← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 181 OF 211

Sashe 181

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru ya zauna yana tunanin ina ta yi? Yana son zuwa ya dubata yana kuma jin kunyar shiga É—akin bappa tambayar ina take, yasan bazata wuce tana can ba. Addu'a ya yi Allah ya kawo dalilin da zai sa ta shigo cikin É—akin domin É—aukar wani abin ya kamata.

Aikuwa bai gama rufe baki ba sai gata ta shigo jikinta sanye da hijabi, daga wajen dabbobinsu ta fito, ta je tatsan nono ne suka tsaya hira ita Jumma da ta fito samo kara da itace zata hura wuta.

Sai faɗa Jumma take yi mata a kan fitowar da ta yi da sassafe, ta yi mata faɗa sosai ta ce maza ta koma, baiwar Allah ba ƙaramin daɗi ta ji ba da Mahnoor ɗin ta gaya mata Jaish ya hanata yi wa Nenne aiki, ta tayata murna matuƙa har take kara gaya mata cewa ba ga shi nan yanzu taga banbancin Jaish da Faisal ɗin ba, ai da Faisal aura bai isa ya hanata yi wa Nenne aiki ba, ƙaramin aikin Nenne ne ma ta haɗata ita da Faisal ɗin dik ta zaga, ko ta kamata a gaban Faisal ɗin ta yi mata duka bai isa ya yi magana ba, dan gwaggonsa ce Nenne, amma shi Jaish ai bata isa ba, dan haka ta kara riƙe mijinta da kyau in ba haka ba ta koma cikin azabtarwar Nenne.

Ta ji daÉ—i shawarin Jumma sosai a wannan karon, dan ta ankarar da ita abin da bata ankara da shi ba wato gaya mata da ta yi idan Faisal ta aura ba zai hana Nenne azabtar da ita ba, amma Jaish kuwa bata isa ba, hakan yasa ta ji wlh bari ta koma ta kula da mijinta sosai, yanzu ta yarda zata daina son Hamma Faisal, kuruci dangin hauka, yaro dai yanzu zaka yi mashi dabara ka juya shi ta yadda kake so, ji fa kalma É—aya tasa wai ta dai'na son Faisal, sai kace soyayyar wasa ce, dama can bata san me ake cewa son soyayya da son Æ´an uwantaka ba, ita dai tana son Hamma Faisal kawai.

Ba ƙaramin daɗi ya ji ba na ganinta ta shigo cikin ɗakin, sai dai kuma wani irin kunyarta ne ta lulluɓesa na tuna abin da ya faru a dare jiya da ya yi, sai ya ji ba zai iya haɗa idanu da ita ba, ya yi ƙasa da kai yana faɗin. "Ina kika je da sassafen nan?".

Ita ma kanta a ƙasa, kunya kamar ta juya ta fice daga cikin ɗakin, amma ba dama, tana son kashe shi da soyayya kamar yadda Jumma ta gaya mata, wato Jumma fa ƴar air ce, ce mata ta yi ta je ta kashe shi da soyayya da sanyin safiyar nan, shi ne ta zo aikatawa..............😅

"Waje na je?". Ta faÉ—a a sanyaye.

"Kin tamnayeni ne?". Ya jefa mata tambayar ba tare ya kalli in da take ba.

Kai ta girgiza mashi alamar a'a tana amsawa da a'a É—in.

"Bana ce kada ki sake yin abu ba tare da kin tambayeni ba?".

"Ka faÉ—a, ka yi hakuri ba zan sake ba". Kamar zata yi kuka ta yi maganar.

ÆŠago kai ya yi da nufin ya sace kallonta, sai kuma aka yi dace ita ma ta É—ago dan ta saci kallonsa, ai kuwa suka yi ido huÉ—u, da sauri ta kawar da nata kallon shi kuma ya cigaba da kallonta.

"Zoki kwanta". Ya faÉ—a yana gyarawa shi ma ya kwanta. Wani irin daÉ—i ne ta ji ya kamata, da yanzu fa zata tafi cikin sanyin nan ta kama yi wa Nenne aiki, amma Allah ya kawo mata sauki, yau waye zai yi wa Nenne aiki? Idan bata fito da kanta ta yi ba asirinta zai tonu wajen bappa cewa dama ba ita take yin aikin ba kullum.

Cike da farinciki ta nufi mattress ɗin, can gefe ta kwanta tana tunanin yadda zata yi ta kashe shi da soyayya da safiyar nan. Shi kuwa da yake ya ji daɗin kwanciya a jikinsa da ta yi jiya, ya ji daɗin da bai taɓa jin irinsa ba har da makara sallar asuba, sai ya juyo gareta.

Abin dariya a miliyan ta datse idanunta, shi fa take ta kallo da ya bata baya, amma yana juyowa ta wani datse idanu.

Shiru ya zuba mata idanu yana tunanin ta yadda zai yi ta dawo jikinsa, ita ma tunanin hakan take yi, dan ta ji matukar daÉ—in kwanciya a jikinsa da ta yi jiya.

Sai dai kuma ba zai iya ce mata ta zo garesa ba, yana jin kunyar yin hakan, addu'a yake yi Allah ya kawo mashi dalilin da zai sa ta dawo jikinsa ta kwanta, ita ma addu'a take yi Allah yasa ya ce ta zo garesa ta kwanta.

Ita dai Mahreen hankalinta a kwance tana É—akin bappanta tana barci, shi kuma bappa yana É—akin Nenne suna diramar da suka saba, ya baro Mahreen tana zuba barci.

