← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 211

Sashe 13

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahreen da Faisal kamar wuta da audiga haka suke, basu shiri kuma basu haɗa hanya, kullum bata da aiki sai zaginsa, ta ce da Mahnoor kada ta yarda ta aure shi, in dai ta aure shi to wlh ba zata je gidanta ba, haka dai suke ta fama, ita Mahnoor da bata san me soyayyar ko daɗinta ba jinsu kawai take yi, ita ina ma ruwanta da wani soyayya, Faisal ɗin ne ma ya koya mata cewa tana sonshi shiyasa take faɗa mashi kalmar, amma bata san me soyayya ko me ake ji idan ana yi ba, bare wannan uwar rawan kan, yo ita idan ba faɗa da kukan shagwaɓa da kuma cin abinci ba me ta sani? Ai ba ruwanta da zancen banza, ta dai san ance za'ayi masu aure, ita kanta Mahnoor da take matsayin babba ma bata san me ake nufi da auren ba bare kuma uwar rawan kai, su dai za'ayi masu aure kawai, kila sai anyi zasu san me yake nufi ko me amfaninsa.

Sai bayan la'asar Bappa ya dawo wajen kiwon hannunsa riƙe da kwanon sha mai rufe da paipai. A saman ɗan'kwalinta ya sameta zaune ƙarƙashin wata bishiyar ɓaure, da alama bata jima da idar da sallah ba, ta buga uban tagumi, idanunta sun ɗan ciko da kwallah, da alama tunanin wani abin take yi wanda ya sanya ta kusan kuka.

Sallamar da Bappan ya yi mata ne yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta afka, da sauri ta goge idanunta tare da cewa. "Bappa ka dawo?".

Zama ya yi a gefenta. "Na dawo Mahnoor, kiyi hakuri ban kawo maki abinci da wuri ba, Nennenku ce ta yi tafiyarta, taki dawowa ta yi girki, ni da kai'na na yi girkin sai yanzu na kammala, ga shi kici sai mu kaÉ—a dabbobin mu koma gida ko?".

Kallonsa ta ɗan yi tare da yin ƙasa da kai. "Bappa meyasa zamu koma gida da wuri yau? Ai naga kamar karfe 6 bata yi ba, ban jima da yin sallar la'asar bafa".

Jinjina mata kai ya yi kafin ya ce. "E haka ne lokacin komarmu bai yi ba, amma zamu koma ne saboda dalilai biyu, na farko Nennenku bata nan, kuma naje gidan Arɗo ɗaukarta ta ce ba zata dawo ba, kinga ba wanda zai yi girkin dare sai ke, dan haka zamu koma ne ki dafa mana abin da zamu ci, sai kuma batun mutumin nan da muka tsinto, ina bincike a kan lafiyarsa, har yanzu ban iya gano yana da rai ko ya mutu ba, shiyasa zamu koma gida yau da wuri, dan haka ci abinci da wuri mu tafi". Ya kai karshen maganar tare da buɗe mata paipain da ya rufe kwanon shan da shi. Abinci ne mai rai da lafiya, tuwo ce da miyar ɗanyar kuɓewa ta ji man shanu, ga nama zuƙu zuƙu.

Hannu tasa ta fara ci, dan hannunta a wanke tas, ba jimawa ta je ta yo alwala a bakin kogi. "Bappa ina Mahreen?". Ta yi maganar tana cigaba da cin abincinta.

"Mahreen tana gida tana zuba barci". Ya bata amsa tare da miƙewa ya nufi wajen dabbobin nasu in da suke ɗan nesa da su, sai gabsarar ciyawa suke yi.

Haɗa kansu ya yi ya kaɗasu tare da fara zuba masu surutu a kan su yi hanyar walde wato in da suke kwana a bayan gidansu kenan, a bayan gidansu walden dabbobin yake, akwai tirke dayawa a wajen, wasu shanayen suna ɗauresu saboda ƴaƴansu su samu damar shan nono kada iyayen su ɓace cikin garke ƴaƴan su sha wahalar nemansu, shiyasa suke ɗaure masu ƴaƴan, wasu kuma saboda mafaɗata ne yasa suke ɗauresu a tirken, saura kuma sai su barsu a sake haka basa ɗauresu, kuma babu in da suke zuwa suna tsaye a wajen.

Ita kuma cinye abincin tas ta yi tare da miƙewa ta nufi bakin kogi da kwanon, wankosa tas ta yi, sannan ta bi bayan Bappan, dama bai yi mata nisa ba, ba jimawa ya wuceta duke tana wanke kwanon.

Kai tsaye walde Bappa ya nufa da shanayen, ita kuma ta nufi cikin gida. Tana shigowa ta nufi kitchen, bayan ta ajiye kwanon a ma'ajiyinsa ta É—auko wani É—an madaidaicin bokiti, ruwa ta É—ebo a cikin É—aya daga cikin randunar dake cikin kitchen É—in.

Kai tsaye bayi ta nufa, a gurguje ta yi wanka ta fito, da sauri ta shige cikin É—akin bukkarsu, sai sauri take yi kamar zata kifa, duk dan ta É—aura zani a kirji, kuma ta sanya hijabi, amma da yake hijabin zuwa gwiwarta kuma shima zanin da ta É—aura a kirji bai kai gwigwa ba, so singalalin kafafunta a waje shiyasa take zuba sauri dan kada wani ya shigo ya kalleta.

