Sashe 182
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau dai ga shi muguntarta ya juyo kanta, Mahreen dai bata iya komai ba face taya Mahnoor surutu idan tana aiki, sai cin abinci da wanka da barci, wankar ma fa idan tsiyanta ya motso sai ta ce lallai Mahnoor ce zata yi mata ko kuma bappa, kaso 70 cikin É—ari na wankanta su suke yi mata, ko bappa ko Mahnoor, kaso 30 ne take yi da kanta.
Dan dole ba dan ta so ba ta fito ta baro Mahreen ɗin, dan ko ta tashi ba wani abin da zata iya taɓuka mata ba.
Wajen wanke wanken ta koma, ruwa ta É—ebo ta fara yi, tana yi tana tsinewa Jaish a cikin zuciyarta, tana ta kwashe mashi albarka da ya hana Mahnoor fitowa.... Ni kuwa nace ki kwana kina tsine masa idan kin ga dama, ai tun da mommarsa ta ce É—an albarka jeka Allah ya yi maka albarka ai sai dai yaga cigaba, ke tsinuwarki ta haÉ—uwar titi rabuwar gate me zata yi mashi in banda ma ta kara mashi lafiya da kwarin gwiwar cigaba da zuba love É—insa da Æ´ar matarsa hankalinsu a kwance, aiki ne dai ya hana kuma ta hanu sai dai ayi wacce za'ayi ato, kuma mu ya yi mana dai'dai!!.
Ta ɗauki almost 1h a wajen wanke wanken nan, tsabar san jiki irin nata ma ta gaza iya tattare wajen wanke wanken ta share ta gyara kamar yadda Mahnoor take yi, ta dai ɗauke kwanikan daga wajen ta yi komai sama sama, sharar gidan ma sharar gongoloso ta yi, iya in da idanu suke gani kawai ta share saɓanin Mahnoor dake ɗage komai ta bi lungu da tsako ta kwakulo datti ta share tsab.
Ita kam sai ta zuba abinta fisha kawai aka wuce wajen.
Haka ta hura wuta ta ɗaura ruwan girki, kada ku so kuga abincin shafshuta, a take ta jajjaɓa komai, miyarma sai da ta gama haɗa komai a ƙasa, cikin ruwan sanyi ta zuba maggin da su gishiri kafin ya ɗaura a wuta, ta ɗauko nama ta banka, yana tafasowa ɗaya ta kaɗe hege, rabonta da yin girki yau a kallah ya kai shekaru 6 zuwa 7, tun Mahnoor tana yar shekaru 8 take girki da sauran aikace aikace, har ta fara manta yadda ake hura wuta, shiyasa ta sha bakar wahala kafin wutan ya kama, sai ta shirya itacen wutar ta kama daga baya itacen su sake watsewa wutar ta mutu, hegiya har murar dole ta yi saboda hayaki.
Haka ta kwasawa kowa abincinsa ta kai masa, a lokacin karfe 9:30 ya yi, dan dole ba dan ta so ba ta kwasawa su Mahnoor, dan tana tsoron Jaish yasa ta yi hakan, ɗakin bappa ta kai masu ta ajiye, dan tana tsoron shiga room ɗinsu. Bayan ta gama ba tattare kitchen ɗin ta gyara ba bare a kai ga wanka a tsabtace jiki, sai haɗa zufa take yi ta jawo mayafi fuuuu ta fice sai gidan Arɗo dan ta je ta gayawa gwaggonta, ta ce da sake, ba zata saɓuba bindiga a ruwa, ba zata iya wahalar nan ba, dole gwaggonta ta samo mata mafitar da zai sa Mahnoor ta koma yi mata aiki.
________________💘🌹_____________
Shigewa jikinsa ita ma ta yi, dukkansu biyu wani irin farinciki na musamman suka tsinci kansu a ciki. Saman waist beat É—inta ya É—aura hannunsa yana cigaba da wasa da su kamar dai jiya.
Shiru ta kwanta, kafin wani É—an lokaci barci mai daÉ—i ya É—auketa. Shi ma bai wani jima ba ya mayar da barci.
Baiwar Allah da yake bata saba barci haka ba, kun san iwar haka tana fama da aiki, sai barcin nata ya gaza nisa, ta gaza yinsa mai nauyi, sai ta rinƙa zabura tana farkawa, idan ta ganta a kwance a jikinsa sai ta sauke ajiyar zuciya ta sake mayar da kanta ta mayar da barcinta.
Dik abin da take yi yana jinta, dan barcinsa bata yi nauyi ba, yana da ɗabi'ar jin dik motsin mutun a cikin barci. Ba ƙaramin tausaya mata ya yi ba, dik in ta zabura zata miƙe sai ya ji hakan har cikin ransa, wato ta saba da tashi a wahalce, a ransa yake faɗin ai wlh ko tsinke ta dai'na ɗagawa a gidan nan, harta gyaran ɗakin nasu ma dole Mahreen ta koya yi dan ta rinƙa yi masu, at least ta huta ko da na one year haka bata yi aikin komai ba.
Around karfe 8 da ta farka daga barcin ne ta fara ƙoƙarin barin jikinsa, a cewarta zata je ta duba ko Nenne ta fito, in bata fito ba sai ta yi aikin, har ta manta da ya ce kada ta sake yin komai sai da izininsa, Allah sarki ba laifinta bane, sabo ne ya ja hakan.
Tana ƙoƙarin lallaɓawa ta bar jikinsa idanunsa a lumshe yasa hannu ya mayar da ita, can kasan maƙoshinsa da murya irin na mai barci ya ce. "Ina zaki je?".
"Aiki zan je na yi hamma". Ta bashi amsa cikin nitsuwa.
