← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 211

Sashe 149

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abubuwan amfanin gida irin nasu na kauye ya je sayawa Mahnoor ɗin kamar yadda yake a al'adance, har da su samiru dikka, ya saya masu katifa da dik abin da za'a buƙata.

Ko da ya dawo gidan Jaish baya nan, ya tafi yawonsa cikin kauye.
Cikin sabuwar bukkar da suka haÉ—a É—in ya shigar da kayan, Mahreen ta tashi barci a lokacin, ita ta taya shi aiki, Æ´an uwansa dik sun ki zuwa in da yake, saboda ya hana Faisal Mahnoor ya bawa wani, abin ku da kauye wai gaba suke yi da shi, da yake su basa raina abin yin gaba, ga basa manta gabar komai daren daÉ—ewa.

Shi ne yasa suka ki zuwa taya shi murnar auren, bawan Allah ko a jikinsa, a cikin zuciyarsa abin ta yi mashi zafi, amma a fuska sam bai nuna hakan ba.

Haka suka shirya komai tsab shi da Mahreen, Mahnoor tana barci. A daren ranar dai a É—akin bappa Jaish ya kwana kamar yadda suka saba, ita ma Mahnoor a É—akinsu ta kwana, dik da an haÉ—a masu É—akinsu bappa ya ce sai anyi biki an gama za'a kaita É—akin nata.

Washegari da safe suka tashi da shirin yin biki, sai hidima Mahreen take yi, tana ta up and down, shige da fice, ba zama busyn body, abin yi ya samu Addarta da Hamma aljaninta suna aure.

Bappa kuwa sai lallaɓa Jaish yake yi yana rarashinsa haɗe da rokonsa da ya yarda ya je wajen bikin nan ya kuma karɓi al'adunsu hannun bibbiyu. Ba dan ya so ba ya amince da hakan, sai dan yana matuƙar ganin girman bappan sosai, yana kuma jin kunyarsa!.

Kuɗi sosai da a kallah zasu kai 100k bappa ya damƙawa Inna Rabi da ta je cikin gari ta yi wa Mahnoor sayayyar kayan kwalliyar da za'ayi mata kwalliya a wajen bikin, da kuma kayan sakawa, sannan ta sayawa Jaish ɗin ma kayan sakawa da dai dik abin da ya dace.

Bawan Allahn nan shanunsa har guda uku ya sayar yau da safe dan ayi hidiman bikin nan cikin gata da birgewa. Kun san bappa fa yana yawace yawace, so ya É—an waye abinsa.

After some hours.

Bayan sun yi sallar la'asar, zaune take ita da Mahreen a cikin É—akinsu, sun yi wanka, ita Mahnoor tana shafa mai a fatarta, ita kuma Mahreen tana zabga powder a fuska kamar dai yadda ta saba.

Sallama aka yi masu a kofar É—akin nasu, kallon juna suka yi suna mamakin jin muryar Inna Rabi yau a gidansu, dan bata zuwa saboda masifar Nenne, kuma su sun mancema yau ake bikin.

Mahnoor ce ta danne mamakin nata tare da amsa mata sallamar, cikin É—akin ta shigo kai tsaye, sai kallonta suke yi har cikin ido, Mahreen ta zaci ma ta biyota ne har gida ta zaneta dan yau basu je islamiyyar ba, dan tasan ita É—in uwar yin laifi ce acewarta.

"Inna ina wuni". Cewar Mahnoor.

Fuskarta cike tab da fara'a ta amsa da. "Lafiya lou Noor".

Mahreen ma É—aga mata gaisuwa ta yi tana cigaba da labtaka powder dai.

"Mahreen a rage powder nan haka mana". Inna ta faÉ—a tana kallonta.

"Ai sai ki ƙarisar maku da shi a tashi ɗaya, ke baki san kaɗan kaɗan ake shafawa bane? In ma kika shafa dayawa ai ba zaki yi kyau ba". Ta kai karshen maganar tana maido da kallonta a kan Mahnoor.

Baki ta turo gaba. "Inna dandali fa zan je, bappa ya ce in je in same shi a can, kin ga kuma yau auren Adda Mahnoor É—ina za'ayi, dole na fi kowa kyau". Kamar zata yi kuka ta kai karshen maganar.

Sai a lokacin Mahnoor ta tuna ashe wai bikinta ake yi yau.

"Dik da haka a dai rage powder, idan kina son ki yi kyau ma ai kaÉ—an zaki saka, sai ki fi kyau haka".

To kawai ta amsa kumatu a kumbure, ita a dole bata ji daÉ—i ba za'a rage mata make up É—inta.

Dawo da kallonta a kan Mahnoor da ta takure waje guda Innar ta yi, ta wani haɗe jikinta waje guda, saboda daga ita sai ɗaurin kirji, mai take son ƙarisa shafawa ta sanya kaya, amma Inna tazo tasa ta jin kunya, sai ta kasa iya ƙarisa shafa mai ɗin ma, ta zauna shiru kanta a ƙasa.

"Mahnoor ki karisa shafa man mana, jiranki fa muke yi mu tafi". Cewar Innar.

To ta amsa kanta a ƙasa, ta kasa iya ɗagowa, tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta kai hannu ta ɗebo man ta cigaba da murzawa a jikinta kunya kamar ta shige cikin ƙasa, ita da kullum ba dare ba rana tana tare da hijabi a jikinta, yau kawai Inna ta zo ta sani kalleta da ɗaurin kirji, dik sai ta ji babu daɗi.