Kasa hakura shi fa ya yi, a hankali ya nufi saman wuyarta da hannunta dake ta faman kerma, ta datse idanu gam tana tunanin yadda ta ti barci cikin farinciki a daren jiya.

Ɗan taɓa wuyarta ya yi tammar bai jin tsoronta. Wani irin ajiyar zuciya da suka sauke a tare ne yasa ya fahimci ita ma tana kewar jikinsa, dan haka sai ya matso kusa da ita tare da sanya hannunsa dikka biyu ya janyota jikinsa.

My people's ba zan bari kuga irin farincikin da suka shiga yau ba🤸 sai gobe idan mai dukka ya kaimu zaku gani 🤪 idan kun ji haushi kuzo na baku Maltina mai sanyin sanyaya zuciya ku kora zuciya ta ɗan yi sanyi🌝😅🤸

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️ 🕊️

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

46

JIMETA

A ɓangaren Nenne kuwa sam bata yi zaton Mahnoor ba zata fito ta yi mata aiki ba, hakan yasa ta koma ta yi kwanciyar kamar yadda ta saba. Sai dai kuma sam bata ji motsin kowa a tsakar gidan ba, hakan ba ƙaramin damunta ya yi ba, ya kuma ɗaga hankalinta sosai, dan ita fa ba iya jure aikin da Mahnoor take yi zata yi na.

Hmmm rayuwa kenan ita ma da take uwa ba iya jure aikin Mahnoor da take yi zata yi ba, amma saboda tsabar mugunta take sakata yi, har ma ta kara mata da wasu miscellaneous, minus aiki da baya a cikin lissafi, Allah dai ya kyauta ya rabamu da sharrin zuciya yasa mufi karfinta.

Har around karfe 7 bata ji motsin kowa a waje ba, hakan ya bata tabbacin Mahnoor bata fito ba, cike da tashin hankali ta miƙe ta nufo wajen dan ta tabbatarwa da kanta shin da gaske ne ko dai kunnuwanta ne basu jiyo mata da kyau ba!.

Bappa bawan Allah shi kuwa tuni ya fice ya tafi gidansu Faisal duba jikinsa, a yanzu ya fara samun sauki har yana É—an fita, sai dai kuma fushi yake yi da bappan, ko bappa ya yi mashi magana baya amsawa, akwai zuciya ne sosai, ya zuciya ya yi fushi. Amma dik da haka baya hana bappa zuwa duba shi, saboda yasan cewa shi ne ya zama silar rashin lafiyarsa.

Ba karamar girgiza ta yi ba a lokacin da ta fito taga tsakar gidan kamar yadda suka barshi a daren jiya, baa kawar da komai ba, ya tabbata dai Mahnoor bata fito ba, ta jefawa kanta wannan tambayar.

Tattare tsakar gidan ta fara yi tana wani uban ɗaure fuska tamkar wadda aka aikowa da saƙon mutuwa. Haɗa kwanikan wanke wanke ta yi ta kaisu mawanki, ta dawo ta shiga ɗakin bappa domin ta taso Mahreen ta zo ta yi mata koda wanke wanke ne, dan ba iya yin aikin nan gabaɗaya zata yi ita kaɗai ba.

Tana son shiga É—akin Mahnoor É—in ta dubata ko Jaish ya fita ita kaÉ—ai ce a ciki take barci sai ta tasota ta zo ta yi mata aiki, amma kuma tana bala'in tsoron ace yana nan su yi arba, ai da ta shiga uku.

Kiran sunan Mahreen É—in ta fara yi a kan ta tashi, amma ina Mahreen sarkin barci kin tashi ta yi, sai ma sa ta matsa mata ta saka mata kuka cikin magagin barci ta fara faÉ—in. "Wai Nenne kekam meyasa baki son ganin mutane suna jin daÉ—in duniyarsu ne? Ni wlh ba zan iya tashi yanzu ba".

"Tashi zaki yi ki je ki mun wanke wanke". Nenne ta faÉ—a.

Turo bakin nan ta yi, cikin tsiwa da magagin barci ta ce. "Nenne ni kuma? Gaskiya ni ban iya ba, ina Adda Mahnoor? Ba ita ce take yi maki kullum ba?".

"Yau ba ita zata yi ba, ni zan yi aikin, dan haka ki taso mu je ki tayani!". Ta faɗa cikin tsiwa da ɗaga murya ita ma, da alama ranta ya fara ɓaci.

"Nenne ita Adda Mahnoor fa bata tashina na tayata aiki, dikka aikin ita kaÉ—ai take yin abinta, kema ki je ki yi aikinki keÉ—ai ni dan ban iya ba". Tana kai karshen maganar ta juya mata baya dan ta cigaba da yin barcinta.

Ranta ne ya kara ɓaci, sai yau ta yi nadamar hana Mahreen ɗin da take yi ta taya Mahnoor aiki, ai ga shi nan yanzu ko wanke wanke bata iya ba bare ta fara taimaka mata, Allah sarki baiwar Allah Mahnoor dikka aikin ita kaɗai take yi har ta dafa masu abin da zasu ci da safe, dik kuma kafin karfe 8 ta gama komai, baiwar Allah tun karfe 5 idan ta yi sallah take fitowa ta hau yin aiki kamar wata jaka maras gata wanda ba'a so.
Chapter 181 · 0% Book details