← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 211

Sashe 38

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin ihu da fito da jama'ar wajen suka fara yi ne yasa Sweetien yi wani irin razana tana ƙoƙarin guduwa, a garin ƙoƙarinta na miƙewa ta gudu ne idanunta suka sauƙa a kan Devil dake gefenta yana zaune saman nasa sofar.
Habawa ai bata san lokacin da ta kurma ihu ba, saboda ba karya Devil ya tsoratata fiye da tunaninku, kun dai san yadda jikin ƴan Wrestling yake ko? Suna cike, damatsan hannun nan nasu kamar zai fashe, ga uban tattoo da suke zanawa a jiki, su tara gashin kai mai tsawo wanda wannan kuma dama al'adar birnin Dark world ne, sannan abu na biyu da ya kara tsorata Sweetien shi ne Devil fuskarsa a turɓune kamar an aiko mashi da cewa uwarsa ta mutu, daga ganin wannan fuska babu imani a tattare da shi, ga idanu manya sai muzurai yake yi, shararren ɗan Wrestling ne wanda shi ne master dake basu horo a kan Wrestling ɗin, shi ya koyar da Ronnie ma, amma shi yanzu baya wasa, dan babu mai yin winning ɗinsa, har yanzu ba'a samu wanda zai iya dokesa ba, shiyasa ya daina shiga wasan yana cigaba da horar da masu tasowa kawai, a yanzu dai Ronnie shi ne zakara a cikin duk ƴan wasan dake cikin empeir ɗin, da yake shi Ronnie yana da siririn jiki kalar nasu na Koreans sai ya zamana shi duk horon Wrestling ɗin da ya samu wajen Devil damatsan hannunsa basu wani cika sosai ba, bai da wani cika, idan ka gansa sai ka yi zaton ba zai iya taɓuka komai ba, sai an haɗu a filli wasa kaga in da yake zubar da maza yana ɗagawa yana wurgi da su kamar yasamu kwalaye.

Sannan shi Ronnie bai wani ɓata jikinsa da tattoo sosai kamar na master Devil ba, tattoo ɗan daidai ya zana na zanen bakar damisa, shi kam Devil duk ya zane ko'ina na jikinsa, ganinsa da ido sai ya baka tsoro, ba'a banza Sweetien ta tsorata ba, rashin mutuncinsa ya yi yawa, kowa tsoronsa yake yi a cikin birnin except Ronnie, ga shi kullum cikin wando three cuters and riga mai gajeran hannu yake, duk ya saki damatsan hannu duk tattoo nasu kunama, damisa da sauransu yana kara razana zuƙatan bayin Allah dan iskaci ya yi mashi yawa.

Ihun da ta zunduma ya janyo hankalin mutane dayawa a kanta har shi Devil ɗin, idanu suka yo kanta. Da sauri Ronnie ya miƙe ya dawo kusa da ita ta ɗayan bangaren da Master Devil yake kenan. Riƙo hannayenta a cikin nasa ya yi tare da tambayarta lafiya?.

Nan take jama'a suka tsareta da ido, sun ga kyau iya kyau, sai suka kasa tantance ita da king of beautyn nasu wato Ronnie ma wanene ya fi kyau?.

Ita ma Floris matsawo ta yi suka fara tambayarta me yake faruwa?. Da kyar ta iya ce masu. "I'm afraid". Ta yi maganar kamar zata yi kuka.

"I'm here to take care of you, don't be scared of anything, nothing will happen, just watch the game let me watch your beautifull face like television". Cewar Ronnie, ya kai karshen maganar yana É—an murmushi.

Ƙanƙame hannunsa ta yi tana tunanin Kamran and Pretty, zuciyarta tamkar zata fashe saboda tsoro, daga karshe ma kwantar da kanta a saman shoulder ɗinsa ta yi tana cigaba da tunaninta.

Shigowar wani ƙaƙƙarfan matashi cikin wajen wasan ne yasa jama'ar wajen suka sake saka fito tare da ihu, wasu suna sakin tafi da hannunsu rap, rap, rap.

