Sashe 101
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Suna shigowa suka isko bappa a tsakar gida yana gyaran harawa, sam basu ji daɗin rashin ganinsa a tare da Jaish ba, da alama kenan har yanzu zuciyar tasa bata sauƙo ba, kullum a tare suke komai da bappan, amma yau yana ɗaki yana kwance shiru, sai tafarfasa zuciyarsa take yi mashi.
Shi kansa bappan zuciyarsa zafi take yi mashi na fushin da Jaish É—in yake yi, haka ya shiga gyara harawansa shi kaÉ—ai yana zubawa awakansa da suka kusa haihuwa ya tsamesu daga cikin sauran ya dawo da su cikin gida.
Wajensa Mahreen ta nufa, ita kuma Mahnoor nonon da suka tatsa da safe suka ajiye shi a ɗakin bappa ya yi bacci dan ya yi kauri ta shiga ciki ta ɗaukowa. Ƙasa ƙasa ta yi sallama cikin natsuwa, yana kwance ko gezau bai yi ba.
Wucewa ta yi ta É—auko kwaryar nonon ta fito, dama haka suke yi kullum, idan ta É—auko sai ta damawa Jaish, tun baya iya sha har ya koya dan dolensa, da idan ya sha sai ya yi ta amai tamkar zai akayar da komai na cikinsa saboda karninta, amma yanzu lafiya lou yana sha, rayuwa kenan, wuya mai koyawa mutun abin da yake ikirarin bai iya ba kuma ba zai yi ba, sai ga shi dai yau kun gani a kan Jaish, duk wanda ya ce bai iya kuka ba to ku ce mashi mahaifiyarsa bata mutu bane, tana mutuwa dole ya yi dan gidansu!!.
Dama mashi fura da nonon ta yi ya damu sosai, haƙiƙa Mahnoor yarinya ce mai abin birgewa, dan kuwa a kullum ta san kowani aiki da ya rataya akanta, ku duba ku gani ko ina ta je tana dawowa dallah dallah zata fara yin duk abin da ta san aikinta ne baiwar Allah, ba sai ta jira an ce ta yi ba, fatan Allah ka shirya mana ƴaƴanmu da jikokinmu.
Bayan ta kammala ta miƙe ta ɗauko mashi ɗan ƙaramin kwaryarsa mai kyau ta zuba a ciki, sannan ta zubawa bappa da Nenne, ta bar masu sauran ita da Mahreen a cikin wannan babban kwaryar, ta ɗauki paipai ta rufewa kowa nasa, ta ɗauki na Jaish ta nufi cikin ɗakin bappan.
Tana shiga ita kuma Mahreen ta zo ta ɗauki na bappa ta je ta miƙa mashi, karɓa ya yi ya ajiye a gefensa ya cigaba da aikinsa. Sannan ta ɗauki na Nennen ta kai mata, sai ta ɗauko wani ludayi ta zo ta zauna tana jiran Mahnoor ɗin ta fito su sha a tare.
Ihunta da suka ji daga cikin É—akin bappan ne yasa suka kai kallonsu a bakin kofar, da sauri Nenne ta fito daga cikin nata É—akin dan tsabar gulma.
Da gudu bappa ya ajiye harawar hannunsa ya nufi É—akin nasa, da gudu ita ma Mahreen ta rufa mashi baya, Nenne kuwa a bakin kofar nata É—akin ta tsaya tana jiran ta ji menene? Sai addu'a take yi a kan Allah yasa kashe Mahnoor É—in ma Jaish ya yi kowa ya huta.
Turus suka tsaya a tsakar ɗakin suna ganin abin da yake faruwa, gabaɗaya Mahnoor ɗin jikinta ya sha wanka da furar da ta kawo mashi ɗin, tana tsugunne a gaban gadon nasa. Abin da ya faru shi ne, ta saba idan ta kawo mashi furar ko da yana kwance ne zata zo gabansa ta tsugunna ta miƙo mashi, wani lokaci har hannu take sawa ta ɗan bubbuga katifar ta ce ya tashi ga furarsa. To yau dai da ta zo ta yi mashi na farko bai motsa ba, sai ta yi zaton bai ji bane yasa bai motsa ba, dan ta san dai in ta yi mashi magana yana ɗaga mata kai kawai alamar ya ji, yau sai taga akasin hakan, kuma idanunsa biyu ba barci yake yi ba.
Shi ne ta sake buga jikin katifar ta maimaita abin da ta faɗa da farko, ita gabaɗaya ta manta cewa da safe ya fusata. Nan ma bai motsa ba, ganin hakan ga idanunsa biyu sai yasa ta kai hanni ta ɗan taɓa hannunsa zata yi magana kenan a fusace ya kai hannu zai dallah mata mari, zaro idanun da ta yi ta sha jinin jikinta tare da kamewa waje guda ne yasa ya fasa marin nata ya sauke haushinsa a kan furar a in da ya yi fatali da shi, ya yi mata wanka da shi, gabaɗaya jikinta ya ɓaci, har face ɗinta, hakan ya ɗaga mata hankali har ta yi kara, dan bata taɓa ganinsa a irin wannan yanayi ba, Allah ya ceceta, wlh da ya sauke mata wannan marin da ya yi niya in da yake cikin fushin nan in bata mutu ba zata sume, amma sai ya danne, tun safe yake ta ƙoƙarin danne zuciyar nan nasa na Modarawa, amma abin ya ci tura bawan Allah. Ba laifinsa bane, zuciya gadon modarawa ne kowa yasan da hakan!.
