← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 188 OF 211

Sashe 188

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rasa abin faɗa ya yi sai kawai ya yi ƙasa da kai, sarai tasan bai san ta ce wa bane yasa ya yi hakan, dan dik wani halinsa babu wanda bata sani ba.

"Ka taya mu da addu'a ka ji? Ka yi mana addu'a Allah ya barmu da masu sonmu na gaskiya".

ÆŠagowa ya yi ya kalleta, kamar tana karanta me a ransa, a sanyaye ya ce. "Allah ya baku mazaje na gari waÉ—an da zasu kasance alkhari a gareku".

Da amin ta amsa idanunta a kansa. Tana son su yi hira amma ba hali, haka ta hakura suka cigaba da zama kamar kurame, sai aikin kallon juna.

_____________🌹💘____________

JIMETA YOLA.

Sosai ya yi kissing É—inta kafin zame É—an bakinsa, sai kuma ya rungumeta yaki bari ta É—ago bare su haÉ—a idanu, ita ma kwanciya shiru ta yi a jikinsa tana jin zuciyarta na harbawa da sauri sauri.

Sai da rana ta ɗaga around karfe 11, sannan ne ya ce su je gida. Ba musu ta ce to, tana wani ɓoye fuska, shi kuwa da alama yanzu ya dai'na kunyarta, dan kuwa idanunsa a kanta har suka nufi hanyar gida, yana riƙe da hannunta, saboda tsabar kunya har ce mashi ta yi ya ɗan saketa sai ya yi gaba ko ita ta yi gaba kada su jera, amma ina yaki yarda, ya ƙanƙame suka nufi gidan.

Ko da suka koma Nenne na tsakar gida tana shirye shiryen girkin rana, ko kallon in da take bai yi ba ya ja hannunta suka wuce cikin É—akinsu.

Suna shiga ya sake rungumota kamar wani ya ce zai rabasu, shi fa yanzu ya ji daÉ—in jikinta sai ku abin da hali ya yi.

"Hamma bari na je na ɗumama mana abincinmu ma daren jiya da bamu ci ba?". Ta faɗa ƙasa ƙasa.

Da to kawai ya amsa tare da saketa. Da sauri ta nufi waje, shi kuma ya karisa bakin mattress ya zauna, arab hairnsa yanzu ta yi tsawo saidai, yaki yin aski kuma, dan su askin reza suke yi, a cire gashi dikka, shi ne yaki yarda bappa ya yi mashi............😅

Ko da ta fito tsakar gida Nenne bata kulata ba, dan tasan yana nan, in ta kulata tasan me zai biyo baya. Kitchen ta shiga abinta, ta hura wuta ta dawo cikin É—akin, abincin nasu ta É—auka ta fita, É—umame mai daÉ—i ta yi masu, ta shiga É—akin bappa zata É—auki man shanu ne ta ga Nenne ta ajiye masu abincin safe, kamar zata É—auka ta kai mashi sabon tuwon sai kuma ta ce bari ta fara zuwa ta sanar da shi tukun nan.

Wanke kwanikan nasu ta yi ta kwashe É—umamen a ciki, ta zuba man shanu ta É—auka ta nufi É—akin su, ajiyewa ta je ta yi sannan ta fito ta É—aura ruwan wankarta, ta koma É—akin ta same shi.

Yana zaune kamar yadda ta barshi, a gabansa ta tsugunna cikin ladabi da biyayya ta ce. Hamma Nenne ta ajiye mana abinci in É—auko maka tun da shi sabon tuwo ne ba É—umame ba?".

Ɗan kwaɓe fuska ya yi kafin ya amsa da. "Bana buƙata, abinci in ya wuce naki ba zan iya cin na kowa ba".

Wani irin sanyi ta ji a ranta, hakika ta ji daɗi sosai, wani irin ƙayataccen murmushi ne ya kubce mata, sai kallonta yake yi.

