Sashe 166
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsabar tsorata da wannan tsawa da ta yi har bata san lokacin da ta saki fitsari a wajen ba, ta tsorata sosai da jin katuwar muryar jami'in.
Ita ga shi bata jin turanci bare tasan me suka faɗa, kan fanko ne, ɓata kuɗin makaranta kawai kawunta ya yi, ko kaɗan babu abin da ta sani.
Jin ta yi shiru tana muzurai ne yasa ransa ya ɓaci, dan sai yaga kamar rai'nin wayo ne, bai santa ba, bai san wacece ita ba kawai ya cire hannunsa dage cikin aljihun wandonsa ya ɗauketa da wani irin gigitattacen marin da ya sanyata ganin taurari.
Haba wani irin baya baya ta yi kafin ta zube ƙasa, ji ta yi duniya ya ɗauke mata cak. Dawo da kallonsa a kan securitys ɗin nasa ya yi, cikin magana ɗaya a takaice ya ce masu su shiga ko'ina a cikin gidan nan su fito mashi da Khadija.
Yadda suka amsa da to haÉ—e da sara mashi ne yasa Hauwa dawowa cikin hanyacinta, dan kunnuwanta sun ji muryoyin maza. Zaro idanu ta yi tana kallonsu, tama kasa kuka, dama idan kun ji abin da ake yi wa kuka to bai kai abin tashin hankali bane, idan bala'i ta yi balai neman kukan ma ake yi a rasa, ita dai yau Hauwa ta ji marin namijin gaske hegiya ta nemi kuka ta rasa.
Ko waye shi hegen kuma?🤔
Ko uban neman me yake yi wa Khadija? Anya ma ba shi ne uban cikin jikin nan nata ba kuwa? Da alama ya ji labarin cikin bai zube bane ya zo karasa shi kome? Dan naga basu shigo gidan da mutunci bane! Dik yadda aka yi ba mutunci ne ya kawosu ba, to koma dai me ai Allah ba azzalumin bawansa bane, sai dai bawa ya zalinci kansa, kila addu'ar da suke yi ne ya karɓu yasa Allah ya basu ikon guduwa Kaduna kafin hegun nan su iso, Allah sarki bayin Allan.
A guje gabaÉ—aya securitys É—in suka danna cikin parlourn, ta ko'ina suka fara nemanta, shi kuwa yana tsaye kekam kamar wani gunki.
After some minutes suka dawo tare da isar mashi da saƙon babu Khadija a cikin gidan. Cikin harshen turancin dai ya yi masu umarnin da su ɗauko mashi Hauwa su wurgata a bayan boot na motarsa su wuce da ita, daga haka ya juya ya nufi waje........... Koma wanene wannan ya cika shafaffe da mai, wato kasar ce ma ba zai taka ba sai an shinfiɗa mashi carpet ya bi ta kanta, hmmmm akwai hegu fa a RAWANIN ZALINCI ba kaɗan ba yaseen, kowa da kalar iskancinsa da iyashegensa, shi kuma ga nasa, to mu ai munga Black Tiger ma a iya mulki, shi babu wanda ya taɓa ganin face ɗinsa ma amma bala'in tsoronsa ake ji tamkar mutuwa, shi da tsabar bala'insa da ya azawa ƴan birninsa ma, gara mutuwa a kan jin komai ƙanƙantar motsinsa ko kuma maganarsa a kansu, to dan haka mu munga Black Tiger ma, ba wani sauran abin da za'a nuna mana kuma, dik wanda zai zo da nasa iskancin dik ya biyo bayan Black Tiger, ko kafarsa ma baku kama ba!!.
Da hannu É—aya É—aya daga cikin securitys É—in ya zo ya É—aga Hauwa sama sai cikin boot ya watsa hegiya, cikin takun isa ya juya ya bar gidan, a guje gabaÉ—aya securitys É—in suma suka bar gidan, suka shiga motocinsu suka tafi.
