← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 211

Sashe 20

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Katse mashi tunanin nasa ta yi da cewa. "Kana mamaki ya aka yi ban shiga damuwa ba duk da na ji abin da yake faruwa ko?".

Da sauri ya gyɗa mata kai alamar e. "Dama nasan dole wani abin ya saɓa, domin kai da Jaish tamkar ƴan biyu kuke, tun kuna yara idan ɗaya ya yi rashin lafita da safe to ɗayan zai kwanta nasa ciwon da yamma, tun jiya da naga yanayinka na fahimci kana taya Jaish ciwo ne, ka dawo wani sukuku da kai, kai da kanka baka san me yake damunka ba, hakan ce ma yasa na biɗi ganin Jaish ɗin dan na tabbatar da abin da yake damunka, shin ciwon gaskiya ce ko dai ciwon shaƙuwa ce? Yanzu na tabbatar, coz ban yi mamaki ba, kuma ban ji cewa Jaish ya aikata ba dai'dai ba, a jikina ina jin ba lafiya yake ba, amma koma menene ni ban haifi rago ba, jarumta a jininmu take, a ko'ina yake ina da yaƙinin da izinin Allah zai fidda kansa, dan babu rago a zuri'armu, bamu san komai ba sai jarumta, dan haka kai ma ka warware ka taya shi da addu'a, Allah kuma yasa ya cinma burinsa a kan abin da ya je nema, zan yi mashi addu'a, sannan bana son ka gayawa kowa wannan magana, dan sanin kankane a gidan ba kowace magana ake yinta da mutane ba, wani lokaci is better ka haɗiye magana a cikinka sai ya fi maka sauki, ko daddynku kada ka gaya mashi, dan zai shiga damuwa, and lastly ka gaya mun gaskiya duk da ni kai'na ban yarda da abin da zuciyata ta gaya mun ba, amma zanso in ji gaskiya daga bakinka".

Dakatawa da yin maganar ta yi tana kallon face É—insa. Tattare nutsuwarsa waje guda sosai ya yi, dan ya ji ta É—auko wani maganan na daban.

"Ka faÉ—a mun gaskiya kai ka shiga É—akin Jannat kwana uku da suka wuce?". Tana magana tana kara kura mashi idanun, dan ta kalli yanayin da fuskarsa zata yi.

Zaro idanu ya yi kafin ya ce. "Momma ina zuwa ɗakin Jannat, amma kwana uku da suka wuce ban shiga ba, kwana huɗu da suka wuce dai na shiga da daddare sosai wuraren karfi 12 haka, har daddy ya zo ya samemu a tare na ɓuya a cikin toilet, bayan haka kuma babu wani abin".

Tabbas ta yarda da maganarsa, tasan gaskiya ya faÉ—a, dama kuma tasan ba zai aikata wannan É—anyen aikin ba, ta san halin Æ´aÆ´an nata sosai, amma sai ta ce. "Me kake zuwa yi a É—akin nata a irin wannan lokacin haka?".

Ƴan kame kame ya fara yi mata yana faman sunkuyar da kai.

"Yau kuma ka dawo Jaish ne da kake ɓoye mun fuska? Yaushe kunya ta ratsa jinin jikinka kai ma? Jaish ma ina ganin rashin kunya ce take damunsa da idan ya zo yake ɓoye mun fuska yake wani sunkuyar da kai, ashe ko dai hakance tun da gashi kai ma ka fara ɓoye fuska".

Ɗan ƙaƙalo murmushi ya yi kafin ya ce........

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

❤️🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 23/9/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

💘STEP TWO....✍️📚🔥

E___________9

Ɗan ƙaƙalo murmushi ya yi kafin ya ce. "Kai our Momma, bafa kunyarki nake ji ba, abin da zan gaya maki ɗin ne yasa na fara jin kunyarki a yanzu".

"Mmmmmm to dai faÉ—i na ji menene? Me yake kaika wajen Æ´ata da tsakar dare haka?".

"Kai Momma addu'a nake zuwa yi mata fa, daga nan sai mu É—an yi hira kaÉ—an haka, bafa dayawa ba, kuma a hiran dukka karatu nake koya mata". Ya faÉ—a yana É—ago da kallonsa izuwa kanta.

Wani irin kallo da take binshi da shi mai nufin ni zaka yi wa karya ne yasa shi sakin siririn murmushi tare da É—an dafa kafafunta kafin ya ce. "Kai our Momma, to zan faÉ—a maki gaskiyar".

"Oya go ahead". Ta faÉ—a tana kara kallon face nasa da kyau, while shi ma kallonta yake yi.

"Magana ta gaskiya zan gaya maki, dan ko zan ɓoyewa kowa ban da ke our Momma, zance ta gaskiya son Jannat nake yi kuma ina fatan ta zama matata, amma da alama bata sona, dan yau kwana uku kenan tana guduna ba tare da ta tsaya ko kallonta na yi ba, taki tsayawa ko tambayarta me nayi mata take gudu na ma taki, ban san me yake faruwa ba, ban san laifin da na yi mata ba, amma a baya tana nuna mun kauna, kwana huɗu da suka wuce ma da na je ɗakinta da daddaren lokacin da zan koma nawa part ɗin sam bata so hakan ba, ta so na zauna mu yi ta hira har wayewan gari, duk da bata fito ta gaya mun hakan ba ni naga hakan a cikin kwayar idanunta, amma haka dai na danne na koma part ɗin na, na rasa me yasa yanzu take guduna, sam bata sonna, ban kuma san laifin da na yi mata ba, please Momma ki tayani da addu'a, wlh ina kaunar Jannat sosai". Ya kai karshen maganar cikin wata iriyar raunanniyar murya.

