← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 211

Sashe 72

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ÆŠan zuba mashi idanu sosai ya yi yana kallonsa yadda yake kwance ya datse idanu gam, shi kansa bappan a yanzu ya fahimci dalilan da yasa dole a kirasa da aljani, wani irin shape mai bala'in kyau face É—insa take da shi, hancinsa ta zauna ta kuma tsaru dai'dai da face É—insa, ga gurbin idanunsa da girma, duk da idanun suke a rufe zaka iya gane cewa manya manya ne sosai, É—an bakin nan nasa ba'a magana sai dai shiru, dole mutane su kirashi da aljani, shi ma yanzu ya É—an ji wani irin yanayi a tattare da shi daya kurawa face É—insa idanu, da duk bai lura da hakan ba.
Amma sai ya yi shiru bai ce komai dan gane da kyansa ba, ya dai matso kusa da kunnensa a ina ya fara yi mashi magana da fullanci a kan cewa ya dubi girman Allah kada ya wahalar da su ya sanar da su idan yana iya yin magana ko kuma idan yana jinsu.

Sarai ya ji sun yi magana amma bai san me suka ce ba, dan haka sai bai motsa daga in da yake ba, shiru bappa ya yi yana tunani, da yake tattijon kirki ne ga tunani mai nisa, sai ya yi tunanin to taya ma za'ayi Jaish ya ji fulatanci tun da shi ba a ruga yake ba, ƴan cikin rugarma gudunsa suke yi hakan ya nuna bashi da wata alaƙa da fulani, duk yadda aka yi shi ɗin ɗaya daga cikin biyu nan ne, wato ko bature ko balarabe, hakan yasa bappan da ya tuna hakan sai ya sake matsowa kusa da kunnensa cikin dattaku ya ce mashi. "Kanajin larabci?". Cikin harshen larabcin ya yi mashi magana.

A hankali ya É—an motsa idanunsa kafin ya warosu a hankali izuwa kan face É—in bappan! Sake mayar da su ya yi ya datsesu ba tare da ya ce ko uppan ba. Bappan ya lura da cewa tabbas yana jin larabci, dan tun da suka yi ta yi mashi magana bai motsa ba sai da suka yi mashi larabci, hakan na nufin yana ji sai dai kamar ba zai iya buÉ—e baki ya yi magana ba.

Sake ce mashi bappan ya yi. "Dan girman Allah idan har kana jin larabcin ka nuna mana alamar hakan ko ka amsa mana, dan Allah kada ka wahalar da mu ka ji?".

Shiru ya yi nan ma bai motsa ba, sai dai tsab ya ji me bappan ya ce. Ya É—auki a kallah tsawon 2mins har bappa ya cire ran zai tanka masu, yama cire rai a kan yana iya magana, sai kuma ya ga ya É—an buÉ—e idanu kaÉ—an tare da gyaÉ—a mashi kai alamar e yana jin larabcin, amma bai buÉ—i baki ya yi magana.
Wani irin daÉ—i na musamman bappan ya fara ji na ganin cewa an samo yaren da bakon nasa yake ji, abin ya yi mashi daÉ—i sosai, bai damu da rashin amsa mashi da bakinsa da bai yi ba, saboda dama yana son ya san cewa bakon nasa yana jinsu shi ne burinsa, dan ko baya magana in dai yana jinsu to Alhdulillah zai iya yi mashi bayani kuma su fahimci juna, dan shi yana da baiwar iya yin magana da kurame, ya iya maganarsu da Æ´atsun hannunsa, dan haka bashi da damuwa a kan wannan!!.

Gyara zama da kyau bappan ya yi a in da ya shiga yi mashi bayanin halin da yake ciki da abin da ya faru da shi na tsintarsa a cikin ruwa da suka yi, ya yi mashi hakan ne kuma dan ya samu Jaish É—in ya saki jiki da su ya san su ba cutar da shi zasu yi ba, dan ya fahimci sarai Jaish É—in yana gudunsu, bai kawowa ransa cewa saboda kyamarsu yake ji yasa yake gudunsu ba, ya É—auka saboda yana tsoron kada su cutar da shi ne yasa yake guduwa! Basu san dalilinsa daban ba, ai duk yaran King Zuhair babu matsoraci a cikinsu bare ace yana jin tsoronsu kada su cutar da shi ne!.

Duk abin da bappan ya faɗa yana jinsa sarai, ya ji dukkanin bayanansa, sai dai sam bai motsa daga in da yake ba, sai ka yi zaton bai ji me aka ce ba. Mahreen dai ta ji bappanta yana wani yare daban da bata taɓa ji ba, sai ta zaro idanu tana kallonsa. Bayan ya gama yi wa Jaish bayani ne ta ce. "Bappana dama kaima ka iya yaren aljanu ne?".

Kai kawai ya gyaɗa mata alamar e. "To bappa dan Allah ka koya mun, kaga dai shi ɗin aljanina ne, zan rinƙa yin magana da shi".
Shiru ya É—an yi mata kafin ya ce. "Ba shi ne idan nace ki nutsu ki karanta NAHHU a islamiya zaki iya larabci sosai sai ki ce mun yana da wahala Nahhu nawa hore ba? (Nahhu ciwon kai take cewa) To ai a cikin Nahhu nima na koyi yarensu".
Da sauri ta ƙara zaro idanu waje. "Bappa kenan aljanu yarensu shi ne larabci?".

