← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 211

Sashe 41

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah sarki ko daga ina ta dawo? Suwaye suka ɗauketa? Daga dawowa kuma ta hau karɓar dukan mahaukaci Haidar, baiwar Allah daga ganin face ɗinta cike take tab da damuwa, idanunta sun sha kuka har sun gaji, ga dukkan alamu koma daga ina ta fito bata yi zaman daɗi a wajen ba, sai dai kuma jikinta ya nuna ta samu kula sosai duba da yadda ta yi ƙiba ta kuma yi haske, da alama wlh zuciyar Khadija a yanzu ya bushe bata jin tausayin komai.

Ganin da gaske zai iya hallaka Æ´ar mutane yasa mamar tasa ta fara ihun neman taimako, a guje ta yi waje dan ta nemo mai agaza mata. Haniyarsu dake kwance rai a hannun Allah ne ta ji Haidar zai kashe mata jika Khadija da duka, nan take jikinta ya tsananta ciwo, tana kaunar jikokin nata a yanzu kam, dan ta yi nadama, su Khadijah É—in zata gani ta tuna babansu, kuma ace Haidar zai kashesu ai ba zaman lafiya.

Nan take jininta ya sake haurawa sosai, jiki ya tsananta ciwo, suna can su kuma suna hauka babu wanda ma yasan ciwon nata ya tashi, sai numfashi sama sama take yi tamkar rai zai yi halinsa.

Sadiq dake asibiti yana ƙoƙarin haɗawa Zainab tea ta sha kafin a kawo masu takardar sallama ne ya ji wayarsa tana ringing, yau dama za'a sallami Zainab ɗin, dan ta ji sauki sosai, sai dai rashin maganar ne har yanzu dai shiru ba wani cigaba, komai kace mata sai dai ta ɗaga maka kai sama kawai alamar ta ji.

Haɗa mata tea ɗin ya yi ya miƙa mata tare da ciro wayar tasa daga aljihunsa, my friend shi ne sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar. Picking ya yi ƙoƙarin yi call ɗin ta katse, dama call ɗin farko ta katse saboda yana haɗa tea, hakan yasa bai samu damar ɗauka ba.

Cire password na wayar ya yi tare da fara ƙoƙarin kiran abokin nasa sai ga kiran ya sake shigowa. Picking na call ɗin ya yi tare da kara wayar a kunnensa.

Tun kafin ya yi magana ya tsinkayo muryar abokin nasa cikin tsananin tashin hankali yana faÉ—in. "Sadiq duk in da kake ka yi maza kazo, kome kake yi ka yi maza ka bari mama ta faÉ—i yanzu zamu kaita asibiti".

A ruÉ—e ya ce. "Meyasameta ta faÉ—i?".

"Nima dai ban sani ba, na zo gaisheta ne na sameta tana waya, ina ga a wayar ne aka gaya mata wani magana mai É—aga hankali da har yasa ta faÉ—i, ka yi sauri kazo".

Bawan Allah tsabar ruÉ—ewa da shiga tashin hankali bai san lokacin da ya fice daga É—akin ba, sai ya mashi kamar a Kaduna yake ba Kano ba, ko katse kiran bai iya samun dama ya yi ba, shima abokin nasa bai katse kiran ba ya tura wayar a aljihu suka É—auki maman zuwa asibiti, shima Sadiq É—in haka ya tura wayar a aljihunsa ya fice daga hospital É—in, tashin hankali yasa ya mance da Zainab a asibitin ya tafi, wlh Sadiq yana da karfin imani da tawakkali, da wani ne irin wannan tashin hankali daga wannan jarabawa sai wannan wlh da wani ne da ya jima da haÉ—iyar zuciya ya mutu, wannan bala'i sai kace ba lafiya ba, ko da yake Ubangiji ya fi jarabtar wanda yake kauna, Allah dai ya baku ikon cin wannan jarabawa, amma gaskiya wannan family na Baban Zainab kuna ganin rayuwa, Allah dai ya saka maku da mafificin alkhrinsa bayan kunyi hakuri da juriya kun cinye jarabarwarku.

Haka Sadiq ya tafi ya barta kwance a asibitin, Dr ya kawo mata takardan sallama, zaman jiran kawun nata ta yi har dare bai dawo ba, hakan yasa ta fara tunanin ko dai ta koma gida ne? Wani zuciya kuma ya ce mata idan ta koma gida ya dawo bai sameta bafa? Tun da rana wannan tunani na idan ta tafi ya dawo bai sameta bafa É—in nan shiyasa ta zauna a asibitin har dare ta kasa tsayar da hukuncin da ya dace da ita.

Sai da ta ji ana sallar isha ne ta ce bari dai ta lallaɓa ta tafi gida in yaso idan ya zo gida sai ta bashi hakuri. Wannan shawara da ta yanke shi ta bi a in da ta tashi ta haɗa komai nasu, da kyar take tafiya har ta fita daga asibitin, bata da ko naira biyar haka ta tari abin hawa ta hau da nufin ya kaita gida.