Sun bar ko'ina na gidan a wangale basu rufe ba, ni kam nace Allah yasa kada ɓarayi su shigo su ɗauke jakar kuɗin Khadija, wayyo wannan kuɗi yana ganin rayuwa, ko me yasa suke neman Khadijan? Allah yasa su yi ta jibgar Hauwa har sai ta koyi turanci a ranar ta gaya masu ina su Khadijah suka je.....🤸😂
Kai tsaye hanyar Kaduna motocin suka nufa domin komawa villah Abuja kenan.
Allah da ikonsa kuwa, suna shiga Kaduna a tsakiyar gari suka samu saɓani da motar da ta ɗauki su Khadija dake sume kamar gawarwaki, har saura kaɗan ma su ɗan yi karo motar su Khadija ɗin ta kauce ta basu hanya, a takaice dai an sace su Khadijah sun kuma yi saɓani da motocin da suka ɗauko hauwa dan nemansu.
Ko su waye suka sace su Khadijah? Ina kuma zasu kai su? Su kuma waÉ—an can ina zasu kai Hauwa?!
Hmmm akwai dai cakwakiya, Allah sarki su Khadija bayin Allan, mai keken napep É—in nan ne ya cucesu, ashe mugu ne mai safaran mutane, dama Zee bata yarda da shi ba Khadijah taki jin maganarta. To yanzu dai ga shi ya cucesu, Allah yasa ma ba sayar da su ya yi ba.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...âœï¸ðŸ”¥ðŸ•Šï¸
JIMETA
A hankali ta waro idanunta da suke cike da barci, bata taɓa yin barci mai daɗi irin wannan ba a gabaɗaya tsawon rayuwarta, kullum tana tsaka da barci Nenne take tashinta, ta katse mata farincikinta, sai ga shi yau ta yi barci cike da annashuwa kuma mai tsawo, ya lulluɓeta da bargo mai ɗumin gaske, ta ji matuƙar daɗin hakan.
Barcin ma bai isheta ba, kawai ta farka ne saboda rashin sabo, bata saba rana ta tsala tana barci ba, shiyasa ta gaza iya cigaba da yi ta farka.
Saman ɗakin nasu ta fara bi da kallo, kamar wadda aka tsikara, ko me ta tuna ta yi hanzarin miƙewa zaune a dubu tana kai kallonta wajen da ya kwanta.
Wayam babu shi babu labarinsa a ɗakin, tuni ya fice abinsa, dan ya ƙasa yin barci bawan Allah, ya zuba mata idanu yana ta kallonta tana barci, hakan yasa shi ya kasa rintsawa, da ya gaji da kallon nata sai ya miƙe ya fita abinsa.
Wani irin ajiyar zuciya na musamman ta sauke ganin baya nan, hannu ta É—an É—aura a saman kirjinta tana sauke numfashi a hankali hankali.
Ta ji daɗi da baya nan, a hankali ta sauƙo ƙasa, jikinta dik a mace ta nufo waje. Ga mamakinta sai taga babu kowa a gidan nasu.
To ina bappa da Mahreen? Ta jefawa kanta tambaya.
Ganin babu mai bata amsa ne yasa ta wuce ta nufi É—akin bappa. Wayam babu kowa, dawowa cikin É—akinsu ta yi, bargon nasu ta fara naÉ—ewa kafin ta hau gyaran É—akin.
Ta É—auko tsintsiya ta share fes, ta fito ta share waje, abinku da jiki ya saba da aiki, ta gyara É—akin bappa dana Nenne tsab, sannan ta fito ta gyara É—akinsu wanda ya zama mallakin Mahreen ita kaÉ—ai a yanzu.
Sai da ta gama da sharan gidan tsab sannan ta shiga kitchen, wuta ta hura ta É—aura ruwa a katon tukunya, ta haÉ—a kwanikan wanke wanke ta kaisu wajen wankewa.
A hanzarce take yin aikin nata, da yake ta saba sai yazamana cikin ƙanƙanin lokaci ta gama wanke wanke, ta share wajen ta gyara bayan ta kwashi kwanikan ta kai cikin kitchen.
