Sashe 154
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sauko da kallonsa a kanta ya yi, can ƙasar maƙoshi ya furta. "Yau kece da tsoron ruwa? Kin manta a rafi kike wanke mana kayanmu ne?".
Ita dai ta kasa yarda da cewa shi yake magana, dan bata taɓa jin murya mai zaki da daɗin nasa ba, ni kam na ce dan ma baki ji muryan Guyson nawa ba, ai da kin ruɗe saboda daɗi.
Kasa haƙura ta yi har sai da tamkar zata yi kuka ta ce. "Hamma da gaske kai ne kake yin magana?".
Yadda ta yi maganar ba ƙaramin burgesa ta yi ba.
"Kina tantama ne?".
Kai kawai ta iya gyaɗa mashi alamar e, ta ƙasa sake yin magana.
Shiru ya yi bai sake magana ba shi ma, yayyafin da ya kara tsananta ne yasa ya cigaba da tafiya da ita, ya mayar da kallonsa a kan in da yake takawa.
Tun da ya cigaba da tafiya idanunta suke a kansa, ta dai rasa ya zata yi da mamakin da yake son kasheta. Wasa ruwan saman ya rinƙa yi kamar zai zubo kamar kuma ba zai zuba ba, har suka ƙarisa hayewa sama gabaɗaya, around karfe 11 na dare suka isa.
A ƙasan wani katan dutse mai cike da zane zanen sunaye da larabci haɗe da abubuwan hannu ya sauketa, idan amarya da ango suka hau wannan dutse suna iya kaiwa karfe 2 kafin su isa sama, saboda su tafi kaɗan su hutu su tafi kaɗan su huta, amma shi kunga ai bai wani ɓata lokaci wajen tsayawa hutu ba, shi ne yasa suka isa da wuri.
Tun da ya zaunar da ita take ta aikin bin shi da kallo, shi kuma ya juya ya bata baya a in da yake kallon ƙasa yana hango garuruwa da ƙauyuka, waje ya yi clean daga saman, shiru ya tsaya yana jin kansa tana ɗan jujjuya mashi tamkar mai san tuna wani abin, yana dai ji kamar ba shi ba.
Miƙewa tsaye ta yi, wani ɗan ƙaramin karfe ta hango a jikin dutsen wanda kamar ɗan keji aka yisa, dama Inna Rabi ta yi mata bayanin abin da zasu yi idan suka haura saman, wanna ɗan kejin ta nufa, tun iyaye da kakanni aka buga shi a saman dan ajiyar kifiyar da suke rubutu a ciki.
Jin motsin ta miƙe yasa ya saci kallonta ta wutsiyar idanunsa. A hankali ta tattaka ta je ta buɗe ɗan kejin, kifiyar ta ɗauko ta dawo wajen dutsen, yana ta kallonta shi dai yana jiran ya ga me zata yi.
Ita ma satar kallonsa take yi, da yake ita take riƙe masu da light ɗin sai hakan yasa bai gane tana satar kallonsa ba.
Jikin dutsen ta sanya kifiyar, yana da tsinin baki sosai, karfinta tasa ta zana design of heart a É—an karkace saboda rashin sabo, hannunta na rawa.
Juyowa ya yi da kyau dan ya kalli me zata yi, sai a lokacin kuma ya lura da sunayen mutane dayawa a jikin dutsen, an zanasu ta yadda ruwa ba zai wankesu ba, ba zasu taɓa gogewa ba har abada, sai yanzu ya gane wato dik amarya da angon da suka zo sai sun rubuta sunansu da yadda suka iya, in ma da arabic or da boko, su killace shi a cikin design of heart.
Ita fa bata ma san menene ma'anar design of heart É—in ba, kawai taga dik waÉ—an da suka rubuta sunansu a cikin irin design É—in suka rubuta ne yasa ita ma ta zana design É—in.
Da karfi ta fara zanen sunansa wato Hamma a sama, ta rubuta sunanta Mahnoor kuma a ƙasan nasa sunan, tana yi tana kallon design da mutane suka yiyyi tana kofa, da larabci ta yi masu zanen sunayen nasu, bata iya karatun boko ba, amma ta iya Arabic sosai.
Bayan ta gama sai ta kallah a sauran zanen sunayen dake wajen ai an sake zana karamin heart a tsakiyan sunan ango da amaryar, dan haka ita ma sai ta sake zana masu heart ɗin kamar yadda ta gani, sai Allah kaɗai yasan waye ya fara zana wannan design ɗin da kowa ya zo sai ya kofa, abin ya ƙayatar sosai.
Shiru ta yi tana kallon zanen nata ta kuma kalli na mutanen dake wajen dan ta kara dubawa shin ta yi dai'dai ko da sauran gyara?. A ƙaida angon ne zai zana sunayen, amma ita tana ganin kamar ko ta ce ya yi ba zai yi bane yasa ta yi da kanta.
Tana tsaka da ganin zanen kamar daga sama ta ji shi a bayanta, a hanzarce ta yi yunƙurin juyawa dan ta ga shi ɗin ne? Ko ba shi bane?.
Bata kai ga juyawa ba sai taga hannunsa ya sauka a saman nata da take riƙe da kifiyar, riƙo kifiyar ya yi haɗe da hannun nata ya mayar jikin zanen.
Dogon mashin kauna ya zana a tsakiyar sunayen nasu har ya ɗan fi heart ɗin tsawo, kamar yasan haka ake zanawa, a dai dikka al'adun nan nasu sai da ya kawo masu sabon salo, dik cikin zanen da jama'a suka yi a wajen babu mai zanen mashin kauna sai nasu da ya wani zana masu, kuma abin ya yi matuƙar kyau da ɗaukar hankali sosai.
