Sashe 151
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baiwar Allah kunya kamar ƙasa ya buɗe ta nutse ciki, haka ta miƙe tsaye, idanun gabaɗaya jama'a a kanta, tamkar zata kurma ihu, Jumma ya ɗan riƙota suka nufi wajen da Inna Rabin take zaune cikin mata a ƙarƙashin runfar da aka kafa saman tabarma.
Sabuwar plate dal a ledarta Innar ta basu, da yake bappa yasan al'adun nasu sai ya shirya komai da kansa, har plate ɗin dik shi ya saya, dozen ya sayo, sai ya ajiye mata sauran a cikin bukkarta. Dik wannan bidiri da ake yi Nenne bata nan, ko leƙau taki leƙowa, harda Arɗo yana wajen saman kujerar sarautarsa na musamman, amma ina bakar zuciyar Nenne ya hanata zuwa. Kun san yan uwan Arɗo su ne ƴan uwan bappa, dan shi ne kawunsa, ƴan uwan maman Mahnoor da nace maku sun zo yan uwan Inna kakarta ce. So shi Arɗo ya zo, ƴan uwansa ne suka ki zuwa.
Wajen gasa namar ta nufa, a tare da Jumma suka je, gabaɗaya masu gashin namar matsawa suka yi suka bata wajen, dan da kanta zata zuba mashi, da ƴan uwansa suna nan zasu gani ne tasan abu mai kyau ne ko bata sani ba, idan ta zaɓo tsokoki masu kyau da laushi to tasan abu mai kyau kenan, ana sa ran abubuwa masu kyau zata rinƙa bashi idan suka tare a gidansu, idan kuma ta zaɓo irinsu hanji da huhu tun daga nan ƴan uwansa zasu fara jefanta da maganganu ace ya yi zaɓen tumun dare, bata san abu mai kyau ba.
Yo Mahnoor da take nutsestsiya mai hankali yaushe zata ɗauko abu maras kyau?. Dama dai Mahreen ce kila ta zaɓo mashi ra'ayinta, amma Mahnoor jajayen tsokoki masu kyau da laushi ta zaɓo mashi, da zafinsu, sai titirin hayaki yake yi, ga shi sun gasu sosai.
Tun da ta fara zaɓar namar bappa ya tashi ya bar wajen, dan kunya ba zata barshi ya iya kallonsu ba, dama saboda Jaish ɗin ya zauna a wajen, a gefensu Arɗo yakamata ya zauna, shi kuma Jaish dama da abokansa zai zauna, amma da yake bashi da aboki ne sai yasa bappa da kawu Ibrahim kanin maman Mahnoor ɗin suka zauna a tare da shi, to kunga a matsayin bappa na uba ai ba ya zauna ayi wannan abin da ake yi tare da abokan ango ayi da shi ba ko?.
Shi ne yasa ya bar wajen, ya bar Jaish ɗin da Ibrahim, shi ma Ibrahim ɗin yaso barin wajen a matsayinsa na kawunta, amma bappa ya ce mashi ya daure ya zauna tun da Jaish dai bashi da kowa........ Wayyo wai ina Yah Jawad, ya zo ya ga ikon god yau, ina ga da idan Jawad ya fara dariyar mugunta sai ya suma saboda dariya, dan ɗan duniya ne, yana can yana cin amanar Yah Rizwan, ya sanya Chuchu a ɗaki har da kashe wuta....😂
A gabansa tazo ta tsugunna ita da Jumma, kansa ya É—ago ya kalleta, dik sai ta ji tsoro da shakkarsa ya kamata, kasa É—aukar wukar ta yi ta yanko ta sa mashi a baki.
Sai jira jama'a suke yi su ga kwakwaf. Mahreen sarkin wutar ciki ne ta ce. "Adda Mahnoor ki bashi mana". Wato ita Mahreen an katse mata jin daÉ—i ne, ayi maza ayi dan a sakar mata kiÉ—a ta cigaba da taka rawanta, ta cire gyalen kayan nata ta É—aura a kunkuminta, rawa ne ya yi daÉ—i, sam kada ku ga laifinta.
