Sashe 140
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru shiru bai amsa mata ba, sai dai kallonta da yake ta yi yana jin ƙwaƙwalwarsa tana wani irin juyawa tamkar agogo.
One step ta yi baya kafin ta ɗan ɗago da kallonta a kansa. Ai a fujaje ta sake yin ƙasa da kai ganin ita yake kallo sun kalli juna ido cikin ido. Shi dai ba komai yasa ya ƙasa dai'na kallonta ba face wannan tunani da yake ji na daban idan yana kallonta, abin yana bashi mamaki da yasa baya son kawar da kallonsa daga kanta.
Ita kuma sarkin tsoro, ganin yana ta kalleta yana kalle kayansa, e mana kayansa tun da dai aure ya ɗauru in ji ni princess Teema taku ta amana..........😂
Yana ta kalle kayansa yasa ta tsorata, nan take kirjinta ya fara dukan uku uku, a tunaninta wani abin zai yi mata, shege shaiÉ—an da kuma munafukar zuciya mai sake sake sai ta fara saka mata cewa ai dama jama'a sun ce maki shi maye ne, ba ga shi yanzu yana kalle maki jiki yana neman ta in da zai fara cinye maki tsokar jiki idan ya samu dama ba.
Ai kuwa wani irin ihu ta zunduma wanda bata san ta yi ba, kamar mai wani motsi a kai, kawai zuciya ya kai ta zai barota, wlh yarinyar nan ta zaci a cikin zuciyarta ta kurma wannan ihu, bata san a fili ta yo shi ba.
ÆŠan zaro idanu ya yi yana mamakin ihun nata, kamar wadda aka yi wa allura ko wadda aka kwalawa guduma a kai, ta wani kware baki ta zundumota, anya ma lafiya take kuwa?. Ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa.
Ita kuwa ihun da ta yi ya yi dai'dai da ta É—ago kai ta kallesa, ai kuwa hakan ya yi dai'dai da idanun da ya zaro dan mamakin abin da ta yi.
Habawa tana haÉ—a ido da shi taga ya zaro nasa me zata yi? Ai sai ta zunduma a guje ta yi wani irin juyawa da karfi ta nufi hanyar gida, kafa me na ci ban baka ba? Ai sai gida.
Bata ma san lokacin da takalmar kafafunta suka cire ba, ita dai gida kawai take burin ta shiga.
Sai dai bata kai ga isa gidan ba ta faɗi ƙasa tare da kurma ihu mai sautin gaske.
Yana dai tsaye yana kallon ikon god da wannan yarinya, yana gani ta watsa a guje bai yi wani motsi ba, sai da ya ga ta faɗi ƙasa ta kuma zunduma wani ihun ne ya ɗan lumshe idanunsa tare da jan dogon numfashi. Ni kuwa nace har yanzu dai wannan fadanci ta jinin sarautar tana nan bata rabu da shi ba.
A hankali ya fara takawa ya tinkari in da take, a gabanta ya tsugunna dan yaga me yasameta ta faÉ—i take yin wannan ihu kuma.
Jini ne yake zuba daga kafarta ta dama, da sauri ya kai hannu ya riƙo kafar tata, jini sosai yake zuba, sam bai iya gane me ya sameta a wajen ba, saboda jinin ya wanke wajen, shin yankace ko dai wani abin ne ya soketa har ya fasa fatar kafar haka? Jini sosai ya rufe wajen ciwo baka iya gani, ga jinin nata jajir da shi.
Dawo da kallonsa saman face ɗinta ya yi, ta datse idanu gam, ba abin da zaka gani face hawaye dake bin ƙuncinta kamar ruwa ya faso hanya. Da alama bata ma san yana kanta ba.
Ɗan miƙewa ya yi, ya duƙa ya ɗauketa cak suka nufi cikin gida. Bappa dai yana ta ƙoƙarin gyara wajen da zasu yi bukkar kusa da ɗakinsu Mahnoor ɗin ta gefe haka.
Gabaɗaya kunya ya ji tamkar ƙasa ta tsage ya shiga ciki na ganin bappa a tsakar gidan, sai ya ji dama bai ɗauketa ba, wato shi fa wlh kunyar a jininsa take, ba wai tsiya bace kamar yadda Jawad yake tsokanarsa da shi, ai kunga ko zai ji kunyar kowa ban da Yah Jawad, so shiyasa Jawad ɗin yake ganin kamar iyashege ne ba kunya ba dan shi baya nuna mashi yana jin kunyarsa.
Ko kallon in da bappan yake yaki ya yi, yadda kuka san ya gefar da ita a ƙasa haka yake ji, sam bai yi tunanin zai isko bappan a tsakar gidan ba, da Allah ba zai ɗaukota ba sai dai ya taimaka mata ta miƙe ta taka da kafafunta su dawo.
Shi fa wlh ko da Mahreen baya son jerawa mutanen gari su gansu bare kuma bappa, kunya hakan take bashi. Allah sarki yaron Mommarsa mai alkunya.........😂
Saman wata dutse da suke zama su goge kafa idan sun fito daga wanka ya zaunar da ita, sam ɗan tahaliƙin nan yaki yarda ya juyo in da bappa yake, yana ganin kamar idan ya juyo zasu haɗa idanu ne.
Shi kansa bappa abin ya yi matuƙar bashi kunya yadda ya ɗaukota ya keta wajen nan jama'a suna wucewa ya shigo da ita, amma da yake yana kaunarta sosai sai ya danne kunyar a ruɗe ya fara tambayarsu meyafaru kafarta ke jini?.
A dai'dai lokacin Mahreen ta fito daga cikin É—aki tana zabga uban hamma kamar zata ci babu, da alama da yunwa ta taso daga wannan barci.