Matashi ne ƙaƙƙarfa madaki katti, shi ma jikinsa duk zanen tattoo na Black Tiger, chocolate guy ne, jikinsa duk jijiyoyi a tsaitsaye, karfi kam ba'a magana, ga shi kuma kyakkyawa sosai, gashin kansa bai da tsawo sosai, a iya wuya ya tsaya mashi, sannan ya watsa gashin nasa kamar dambun rama bai ɗaure ba.

Sai tafi ake yi ana jiran wanda zai iya gwabzawa da shi ya fito. Almost 10 mins da shigowarsa cikin filin kafin wani haÉ—aÉ—É—en matashi ya shigo, na gaya maku mutanen birnin Dark world fa ni har yanzu banga mummuna ba, kyawawa ne sosai kamar su suka yi kansu, ga cikar duk wata halinta na mata da maza, abin dai ba'a magana, sai dai kash ba musulmi ko guda É—aya a cikinsu, dukkansu abu É—aya suke bautawa, Christian's ne...... Fata na dai Allah ya kawo maku shiriya ku gane gaskiya wata kila zaku daina zalincin da kuke yi, dan musulunci rahmace babba da babu irinta a duniya.

Wani irin fito mai sauti Ronnie ya yi shigowan wannan guy na biyun, bayan ya yi fiton ne ya ce da Floris. "Our Oxil ne zai yi winning".

Delisha ce ta amsa da cewa. "No Feros ne winner". Har ta yanke hukunci.

Harara ya wurga mata da ido tare da cewa zamu gani.

Ita dai Sweetie da bata ma san me za'ayi a wajen ba ta kwanta shiru a saman shoulder ɗinsa abinta, bata san wani irin wasa za'a gudanar ba, ita dai tana ta ganin ƙosassu kuma lafiyayyun maza sai tururuwan zuwa wajen suke yi. Ga ƴan'mata ma nan birjin, kowacce tana ta kallon wanda take burin aura.

Hannu ƴan wasan suka haɗa suka gaisa da juna, dama a ƙaidar wasan kenan, sai an gaisa an rungumi juna kafin a fara. Suna gaisawa jama'a suka sanya ihu haɗe da fito, kowa ka ɗaga idanu ka kallah a cikin jama'ar zaka gansa da murmushi a face ɗinsa, da alama suna cikin annasuwa, tabbas mutanen birnin nan suka jin daɗin ganin wannan wasa, sai murna suke yi.

Master Devil da yake a matsayi commissioner wasannin ne ya miƙe tsaye, yana da tsawo sosai ga faɗi, taku ya fara yi cikin jarumta ya isa cikin tsakiyar filin wasan, Sweetie tana ganin ya miƙe ta ƙara ƙanƙame Ronnie, dama tun ɗazun sai satar kallonsa take yi ya tsoratata ya kuma bata mamaki, bata taɓa ganin mutun irin haka ba a rayuwarta, ko Kamran da yake da damatsan hannu manya saboda horon da Mamma ke bashi bai kai rabin Devil ba, shiyasa ta ruɗe baiwar Allah.

Hand gloves na wasan master Devil ya ƙarɓa a waje rappern wasannin, irin hands gloves ɗinsu masu kauri sosai ɗin nan, shi ya karɓa ya sanya masu a hannu tare da ɗaura masu maroon ɗin handkerchief a gaban goshinsu, sannan ya sanya hannu a tsakiyansu ya yi counting from 1 to 10 kafin ya furta start. Yana faɗin hakan ya bar wajen.

Wasa aka fara bugawa, mazan nan kowannensu ya zage dantse, bugun juna suke yi babu wasa, kowa yana son ya rayuwa, wannan wasa ce tsakanin mutuwa da rayuwa, duk wanda ya faÉ—i shikenan ya bar duniya, kuma a haka suke yarda su yi, dama murnarsu suke shiga cikin wasan.