Zama ta yi a bakin Æ´ar karifarsu, man shafawa ta É—auko, mai ne irin wannan vaseline É—in na 150 Æ´an kananan mazubin nan, shi ta É—auko ta murje jikinta da shi, da yake sun wadatu da nonon shanu skin É—insu yana da kyan gani sosai, kun san madarar saniya tana gyara jiki, so jikinta ya yi luwai luwai.

Bayan ta gama shafa man sai ta janyo wani jaka da aka ɗinka da buhu, kayan kwalliya ta fitar a ciki, powder ce da ƴar janbaki za irin mai green ɗin bayan nan, shi ta ɗauko ta hau murje fuskarta tana gyarawa. Lips ɗinta da suke pink sosai ma kamar an sanya janbaki pink sai da ta sa mashi red janbakin, sam jan kalar bai yi mata kyau ba, kalar lips ɗin tata ya fi yi maya kyau, amma da yake suna kaunar kwalliya ita da Mahreen sai sun sanya, ita iya power da janbaki take sakawa, bata sanya kwalli ko da a iya ido ne kawai, Bappa ne ya hanata sanya kwallin, a cewarsa idan tana sanya kwalli a ido bakin mutane zai yi mata yawa over, yanzu ma jama'a suna yawan magana a kan kyan idanuta, to idan ta sanya kwalli ƙara kyau sosai idanun suke yi, gasu farare tas, hakan ya ja duk wanda ya ganta sai ya yi maganar idanun nata da kyanta, shi ne yasa Bappa ya dakatar da sanya kwalli, kuma ya hanata yin kwalliya idan zata fita, shi yake sayo masu kayan kwalliyar idan ya je cikin gari, amma ya hanata yi idan zata fita, shiyasa kuka ga ita bata yi kwalliya ba time da zasu je kiwo, tana kuma kaunar kwalliyar sosai, ita ma Mahreen duk randa Mahnoor ta yi mata kwalliyar kirki ta yi kyau sai jama'a sun yi ta magana, shiyasa Bappan ya hana Mahnoor ta yi mata kwalliya, ya ce a barta ta rinƙa yi da kanta, dan idan ya hanata yin kwalliyar nan ba ƙaramin rigima zai yi da ita ba, amma idan ya barta tana yi da kanta ta zama kamar mahaukaciya ai kunga ba wanda zai yaba, ba wanda zai kallah ya ji ta burgesa, sai dai ma a mata kallon mahaukaciya, duk ta ɓata fuska, har a kumatu take sanya janbaki, kun ga kuwa ai sai dai ayi mata dariya, ta wannan hanyar ita kuma Bappan ya biyo mata suka zauna lafiya.

Bayan ta gama kwalliyarta ta ɗauko wata koɗaɗɗiyar goduwar riga ta atamfa daga cikin kwallar da suke saka kayansu ta sanya a jikinta, sannan ta ɗaura ɗankwalin rigar. Kasancewar ita yanzu ta ɗan fara girma, akwai tula tula a kirjinta sai hakan yasa bata taɓa yarda ta yi yawo babu hijabi koda kuwa a tsakar gida ne, kullum da hijabi, har barci bata cirewa, tana manne da shi, dan tana jin kunyar a ga tula tulan a kirjinta, sai wahalar da kanta take yi wajen nokesu, idan tana tafiya ta yi ta faman sanya hannu a hijabi wai dan kada ma alamarsu ya fito.

Ita kuwa Mahreen da ɗan'kwalin ma sai randa aka ga daman sakawa ake sawa, idan kun ganta da ɗan'kwalin to fa ranar da ta sanya kayan sallarta ta ci kwalliya mai kyau, to a ranar ne za'a ganta da ɗan'kwali an sheƙa ɗauri kamar bukkar mahaukaciya, sai a ƙwama wani kwandaram ɗin takalma, Allah sarki suna son yin gayu irin na ƴan birni da suke gani idan suka shiga birnin da Bappansu, amma basu da kayan ƴan birni kuma bama su iya irin kwalliyar ba, sai dai su yi iya kar yinsu.

Tana gama shiri ta É—auki hijabi ta sanya sannan ta fito waje ta É—auko tsintsiya, É—akinsu ta fara sharewa kafin ta fito ta share na Nennensu ta gyara, sannan ta nufi na Bappa.

Tana shiga ta ɗan ja birki ganin Jaish da basu san wanenen shi ba kwance a cikin ɗakin na Bappan, ita kwata kwata ta manta da cewa Mahreen ta gaya mata Bappan ya kai shi ɗakinsa ya kwantar, da ta san yana nan ba zata shigo ba, dan tsoronsa take ji, ga shi Bappa da ƙoƙari bawan Allahn nan ya raba shi da suit ɗin jikinsa, ya rage daga shi sai singlet ɗinsa fara kal, daga ta ƙasa kuma wani wandon yadin shadda green color Bappan ya sanya mashi, wandon tana da tsawo, a dai'dai saitin tsakiyar faffaɗar kirjinsa Bappan ya manna mashi wasu ganyayyaki, da alama magunguna ne na gargajiya da zasu taimakawa bugawar zuciyarsa, gaban goshinsa ma hakan ce, Bappan ya janye gashin kan nasa baya ya bi gaban goshin nasa duk ya mammanna mashi ganyen.
Chapter 13 · 0% Book details