Saboda kaifin ƙwaƙwalwa irin nata nan take ta gane lallai lallai akwai mai son shiga tsananinsu a cikin gidan nan, tabbas akwai mai son rabasu, to wanenen? Ta tambayi kanta, sai dai abin da bata gane ba a nan shi ne meyasa Chuchu take gudun Jawad ɗin tun da ba shi ya shiga ɗakin ya yi ƙoƙarin keta mata mutunci ba? Dole wani abin ya saɓa, dole akwai wata makarƙashiya da basu san menene bane.

Shiru ta yi tana tunanin ta gaya mashi gaskiyar abin da ya faru domin ya yi ƙoƙarin yi wa Chuchun bayani yadda zai shawo kanta ne? Ko dai ta yi shiru sai ta gama bincikenta?.

Voice É—insa ne ya katse mata tunanin da take yi ta hanyar cewa. "Momma please ki tayani da addu'a, wlh ina kaunar Jannat sosai, yau tsawon kwana uku kenan ban sanyata a cikin idanuna ba, ki taimakeni na ganta, idan ba haka ba zan iya cutuwa". Cikin raunin murya tamkar zai saka mata kuka ya yi maganar.

Ajiyar zuciya ta sauke tare da fara magana. "Eyeee wato Jawad sam baka kunyata ko? Kai tsaye kake gabatar mun da yadda kake kaunar Æ´ata ko? Ba irin jin kunyar surukai da ake yin nan?".

Kamar zai sa mata kuka ya ce. "Momma please ki daina faɗin hakan mana, ni ban yarda ba, ke mahaifiyar miji kike bana mata ba, ki bar batun surukuwar nan, mummy ce zata zama surkuwa, ni yanzu please Our Momma a samo min mafita, in dai ba so kike yau na ki cin abinci na zauna nan nayi ta yi maki kuka ba to a haɗa ni da Jannat ɗita, Kila ma Momma ke kika ɓoye mun ita saboda kina son na gaya maki me yake tsakaninmu, to dai na faɗa maki surukarki ce, dan Allah a haɗani da ita ko na minti biyar ne".

Dan siririn murmushi ta saki kafin kuma ta sake ɗaure fuska sosai kamar bata taɓa yin dariya ba, a tsanake ta fara bashi labarin abin da yake faruwa dukka, bata ɓoye mashi komai ba, dalilin da yasa Chuchu take gudunsa duk ta gaya mashi da abin da ta ganewa idanunta, daga karshe ta rufe mashi da cewa lallai lallai ya kula sosai, sannan ya kara tsananta addu'a, yanzu haka Chuchun tana part ɗin Aunty MieMie, ya je ya sameta shi yasan ta yadda zai shawo kanta, kada ya yi ƙasa a gwiwa, ya jajirce sosai zai yi nasara.

Sosai ya shiga tsananin ɓacin rai da jin anyi ƙoƙarin yi mata fyaɗe ne, jikinsa har wani tsuma yake yi, bai damu da cewa zarginsa take yi a kan hakan ba, damuwarsa a yanzu shi ne ya gane wanda ya yi mata hakan domin ya hukuntasa, uncle Taheer ƙanin mama baya ƙasar, ya tafi wajen iyayensa dan sada zumunci bare ya ce ko shi ne ya yi mata hakan, Jaish ma baya nan, kuma koda yana nan ma ko giyar wake ya sha ba zai aikata hakan ba, a mazan gidan dai shi kaɗai ya saura a gidan. Tashin sense!!

Ganin alamar ransa ya ɓaci sosai ne yasa ta fara rarrashinsa tare da ƙara mashi kwarin gwiwa. Ina ai yanzu duk maganar da take yi ma bata shiga kunnuwansa, ya yi nisan kiwo wajen tunanin mafitar yadda zai kama wanda ya yi mata wannan aikin, faɗi yake yi a cikin zuciyarsa wlh idan ya kama wannan mutumin koma wanenen sai dai uwarsa ta haifi wani.

Tsabar ya afka kogin tunani da tsananin ɓacin rai bai ma san time ɗin da ya miƙe ya nufi hanyar fita ba, ko sallama bai yi wa Mommar ba, da alama ma ya mance cawa a wajenta yake, kawai ya nufi waje. Har ta buɗi baki zata kira sunansa sai kuma ta fasa, saboda ta lura baya tare da ita, ko ta kirasa ba lallai ya jita ba, dan haka sai ta bishi da kallo tare da fatan nasara.

Yana fita kai tsaye wajen Aunty MieMie ya nufa, zuciyarsa na tafarfasa sosai, tsikar jikinsa har tashi yake yi.

Tsabar ya shiga damuwa ko sallama bai yi ba ya afka cikin parlourn, babu kowa shiru, da yake already ya san in da zai sameta a part É—in idan ta shigo sai ya nufi stair case kai tsaye.

Sama ya haura, kai tsaye ya nufi wani katafaren luxurious bedroom wanda yake zaton zai sameta a ciki. Babu ko sallama ya tura kofar ya afka ciki.
Chapter 20 · 0% Book details