Sashe 42
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ai tsabar haushi bata san lokacin da ta cire hannu zata zabga mashi mari ba, duk ta saki abubuwan hannunta har flask É—in da Sadiq ya saya mata na sanya ruwan zafi a asirbiti ya fashe saboda sakinsa da ta yi, ranta ya sosu da jin maganarsa, bata san cewa yana da gaskiya shi ne nan ya kai mamanta har wajen boka ba, sai dai ya yi kuskure tun da ba tare da su ya kai maman nasu ba, ta kan iya yiwuwa su bama su san ta je ba, ya zo ya haÉ—esu ya yi masu kuÉ—in goro.
Bata kai ga sauke hannunta a saman face ɗinsa ba ta dakata, ba komai kuma yasa ta dakata ba face ta gansa babban mutun ne har da furfura a gemunsa, da yara matasane babu abin da zai hana ta maresu sai dai duk abin da zai faru ya faru, amma a irin tarbiyar da iyayenta suka bata ba zata iya marin wanda ya haifeta ba, dan haka sai ta juya cikin fushi zata wuce cikin gida, ranta a matuƙar ɓace ta fasa marin nasa.
Da sauri ya sauƙa daga kan mashin ɗin ya sha gabanta yana faɗin. "Aww dama marina kenan zaki yi dan nace ku makiya Allah ne? Karya na faɗana ne? Ni malama ki bani kuɗina! Babu in da zaki motsa ba tare da kin biyani hakkikana ba! Da kuma kin mareni da daga yau baki sake marin wani ba!!". Cikin faɗa ya yi maganar.
Datse idanunta gam ta yi kafin ta ce. "Ka matsa mun a hanya malam, ina ganin mutuncinka, idan ka cigaba da yin abin da kake yi wlh zan yi maka rashin mutuncin da har ka mutu ba zaka mance da shi ba, kuÉ—in naka kuma na cinye ba zan biya ba kayi duk abin da zaka yi!!". Da kyar ta yi maganar kamar wadda aka sanya dole.
Ai kuwa shi ma ransa a ɓace wai ta yi mashi rashin kunya, cikin jin haushi ya cire hannu zai mareta. Kaucewa marin nasa ta yi tare da ja da baya tana wani layi kamar zata faɗi, bata da kuzari ne a jikinta ko kaɗan.
Wasu matasa da suka zo wucewa ne suka ga abin da yake faruwa, nan fa suka tsaya suka tambayi me yake faruwa, mai mashin É—in ne ya amsa masu da cewa. "Wannan yarinya zata raina mun hankali, na É—aukota daga hospital zuwa gida ta bani kuÉ—ina wai ba zata bayarba bata da kuÉ—i, tasan bata da kuÉ—i ne ta hau abin hawana? Da nace ba in da zata je sai ta biyani shi ne ta tsaya tana zagina ni kuma zan É—auki mataki, ba zai yiwu ace yarinya kamar wannan wadda na haifa ace tana gaya mun magana ban zaneta ba!".
Ita dai shiru ta bishi da ido tana jin sharrin da yake yi mata, ita burinta ma kawai ta shiga cikin gida ta kwanta, dan jiri take gani yana É—ebarta.
Nan fa matasan suka ce zasu biya kuÉ—in nawa ne ya yi hakuri. Ana cikin hakan sai ga Khadija da hayaniyarsu ya isheta ta taso ta fito dan ta ga su wanenen? Dama tun da yamma take neman Zainab É—in, ga jikinta da yake yi mata ciwo na dukan Haidar da ta sha, bakin nata ma in da ya fasa mata har ya É—an kumbura.
Ganin hayaniyar da Zainab ake yi yasa ta yi saurin ƙarisawa wajen tana tambayar lafiya me yake faruwa?. Zainab da take begen ganinta ne ta buɗi baki da karfi ta furta sunanta Khadija. Nan take ta ji jikinta ya watsake, a ruɗe ta rungumeta tana faɗin.
"Ina kika je? Ina kika tafi kika barni? Meyasa kika tafi kuma? Kin san wahalar da na sha da baki nan? Babu mama babu baba, kema babu ke! Iya kawu Sadiq ne kawai ya rage mun a duniya! Dan Allah ina kika je?......" Da kyar ta iya kai karshen maganar saboda kuka da ya ci karfinta.
Ita ma Khadijan kuka take yi sosai ta ce. "Ba tafiya na yi ba, É—aukata aka yi aka rabani dake, nayi kewarki sosai, na yi kuka rashinki tun hawaye na zuba daga idanuna har suka daina zuba, ina kaunarki Æ´ar uwata, ina mama take?".
Daga mai mashin É—in har matasan dake gefe zuba masu idanu suka yi suna kallonsu, a yanzu fa gabaÉ—aya unguwar su Zainab É—in zagin gidansu ake yi ana tsine masu albarka wai su É—in annoba ne, daga dawuwarsu unguwa sai masifu kala kala yake faruwa, har da kisan kai aka yi a gidansu, maganganu dai kala kala marasa daÉ—in ji ake jefansu da shi.
Sai murna da ganin juna suke yi. "Me ya tsayar dake a waje? Daga ina ma kike haka tun É—azun ina nemanki? Ya na ganki duk a firgice and ina mama?". Dukka Khadija ce ta jero mata waÉ—an nan tambayoyin.
Fuska duk a jiƙe da hawaye ta amsa mata da. "Daga asibiti nake, mai mashin ɗin da ya dawo da ni ne ya tsayar da ni wai na bashi kuɗinsa kafin na shiga cikin gida, ni kuma bani da kuɗi, kawu Sadiq bai bar mun kuɗi ba". Ta kai karshen maganar hawayenta na ƙara tsananta gudu a saman face ɗinta.