Ni kam na ce Jaish dai ya ji daÉ—i wlh, ya samu matar da bappanta ma rabonsa da ya kalli iya wuyarta ma tun da ta fara wayo, kullum cikin hijabi, ta killace jikinta, ko mata Æ´an uwanta bata yarda su gani ba bare maza, ko Mahreen bata samun ganinta babu hijabi, yau É—in ma ta wanke hijabin ne ta shanya yasa Inna ta shigo ta sameta a haka.

Ledar hannunta da ta shigo da shi Innar ta miƙa mata tana faɗin. "Karɓi wannan kaya ne da bappanki ya bani kuɗi a kan naje cikin gari na saya maki, ki sanyasu, akwai na Mahreen a ciki........".

Jin akwai na Mahreen a ciki yasa ta yi zafin namar kwace ledar daga hannun Innar, Mahnoor da ake miƙawa bata kai ga karɓa ba ta rigata, tuni ta miƙe tsaye tana sakin uban murmushi.

A hanzarce ta fito da kayan, blouse ne masu kyau, dogayen riguna ne, dikkansu kala uku uku ta saya masu, rigunar da gyalensu, kayan suna da kyau, sai dai kayan takaici Inna ta tashi ta je ta É—auko masu kaloli marasa kyau kamar mutun ya kurma ihu, wani irin yellow irin mai paw É—in nan, da kuma wani ja jaw haka, sai kuma ruwan omo ta É—auko masu, wai a haka tana gani ba kalar da ya kaisu kyau, ga shi iri É—aya ta saya masu, haka takalmar da ta saya masu É—in ma, yellow da baki, irin takalmar masu high kaÉ—an É—in nan, ba abin da ya fi bakanta mun rai ma kamar wannan yellow doguwar rigar, ga riga har riga amma kamar ka kurma ihu saboda rashin kyan kala.

A haka su kam suka rinƙa murna, wai kayan ya yi masu kyau, tuni Mahreen ta fito da wannan yellow ɗin ta zurmuƙa ga jikinta, da alama dama sun fi son abu paw mai haske haka.

Ai kuwa tana sanyawa sai ta zama kamar aljana albojel, dama ga uban powder da kwalli a fuska, idanun nan sun ji kwalli marau, abin sai wanda ya gani.

Wannan idan ka ganta da daddare ka yi gudu ne har da zawo a wando, dan ba abin da zai hana baka ce aljana bace, da alam yau Jaish ba zai ganeta ba, dik wannan kauna da shakuwa dake tsakaninsu ina ga yau sai ya gudu idan ya ganta.

Ita kanta Inna sai da ta ce. "Mahreen ki cire wannan riga ki saka É—aya mai kalar omon nan, ita ce zata fi dacewa da kwaliyar nan taki tun da tana da É—an duhu, ke kuma kwalliyar taki ta yi paw".

Inna tana son ta cire yellow ne ba dan komai ba sai dan ita kanta taga ya yi wani paw, ga fuskarta kamar jan ƙosai ya ji kayan alatun bature.

Aikuwa make kafaÉ—a ta yi. "Ni Inna wannan nake so gaskiya, yafi kyau da haskakawa".

Bata da zaɓin da ya wuce ta kyaleta, idan ba haka ba yanzu sai ta tsayar masu da iyashege da kukan banza, gara kawai ta rabu da ita taje a kamar aljanar sai ya fi mata.

Ita kuwa Mahnoor da ko ta kan Mahreen ɗin bata bi ba, dan tasan Mahreen dai ba canzawa zata yi ba. Miƙewa ta yi abinta ta ɗauki riga mai ruwan omon ta nufi bayan kofa, ɓuye ta yi ta sanya kayan, ba laifi sun yi mata kyau, dan ita bata yi pente penten komai a face ɗinta ba, hakan yasa kayan suka zauna mata dai'dai.

A takaice dai haka suka shirya, Inna ta yafa mata gyalen rigar a kanta, ta riƙo hannunta suka fito waje. Cincirindon mata ne sosai a wajen, dik makota da abokan arziki haɗe da kawayen mamanta, ƴan uwan Inna kakarta dik sun zo daukarta zuwa wajen taron, ƴan uwan bappanta ne kawai ko mutun ɗaya bai zo ba, sun ki zuwa dan an hana Faisal ita. Inna Rabi ita ce malama shiyasa aka ce ta shiga ta fito da ita.

A can wajen da za'ayi taran bikin kuwa, kasan wata katuwar dutsen dake kauyen ne, gabaÉ—aya an gama shirya komai, matasa da Æ´an'mata a cike ta ko'ina, ga dattawa da sa'anin juna, ta ko'ina mutane, an kafa runfuna manya manyan, sannan an shinfiÉ—a tabarmu manya a cikin runfar, runfar dattawa maza daban, runfar mata daban.

Biki fa gagaru suke shiryawa idan ma baku sani ba, dare suke ɓatawa suna shagali, kowa da irin al'adarsu a duniya, su kuma kunga irin nasu, kuma kowani al'ada ba wai suna yin shi ne dan nishaɗi kawai ba, a'a, kowanne da nufinsu a kansa. An ƙawata wajen sosai, harda kwalliya irin nasu dai na kauye suka yi wa wajen. Abin ya ƙayatar matuƙa.

Daga can gefe akwai wata rami babba a in da ake ta aikin hura wuta a cikinta, dama ramin saboda bukukuwansu suka tonasa, dan aji daÉ—in yin shagali da kyau ana cin nama.
Chapter 149 · 0% Book details