Yaufa wani ɗagun kai na daban take ji da shi, dan ta saka sabon kaya kuma mai kyau na yan birni, sai kallon ƙaskanci take yi wa kowa. Mahreen manyan ƙasa.
Dafa shoulder É—inta Jumma ta yi alamar ta daure ta bashi, shi kuwa kallon face É—inta kawai yake yi, tabbas yana jin daÉ—in kallonta, saboda yanayin da yake shiga na kokarin tunano Zunaira da yake yi.
Kamar zata yi kuka ta sanya hannu ta ɗauki wukar, ɗan ƙarami ta yanka mashi, sai tiriri yake yi, ji take yi kamar ba zai karɓa ba ko ta bashi, kamar zai yarfata a cikin mutane, shiyasa ta kasa iya fara bashi da wuri.
Aikuwa ta gudu bata tsira ba, dan kuwa ko da ta kawo mashi saitin bakinsa sai yaki buÉ—e bakin, ya tsareta da idanu yana ta kallonta.
Sai kallonsu jama'an suke yi suna jira su ji dalilinsa nakin karbar nama. Kamar zata mutu saboda kunya, ga shi ya ki karɓa abin ya kara kunyatata sosai.
Ɗan taɓa shoulder ɗinsa Ibrahim ya yi, nisawa ya yi tare da dawo da kallonsa a kan Ibrahim ɗin, alama ya yi mashi da ido a kan ya karɓi namar da take bashi, kallon namar ya yi da kyau, kamar ba zai karɓa ba, sai kuma ya tuna yadda suka yi da bappa kafin su zo wajen, hakan yasa ba dan ya so ba ya buɗe baki.
Lokacin da ta zo saka mashi a bakin sai da ta ji duniya ya yi wani irin juya mata, saboda a lokacin ta matso sosai ta kuma kalli face É—insa da kyau, hakan yasa ta ji kamar wadda aka jonawa shocking a jiki.
Karɓa ya yi ya fara taunawa a hankali cikin nutsuwa.
A ƙa'ida sai ta bashi namar ya ci ya ƙoshi, amma ina shi ya karya masu doka tun a karon farko, dan kuwa da ta yunƙura zata yanko mashi na biyu, hannu ya ɗaga mata alamar baya da buƙata.
Abin ya yi matuƙar bawa jama'ar wajen mamaki, ba'a taɓa yin angon da ya yi irin abin da ya yi ɗin ba. Bappa kam da yasan halin kayansa sai bai wani damu ba.
Nan take aka fara tsegumin anya angon nan yana sonta kuwa? Anya ba kawai bashi ita aka yi ba? Kun san jama'a da dama burinsu suga laifinka ko kaÉ—an ne su yi ta ririta shi wa duniya, aikuwa haka aka yi, su Nenne dake gida ma har sun samu labarin abin da Jaish ya yi a wajen bikin, ya ce ba zai ci abin hannun amaryarsa ba, wannan ai cin mutunci ne.
Da yake a yanzu yana jin fulatancin sai yake tsinkayo maganganun mutane ɗaiɗai a cikin kunnensa, ya ji sai aibata abin suke yi, har da masu cewa anya wannan ba zaluntar Mahnoor ɗin zai yi idan aka damƙa mashi ita ba kuwa?.
Hakan ta ɗan sosa mashi rai, da farko bai yi niyar yin al'adun nasu ba, amma jin yadda jama'a suke ta faman ririta kin karɓar namar da ya yi har suka sanya Mahnoor ɗin kuka sosai ne yasa ya kuduri niyar zai yi ko dan ita Mahnoor ɗin da take marainiyar Allah.
