← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 211

Sashe 112

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gwaggo ban sani ba, wlh ban taɓa ganinsa ba sai ranar da waɗan da suka ɗaukeni suka kaini gidansa, bani da wata alaƙa ta kusa ko ta nesa da shi, yanzu haka ban san a wace ƙasa yake ba, ban san ɗan wace ƙasa bace, ni sau ɗaya ma na taɓa jin sautin muryarsa, ranar da zamu rabu, a ranar ne ya taɓa yi mun magana, ba komai kuma ya ce mun ba face na kula da kaina sosai sai haɗuwa ta gaba idan Allah ya ƙaddara, shikenan abin da ya ce mun, daga haka ban sake sanin komai ba, tsawon sati ina sume, bayan na farfaɗo da kwana uku aka dawo dani Nigeria, kuma ko da na farfaɗo ban gansa ba, boys ɗinsa ne suka dawo dani kamar yadda suka zo suka ɗaukeni".

"Har kofar gidan nan suka dawo dani, sannan suka bani kuɗi suka ce oga ya ce na rinƙa cin abubuwa masu daɗi, kuma na tabbata ya bani waɗan nan kuɗaɗen ne dan a tunaninsa cikin jikina ya fita kamar yadda suka yi yunƙurin zubar da shi tun farko, so shi ne yasa ya bani kuɗin dan na yi jinyar kai'na......" Ta kai karshen maganar tana sake rushewa da kuka mai sautin gaske.

Wani sabon kuka maman Hanif ta ɓarke da shi, da yake Zee tasan wacece ƴar uwar tata sosai, sai ta iya gano cewa tabbas karya take yi, duk yadda aka yi ta san uban cikin nan, wlh ta san komai dangane da shi, watakila tasan ba kaunar cikin ake yi bane yasa ta ɓoye dan ma kada maman Hanif ta ce zaa je wajensa har yasan da cikin ya yi yunkuri yi mashi wani abin, amma ba ta yadda za'ayi ace mutum ya ɗauketa tsawon wata biyu suna tare, kuma ya yi mata ciki sannan ta ce bata san shi ba, karya take yi, dole ta san shi! To a ina ta san shi? Ita dai Zee bata yarda da wannan magana ba, dan idan baku manta ba Khadijah ɗin ta yi mata karyar cewa bata san in da aka kaita ba har da ce mata tun da aka kaita a sume take tsawon wata biyu nan, har da ƙarawa wai ƙasar Russia aka kaita, kunga kuwa ai dole ta karyatata a yanzu ma.

Sai dai abin da Zee ɗin bata sani ba a nan shi ne, wlh maganganun Khadeejerh a wannan karon kam zallar gaskiya ce, duk abin da ta faɗa hakance ta faru, dama da farko taso ɓoye abin ne shiyasa ta yi wa Zee karya, to yanzu da komai ya tuno kansa me amfanin ɓoye gaskiya? Ai kunga babu, to wlh gaskiya ta faɗa, shi dai uban wannan ciki bata san shi ba, hasalima ba a nan Nigeria yake ba, ɗan Nigeria ne ko ɗan waje ne duk bata sani ba.

Ko a ina ya santa? Wannan ne abin tambaya, yanzu kuma a ina zata gansa har ta kai mashi ɗansa ko yarsa idan Allah yasa ta haife? Sannan ɗan wani ƙasa ne uban? Ina yake a halin yanzu? Shin yasan tana ɗauke da cikinsa? Wacece wadda Khadijah ɗin take yawan tunano muryarta tana ƙoƙarin zubar mata da cikin? Ya tabbata kenan kamar yadda Zee take hasashe ba'a kaunar wannan cikin kenan? Tun da ga shi har alluran zubar da shi aka yi mata! Lallai akwai cakwakiya sosai, haƙiƙa akwai abin da Khadijah ɗin ta rage bata sanar da su ba, dan kuwa bayan rayuwar da ta yi daga ita san uban cikin nata tabbas ta yi wani rayuwa da wata na ɗan lokacin, dan in baku manta ba bata tuna uban cikin nata kamar yadda take tuna sautin muryar wannan mata da zata zubar mata da cikin, ta ɓoye wannan labarin baya gaya masu ba. To wacece wannan mata?.

Ni kam na ce amma lallai wannan uban ciki na Khadijah anyi ɗan duniya na bugawa a jarida, tsabar isa da iskanci kawai kasa a ɗauko maka yarinyar mutane, ka ɗirka mata ciki ba gaira ba dalili, sannan ka yi yunƙurin zubar da ciki, ka kuma sakota a jirgi a dawo da ita Nigeria kamar yadda ka ɗauketa, wai ma a ina ya santa? Da alama guy ɗin ɗan balai ne, fata nama dai ni kam Allah yasa musulmi ne ba kafuri ba, amma dai wannan ya kai duk in da ɗan iska dan duniya ya kai wlh, anya yana da iyaye ma kuwa? Daga gani da wuya idan yana da mafaɗa gaskiya!.

ÆŠan rungumuta maman Hanif ta yi tare da shiga rarrashinta sosai.

After some minutes, da kyar suka samu ta yi shiru, bayan ta yi shirun komai ya lafa sun kudundune waje guda ita da Zee.

Kallonta da kyau maman Hanif É—in ta yi, cikin sanyin murya ta ce. "Khadijah to me zai hana mu je asibiti a zubar da cikin nan, kinga sai ki fito da miji kawai ki yi aure ki hutawa ranki".

