← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 211

Sashe 121

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da daddy ya ratse masu ba leƙen asiri jami'an suka je yi ba, da yake suna matsayin kawaye sai ta hakura zata basu su, amma mugun munafurtar juna fa suke yi, dukkansu suna yi wa junansu kallon wawaye, a duniya idan kana raye babu abin da ba zaka gani ba wlh. Smart dai da daddynsa sun zama ƴan duniya, wato sun iya siyasa ne na bugawa a jarida, yanzu sai su saka mutum a kwana.

Sai da ya tabbatar antafi da jami'an cikin aminci, sannan ya kwashi boma boman da ya cire masu bayan ya kashe É—in ya nufi eagle É—insa.

Office nasa ya koma, a can ya ajiye boma boman a kan idan ya samu time zai dubasu, daga haka ya wuce gida, dan mom taki barinsa ya huta, sai kira take ta danna mashi babu kakkautawa.

Ni dai securitys dake tsaron gidan nan nasu suna ɗaga mun hankali har bana son zuwa ɗauko maku labarai, waɗan nan ganinsu kawai ya isa ya sanya mutum sakin fitsari a wando, dan ma dai na riƙi Allah ina da kwarin zuciya ne, kuna ganinsu wasu jiga jigan turawa, sai dai kyawawa ne kuma duk da fuskokinsu babu alamar annuri bare imani, ga su ta ko'ina tun daga farko titin ketowa unguwar har izuwa cikin gidansu, ai kunsan yadda gidan shugaban ƙasa yake, ba'a wasa da tsaro!!.

Yana shigowa main parlourn ƙasa wani irin ɗaure fuska na musamman ya yi, ya cunkushe rai dan kawai ya ga baƙi a gidan nasu.

Ko kallon in da suke bai yi ba bare su sa ran zai ce masu sannu, kai tsaye ya nufi elevator domin ya wuce room É—insa.

Da sauri mom ta miƙe tana faɗin. "Baby come here".

Wani irin kallo ya wurga mata, irin kallon nan na mom kin fara ko. Mayar mashi da makamancin irin kallon ta yi na e É—in na fara maza zo nan. Abin gwanin birgewa da ban dariya.

Tsayuwa ya yi kusa da elevator ba tare da ya ƙarisa in da take ɗin ba, ƙarisowa gabansa ta yi tana faɗin. "Baby don't you see ur uncle? Come and greet them".

"Mom i have a lot to do now, you just go and greet them for me". Ya yi magana ba tare da ya kalli in da suke ba, yana kai karshen maganar ya haura sama. Haushinsu yake ji dan ba yadda dad ɗinsa bai yi da su a kan su musulunta ba sunki, a haka kuma suke son haɗa alaƙa da shi, tab lallai kuwa!.

Bin bayansa izuwa saman ta yi, already har ya shige toilet dan yin wanka, a gefen bed ɗinsa ta zauna dan ta jirasa, ita kanta kirjinta bugawa yake yi da sauri sauri, tana jin tsoron bayyana mashi maganar da ta zo da shi, tasan ba wanda ya tsana biyun Heleena a gidan, baya son ganinta sam, tana fargabar yadda zasu kwashe da shi, ita ma kenan da yake matuƙar kauna yake kuma jin maganarta, ina ga ace uncle ɗin nasa ne zai yi mashi maganar, me kuke tunanin zai faru?.

After 40 mins

Bathrobe ce a jikinsa fara tas ya fito daga toilet É—in, da yake tsakanin in da bed É—insa take da toilet É—in akwai nisa saboda girman bedroom É—in, sai bai san tana cikin É—akin ba, ya yi zaton tana parlourn, duk da ta san password na buÉ—e kofar room É—in nasa dan ba iya fingerprint bane kawai da kofar, zaka iya buÉ—ewa da password ma, duk da yasan tasan password É—in bai yi tunanin zata biyo bayan shi ba.

Dressing room ya shiga daga toilet É—in, girman room É—in nan ba'a magana, gabaÉ—aya show glasses, transferred glasses su ne cike a ciki, kowani irin kaya da glass wardrobe É—insa, daga waje kana iya ganin duk wasu kayan da suke ciki kowanne, ba sai ka sha wahalar neman in da ma'ajiyinsu take ba, part na set É—in takalma daba, abubuwa dai sai wanda ya gani.

Shiri ya yi cikin denim short mai bala'in tsada, and white single, da alama kwanciya zai yi. Ya zuba wani haÉ—aÉ—É—en perfume É—insa mai kamshin kwantar da hankali a jikinsa.

Cikin room É—in ya nufa bayan ya kammala shirin nasa. He was so surprised ganinta da ya yi a zaune a bakin bed É—in.

ÆŠan kara cukule fuska ya yi, dan yasan takura mashi kawai ta zo yi.

Ganin ya kara cukulewa yasa ta saki murmushi tana binsa da kallo from down to up.

Haye gadon ya yi da nufin ya kwanta, cikin sanyin murya ya ce. "Mom what are you doing here again?". Ya yi maganar yana sauke kansa a saman lallausan pillownsa.

Juyowa ta yi garesa da kyau, cikin sigar rarrashi da lallaɓa mutum ta fara magana. "My baby please come and greet ur uncle and ur aunty, i will be happy if you do thet". A marairace ta kai karshen maganar.