A ɓangaren Khadija da Haidar kuwa, kafin mamarsa ta samo maza su kama mata shi har ya jiwa Khadija rauni, ya fasa mata baki sai jini yake yi. Da kyar aka iya kama shi, sai huci yake yi yana faɗin wlh sai ya kashesu kamar shi ya kawosu duniya. Haka matasa suka jashi izuwa waje, jin yana ambatar sai ya yi kisan kai ne yasa matasan basu yi ƙasa a gwiwa wajen miƙashi ga hukuma ba, dan kar ya jajumo masu masifa irin na sati bakwai da suka wuce da mmn Zee ta kashe bbn Zainab, ranar sun ga tashin hankali a unguwar, so gudun kada Haidar ɗin ya kara jajuɓo masu wata bala'in yasa suka wuce station kai tsaye da shi......

_________________________🔥

A bakin kofar gida mai mashin da Zainab ta tara ya kawota.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 3/10/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

💘STEP TWO....✍️📚🔥

E_______15

A bakin kofar gida mai mashin da Zainab ta tara ya kawota.

Sauƙa ta yi tare da kayan nata, nan fa ta tsaya shiru tana tunanin waye zai bata kuɗi ta biyasa hakkinsa? Ita dai tasan bata da ko sisi, sannan mamarta bata gidan bare ta yi tunanin shiga ciki ta karɓa, to ya zata yi kenan?.

Ta jima a tsaye a wajen tana tunane tunane har sai da mai mashin ɗin ya ce mata. "Malama sallame ni in tafi". Dogon numfashi ta ja tare da sauƙewa a hankali. Murya a sanyaye ta furta. "Ka yi hakuri bawan Allah, wlh bani da ko naira biyar, dan Allah ka yafe mun kuɗin".

Ɗago idanu ya yi ya kalleta da kyau, sannan ya mayar da kallonsa kan gidan nasu, ɗan taɓe baki ya yi, ko ba'a gaya mashi ba ya gane Zainab ƴar matar da ya ɗauka zuwa bayan gari wajen boka ne ranar, dan har yau kamannin maman zainab ɗin yana face ɗinsa ya kasa mancewa da ita, dan abin da ya jiyo da kunnuwansa a gidan bokan ya tsaya mashi a rai, sannan yasan a unguwar nan ya ɗauki mamarta ya kuma kaita ya dawo da ita, dan haka a cikin zuciyarsa ya furta. "Tun da uwarki tana da kuɗin zuwa wajen boka to wlh ba zan yafe kuɗina ba sai an biyani, dama ku mutanen arziki ne sai na iya yafe maki".

"Ke malama bani kuÉ—ina kawai, ni ba wai na fito dan na É—auki mutane irinku na kuma yafe masu kuÉ—i bane, nema na fito yi! Dan haka biyani hakkina kawai na wuce".

Shiru ta yi tana tunanin ya zata yi ta biya wannan bawan Allah. Tsawa ya daka mata a kan ta bashi kuÉ—insa shi yana son ya tafi.

Narai narai ta yi mashi da idanu, babanta ne kawai ya faɗo mata a ranta, da yanzu yana nan waye ya isa ya yi mata walaƙanci irin haka, da yanzu yana raye ai ko mashin ɗin haya ma ba zata hau ba bare har ta rasa kuɗin biya, baiwar Allah tasan gayyar shaiɗanu ne kawai a cikin gidan nasu, ko ta shiga ma babu wanda zai ɗaga idanu ya kalleta bare har ya taimaka mata da ko sisi.

Can kuma tunanin maman Hanif ya faÉ—o mata, nan take ta fara addu'ar Allah yasa maman Hanif É—in tana gidan nasu, tasan ita ce kawai zata iya taimaka mata, a lokacin kuma mai mashin É—in ya fara surfa mata ruwan balai a kan lallai ta bashi kuÉ—insa.

"Kayi hakuri malam, bari na shiga cikin gida na karɓo maka kuɗin". Da kyar ta iya idasa maganar saboda tsananin nauyi da tongue ɗinta ya yi mata, maganar tata ma bata fita sosai saboda wahala, ga bakin nata babu ɗanɗano ɗaci rok kamar shuwaka.

"Wlh ba zai yiwu ba, babu in da zaki shiga, a nan zaki bani kuÉ—ina, salon ki shiga ki gudu ki barni, wlh ba zai yiwu ba, kawai fito da kuÉ—i ki bani kayana hakkina".

Wasu zafafan hawayene suka cika mata idanu a in da suka fara ganganrowa da ƙaɗan da kaɗan.

"Ke ko kukan jini zaki yi yau sai kin bani haƙƙina, ai ba irinku musrikai mutanen banza ake yafewa kuɗi ba!!"

Jin ya dangantasu da musrikai ne yasa ta ɗago da idanu cikin sauri ta wani wurga mashi wani irin kallo wanda yasa sai da ya haɗiyi yawu ba shiri, dama fa kun san ita Zainab ruwa ne ya daki babban zakara, badan haka ba mafaɗaciyace number ɗaya, dan haka ranta a ɓace dama ga ciwo ga bakinciki tana neman in da zata amayar da bakincikin dake cikinta ko abu zai ragu mata. Cikin fusata ta ce. "Musrikai kuma mutanen banza? Su waye kenan?". Ta yi maganar tana goge hawayen dake fita daga idanunta.

"Gaku kuwa, wlh tun da kuna da kuÉ—in zuwa wajen boka sai an biyani hakkina makiya Allah da Manzonsa kawai".
Chapter 41 · 0% Book details