Girgiza kai ya yi. "Larabci yaren kowa ne, aljanun gaske ma akwai masu jinsa kuma suna magana da shi, yaren annabinmu ne, da shi za'ayi magana a lahira". Shiru ta yi kamar mai nazari a kan maganganun bappan nata, can kuma ta ce. "Bappa daga yau zan fara koyan yaren, kuma zan fara karatun Nahhu har da muɗalaa da malumat, duk zan rinƙa karatunsu, kaima ka rinƙa ƙara mun da naka karatun a gida yadda zan iya yaren sosai".
Jinjina mata kai ya yi alamar to shikenan babu damuwa. Ita dai Mahnoor tana jin larabci dai'dai gwargwado, dan tana mayar da hankalinta sosai a kan karatun islamiyar, bata wasa da shi haka zalika bata fashin zuwa sai idan bappan nasu ya yi tafiya, in baya nan bala'in Nenne yake hanata zuwa, sai ta yi ta sanyata aiki har lokaci ya ƙure bata samun zuwa, amma idan bappansu yana nan lafiya lou take zuwa, sai dai fa bappan idan ya tafi yana kai irin wata biyar haka bai dawo ba, idan kuma ya dawo baya wuce yin wata uku zuwa huɗu ya sake tafiya, bappa yana jin yaruka da ɗan dama, ciki har da yarabanci, dan yana zuwa har kudu a wajen yawonsa, yana jin broken English sosai, haka yaren ibo sosai, yana jin Hausa sosai, yana da baiwa ta iya yarika daban daban, kun san mutun mai yawo irin haka ba yaren da ba zai iya ba, sannan kun san akwai fulani irin bappa sosai masu yawan fita yawata ƙasashe da dabbobinsu, wani lokaci ma idan suka bar gida sai sufi shekaru 2 basu dawo ba, sai ka manta da su ma rana tsaka sai kaga kiwo ya juyo da su ta wajenku kwatsam sai ka gansu, kamar wasu aljanu ta bakin Mahreen ɗin. Sai dai shi bappa baya jimawa sosai, idan ya yi nisa ne wata biyar, ko dan saboda Mahnoor yana dawowa gida!.

Kuma sanadiyar wannan kiwon da yake tafiya wurare daban daban Allah ya albarkace shi da samun shanu dayawa gasu suna ƙoshe ɓul ɓul sosai gwanin ban sha'awa.

In short wannan labarin da bappa ya bawa Jaish ne yasa shi ya ɗan yi sanyi ya kuma daure ya dai'na nuna masu cewa yana kyamarsu, dan kuwa jinin King wlh basu manta alkhari ko mai ƙanƙantar idan aka yi masu, haka zalika komai ƙanƙantar sharri idan ka yi masu basa mantuwa, kar suke ba wata kwana kwana, yanzu yasan bappa ya taimakesa sosai, dan haka sai shi ma ya kudurta a ransa zai yi ƙoƙarin dai'na nuna masu kyama ya kaunacesu.

In short sai da ya shafi wata biyu dai'dai a tare da su kafin ya fara sakin jiki da su, a wata biyun da suka shuɗen sam baya yarda ya yi kusa da su, dan kada ya yi amai a gabansu su ji babu daɗi, baya son ya ƙuntata masu hakan yasa yake daurewa yana dannewa ya kawar da kai, haka zalika bai taɓa yin magana ba a tsawon wata biyun nan, sai dai bappa ya yi mashi magana kuma yana jinsu, ko meyasa baya amsa masu?.

Mahreen ta zage sai koyan larabci take yi dan ta rinƙa hira da shi, bata san shi kam ba abin da ya tsana a rayuwarsa kamar surutu ba, ita kuma Mahnoor har yau har gobe ita da Nenne suna tsoronsa, sai dai Nenne ta fi jin tsoronsa sosai, Mahnoor tsoron ya ragu, ba komai kuma yasa ta rage tsoronsa ba face muguntar Nenne, Nennen tana yawan aikanta cikin ɗakin na bappa dan tsabar mugunta, tana jin tsoronsa shi ne take aikata wai dan kawai taga Mahnoor ɗin tana zubar da kwallah, da yake Allah ba azzalumin bawansa bane sai yasa Mahnoor ɗin ta fara sabawa da shi, ta rage jin tsoronsa, yanzu ta san ba cutar da su zai yi ba, dan a koda yaushe idan ta shigo ɗakin bappan ma har ta ɗauki abin da zata ɗauka ta fito yana kwance ko kallon in da take bayani, yana dai jin motsin shigowarta a koda yaushe, baya ɗagowa ne ya kalli wace? Kun dai san halinsa dama, akwai miskilanci da shege izza. Amma fa har yanzu a matsayin aljani yake a idanunta, ta ƙasa yarda cewa mutun ne!!.

Har yau har gobe wannan kunyan na Jaish tana tare da shi, wlh baya taɓa yarda ya haɗa idanu da bappa sai idan by mistake, amma kunyar haɗa idanu da bappan yake yi, tsawon wata biyu suna kwana a ɗaki ɗaya amma baya yarda su haɗa idanu, kunya gareshi sosai, halittarsa ce a haka. Sarai bappa ya lura da cewa yana da kunya sosai, hakan bai yi mashi daɗi sosai ba, saboda yaso ya saki jiki da shi su saba sosai, amma ina kunya ta hana shi, ga rashin yin magana da yake fama da shi, lokacin da ya samu lafiya sosai tsakaninsa da bappan ya bashi hannu kawai su gaisa, shikenan ko hira bappa yake yi mashi baya cewa ko uppan ko kuma ya nuna alamar ya ji me bappan ya ce.
Chapter 72 · 0% Book details