Ganin abin dake faruwa yasa ta yi saurin ƙarisowa wajen tana tambayar hamman nata me ya faru?.
Bai kulasu ba ya yunƙura zai miƙe ya bar wajen, cikin jin raɗaɗin ciwo ta riƙo wuyarsa yadda ta saƙalosa lokacin da ya ɗauketa haɗe da faɗin zafi kafarta yake yi mata, su taimaka mata su cire mata zafin.
Shi kuwa kunyar bappa yasa zai bar wajen dama, baya son su haÉ—a ido, ba wai dan baya son taimaka mata ko bai ji tausayinta ba, aa, ko É—aya, hasali ma ya so ya wanke mata kafar, ya wanke jinin sai ya duba menene ya ji mata ciwo a wajen.
Bappa ya lura da kunyarsa yasa Jaish É—in yake son gudu ya bar wajen, bai san cewa shi kansa abin ya bashi kunya ba, in gaya maku Mahreen ce kawai bata ji komai ba, dan kun san ita kunya ya yi gabas ne ita kuma ta yi yamma, sam basu da haÉ—i.
Ganin yadda ta riƙe mashi wuya gam tana kuka haɗe da magiyar a cire mata zafin ne yasa ya koma ya tsugunna a gaban nata, a hankali ya kai hannunsa ya fara ƙoƙarin cire hannunta da ta sarkafe wuyarsa da shi.
Hakan yasa bappa ya ji ba zai iya ganinsu ba, sai kawai ya fice daga gidan ya basu waje, ya nufi gonarsa na su tomatoes dake kusa da gidan, dan ya je ha fara saro itacen da zai haÉ—a masu bukka da shi kafin su gama abin da suke yi.
Ganin bappan ya fice ya basu waje ne yasa sai ya fasa cire hannun nata daga wuyarsa, dama wai zai cire hannun nata ne dan ya samu ya bar wajen, yana son taimaka mata amma idan bappa na wajen ba zai yi ba, da tafiyarsa zai yi abinsa, amma tun da bappan baya nan sai ya kai hannu ya kamo kafar tata.
A gabansu Mahreen ta tsugunna, idanu jajir da su saboda barci, ga yunwa, sai daka hamma take yi, kamar zata yi kuka ta kai hannu ta saƙalo wuyarsa saman hannun Mahnoor dake wuyar tasa, lallausan kumatunsa ta shafa da ɗayar hannun nata, cikin fuskar tausayi ta ce. "Hamma meyasami Adda Mahnoor ɗita?".
Dawo da kallonsa saman face É—inta ya yi, hannunsa É—aya ya kai ya shafi face dinta kafin ya yi mata alama da ba komai, sannan ya yi mata alamar ta kawo mashi ruwa.
Ba shakka akwai shaƙuwa sosai a tsakanin shi da Mahreen, shaƙu kam mai karfi ma.
Da sauri ta miƙe ta nufi cikin kitchen, ruwa ta ɗebo a cikin butar karfe irin na mutanen da ɗin nan ta dawo da shi in da suke.
A gabansu ta tsugunna ta miƙa mashi. Karɓa ya yi, hannunsa yasa a saman wajen ciwon ya fara zuba ruwan yana wanke mata jinin.
Sosai ta kara tsananta kukan nata, saboda ruwan sanyi da ya taɓa ciwon, sai ya kara azabar zafi.
Yana wankewa wata jinin tana ɓulɓula, sai dai kuma da ya wanke ya gano babbar ciwo ta ji sosai, wani kwalba ne ya fasa mata fatar har nama, ya yanketa sosai da sosai.
A hankali wani irin tsananin tausayinta ya ratsa zuciyarsa sosai, tsumma mai tsabta ya buƙaci Mahreen da ta kawo mashi.
ÆŠaure mata kafar ya yi ko zai samu jinin ya É—an tsagaita su saka magani, dan shi ma a yanzu ya san magunguna da dama na gargajiya.
Miƙewa ya yi ya ɗauketa izuwa ɗakin bappa, da sauri Mahreen ta rufa masu baya. Saman gado ya zaunar da ita, sai a lokacin ta sakar mashi wuyarsa, dan ta ɗan ji sassaucin zogin.
Juyawa ya yi zai fita sai kuma kamar wanda aka cewa ya juyo, yana jiyowa suka haÉ—a idanun, dan jin zai fice yasa ta yi saurin waro idanu dan tagansa kafin ya fita.
Yana haÉ—a idanu da ita tunanin yadda ta tashi hankalinta a É—azun da kaska ta hau hannunsa ya faÉ—o mashi, ya ji daÉ—i sosai yadda ta ruÉ—e ta kuma taimaka mashi, ta nuna tsantsar tausayinta a gare shi, tuna hakan yasa ya juyo ya dawo, ya fasa ficewa.
Da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa tana mamakin me ya dawo da shi kuma?.
Sai surutu Mahreen take zuba masu babu wanda yake iya jin me take faÉ—a, dan kuwa duk sun afka duniyar tunani.
A kusa da ita ya zauna yana kai hannu ya riƙo kafar tata, mamaki ne ya kusa sanyata suma, bata taɓa zaton hakan ba. Ita dai Mahreen sai tambayar ina Nenne take take yi, ba wanda ya bata amsa, ni kuwa princess Teema na ce Nenne ai ta saki kanta da kanta, bappa dai ba ruwan, ta haɗa kaya sai gidan Arɗo abinta, dan dai bappa namu na gargajiya kam bai sake ta ba, kuma bai ce ta tafi gidan Arɗo ba, rashin albarka ne irin tata da rashin ilimin sanin darajar miji, kai ita bama tasan me ake nufi da miji ba, kan fanko ne.