Waro idanunsa ya yi a kanta. Kallon face É—inta da kyau ya yi kafin ya mayar da su ya limshe da alama barci bata ishashi ba.
"Babu in da zaki je" . Shi ne kawai abin da ya furta, daga haka ya kara ja masu bargo suka cigaba da yin barci.
Hajiya Mahreen tamu kuwa, sai karfe 10 ta tashi daga barci, nan fa suka saka sabon dirama ita da Nenne, dan kuwa ita Nenne bata É—aura mata ruwan wanka kamar yadda Mahnoor take yi ba, har gidan ArÉ—o ta bi Nennen nata dan ta tambayeta ina ruwan wankanta.
Nan fa Nenne ta ce ta je ta hura wuta da kanta ta ɗaura, aikuwa ta ce ita wlh ba zata iya ba, ai kullum Mahnoor ce take ɗaura mata, dan haka wlh ba zata iya hura wuta ba. Ta saka masu kuka tana birgima a ƙasa kamar mai aljanu.
Gwaggo kakarta ce ta ce. "Taso kizo muje na É—aura maki ruwan sai ki yi wankan a nan".
Make kafaÉ—a ta yi, ta ce Allahn baram ba zata yadda ba, domin bappanta ya hanata cire kaya a koma ina ne in ba a gidansu ba, saboda haka ita ba zata yi wanka a wannan gidan ba, sai dai gwaggon ta biyota gidansu ta É—aura mata tuwan wanka a can. Tashin hankali kenan, Mahreen duniya, wai gwaggo ta bita gida ta É—aura mata ruwan, wlh mugunta babu kyau jama'a, yanzu dai da Nenne da Mahnoor waye yafi wani cin riba? A tunaninta ta cuta mata, to ku yi masu alkalanci! Ai ko da bata auri Jaish ba ita ta ci riba a kan Nenne tun da ta iya aikin komai!.
Taɓe baki gwaggo ta yi tana salati ta ce. "Ke bappan naki ma ya ci gidansu, wuce muje nayi maki wanka a nan, da zai ce kada ki cire kaya a ko'ina nan ba gidan da uwarki ta yi wasan kasa bane?". Cewar gwaggo da haushin bappa ya kamata, a ganinta ai nan gidan ya wuce ya yi wani magana a kai, bata san yana da gaskiya ba, idan zaka hana yaro abu tofa ka hana shi gabaɗaya ne, kada ka kuskura kace mashi a nan zai iya yi a nan ne karya kuskura ya yi, in ka yi haka wlh in mai yi ne tsab zai yi a koma ina, dan kuwa sai ya ce ai baka son waɗan nan ne yasa zaka ce ya yi a nan kada ya yi a nan, so the best way kawai ka hana shi gabaɗaya shi ne zaka ci riba ya kuma hanu ɗin, misali kaman dai Mahreen ɗin, kun dai san gidan Arɗo gidan baffan bappn ne, sannan gidan surukansa ne, mata biyu Arɗo ya bashi a cikin gidan, amma kunga da yake ya hanata gabaɗaya har nan ta ki yarda.
Gwaggo ta kara jin haushin bappa sosai, dama yanzu ma haushinsa kamar ta shakesa, saboda ya bawa Mahnoor bango majigina ya zama garkuwa a gareta ya hanata yin komai sun bar mata Æ´a Nenne tana wahala.
"Ni fa gwaggo ba zan yi wanka a nan ba, koma me zaki ce bappana ya hanani cire kayana a gidan koma waye, kuma ni ba zan cire ba, sai dai ki bini gida ki É—aura mun ruwan a can, idan ya yi zafi ki juye ki kai mun banÉ—aki kamar yadda Adda Mahnoor É—ina take mun, in ba haka ba ni ba zan yi wankan ba". Cikin tsiwa take maganar, tsabar kwarewa a masifa yarinyar nan har da rufe idanu.
Tun da ta fara surutan nata gwaggo ta taɓe baki tana kallonta har ta kai aya, dama ta san Mahreen ba kunya ce da ita ba, to yanzu kuma bappa ya kara mata wasu huɗuba ai kuma shikenan.
"Eyeeee to sannu uwata, wato na biki gida na É—aura maki ruwan ko? To dan uwarki sai dai kada ki yi wankan, ke dama baki da kunya ai na sani ba sai kin kara jaddada mun ba, sai ki wuce uwraki Mahnoor É—in ta É—aura maki!!". Cewar gwaggo masifa, cikin faÉ—a ta yi maganar
Miƙewa tsaye ta yi tana yi wa kakar tata kallon uku goma. "Ke dama gwaggo waye ya ce ma ki ce zaki ɗaura mun ruwan? Ni ai ba wajenki na zo ba da zaki ce kada na yi wanka, so kike na zauna da datti jikina ya nannaɗe kamar taki ko?".
Mahreen duniya ita a tunaninta tamu tamun da jikin gwaggo ya yi na tsufar nan datti ne yasa hakan ba komai ba, yarinta akwai daÉ—i, Allah na tuba idan datti ne ina mutun zai tsaya da wari? Kai Mahreen akwai iya goge hadda wlh.
"Dama ba sai kin mun haka zan gane rashin kunyarki ta karu ba, shegen ido kamar na ubanki, ni zo ki wuce ki bar mun gida ko na zaneki". Cewar goggo.
(Yau kaka da jikarta an ɓata fa jama'a ku zo ku yi sulhu.)
"Wlh idanuna sun fi naki kyau goggo, kuma bappana dai ya fiku kyau dikkanku gidan nan, kuma dama ni me zan yi da wannan gidan naki da dik datti baki share kofarki da É—akinki?". Tana magana tana murguÉ—a baki.