Cike da farinciki ta miƙe ta nufi waje, ruwan zanfin ta juye a bokiti tare da surkawa ta ɗauka ta nufi banɗaki dan ta yi wanka, shi kuma bai ci abincin ba yana jiran ta dawo su ci.

Bayan ta yi wanka sai ta É—auro alwala azahar dik da lokaci bai cika ba, sannan ta nufi cikin É—akin. Still dai yana zaune in da ta barsa. Ta yi mamakin ganin yana zaune a wajen, dan haka sai ta ce.

"Hamma ya baka ci abincin ba?".

"Ke nike jira". Ya bata amsa idanunsa a kanta babu ko kyaftawa.

Murmushi ta É—an yi kafin ta wuce ta É—auki kayan da zata saka, sannan ta nufi hanyar fita dan ya je É—akin Mahreen ta shirya.

"Zo nan". Ya faÉ—a kamar ba shi ya yi maganar ba.

Ba musu ta juyo ta nufosa. Zata tsugunna a gabansa kenan ya yi saurin riƙo hannunta ya jawota ta faɗa jikinsa, daga ita sai ɗaurin kirji sai kuma hijabin dake jikinta.

Hijabin ya yaye ya ajiye shi a gefe, shiru bata ce mashi komai ba. Ya kai hannu ya karɓi ɗan basken ɗin kayan kwalliyar tata, gyara mata zama da kyau a jikinsa ya yi kafin ya ɗauko powder ya zuba a soson. Cikin nutsuwa ya fara goga mata a face ɗinta, dan tun da ya yi mata shi a wajen bikinsu ya haddace komai.

Kwalliya mai kyau ya tsantsara mata, yana yi idanunsa suna a kan gurun wuyarta, sai da ya gama yi mata komai sai ya kai É—an bakinsa saman gurun wuyar tata. Iya sumbatarta ya so ya yi, sai ga shi ya fitar da tongue É—insa yana yi mata tafiyar tsutsa a wajen.

Ji ta yi mamar cakulkuli yake yi mata hakan yasa ta fara dariya tana muku muku, ta ƙanƙame shi. Cigaba da yi mata hakan ya yi har sai da ta saki jiki sosai tana dariya mai ɗan sauti, tun da yake da su a gidan bai taɓa ganin ta yi dariya mai sauti na sai yau, murmushi ma ba kasafai ta cigaba yi ba, sai Mahreen ta zage sosai take iya sanya murmushi, yau sai ga shi tana dariya mai sauti.

Sosai ya ji daɗin hakan, ya kuma rungumeta a jikinsa, ta yi matuƙar kyau a simple make up da ya yi mata.

Sallamar Mahreen a bakin kofar ɗakin nasu ne yasa ya yi saurin sakinta tare da cire tongue ɗin nasa, ya miƙa mata hijabinta yana kallonta.

A hanzarce ta sanya hijabin kafin ta miƙe daga jikinsa tana amsa sallamar.

"In shigo". Cewar Mahreen, bappa ne ya ce lallai kada ta kuskura ta shiga masu É—aki kai tsaye, dole sai ta tambayesu ta shigo, idan suka ce mata e sai ta shiga, to shi ne fa kuka ji tana faÉ—in ta shigo.

"E shigo" Mahnoor ta bata amsa.

Sake yin wani sallamar ta yi kafin ta sa kai ta shige ciki, ashe kasuwan kauyen dake gaban nasun nan Mahreen ɗin ta je ita da Inna Rabi, bappa ya basu kuɗi su sayawa su Mahnoor wasu abubuwan buƙata har da sugar da lip tom da dai sauransu, shi ne ta kawo masu.

Tana miƙawa Mahnoor kayan ta nufi Jaish dake ta kallonta, daga jiya zuwa yau da basu kasance a tare ba ya yi kewarta sosai.

Tana zuwa ta faɗa jikinsa tana dariya tana faɗin. "Hamma yanzu baka fitowa mu je wajen bappa mu yi hira". A shagwaɓe ta yi maganar.