Zaro idanu ta yi tana kallon yadda abin ya yi mugun kyau ba kaɗan ba, a hankali ta ɗago kai ta kallesa. Ita yake kallo shi ma, hakan yasa idanunsu suka sarƙafe cikin na juna.............. Wasa wasa fa wato Jaish ma taƙadari ne.😂
10 mins suka ɗauka a wajen a haka, sannan ya sanya hannunsa ɗaya ya juyo da ita garesa, har lokacin ɗayan hannunsa na saman nata dake riƙe da kifiyar.
Ƙasa ta yi da kai kamar mai ɗaukar darasi a islamiyar Inna Rabi.
"Muje ko?". Can ƙasan maƙoshinsa ya furta hakan, daga jin yanayin muryarsa akwai alamar tanbaya, dan ta sauya......... Ni ko nace shi soyayya da sha'awa ina ruwansa da baka cikin hayyacinka? Sai dai idan bata taso ba, cap zai capkeka ba ruwansa, to gara ma ka sani ato!!...
Kai ta gyaÉ—a mashi alamar e. Rage tsawonsa ya yi ya É—auketa cak, kai tsaye wajen ajiye kifiyar ya nufa da ita, yana É—auke da ita ta buÉ—e É—an kejin ta mayar da kifiyar ta rufe.
Saƙalo wuyarsa da hannunta ɗaya ta yi tare da kwantar da kanta a saman kirjinsa, har lokacin ana yin ɗan yafyaf na ruwan sama.
"Hamma naga kai baka huta ba, ko zamafa baka yi ba". A raunace ta yi maganar, baiwar Allah ta damu sosai, sai take ganin kamar tana gajiyar da shi, bata san cewa shi É—in jinin Modarawa jinin Akka bane, jarumta a jininsu yake.
Hannunsa É—aya yasa ya É—an shafi face É—inta kaÉ—an ba tare da ya furta uppan ba, alama dai ya yi mata a kan kada ta damu sam bai gaji ba.
Cigaba da gangarowa suka yi, a hankali yake tafiya gudun kada su gangara su faɗi, saboda gangarace sosai. Akwai lokacin da wani ango ya yi ganganci wajen gangarar nan, ai a dubu ɗari ya gangaro kasa, bai tsaya ko'ina ba sai a kusan karshen garin ya afka cikin wani rami, badan wannan ramin bama ina ga sai ya fita garin saboda gudu, tuni ya yi wurgi da amaryar tasa ya rinƙa gudu kamar wanda birkinsa ta tsinke, sai da ya kai wata yana jinyar jikinsa, dan ma Allah yasa jama'a sun biyo bayansa da gudu, hakan yasa yana faɗawa cikin ramin aka yi maza aka cirosa, badan haka ba ai da sai dai wani ba shi ba, so sai da kulawa wajen wannan gangara.
(Tab wayaga Jaish yaro ɗan Mommarsa an samu akasi ya gangaro a miliyan? Birkinsa ta tsinke bata kamuwa, ai ina ga daga nan har ƙasar Tunisia zai tsaya, sai Akka ta taresa😂 ba ruwana kada kuce ni na faɗa.)
Sai da suka kai kusan sauƙa da misalin karfe 2:30, sannan ne ruwan saman ta kece kamar da bakin kwarya, hakan yasa ya ɗan ƙara saurin tafiyar tasa, ita kuma ta ƙanƙameshi sosai tare da kwantar da kanta ta ɗan saman kirjin nasa.
Su Mahreen kuwa har wajaje shabiyu da rabi tukun nan suka dai'na rawa, wannan ma sai da bappa da ya dawo wajen ne ya tsawatar masu a kan su kashe mpn nasu dare ta yi sosai, ba dan haka ba da kwana zasu yi suna yi, bappa misalin karfe 10 ya dawo wajen domin yana son su Mahnoor su sauƙo a gaban idanunsa ya tabbatar da babu abin da ya sameta, shiyasa ya dawo.
Gari ya yi shiru sai tashin hiran jama'ar dake wajen bikin kawai zaka ji, sai hira suke yi kamar ba dare ba, sai da aka fara ruwan sama ne suka shige cikin runfunar nasu suka tsaya tsit suna ganin zubar ruwa.
Tun da ruwan nan ya fara a kansu ya fara, ga shi zuba yake tamkar da bakin kwarya, ga iska mai karfi, ta manne da jikinsa tana jin wani irin sanyi na ratsata, ga sanyin fitowar alfijir ya keto, sai ya haÉ—e masu.
Around karfe 4 daidai suka sauko daga ƙasa saman, sun jiƙe sharkaf da ruwa, har lokacin kuma ruwan ake zubawa kamar me.
Tun da aka fara ruwan Mahreen ta fara yi wa bappa kuka a kan ruwa zai jiƙa mata ƴar uwa da kuma Hammanta, shi kansa bappan ya shiga damuwa, sai dai ya danne ya rinƙa rarrashinta, da kyar ya samu ta yi shiru.
Idan ran Jaish ya kai dubu a wannan lokacin to ya ɓaci, a ransa yake faɗi ko uban waye ya kafa waɗan nan al'adu to lokacin rusheta ya yi, bai ga uban da zai sake yin wannan al'adar a wannan kauye ba idan har yana nan, wannan ai sai su kashe ƴaƴan nasu da hannunsu, dan kuwa ba kowa ne zai iya hawa wannan dutse ba, musamman waje saukowa ba karamar kasada ake ɗauka ba, idan ka yi wargi kaɗan wajen saukowa to faɗowa zaka yi ko ka gangaro a miliyan ka yi gudun wuce ƙaidar ɗan adam.