Zaro idanu waje sosai ta yi, tamkar zata sa kuka ta ce. "A'a gwaggo, ina son cikina, idan na zubar da shi me ribana? Mutumin nan ya zalunceni, ya cuceni, ya lalata mun rayuwata, sannan da ya fahimci ina da ciki shi ne yasa a zubar mun, yanzu a tunaninsa an zubar da cikin, da alama babban mutum ne wanda baya son sunansa ta lalace na ya haifi ɗan shege, shi ne yasa ko ta halin ƙaƙa a zubar mun da cikin, ba abin da basu yi ba sai dai jinina ya zuba, amma cikin yana nan, tun da kika ga haka cikin nan yaki fita gwaggo to tabbas akwai wata aya da Ubangijinmu yake son nuna mana, kuma ni kai'na ina son haifar cikin, ko dan na ɗauki fansar abin da suka yi mun".

"Kullum mama tana yi mana nasiha, hakan yasa ta ja na yi wa É—an shege muguwar tsana, sai ga shi yau ni ce da kai'na zan haifi É—an shegen kuma a cikin gidanmu innalilahi wa inna ilahir rajiun....." Wani sabon kuka ta fashe da shi.

Shiru maman Hanif ta yi tana jinjina wannan al'amari a ranta, tabbas Khadija tana da gaskiya, tun da ba abin da ba'ayi wa wannan ciki ba yaki fita to gara kawai su barshi kada su ja rayuwar yarinya ya salwanta a banza, sannan kuma kamar yadda ta faɗa ne, tun da uban cikin baya son ɗan har ya yi yunƙurin zubar da ciki to tabbas yana da kyau ta haifi ɗan, idan ma uban nasa babban mutum ɗin ne ta yi amfani da wannan dama shi ma ta rusa mashi farincikinsa kamar yadda ya lalata mata tata, dan haka ya cancanci a bar wannan ciki ta haifesa, kuma cikin ma ya wuci munzalin zubarwa a yanzu, dan ya kai ɗa......... Tirƙashi ana yinta a RAWANIN ZALINCIN!!.🔥

Wunin yau cikin tsananin rashin daÉ—i suka yi shi, duk suna cikin damuwa, walwala ya kau daga tattare da su, Hauwa kuwa ta ja jiki ta kai kanta hospital dan ta jibgu ba karya.

Sai da aka yi kwana bakwai da rasuwar Hajiya sannan maman Hanif ta koma gidanta, maman Haidar dai shiru bata ba labarinta bata san mamansu ta rasu ba.

Allah sarki, time da maman Hanif take tare da su a gidan Khadija taga kula sosai irin wadda kowace mai ciki zata buƙata, tana komawa gidanta kuma suka fara fuskantar matsala da Hauwa, da maman Hanif tana nan sam bata shiga harkarsu, dan kuwa tana tsoron ta sake cin jibga, da farko ƴan'sanda taso kirawa maman Hanif ɗin, sai kuma ta fasa, dan bata son case ɗin ya zama babba, saboda tana son maman Hanif ta koma ita kuma ta fara gallazawa su Khadija har sai sun gudu da kafafunsu sun bar gidan, shi ne shirinta, sannan tana son yi wa maman Hanif ɗin wani mugun abin dan ya zama ita ce kaɗai zata cinye dukiyar bb Zee, shiyasa bata kira ƴan'sanda ba, dan idan ta yi mata abin ya faru ƴan'sanda zasu iya shiga case ɗin, idan suka shiga kuma za'a iya bukatar waɗan da suka taɓa sa in sa da maman Hanif ɗin dan bincike, kunga a nan asirinta zai iya tonuwa, shi ne yasa ta hakura bata kirasu ba

Ai kuwa haƙarta yana son cinma ruwa a wannan karonma, dan kuwa da alama burinta zai iya cika, saboda kuntata masu da take yi tana shiga harkarsu ta yi ta lalata masu abubuwa idan suka ajiye, idan suna girki ta zo ta zuba omo ko ta juye kedar gishiri a ciki, da kyar da suɗin goshi suke samun abin da zasu sanya a bakin salati, sai suna girkawa ta lalata masu.

Wani lokaci haka suke kwana su wuni da yunwa, hakan yasa Khadija ta fara bawa Zee shawara a kan su je Kaduna su nemo su Sadiq, daga nan su nemi aikin yi wanda zasu rinƙa yi dan su rufawa kansu asiri, yunwar nan ta yi yawa.

Da Zee ta ce. "To Aunty khadina baga kuÉ—in da kika dawo da shi É—in nan ba, ki fitar mu fara sana'a da shi".

Girgiza kai ta yi tare da cewa. "Zee ki bar batun wannan kuɗi, ina tanadinsu ne domin in ɗauki fansa a kan wannan mutumi, jira nake yi na haifi cikin tukun nan, dan mu gwabza shari'a, shiyasa bana son taɓa kuɗin". Tana magana tana shafa cikin nata da a yanzu ya kai almost 6 to 7 month. Ashe dai tasan da zaman kuɗin ba mantawa ta yi da su ba, ashe tanadinsu take yi dan gwabza faɗa ta kwatarwa da kanta ƴanci, akwai cakwakiya kenan, muje zuwa, da alama Khadija zata ɗauki dala ba gammo, idan babban mutum ne kuna tunanin zata tona masa asiri kamar yadda take tunanin nan kuma ta zauna lafiya? Ya zuba idanu yana kallonta?. Hmmmm akwai matsala gagarumin ma kuwa!!.

"Haka ne kuma, nima zanso ki É—auki fansa a kan wannan bakin shaiÉ—ani azzalumin". Cewar Zee.
Chapter 112 · 0% Book details