Satar kallon Mahnoor ya yi kafin ya ce. "Ba laifina bane, amma zan rinƙa fitowa, na yi kewarki ai nima".

Labarin kasuwa ta fara bashi tana yi mashi wasa da gashin kansa, biye mata ya fara yi daga karshe suka sauko saman dadduma suka ci abinci a tare su ukun, su Mahnoor yanzu ta rage jin kunyarsa.

After some times. Bayan wani lokaci.

In short yanzu dai shaƙuwa sosai ta shiga tsakaninsu, kunya ta ragu sosai, Mahreen bata takura masu, dan bata ma shiga room ɗinsu kwata kwata, iyaka su haɗu da ita a waje, bappa ma baya takura masu, yana basu waje, sai dai har yau har gobe dikkansu kunyar bappan suke ji sosai, basa yarda su haɗa ido da shi, idan ma yana nan basa fitowa, in sun shiga ɗaki su kashe junansu da soyayya, idan suka fito waje kuma sai kaga kamar waɗan da basa yi wa juna magana.

A satin da ya wuce aka sha bikin Jumma, sai dai ita Mahnoor bata je ba, Jaish ya hanata zuwa, sosai Jumma ta ji babu daɗi, amma ya ta iya to? Yanzu Jaish ɗin ne sai addu'a, ya samu tula tulan yar mutane yana matse mata, tin da ya matsa sau ɗaya ya ji da daɗi shikenan kuma ya dai'na barinsu su huta, amma har yau har gobe a iya matsesu ya tsaya, baya taɓa yarda ta fita ko nan ca kofar gida, ya yi mata iyaka da Nenne kuma, yanzu bata shiga harkarta.

Bappa kuma ya ɗauko maganar karin aurensa gadan gadan, nan fa Nenne ta ce idan ya isa shegiya take, bare kuma da ya kasance kanwar maman Mahnoor zai aura, yanda basa shiri iyayensu ma basa shirin nan ai ba ƙaramin ɗagawa Nenne hankali suka yi ba, nan fa gwaggo ta ce zama bai gansu ba, dole su fita naman mafita, dan idan wannan Mairon ta shigo gidan bappa fa akwai gagarumin matsala, dan haka ba zasu bari hakan ya faru na.

Gaskiya akwai case a gidan bappa wlh, dan kuwa za'a buga game tsakanin Nenne da Mairo, mu dai namu ido, kuma muna da Maltina mai sanyi, ana yi muna sha, dik wadda aka sumar sai mu yayyafa mata maltina ko ya kuka ce?.

Ga Nenne yanzu dan dole take aikin gida, ita kuma Mahnoor tana yi masu girki ita da mijinta, dan baya cin abin hannun Nenne, abin dariya baya karewa Jaish, idan bappa yana cikin gidan har Mahnoor ta yi girki ta gama ba zaku ga kafarsa a waje ba.

Idan kuma bappa baya nan iya Nenne ne wlh har kitchen yake shiga ya tayata aiki, suna yi suna hira.

Yau ta kama ranar Sunday, tsaye take a bakin ruwan kogin nan da suke wanke kaya, wanke kafarta ta yi ta fito, daga saman dutsen ta tsaya tana kallon ruwan kogin yadda yake tafiya, bappa ta kawowa abinci zata koma.

Bappa kuma yana ta kusa da ita yana É—an tsistsige ciyayin da suke takuwa wakensa da ya shuka.

Kamar daga sama ta hangosa yana nufosu, kasa ta yi da kanta tana guntse dariyar da ya ciyota, ai ma taki guntsuwa bata san ko da ta kwashe da dariyar ba, sai dai ta yi ƙasa da kai tana toshe baki.

Shi kansa bappa bai san lokacin da ya kwashe da dariya ba na ganin Jaish É—in da ya yi ya iso wajen nasu.
Chapter 188 · 0% Book details