Sannan ta zo ta ɗebi ruwan zafin dai'dai wanda zai isheta wanka, sauran kuma ta yi talgen garin masara zata tuƙa masu tuwo.
Surka ruwan ta yi tare da ɗauka ta wuce banɗaki dan ta yi wanka. Kafin ta fito talgenta ya nuna, dan haka sai ta zura hijabinta kawai ba tare da ta sanya kaya ba ta zo ta tuƙa tuwon.
Bayan ta tuƙa ta ɗan sanya mashi ruwa kaɗan ta bar shi ya ɗan silala na ƴan mintuna, sannan ta fito ta shiga ɗakinsu domin ta shirya. Ɗaya daga cikin sabbin dogayen rigunar da bappa ya saya masu ta sanya jan, ta ɗan yi kwalliyarta sama sama sannan ta fito ta shiga ɗakin bappa, ta yi kyau abinta, sai dai a jikinta tana jin zazzaɓi da ciwon kai, ba komai bane ya ja mata hakan kuma face wannan ruwan saman da ya yi masu dukan tsiya.
Naman zabo da man shanu ta É—auko a É—akin bappa ta wuce kitchen da shi. Tukunyar miya ta É—auko ta fara haÉ—a kayan miya a ciki, sannan ta sauke tuwon ta É—aura miyar.
Ta sake tuƙa tuwon ta kawo kwanika ta kwashewa kowa nasa, ta ɗebo daddawa ta daka ta zuba a miya, sannan ta saka maggi. Ta miƙe ta ɗauki tuwon kowa ta fara kai mashi ɗaki kafin miya ya nuna ta raba ta kaiwa kowa.
Ko da ta zo É—aukan na Jaish sai ta rasa a wani É—aki zata kai mashi, wani zuciya ya ce ta kai mashi É—akinsu wani kuma ya ce mata ta kai É—akin bappa. Daga karshe dai ta ce bari ta kai mashi É—akin nasu tun da jiya a nan ya kwana, kila ya dawo É—akin kenan.
Can ta kai mashi ta dawo ta zauna a kusa da murhun tana aikin hura wuta har tsawon awa É—aya miyan na tafasa, ruwa ya kare ta kara wani, sannan ta kaÉ—a garin kuka ta sauke, ta kwaso kwanikan miya ta fara zubawa kowa nasa, naman zabo da miyar kuka sai a girkin Mahnoor manya, ba'a iya miyar kuka kawai ba, ita idan bappa ya yanka nama a koma wani irin girki idan zata yi banka shi ciki take yi abinta, ba dai nama nama bane? Ai shikenan kuma.
ÆŠaki ta kaiwa kowa miyarsa kusa da abincinsa, sannan ta zo ta É—auki wani karon kula da ta kwashe ragowar abincin a ciki ta fito da shi waje, ta zuba miya a kular miyan, daga kasar Niger bappa ya sawo masu wannan kula, suna ji da shi sosai.
Ta É—auki kwanikan Æ´an madaidita guda uku ta haÉ—a, ta haÉ—o da maran kwasan tuwon dik ta ajiye a sakar gidan, alwala ta je ta É—auro dan azahar ta yi.
Sai da ta gabatar da sallarta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, sannan ta fito ta ɗauki wannan kular abinci da kwanikan da ta ajiye ta nufi waje, da nufin zata kaiwa su bappa abinci a gonarsa. Su dai kauye sun huta, babu ruwansu da garƙame gida da kwaɗo or key, haka zasu yi ficewarsu su bar ko'ina a wangale abinsu.
Dab zata fita waje ita kuma Jumma tana shigowa, saura kaÉ—an su yi karo Jumma ta ja birki.
"Kai amarya da fita waje? Ina zaki je to?". Jumma ta jefa mata tambaya cike da mamaki tana taɓe baki.
"Su bappa zan kaiwa abinci". Ta bata amsa a sanyaye.