Bappa yana ɗaura idanunsa a kansu ya fahimci abin da ya faru, hakan yasa ya ce mata ta je ta canza kaya ta wanke jikinta. A hanzarce ta miƙe, sarki tsoro jikinta har kerma yake yi ta fito waje a tsorace.
Tana fitowa Nenne ta dakatar da ita a kan ta gaya mata me ya faru a cikin É—akin?. Murya na rawa ta bata labarin abin da ya faru, wani irin murmushin mugunta ta saki tare da juyawa ta shige cikin É—akinta.
Bayan Mahnoor Mahreen É—in ta biyo tana bata hakuri. Shi kuwa bappa rarrashin Jaish É—in ya shiga ya fara yi. Da yake ya É—an samu ya yi wa Mahnoor patali da furarta sai ya É—an ji zuciyar tasa ta yi sanyi, hakan yasa ya kara zagewa wajen dannar zuciyar har ya iya amsawa bappan ta hanyar jinjina kansa alamar ya ji. Sosai bappa ya ji daÉ—in hakan tare da sanya mashi albarka.
Shi ma ya ji daÉ—i da Allah ya taimakesa wannan bakar zuciya tasa bata ja mashi ya cutar da bappan ko ya yi mashi wani abin da ba dai'dai ba, godiya ya yi ga Allah. Kiraye kirayen sallar mangariba da yara suke yi ne yasa ya ce mashi lokacin sallah ya yi ya fito su tafi masallaci. Alamar wanka zai yi ya nunawa bappan. To ya amsa mashi da shi tare da fitowa ya umurci Mahnoor da ta sanya mashi ruwa a wuta.
Baiwar Allah haka ta tafasa mashi ruwan tare da surkawa dana sanyi, ta kai mashi banÉ—aki ta fito. Yana fitowa da nufin ya shiga wanka da ita suka fara haÉ—a idanu, kawar da kallonsa daga kanta derect ya yi tare da satar kallonta ta wutsiyar idanu, sai ya ji bai kyauta ba abin da ya yi mata, ta mashi alkhairi ya sauke haushin laifin da ba nata ba a kanta, dama idan baku manta na yana jin tausayinsu ita da Mahreen.
Toilet ya nufa yana aikin satar kallonta, ita kuma a tunaninta baya kallonta sai ta tsare shi da idanu tana ta kallonsa har ya shige.
After some minutes. Bayan sun yi sallar mangariba da isha'i sun dawo, zaune suke a tsakar gida kamar yadda suka saba, sai hira suke zubawa abin gwanin birgewa, bappa, Mahreen and Mahnoor ne suke yin hiran, Jaish dai shiru yana sauraronsu, Hamma Faisal bai rigada ya ƙariso ba.
Fitowa daga ɗakinta Nenne ta yi, a kusa da bappa ta zauna, ko wanka matar nan bata yi ba tun da ta dawo, da alama dai akwai wata ƙasa.
Cikin rawar jiki bappa ya ce. "Kin fito ne?".
Kai ta gyaÉ—a mashi hasken fitullun kwai na haska su, da dayake wata ta É—an yi nisa.
"Wata magana nake son yi da kai". Ta faÉ—a da wata iriyar murya kamar masoyiyarsa ta gaske, da alama wani makircin zata haÉ—a.
Jin ta ce tana son yi magana da shi ne yasa Mahreen and Mahnoor suka miƙe tare da shiga kitchen suka ɗauki abincinsu suka wuce nasu ɗakin.
Shi kam Jaish miƙewa ya yi ya nufi waje mai gabaɗaya, a karkashin bishiyar kofar gida ya zauna yana ganin yadda mata da maza suke zirganiya tamkar ba dare bane, kowa da firillar kwai a hannunsa yana haskawa, ƙananan yara sai yawo suke yi a tsakanin gidan makota.
Dawo da hankalinsa kacokam a kanta ya yi tare da ce mata yana sauraronta. Gyara zama ta yi tare da lankwashe kafafunta ta juyo suna fuskantar juna. Cike da makircin ta ce. "Wani alfarma nake nema idan ba damuwa?".
A takaice ya ce. "Ba damuwa ki faÉ—a ina jinki".
Sai da ta sakar mashi murmushi kafin ta fara kora mashi jawabin abin da take buƙata. "Ina son in ba damuwa ka aurawa wannan bakon namu Mahnoor, nasan zata samu kulawa daga wajen shi, ai kama fini sanin halinsa, kuma.........."
ÆŠaga mata hannun da ya yi ne yasa ta dakata da yin maganar.
"Ba sai kin ƙarisa ba, duk abin da kike so shi kowa zai yi a gidan nan". Ya faɗa a sanyaye.