"Meya kai ki asibiti? Amma dai bari mu shiga ciki sai ki gaya mun, yanzu jirani bari na É—aukowa mai mashin É—in kuÉ—insa". Tana kai karshen maganar ta raba jikinsu dana juna tare da sa kai da sauri ta wuce cikin gidan.
Matasan da suka ce zasu biya mata kuɗin ɗin jin cewa Khadija zata ɗauko kuɗin ne yasa suka hakura suka wuce abinsu, dama kawai dai dan sun ga macece yasa zasu biya mata ba wai suna da wani ishasshen kuɗi a jikinsu ba, kun san mu a arewacin Nigeria Allah ya horewa matasanmu zuciyar taimakon mata a duk lokacin da suka ga za'a ci zarafinsu, basu bari a ci zarafin mace koma ya take, in ma matar aure ko budurwa or bazawara, su dai koma wace iriyar macece zasu taimaka mata matuƙar suka ga za'a ci zarafinta musamman ma kanawa suna da wannan dabi'a, sai dai muce Allah ya ƙarawa zuciyarsu taimako da tausayi.
Mai mashin É—in kuwa yana tsaye yana bankawa Zainab da hankalinta baya a kansa harara, hankalinta na'a kan kofar gidansu tana jiran fitowar Æ´ar uwarta Khadija, ta yi kewarta sosai, badan bata son masifaba da ta bi Khadija É—in cikin gida, amma idan ta ce zata bita mai mashin É—in nan zai sake tsayar masu da tijara, so gara mata ta daure kawai ta jirata har zuwa ta fito.
Da sauri Khadija ɗin ta fito har kamar zata kifa ƙasa, Allah sarki duk dan kewar ƴar uwarta, hannunta na riƙe da dala ba naira ba, tana zuwa ta miƙawa mai mashin ɗin dollar dubu ɗaya sabuwa kal sai kyalli take yi.
Ai wannan mai mashin ɗin bai san lokacin da ya sauko ƙasa daga saman mashin ɗin nasa ba, zaro idanu waje ya yi yana kallon kuɗi ya kuma ɗago ya kalli Khadija da ta tsugunna ƙasa tana kwashe kayan da Zainab ta zubar, ita sam bata ma san yana kallonta ba, ita kuwa Zainab ta tsaya sai banka mashi harara take yi na yana kallon mata ƴar uwa, bata san shi al'ajabi da mamakin kuɗin da ya fito daga hannunsu ma yake yi ba, dala dubu ɗaya a yanzu wajen million ɗaya da dubu ɗari shidda kenan take, amma Khadija ta zo ta miƙa mashi ta kama harkar gabanta tamkar wadda ta bashi naira ɗari ko ɗari biyu, ko a jikinta, ko daga ina ta samo dala sabuwa kal haka?.
Kwashe kayan tsab ta yi tare da miƙewa tana faɗin. "Zainab mu shiga ciki dan Allah ki gaya mun ina mama kuma me kika je yi a hospital?".
Wucewa suka yi ba tare da Khadija ta sake bi ta kan mai mashin É—in ba, ko kallon in da yake ma ba ta sake yi ba ta ja hannun yar uwarta suka nufi ciki.
Shi kuwa mai mashin sai Allah Allah yake yi su shiga ciki basu tambayi canji ba ya samu ya gudu da kuÉ—in ya ci bulus a ganinsa, e mana a ganinsa ne ya ci bulus ya samu kuÉ—i a sama, da ni daku kuma duk mun san cin hakkin wani dai ba cin bulus bane, akwai ranar biya, dan Allah baya yafe hakkin wani a kan wani, dole sai mai shi ya yafe maka, laifi tsakaninka da Allah ne wannan idan ka tuba Ubangiji gafurur rahim zai yafe maka, amma tsakaninka da wani, dole sai ka nemo shi ya yafe maka tukun nan, in ba haka ba Allah ya bi mashi hakkinsa.
Ai kuwa suna shiga gida ya yi maza ya haye mashin É—insa, jikinsa har yana kerma wajen yin saurin kunna mashin É—in, da gudun gaske ya bugata ya bar unguwar, sai murna yake yi ya samu kuÉ—i har naira miliyan É—aya da É—auri.
Suna shiga cikin parlour suka isko Hauwa da maman Haidar suna zaune suna aikin da suka saba wato hira, maman Haidar ta ce a rufe Haidar na kwana biyu a cell sai ya nutsu a sako mata shi, ita kanta bata iyawa da haukarsa, ita da ta haife shi ma kenan, amma dan tsabar son zuciya da mugunta a haka take son a ƙaƙabawa Khadijah ƴar marainiyar Allah shi, kai wlh jama'a mu rage son kai da son zuciya, ba in da hakan zai kaimu face halaka, Allah mun tuba ka yafe mana zunubanmu, a yawaita tuba jama'a, dan babu wanda yasan a ina karshensa zata zo, yawaita tuba zai sa koda kana da zunubi mutuwa ta riskeka zunubin naka su ragu koma Allah ya yafe maka gabakiɗaya, dan haka mu yawaita tuba kafin mutuwarmu, Allah kasa mu dace.
"Ku zo nan munafukai! Ina kuka fito?". Cewar maman Haidar. Khadija ce ta amsa mata da. "Daga waje muke gwaggo". Zainab sai aikin binsu da wani matsiyacin kallo take yi, da yake akwai solar a gidan haske ya gauraye parlourn sai ya zamana suna ganin juna sosai, hakan yasa Hauwa taga irin kallon rainin wayon da Zee take binsu da shi.
"Ke rasa kunya ɓerar tanka uban waye kike harara? Ko akwai sa'an ki a cikin nan ne?". Cewar Hauwar.