai waɗan da Aunty ta kawo su zasu yi wa amaryarsu lalle. Haka ta ciro makudan dollars ta miƙawa masu lallen Aunty MieMie ta ce su koma kawai. Maga ake ta dollars ta manyan kai jama'a! Babu harkar wasa ko harkar karanta, dollars ne kawai suke amshi a cikin kingdom of power my people's, wacece zata je bikin ta shirya mu tafi a tare?

Sai dai Aunty ta shiga tashin hankali na ganin Jawad a kwance babu lafiya, ta shiga damuwa matuƙa da har ta kasa samun nutsuwa, dan ta fi son Jawad ma a kan Rizwan, saboda shi yafi zuwa wajenta, in dai ya shiga united state to fa a wajenta yake sauka shi da Jaish, Rizwan kuwa sau ɗaya ya taɓa zuwa in da take saboda kun san halinsa ɗaya da su Ramish, gidan iyayensu kingdom of power ma basu zo ba bare wani wajen, ba in da suke zuwa, Abu Abdussalam ya mallakesu, suna tare da shi kawai.

Shiryawa masu lalle suka fara yi Aunty MieMie ta sanya Chuchu ta shirya cikin wando short zuwa gwiwowinta, da kuma riga mai ƙaramin hannu dan za'ayi mata lalle.

A lokacin da Auntynsu Jawad ta ɗaura idanunta a kan Chuchu ai bata san lokacin da ta ce. "Ashe Rizwan yana rage maki kyau ne a hotunan da ya ɗaukeki ya tura mun, wow Masha Allah, Jannat wutar kyau, kai ai waɗan nan kaya da muka kawo ma sun yi kaɗan, kin cancanci fin haka, ba shakka Rizwan bai yi karya ba da ya ce ke ƴar wanka ce, gaskiya ya faɗa, yama rage ashe kin fi haka a zahiri, a gaskiya mun karɓi wannan amrya hannu goma goma ba bibbiyu ba, bibbiyu ya yi kaɗan, sai dai kuma Raeesa (Aunty MieMie) me ya samu amaryar tamu idanunta suka yi ja suka kumbura haka?". Fuska a ɗauke da fara'a ta yi maganar.

Nasan dayawa daga cikinku kun manta sunan Aunty MieMie na gaskiya, shiyasa da ta ce Raeesa na sanya maku Aunty MieMie yadda zaku fi ganewa, Raeesa shi ne sunanta na gaskiya MieMie inkiya ce.

Auntynsu Jawad fa irin wayayyun matan nan ne da suke very friendly, bata da wata damuwa a rayuwarsu, ga fara'a da iya zama da mutane, ga shi ta iya wa'azin zama da miji da shegen iya soyayya, dan masu miƙo flowers ta aura, wato bature sarakan iya soyayya ba, hakan yasa ta zama malamar soyayya, dik wata amaryar da zata fita ko zata shigo cikin familynsu ita ce nan take yi mata wa'azin zama da miji, ta kuma koya mata dik wasu abubuwan da bata iya ba, sam bata da girman kai dik da wannan uban arziki da suke da shi, yanzu haka ta tsaya haikam a kan bikin Rizwan ɗin nan, sai dai kuma dik da wannan Allah bai taɓa bata haihuwa ba, shiyasa take son ƴaƴan ƴar uwar tata sosai wato su Jawad, ta so ɗaukar Jawad da mommynsu ta rasu, Momma ce taki yarda, ta ce ita aka bawa amanarsa dan haka zata haɗa shi da Jaish ta yi renonsu, dan dole ta hakura baiwar Allah, tun tana sa rai da samun haihuwa har ta cire rai gabaɗaya tana addu'ar Allah yasa ta cika da imani kawai.
____________________________🕊️

Shiru Aunty MieMie ta É—an yi kafin ta ce. "Babu komai Aunty, kukan rabuwa da su momma and su Auta take yi".

Matsowa Aunty ta yi ta rungumeta tana faÉ—in. "Sorry my daughter, In Sha Allah babu wanda zai rabaki da Æ´an uwanki, ai kina a tare da su, dan haka ki dai'na kuka kin ji ko?".

Wani irin kuka mai karfi ne Chuchu ta ji ya kubce mata, ba zasu gane me take ji bane, da sam ba zasu yi ƙoƙarin bata hakuri ba.

Ganin haka yasa Aunty MieMie ta matso ta karɓeta daga jikin Aunty tana faɗin. "Ya isa haka Jannat, ki yi shiru kin ji?".

Kasa iya motsa laɓɓanta ma ta yi bare ta yi magana, sai dai ta kwantar da kanta a jikin Aunty MieMie tana kuka ƙasa ƙasa.