Jama'a sai fito suke yi, su dama kun san ƴan karawa abu armashi ne, ai kuwa sai yi suke yi. Wasa ya fara ɗaukar zafi, wasu maza dake zaune a saman nasu sofar sai kace da su ake faɗar, sai wani wuwwurga hannu suke yi, idan ƴan wasan ɗaya ya ɗaga ɗaga zai buga da ƙasa sai kagansu su sanya hannu kamar zasu tare shi, yadda kuka san da su ake yi, ƴan karawa abu armashi wato masu ihu da fitoma suna yin nasu, yanzu almost karfe 11 na dare amma babu alamar zasu je su kwanta su yi barci, ita ma Sweetie yanzu ta ware idanunta tana ganin wannan wasa mai abin al'ajabi a gareta, sai dai kuma tausayi ne cike taf a ranta, dan yadda suke jibgar juna tsakaninsu da Allah sai da idanunta suka kawo kwallah, abin ya ɗaga mata hankali sosai, amma ba yadda zata yi dole ta hakura ta kallah.

Wasa ta ɗauki zafi, Feros ya fasawa Oxil baki, nan take Ronnie ya ɓata rai, dan Oxil mutuminsa ne, ita kuwa Delisha murmushi ta fara yi dan ita tana backing na Feros ne, Floris da dama bata bin bayan kowa wasa kawai ta zo gani hankalinta a kwance yake abinta, duk wanda aka daka shi ya sani.

Wasa fa ta yi tsamari sosai, Feros ya sake fasawa Oxil hanci, nan fa hankalin masoya Oxil suka tashi, ciki kuma harda Ronnie wanda yake jin kamar ya je ya karɓawa Oxil ɗin, ransa ya ɓaci, shi gani yake naushi ɗaya ya ishe shi ya gama da Feros, faɗi yake yi a ransa in dai Feros ya yi winning ya ja aka kashe Oxil to tabbas next wasa da shi zasu buga ya ɗaukarwa Oxil fansa....... Babbar magana, yau dai ake yinta, wato wasan ma wasu suna shiga ne dan ɗaukar fansan ƴan uwansu kamar dai yadda Ronnie ya kurta a ransa yanzu! E lallai black tiger kafi kowa tara makiya a duniyar nan, dan kai ne silar komai, tab da mutanen birnin nan zasu samu dama ina ga cinyeka ɗanya zasu yi, dan dai kawai ba wanda ya san kai mutun ne ko aljani, amma fa my people's akwai matsala babba a wannan birnin, Allah ka dawwamar da mu a cikin addinin musulunci addinin ni'ima, yo idan ba rashin musulmar zuciya ba zasu yi irin wannan wasa da ransu haka ne? Sun ɗauki rai ba'a bakin komai ba! Allah yasa su samu dai su musulunta ko a rage zalinci kam in ba haka ba akwai babbar matsala.

A hankali tausayi yasa Sweetien ta fara kuka da hawayenta, musamman yadda taga sai jibgar Oxil Feros yake yi, abin ya yi matuƙar ɗaga mata hankali, kamar ba jini da tsoka bane a jikunansu, sun zage sai jibgar juna suke yi kamar basu jin zafin jikinsu?.

Wani irin naushi da Feros ya kaiwa Oxil ne yasa shi ya yi baya baya yana ƙoƙarin faɗuwa, cikin zafin jini Feros ɗin ya sake binsa da nufin ya ƙarisa shi kawai ya cinye gasar.

Rai a matuƙar ɓace Ronnie ya kurma ihu da sunan Oxil ɗin wanda hakan ya yi sanadiyar sanya Oxil ɗin ya farga tare da dawowa cikin hayyacinsa, cikin fusata ya sanya hannusa ya kare naushin da Feros ya kawo mashi, da karfin gaske ya murɗe hannun Feros ɗin baya tare da miƙewa tsaye da kyau ya fara ƙoƙarin kwatar kansa.
Chapter 38 · 0% Book details