Tana tsugunne a gaban nasa ta kasa miƙewa saboda tsananin kunya, kuka ta fara yi jin yadda jama'a ke tufa albarkacin bakinsu a kanta, wasu sun yi mata dariya, ƴan uwan bappa da basu a wajen, tsintar labarin ma suka yi har da cewa Allah ya kara Allah yasa angon ma ya azabtar da ita dan kawai Allah ya ƙaddara ba rabon Faisal bace ita ɗin shikenan daga samun labari suka hau banka munanan fata.
Sam ran bappa bai ji daɗin yadda jama'a suke ta zagin ba, ba'a taɓa yin amaryar da aka zaga haka kamar ita ba, abin ya sosa mashi rai!.
Kwatsam suna tsaka da surutansu sai ya gwada masu shi ma ɗan duniya ne, ya yi abin da ya ja suka rufe bakunansu tsit. Abin da ya yi kuwa shi ne yadda take tsugunne a gaban nan nasa tana kuka sai ya kai hannu ya riƙo shoulder ɗinta, ɗagota ya yi tare da zaunar da ita a kusa da shi in da bappan nata ya tashi kenan, dama shi zamansu a kusa da shi ba bakon abu bane a wajensa, kada ku manta shi ɗin aljanin Mahreen ne, abin da har saman cikyarsa Mahreen ɗin tana zama. So bai ji wani shakkar zaunar da ita a kusa da shi ba!.
Karɓar plate ɗin namar dake hannunta ya yi ya miƙawa Jumma dake tsugunne a gabansu ta miƙe da shi ta mayarwa Inna. Sannan ya hau share mata hawaye da kyawawan fararen tafukan hannunsa tare da nuna alamar rarrashi. Daga karshe ma sai ya ɗan jawota jikinsa, ya kwantar mata da kanta a saman gefen kirjinsa yana ɗan bubbuga bayanta da hannunsa ɗaya alamar rarrashi.
Habawa ji kake tsit ya kashe bakin masu cewa baya sonta, ba'a taɓa yin irin angon da ya yi hakan a kauyen ba, harda runguma e lallai a cewarsu ya tabbata kula na daban zai bata.
Bappa ransa fes, ya ji matuƙar daɗi hakan, dama shi bai ji haushin abin da Jaish ɗin ya yi da farko ba, haushin jama'ar kawai ya ji, dan in baku manta ba shi yana ganin kamar suna son junansu, so yasan Jaish yana sonta, shiyasa bai damu ba. Yanzu kuma da ya rarrasheta sai abin ta ƙara faranta mashi rai.
Shiru ta kwanta a kirjin nasa tana shesshekar kuka a hankali hankali, gabaÉ—aya ta rasa a wani duniya take, ta rasa farinciki take ji ne ko bakinciki.
Ihu jama'a suka fara yi suna yi masu tafi suna faÉ—in wai ya kai namiji.
Inna Rabi ce ta katse masu ihun nasu ta hanyar kawowa Jaish É—in kayan kwalliya cikin tray a gabansa, wai ya yi mata kwalliya su hau dutse, dan bappa ya cire batun girki a ciki, saboda shi da kansa yasan Jaish kam ba zai iya yin girki ba gaskiya, dan haka kada su wahalar da shari'a.
Ba musu ya karɓi kayan kwalliyar, irin kayan kwalliya ce dai ta kauye. Shiru ya zubawa kayan kwalliyar idanu yana kallonsu, shi da bai san me ma ake yi da su ba, bai san a ina ake sanyasu ba.
Muryarta cikin kuka ƙasa ƙasa ne ya katse mashi tunani da cewa. "Hamma zan taimaka maka". Tana daga kwance a jikin nasa ta yi maganar....... Eye su Mahnoor an fara sanin daɗin duniya, har da wani zata taimaka mashi, eye amarya ta angonta kenan, da gaskiyarki taimaka mashi kada ayi mashi dariya.
Kawo mata kayan kwalliyar ya yi gabanta alamar to ta taimaka mashi É—in, dama a cikin tray É—in silver aka zuba su.