Chuchu na kuka a nan, Aneesa ma tana nata kukan a cikin ɗaki Fanan tana tayata, tun daga sa'ar da Aunty MieMie ta isar mata da saƙon gobe za'a ɗaura aurenta da Jawad tare da na su Rizwan, tun daga lokacin ta rasa nutsuwarta, sosai take kuka kamar zata haɗiyi zuciya ta mutu, saboda Rizwan take so ba Jawad ba, babu soyayyar Jawad a ranta ko kaɗan face kauna ta tsakanin yaya da kanwa, how comes za'a ce mata ta auresa fisabilillahi? Wlh ita dai ba'ayi mata adalci ba take faɗe.

Su Aunty basu san da batun auren Jawad da Aneesa ba sai da suka iso ne suka samu labari, dan haka Aunty ta ce yazamar mata dole ta É—aga jirgi zuwa Dubai ta je ta sayowa Aneesa É—in ma kaya kamar yadda ta sayawa Chuchu, hanata su momma suka yi, suka ce ta bari idan ya so sai bayan auren tun da dai abin ya zo unexpect haka.

Da farko kin yarda ta yi, sai daga baya da King ya sanya baki sannan ta yi shiru ta hakura, amma da nufin idan an É—aura aure gobe jibi ita kuma zata wuce Dubai É—in. Su momma sun yi na'am da hakan.

Rakuma manya manya guda goma, shanu goma aka yanka saboda wannan biki, hidima dai babu kama hannun yaro, amarya kuma tana can tana faman kuka ana zuba mata lallen. Sun kuwa iya tsara lalle ba'a magana, har saman singalalin ƙafafunta aka zuba mata lallen.

Ita kuwa Aneesa da farko cewa ta yi a barta haka ba zata yi lallen ba, sai da Aunty MieMie ta ɓata rai sannan ta yarda aka shirya yi mata.

Dik wannan sharholiya da ake yi fa ba Sarina a cikinsu, tana can tana ƙoƙarin binciken waye mammiensu ta zaɓa mata a matsayin miji, ita bama ta su Chuchu take yi ba, ta kanta take yi a halin yanzu, sai dai kuma da kamar wuya ta iya gano shirin mammmien tasu a kanta, dan kuwa ta buga ta raya, har Aunty Aliyarsu sai da ta tambaya amma ta ce mata ita fa wlh bata san shirin Mammien nan tasu ba, har da kara mata da cewa Mammie kun nan kamar Aljana take ba'a taɓa gane ina ta dosa.

A can wani ɓangaren kuwa Adam ne yake ta ƙoƙarin yadda zai yi ya sace Sarinar ya dawo da ita EVIL KINGDOM, domin ya kwaɗaitu da surar jikinta, tun da ya koma ya gaza samun sukuni, dik hankalinsa a tashe burinsa kawai ya ɗanɗaneta, idan baku manta bama yana ɗaura idanunsa a kanta ya ce zazzafa, so gaskiya ta tafi da shi ainun, in baku manta ba na gaya maku tana da surar jiki mai ɗaga hankalin dik namijin da zai kalleta.

Sai saƙa ta yadda zai shigo cikin kingdom of power ya ɗauketa yake yi, shi kansa Yusuf har yau akwai kwaɗayin surar jikinta a cikin zuciyarsa, burinsa kawai ya sameta ya biya buƙatursa da ita....... Ni kuwa nace Allah ya ceci uncle Abbas, dan kuwa dik abin da zai sami Sarina tamkar shi ya sama bawan Allah, dik abin da suka yi mata tamkar kingdom of power gabaɗaya suka yi wa, familyn Akka zasu zubarwa da mutumci, hegiyar yariya bata jin magana, ana tausaya mata ita kuma bata tausayawa kanta.

One sweet thing shi ne, hidimar bikin Chuchu ya É—auke hankali King Zuhair bai yi wa uncle Abbas hiran da suka yi da Ramish a kan yaki ba, yana ta busy da manya manyan bakinsa da suka fara dira a cikin masarautar daga jiya, har yanzu kuma baki ne suke ta tururuwan zuwa, abin dai ba'a magana.

_________________🌹💘______________

JIMETA YOLA🦋🕊️🌹

"Hamma lafiya ka tsareni da idanu haka kana ta kallona". Ta faɗa kanta a ƙasa, tana zaune saman wannan itaciyar gwaiva da yake zaunar da ita.

"Da wani ido kika kalleni har kika san ina kallonki?". Ya jefa mata tambayar yana riƙo ƴan hannayenta.

"Ni ai ban ganka ba, kawai a jikina nike jin kana kallo na". Tana magana tana É—an turo baki kamar Mahreen.

"Da gaske?". Cikin zolaya ya yi maganar. "Kai hamma da gaske fa nike yi".

"FaÉ—a mun meya ja hankalinki kika mun kwalliya da kika yi mun?".

Girgiza kai ta ɗan yi tare da sake ƙayataccen murmushi, ya tuna mata da batun kwalliya. "Babu komai". Ta bada amsa tana wani kara yin ƙasa da kai kamar wata saliha.
Chapter 200 · 0% Book details