Yana cigaba da cukule fuska ya ce. "Mom i want to sleep, because am feeling to much of sleeping, if they're here, they haven't left, by the time I wake up we should say hello". Yana kai karshen maganar yaja katuwar lallausan duv É—insa ya rufe harda face É—insa gabaÉ—aya dan ma tasan da gaske barcin yake ji....... Smart wato idan kun lura shi fa jan ajin nan kamar a jininsa take, komai sai ya ja aji a kanta kafin ya aikata kamar ba gobe.

Miƙewa tsaye ta yi, sam bata ji daɗin hakan ba, amma kuma farincikin ɗanta yafi mata komai, wannan barcin da ya ce yake ji to ya yi sa ya fi mata auren ma gabaɗaya, tana kaunarsa sosai.

Parlourn ta iskosu suna zaune, hakuri ta shiga basu tare da gaya masu cewa ai ya dawo a gajiye ne shiyasa, yanzu ma haka ya yi barci, su yi hakuri sai ya tashi.

Baban Heleenar ne ya nuna ɓacin ransa a kan hakan, ya ce dan Smart ɗin yaga Heleena tana haukar sonsa ne zai na yi wa mutane walaƙancin? To su wlh sun ma fasa ba zasu haɗa wannan aure ba.

Nan fa Heleena dake zaune tana cikin wani irin tantirin shiga nasu na turawa ta fara faɗin wlh baban nata bai isa ba, ita Smart take so, shi take son yin rayuwa da shi, dan haka dole su jirashi kuma su yi duk abin da yake so, bata son ma su ɓata mashi rai....... Idan kana raye dai babu abin da ba zaka gani ba, kuma su fa hakan a wajensu normal ne ƴa tasa iyayenta dole su nema mata soyayyar wadda take so, su kuma kaunar ƴaƴan nasu ne yake rufe masu idanu ya kaisu ga halaka.

Hakuri mom ta basu a in da ta ce musu shi fa Smart bai ma san Heleena tana son shi ba, infact bai ma san me ya kawosu gidan a yanzu ba, dan haka su bi a hankali, gaya mashi batun auren ma sai an bishi a hankali.

Taɓe baki baban Heleenar ya yi, yana mamakin irin son da suke yi wa ɗan nan nasu, shi baya laifi, komai ya yi daidai ne, ita kuwa mum Heleenar bata ji komai ba, ita burinta yarta ta samu abin da take muradi.

Haka suka yi ta zaman jiransa har barci ya É—auki mum Heleenar. Dad kuwa shi ne bai dawo ba sai can da yamma, shi ma a tare da manya manyan bakinsa ya dawo.

Mom ta sha mamakin ganinsa da baki, har ƙasa hakuri ta yi sai da ta tambayesa waɗan nan kuma daga ina? Taga mace da namiji masu kama ɗaya, kuma ga dukkan alamu dangin gidan sarauta ce, sarauta ma mai karfin iko duba da yanayin shigarsu, sun haɗu sosai, da alama maƙudan dukiya ta yi masu mubaya'a, domin kuwa sun jiƙu da dukiya ba kaɗan ba, shi namijin ma takalmar sarauta dake kafarsa ta zallar madarar gold ce.

Shi ma dad he was so surprised na ganin iyayen Heleena a gidan nasu, da izinin mom kenan suka iya ketowa cikin gidan, dan babu wanda ya isa ya keta arearsu ba tare da izinin É—aya daga cikinsu ba bare har ya iya shigowa cikin gidan, koda kuwa securitys É—in sun san kasan mutumin to fa dole sai ka sanar da su zai zo zasu bashi hanya bayan sun gama cajesa in and out tsab!.

Gaisawa suka yi cikin mutunci da mutunta juna, sannan ya wuce izuwa sama bayan ya damka amanar bakin da ya zo da su a hannun mom ta kula mashi dasu bari ya duba Smart sai ya yi wanka ya zo su tattauna.

Lokacin da ya shiga ɗakin ɗan nasa barci ya iskosa yake yi, har lokacin bai farka ba, a hankali ya lallaɓa kamar wani ɓarawo ya fito waje, wai duk dan kada ya tashesa daga barcin.

Nasa room É—in ya nufa, a nutse ya yi wanka, ya shirya cikin hoodie, kyakkyawa ne dad É—in nan fa sosai.

Ƙasa ya sauko, a lokacin already mom ta sa masu aiki sun tashi kan bakin dad da kayan abinci masu rai da lafiya, president food ma ta sa suka shirya masu, wato irin abincin da dad ɗin yake ci, na gaya maku mom mutuniyar kirkice mai zuciyar zinari, musulunta ne dai har yanzu taki yarda ta yi.

A rest parlourn suka haÉ—u dukkansu bayan bakin sun gama kwasan abinci daidai gwargwado.

A nan dad ya ce da bakin nasa su zo ayi magana, da yake ita ma mom tana son su yi magana da shi da iyayen Heleena sai ta ce duk su haÉ—u a rest parlourn kawai. A cikin bappan parlourn wannan rest parlourn yake, ya ji komai na more rayuwa, waje ne da suke yawan zama dan hutawa ko su tattauna abubuwa masu mahimmanci.

Saman sofa suka zazzauna, a nan dad ya gabatarwa da Mom bakin nasa, ya nuna namiji tare da ce mata shi ne Prince mai jiran gado na ƙasar England, macen kuma babar yayarsu ce, kara gaisawa suka yi cikin mutumci.

Ƙarawa dad ya yi da cewa. "Prince they came for the issue of their sister's marriage which they are asking for Smart to do, saying that the girl is determined that she want him to marry her or she will kills herself".
Chapter 121 · 0% Book details